HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Gaba ɗayan su wani irin kuka suka sa yayin da shi kuma yake baza ido ko zai ga Suhaila itama ya mata sallama, amma ina be ganta ba, ita kuwa tana kallon shi itama tana nata kukan don ta gama yadda da son Ahmad take yi.

Fita yayi yayin da Kausar ta mara mishi baya, ita kuwa Ummi sama ta koma ta shiga ɗaki tana cigaba da kukan ta.

Cikin mota ya shiga inda Kausar da Zainab suke biye da shi.

Kallon Kausar yayi yace mata; “Suhaila, ki faɗa mata ina mata son mutuwa, kuma ni ba abunda take tunani bane”.

Yana gama faɗan haka ya tada motar ya kalle su na ƙarshe sannan ya fige ta a million ya fice daga gidan.

Ɗaki Kausar ta koma inda ta tarar da Suhaila a jikin window sai kuka take yi kamar ranta zai fita.

Dafa kafaɗar ta tayi tace; “Me yasa baki mai good bye ba, kika ɓoye a nan kina kukan da bashi da amfani tunda besan kinyi ba, he sai that he loves so much Suhaila, ya Ahmad yana miki wani irin so”.

Saurin ɗagowa tayi ta kalle ta tace; “Haka yace miki, ba wani nan bayan Zainab yake so bani ba nasan komai fa”.

“Go, go ki mai good bye na san halin shi, he will wait for you kafin ya tafi sai dai idan baki je ba ya tafi”.

Kallon Kausar ɗin ta ƙarayi, ita kuwa gyaɗa mata kai tayi alamar taje.

Mofula ta ɗauka ta naɗa a wuyan ta sannan ta saka coat akan abayar ta saka wani half cover shoe, ta zura da gudu tayi ƙasan gidan bata wani tsaya jira ba, ta fita a gidan tana waigen shi.

Ɗan tafiya ta fara tana yin gaba tana waigen inda zata ganshi amma ina ko alamun shi babu.

Sai dai tayi tafiyar kusan 20 minutes bata ganshi ba haka nan ta haƙura ta kama hanyar komawa gida.

Dai-dai wani bus stop ta zauna tana tuna rayuwar ta. Haka ta dinga zubar da ƙwalla tana dana sanin shigowa rayuwar wainnan bayin Allahn da suka ƙara rikita mata lamuran ta.

Maganar mutum taji kawai a kusa da ita.

“Kin damu dani har haka?”

Wani irin juyowa tayi ta zuba mishi idanun ta, sai kuma ta haɗe rai kamar ba ita ba.

“No, inason nace maka good bye ne kawai, amma bayan haka babu wani abu”.

Kallon ta yake yana jin wani irin abu yana taso mai nan da nan kuma yaji kanshi ya fara sara mai numfashin shi yana neman ɗaukewa.

Wani irin shiɗewa yayi wanda hakan ne yasa ta juyo ta kalle shi.

Da sauri ta miƙa hannun ta tana riƙe shi haɗe da tambayar shi meke faruwa.

Barin jikin ta yayi yana faɗin “Am… Am okay i wll be fine just go home”.

Tana kallon titi nan ta tsare taxi tana miƙa mai hannu yazo su tafi asibiti.

Wani murmushi ya mata yana kallon hannun nata.

Matso shi tayi tana kama hannun shi ya ƙwace.

Ƙara miƙa mai hannun tayi tace; “Ahmad kazo mu tafi please don Allah stop it”.

Kallon hannun yayi yace; “Idan har na kama hannun nan i will never let it go again”.

Gyaɗa mai kai tayi ba tare da ta sani ba, ta kama hannun shi ta saka shi a taxy ta tambaye ahi sunan hospital ɗin ya gayawa drivern.

*****

*_Tofa! Kunji abunda Ahmad yace, ko ni kaɗai naji, ku biyo ni don jin yadda wannan dramar zata ƙare_*

*_Asslama alaikum, faɗma Ahmad._*
[8/11, 9:11 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*wattpad@cynosure3*

*Page 6️⃣5️⃣to6️⃣6️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu’a Idan Abin Hawan Mutum Ya yi tuntube;*

بِسْمِ اللهِ،
bismillah.

Da Sunan Allah.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

_*The Therapist*_

Basu fi15 minutes ba suka isa bakin asibitin, babu wani ɓata lokaci ta janyo shi suka fito ta saƙala hannun ta a kafaɗar shi ta ɗora hannun ta akan ƙugun shi.

Ɗagowa yayi ya kalle ta ita kuwa bata san ma yana yi ba.

Direct ta shigar da shi tana neman doctor, wata nurse ce ta temake su ta kai su wani ɗaki nan doctor tazo ta duba shi.ɗan kallon Suhailan tayi tace; “Are you his wife?”

Haɗa ido suka yi ita da Ahmad ɗin, bata kawo tunanin komai ba tace ; “Yes mam”.

“Okay kizo office zamu yi magana da ke”. Ta faɗa cikin harshen turanci.

Kallon shi Suhaila tayi sannan suka wuce zuwa office ɗin ta suna shiga ta nuna mata mazauni ta zauna kafin ta cire glasses ɗin da ke maƙale a idon ta, ta fara magana cikin harshen turunci.

“Ammm mun duba shi ba wani serious ciwo bane yake damun shi sai depression, wanda yayi tsanani sosai, naga alamar har magani yana sha ma, amma kuma duk da haka kamar abun baya sauƙi, kuma hakan yana da nasaba da yawan tashin hankalin da yake shiga, don a yanzu haka yana tattare da low bf saboda yanayin da yake ciki, so a matsayin ki na matar shi kamata yayi ace kina ɗebe mai kewa duk abunda yake so kiyi mai, ko da yaushe ya zamto hakalin shi a kwance yake, saboda indai yana cikin tashin hankali bazai warke ba gaskiya, sannan kuma zai dena shan magani you will be the one ki dinga ɗebe mai kewa han, am i clear?”

Gyaɗa mata kai tayi hankalin ta na ƙara tashi.

“Now, zan haɗa ku da wata therapist, idan ya rage abunda ke cikin zuciyar shi zaiji sauƙi sosai, and za a baku appointment, zai dinga zuwa lokaci bayan lokaci yana ganin ta, kuma zai samu sauƙi sosai, na san tana off a aiki so zata iya ganin ku muje na kai ku gurin ta”.

Sa ke gyaɗa mata kai tayi tana bin bayan ta.

Ɗakin da yake suka koma, suka ɗauke shi inda yake bin su kamar raƙumi da akala saboda be san inda za a kaishi ba.

Wani guri suka shiga gurin tsit yake babu mutane da suke yawo sai dai masu wucewa kamar su, sai kuma daga cikin glass ɗin ƙofofin gurin suna hango mutane tare da different therapist suna ganawa.

A dai-dai office ɗin ta suka tsaya inda aka rubuta, *Laika*, room 5.

Tura ƙofar su kayi a hankali suka shiga inda suka fara gaisawa da doctor ɗin sannan ta mata bayanin matsalar su, tayi handling nasu sannan ta musu sallama ta fita.

Bayan ta fita ta nuna musu kujera two seater suka zauna su biyun, sannan ta sakko daga ainahin kujerar ta ta zauna a one seater da take kallon su.

Cikin sakin fuska ta ɗago ta fara musu magana.

“Hyyy am Laika from Philippine, i am a therapist how can i help you”.

Ɗan kallon ta Ahmad yayi itama ta kalle shi, sannan ta sauke wani deep breath ta fara magana cikin nutsuwa da harshen turanci”Sunana Suhaila, and my husband Ahmad”.

Ɗan shiru tayi saboda jin yadda maganar ta mata nauyi a baki, kallon ta yayi ya saki wani murmushi, harara ta galla mai sannan ta matsa kusa da kunnen shi tace ; “Am doing this just because you are sick, so, stop being excited, don ba canzawa zan yi ba i still hate you”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button