HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Yarinyar da tayi maganar na kalla bata fi Shekara biyu da rabi ba, wai amma ita ce take cewa a bata ɗumame yunwa take ji.

“Wayyo my princess am sorry, na tashi ina ta surutu ban ɗora miki ba, am sorry kin ji ko”.

Abba ne da yake fitowa daga ɗaki ya ce”Kai Fatima amma wannnan yarinyar taki da shegen surutu take, wai a bata ɗumame. To a ina ta san shi?

“Wallahi Abbu tun daga yaye baban ta ya saba mata da ta tashi daga bacci sai yace mu je in baki ɗumame kafin Umma ta tashi, shikenan fa ta riƙe shi a baki kamar me”.

“Lallai kuwa, Allah ya raya mana ku. Ina shi Walid ɗin yake?

” Hmm yana tare da Mubarak inajin may be ma sun tashi daga baccin sun fara buga game”.

“Game kuma da safiyar nan?

Suhaila ce tayi saurin leƙowa daga kitchen ta ce” Hmm dama nace zan faɗa maka wallahi har 12 yake kaiwa yana game. a kwashe kayan nan kawai a ɗakin shi Abbu. Sam Mubarak baya karatu saboda games ɗin nan”.

Ammi da ta fito daga ɗaki yanzu ta ce” A’a dai Suhaila banda sharri”.

“Wallahi Ammi da gaske nake a tambaye shi ma”.

“Hmm Allah ya kyauta” Cewar Abbu yana fita daga ɗakin”.

******

Habib kam 11:00 a gidan Surayya tayi mai, amma tunda ya je ya kasa ce mata komai sai kame kame yake yi, yayi tsuru tsuru da idanu kamar wanda aka ce yayi wa me gari ƙarya.

Sai da Surayya ta gaji kafin ta ce”Uncle Habib meye ne a bakin ka? Tun ɗazu sai juya magana kake a ranka amma ka kasa faɗa”.

“Uhmm kunyar ki nake ji ne, ina jin kunyar abunda zan tambaye ki ne yanzu”.

Wata bazawarar dariya Surayya tayi, har sai da tasa Habib ya fara jin haushi.

“Wai meye haka ne kike ta wani dariya? Kinga sai inyi tafiya ta wallahi”.

Cikin dariya tana sassauta wa tace”Am sorry Uncle Habib, wallahi kai ɗin ne ka bani dariya wai ni kake jin kunya. Inajin ka me kake son tambaya ta”.

“Sure zaki bani amsa dai dai?

” Me zai hana kuwa indai har na sani Uncle H”.

“Ammm ƙawar ki Suhaila……..

” Uhmmm ina jin ka, me tayi?

From no where be san daga inda maganar ta fito ba sai jin ta kawai yayi ya ce”Tana da saurayi ne? I mean is she engaged in a relationship?

“Why do you ask Uncle Habib?

” Ha’an.. Answer my question kafin kiyi mun tambaya mana”.

“No… She is not engaged in a relationship, and kuma bata da saurayi,me ya faru?

Straight, ba wani kwana kwana, ba wani jan aji, ba wani ƙumbiya ƙumbiya ya ce”i am in love…i think i like her Surayya”.

Mamaki kwance kan fuskar Surayya da kuma daɗin jin maganr ta fito daga bakin shi yasa ta ce”Uncle Habib da gaske kake ko wasa!!!

“Uhmm Surayya zan miki wasa da irin wannan abun ne”.

Tana zaune akan two seater couch bata san lokacin da ta dawo kusa da shi ta rungume shi ba.. Haɗe da cewa”Wooooo Uncle Habib you are the best! Ban taɓa tunanin abunda za ka tambaye ni ba kenan ko da ka fara maganar. Baka taɓa mun abunda naji daɗin shi sosai ba sai yau, wow gaskiya am proud of you Uncle “.

” Eyeeee haka ne? Haka kika ce? what about the ice-cream da na siya miki last birthday ɗin ki kafin kiyi aure?

“Umm ko shi be kai wannan ba gaskiya. Allah kuwa”.

“Lallai na yarda kinji daɗin wannan maganar”.

“To yanzu duk ba wannan ba, ya za ayi ki shigar dani? Don wallahi ta burge ni sosai da sosai”.

“Umm uncle Habib are you serious?? Ta faɗa in a charming way.

” Yesss now, why do you keep on asking questions ummm?

“Nothing, kawai dai nasan kana son ƴan mata ƴan gayu, ƴan chilling yanzu kuma naga ka dawo kan ustaziya, hijabyt niqabyt a pure Muslim sister”.

“Hmm dama wai’nan ai kawai na kare yawa ne, kar dai ka zauna haka kawai, amma ai nutsuwa ake ana neman matar aure, wa ya gaya miki ko wacce tom and jerry mutum zai je ya aura”.

“Kai uncle Habib, dama haka abun yake?

” Eh mana da ke baki sani”.

“Uhmm shiyasa ku maza kuka iya breaking heart ɗin mata kenan?

“What ever ni dai a shigar da ni kawai shi ne magana”.

“To kar ka damu indai Suhaila ce zan shawo maka kanta in sha Allah”.

“Wow you are my best daughter duk dangi shiyasa nake son ki wallahi”.

******
Da misalain ƙarfe 1 na rana Abban su Nihla ya kira su ya sanar musu cewar su shirya yau zai zo su koma gida kaduna.

Ai kuwa cikin minute kaɗa suka shirya,da misalin ƙarfe 2:00 suka ɗau hanya.

Suhaila tayi missing babies ɗin ta sosai, sai ta ji dama a bar mata su ko da na sati ɗaya ne amma ta san baban su bazai bari ba.

Bayan sun dawo daga rakiya tazo ta ga 2 missed call na Surayya.

“Ohhh Allah, na manta ban kira wannan yarinyar ba yanzu zata ishe ni da mita”.

“Assslama alaikumm, Sury how far naga missed call naki naje raka ya Fatima sun tafi gida yau”.

“Wa alaikum salam, dama cewa nayi bari naji kin tashi lafiya ya gajiyar jiya”.

“Gajiyar jiya kam Alhamdullilah tabi jiki”.

“Do you know what?

Surayya ta faɗa daga can ɓangaren daga ji kai kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa.

“Nop, bani nasha ƴar uwa me hanjin lagwani, daga ji abun zai yi onga don naji ki cikin farin ciki, ko mun samu Nu’aman ne??

” Hmm kedai bari, ai idan wannan ne ma duk da sauƙi”.

“You are getting married in sha Allah, and soon ƴan mata”.

Sai da Suhaila tayi jimm kafin ta ce”Yess Sury soon amma me ya faru ne?

“Ya Habib is in love with you friend, and kuma yace baya so abun ya daɗe kyanta ma kafin ya gama mu tafi service za ayi kawai a wuce gurin”.

Sai da ƙwalla ta cikawa Suhaila ido, ji tayi wani abu ya ƙulle mata maƙogaro, wato har daɗewar nata ya kai Surayya tayi tallanta ga Uncle ɗinta.

Cikin hosky voice ɗin ta tace”Surayya bana son irin wannan abun, nace miki am eager to get married ne!? That you are planning to match make me ummm? look Ina nan ina jira kuma na san in sha Allah soon Allah zai kawo mun mijin nan. Ke wallahi ko shekara 30 na kai a gida babu komai lokaci ne be yi ba na san idan lokaci yayi zanyi auren, idan kuma Allah be yi zan yi aure ba har na koma gare shi ko wani irin effort zaku sa wallahi bazan yi auren nan ba, so please let be patient, saboda ni bana son kiyi forcing ɗin shi nan gaba kuma azo ana samun matsala kinga hakan babu daɗi”.

“Look Suhaila! Bana son abunda kike mun wallahi, yanzu ko match making ɗin na miki sai me umm? Ko ban kai wannan matsayin a gurin ki ba? Kuma fa karki manta brother ɗin Hajiya ne ko me zanyi bazan taɓa iya bari naga kin wulaƙanta ba. But amma idan kinga you are not interested tau, amma ni bani na haɗa ku ba, shi da kanshi yazo har gida na yau da safe ya roƙe ni akan na miki magana”.

“Na bashi phone no.ɗin ki idan kin gadama karki ɗaga kiran shi kinji ko”.

Nan Surayya ta kashe wayar ta ranta a ɓace.

Suhaila sai bayan Surayyan ta katse wayar sannan ta fahimci abunda tayi mata sam be kamata ba.

Nan ta ɗaga wayar don ƙara kiran aminiyar tata.

“Hello inajin ki me ya faru kuma?

” Am sorry Surayya ba haka nake nufi ba wallahi, i thought ke kika haɗa mu shiyasa”.

“Haba Suhaila ko ni na haɗa ku sai me? Ina ce dai idan baki yi mai ba zai ce baya so, ballantana ma ba haɗa ku nayi ba shi ya gani ya kuma ce kinyi mai yana son ki a haka”.

“Naji ya wuce ai, yanzu yana gidan naki ne??

” A’a baya nan yanzu ya fita zai koma can gurin Hajiya, if kinji abun be kwanta miki ba yana kira kawai ki faɗa mai kar ki tsaya wani ɓoye_ ɓoye”.

“To shikenan in sha Allah zanyi abunda ya kama ta ki gaida Abbu Nu’aman”.

“Zai ji in sha Allah”.

“Sai na kira ki tau, duk abunda mu kayi da shi zan sanar da ke in sha Allah”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button