ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ta ƙarashe maganar tana komawa mazaunin ta, “We need your help, i hope zaki iya temakon mun”.
“Yess why not, now bari mu fara magana da shi”.
“Mr Ahmad, wannan shine lokacin ka na farko da ka fara ganin gurin theraphy?”..
“No,bashi bane na farko, but ban taɓa tsayawa nayi having long conversation ba, just a short conversation and then sai a bani medicen”.
“Okay this time around, no medicen but a long conversation and we will start just now, we are stopping by 11pm umm, so i hope zaka bani haɗin ka muyi abunda ya kama ta, you know idan ka fitar da abunda yake damun ka you feel much better, yafi kasha maganin ma mostly indai ba wai worst yayi ba”.
Gyaɗa mata kai, yana sakuke numfashi ko zai iya oho.
“Meye matsalar, is it your parent, your wife, friends, drugs, alcohols uhmm?”
Deep breath ya sauke sannan yace ; “Yace my parent”.
“Okay ka bamu labarin abunda yake faruwa so that i can help”.
Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara bata labari, yafi ten minutes a haka, sai kuma ya rumste ido yace ; “, I can’t do that”.
“You have to mr, please we are running out of time can we start?”
Suhaila ce ta ɗaura hannun ta akan nashi tace; “Ahmad”.
Kallon ta yayi sannan ya gyaɗa mata kai sannan ya fara magana cikin nutsuwa da karyewar zuciya yau zai fitar da sirrin shi.
_”Shekarun baya da suka wuce Familyn Alhaji Umar me shadda sun kasance cikin farin ciki mara misaltuwa. Baba na da Umma na wacce Allah yayi mata rasuwa sunyi auren soyayya kamar za su cinye junan su inda suka yi shekara bakwai ba tare da ta haihu ba hakan ne yasa Hajiya maman daddyn mu tace dole sai ya ƙara aure, anyi bata kashi da shi sannan ya haƙura ta nema mai mata ya aura, that is Ummi na, sai da suka yi aure da shekara ɗaya itama bata samu ciki ba, a wannan lokacin kuma Umma na ta samu ciki bayan wani lokaci ta haifi ƴar ta mace aka sa mata Aisha, a lokacin Kuma Ummi na tana ɗauke da ciki na, itama bayan wata tara ta haife ni aka sa mun Ahmad, sai dai kuma Abba na baya son Ummi na ko kaɗan saboda kamar auren dole ne Hajiyar shi ta mishi, haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda ko da yaushe Aisha na gurin Ummi na, ni kuma ina gurin Umma na, Umma tana son Ummi na ba abunda suke sai zaman lafiya, dangin Abba kuwa basu da abinyi sai zuga Ummi ganin ita Hajiya tafi so ko bayan Da Umma ta haihu, bayan wani ɗan lokaci Umma ta haifi Jibril, Ummi kuma ta Haifi Kausar, Abbu yana son Kausar, ni kuma dai to sai addu’a don ko a lokacin be wani damu da ni ba, sai dai tun da muka taso nafi Jibril ƙoƙari don Allah ya bani talent na zane-zane, painting ba abunda bana yi, bayan mun kai kamar shekaru 18 Daddy ya samu aiki a London muka dawo nan da zama. A kwana a tashi ba wuya har muka fara zuwa school ina karantar harkar zane shi kuma yana karantar harkar likitanci, a lokacin ne kuma ciwo ya kama Umma har Allah yayi mata rasuwa, anji mutuwar ta sosai tun daga nan komai ya ƙara canzawa a gidan namu”._
Shuru yayi ya sunkuyar da kanshi yana sauke wani deep breath.
Kallon agogon hannun ta tayi tace; “Its already time, bari mu bari haka till tomorrow, you people should be here by 10:00am.
Kallon shi tayi, shima ya kalle ta, sai kuma suka ɗaga mata kai a tare sannan suka fice daga ɗakin..
Kallon ta yayi yace ; ” Thank you very much and am sorry for everything, na gode sosai bazan taɓa manta abunda kika mun ba yau na gode, let me do the payment sai nazo mu tafi”.
Juya mai baya tayi, shi kuma ya wuce yaje ya biya kuɗin sannan suka fito a tare, taxi ya tsare musu, ya kaita gida sannan ya wuce da shi wani hotel, da washegari yake son komawa America amma wannan appointment ɗin ya ɓata komai, duk da yanzu ya ɗaukarwa kanshi alƙawarin yaƙi da iyayen nashi, tunda yanzu he is not part of there family, shi kuma indai har Suhaila tana son shi babu abunda zai hana shi auren ta ya ɗaukarwa kan shi wannan alƙawarin zai yi sabbabin iyaye don sai ya riga su zuwa Nigeria ma.
Suhaila kuwa tana shiga gida Jibril ya hango ta, da sauri ya fito yana tambayar ta daga ina ta take har wani jijiga ta yake yana daka mata tsawa kamar Ubanta.
Cikin ɓacin rai tace; “Ya ishe ku haka!ni fa ba ball ɗin ku bace da wannan zai buga ni waccen ya buga ni, kun maidani abun taɓawar ku kowa sai ya ɗaga hannu ya taɓa ni to wallahi bazai yiwu ba, kar ka sake taɓa ni wannan ita ce magana ta ta ƙarshe da kai aikin banza kawai, don nace zan aure ka ban zama matar ka ba da zaka taɓa ni sanda kake so sannan ka dinga mun tsawa kamar wani uba na ba”. ta ƙarashe maganar tana barin gurin ranta a ɓace.
Tana shiga taga Kausar na safa da marwa, da sauri ta ƙaraso ganin Suhailan.
“Me ya faru da ya Ahmad han? I can feel it wani abu ya same shi”.
“Kausar ki kwantar da hanklin ki please, he is fine now, munje asibiti munga therapy zamu koma gobe ma, sai muje tare umm amma karki gaya Ummi kinji ko”.
Gyaɗa mata kai tayi tana rungume ta haɗe da ƙara mata godiya, taji daɗin kula da Ahmad ɗin da tayi yau.
Washegari da safe da Kausar zata tafi gurin aiki suka fita tare suka haɗu da shi a bakin hospital ɗin, nan suka gaisa da Kausar taga lafiyar jikin nashi kafin ta wuce gurin aiki ta barsu a gurin.
Jibril kuwa kwana yayi yana tunanin inda Suhaila taje da kuma maganganun da ta faɗa mai, anya kuwa babu wani abun a ranta, anya ba wani abun take shirya mai ba, haka dai ya gama tunanin shi ba tare da ya samo amsa ba.
Suna shiga suka tarar tana ganin wasu, sai da ta gama da su sannan suka shiga, guri suka samu suka zauna aka gaisa sannan suka ɗora daga inda suka tsaya.
_”Abba na ya kasance ba wanda ya tsana a gidan irin Ummi, komai tayi bata burge shi sai yace ai da Umma ce da baza tayi kaza ba, haka nan ta cigaba da daurewa har daga baya yace zai sake ta, sai da Hajiya ta buɗe mai ido ta kuma sanar mai da ko bayan ranta idan ya sake ta baza ta yafe mai ba, daga nan ne kuma ta samu ɗan sauƙi har ya fara sake mata amma ƙiyyayar nan ba a rasa ta ko kaɗan ne. A wannan lokacin ne aka kawo Zainab gidan mu, a gidan mu tayi primary suka shiga secondary ita da Kausar komai nasu kusan iri ɗaya ne duk da ta girme ta. Tun tana yarinya nake son ta sosai kuma ba ni da wani buri sai tana gama karatu in aure ta, ko da yaushe tana tare da ni bata barin waje na, ko wani lokaci tana manne da ni, a library ne ɗaki na ne ko ina, ni nake musu komai ita da Kausar some times ma har kwana suke a ɗaki na. A wannan lokacin ne kuma mamanta ta fara wani mahaukancin tunani kan tana so na auri ƴar ta ko ta wani hali ne, ba tare da ta san ina son Zainab ɗin ba…..”_
******
*_ma’asalam Faɗama Ahmad.. _*
[8/12, 3:39 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*wattpad@cynosure3*
*Page6️⃣7️⃣to6️⃣8️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*