ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Thank you so much, you’re the best therapist da na taɓa haɗuwa da ita”.
Murmushi tayi mai ta gyaɗa mai kai sannan ya juya ya fita.
A zaune ya same ta nan ya sanar mata da tana buƙatar ganin ta.
Shiga tayi ta samu guri ta zauna, a hankali Laika ta fara mata magana.
“Ya sanar da ni ke ba matar shi bace, amma ina so ki sani Ahmad yana son ki sosai sannan kuma a gurin ki ne kaɗai zai iya samun farin ciki da abunda familyn shi suka mai, if not zai iya komawa rayuwar da yayi a baya, ki aure shi ki kula da shi ki bashi duk wani farin ciki, he feel will much better, sannan kuma nasan cewar zaki iya dai-dai ta komai tsakanin shi da familyn shi amma hakan zai faru ne idan shi kika aura ba brothern shi ba, maman shi tana son shi, and shima baban shi yana son shi yanayi ne yasa komai ya faru a hakan, so abunda nake requesting a gurin ki kenan, hope zaki iya yin hakan ko?”
Shiru tayi ba tare da tace komai ba, ta tashi ta miƙa mata hannu suka gaisa tayi mata godiya sannan ta fice a office ɗin zuciyar ta na mata zafi sosai, gaba tayi ba tare da ta jira shi ba.
Da gudu yabi bayan ta yana kiran sunan ta.
“Just leave me alone Ahmad, ka tafi am going home wannan shine haɗuwar mu ta ƙarshe tunda an gama komai”.
“Ki tsaya ki saurare ni please, kinji ko”.
Tsayawa tayi tana kallon shi, sannan tace ; “Naji komai , and i need sometime, sai anjima”.
Barin gurin tayi ta barshi da baki a buɗe, bus stop taje ta tsaya tana jira ta ƙaraso, yayin da shi kuma ya tsaya a opposite ɗin da take a tsaye yana kallon ta har bus ɗin ta ƙaraso ta shige abunta.
Tana isa gida ta jefar da komai da komai, sannan ta fara zagaye ɗakin tana tunanin abunda Ahmad yake faɗa ɗazu.
Bayan Kausar ta dawo ta tambaye ta yadda suka yi duk ta bata labari.
Ummi kuwa har yanzu bata dawo dai-dai ba don ko fitowa bata yi abinci ma kai mata ake yi, kuma har yanzu fushi take da Daddy.
Jibril ma har yanzu Suhaila bata sakar mishi fuska ba don duk haushin su take ji kamar ta bindige su, su duka biyun.
Bayan sati biyu, mutanen gidan ba abunda suke sai shirye-shiryen tafiya Nigeria inda kowa yake cikin farin ciki za su je gida a haɗu da family, Suhaila kuwa ba a magana bakin ta har kunne.
Nigeria….
Zaune suke a Palo da Farida da Mubarak suna kallo inda suka fara jiyo hayaniyar iyayen nasu kamar za su fasa gidan.
Mubarak ne ya tashi ya fita daga Palon ya koma ɗakin shi don ya gaji da wainnan abubuwan da iyayen nashi suke yi.
“Wallahi baka isa ba dole a gyara a gidan nan ayi penti da sauran su, tun da dai har yarinyar nan ta faɗa idan suka zo sunce za ayi maganar aure ai ayiwa gidan kwaskware ma ko, su ganmu da arkiziƙin mu, basu ga gidan kaca-kaca ba”.
“Uhmmm Asiya kenan, mutanen nan masu kuɗi ne, ba kwaskwarima ba ko me za ki yi idan suka zo gidan nan a matsayin talaka kike wallahi, yo akwai abunda ya kai haka ma tunda ƙarewar ta ƴar ki aikatau take yi a gidan nasu”.
Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙewa Ammi zuciya wato har ita zai ciwa mutunci haka, ai kuwa zai san da ita yake zancen za tayi maganin shi yanzu-yanzu.
“To wallahi indai haka ne sai dai ka zaɓa, ko ka sake ni ka karɓi auren kai ɗaya kaji kunya, ko kuma ka yarda ka bada kuɗi ayi gyaran nan, idan ba jaraba ba mutum ba abunda ya iya kira sai babu, saboda kaine ƙarshen matsiyacin duniy….
Be bari ta ƙarasa abunda zata faɗa ba ya ɗauke ta da mari ya ƙara ɗauke ta da wani marin sannan ya nuna ta da hannu yace; “Na sake ki saki ɗaya, kije can ki ƙarata na gaji! “.
“Wallahi baka isa ba, baka isa ka sake ni ba yauwa, ina nan yanzu ma na fara zaman aure yauwa gwara ma in faɗa maka”.
Be ƙara sauraron ta ba ya fice a gidan kar zuciya ta ɗauke shi ya ƙarasa mata saki ukun.
Farida tana zaune a Palo ya fito, ya fice abun shi…
*****
_*Ma’asalam, faɗma Ahmad..*_✍????✍????
[8/15, 3:52 PM] Fatima Batula: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure*
*Page6️⃣9️⃣to7️⃣0️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
Addu’a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.*
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ.
A’oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*_This page is Dedicated to Addan Zainab and saleem, small Aisha, and other members of Mijin bahaushiya, inajin daɗin comment din ku, so keep it up_*????????❤️????❤️…
_*Nigeria*_
Abba kuwa can makarantar su ya tafi da daren nan yaje ya kwana washegari kuwa duk malamin da yazo a nan ya tarar da shi me gadi ne kaɗai yasan sanda yazo.
Ammi kuwa tana nan ko a jikin ta, wai ai annabi cewa yayi mace tayi idda a ɗakin ta don haka babu inda zata je, Farida kuwa ji take kamar ta mata duka ta rasa wacce irin Uwa Allah ya haɗa su da ita, sam babu abunda ya dame ta da su sabgar gabanta kawai take yi.
Farida ce ta sanarwa da Fatima halin da ake ciki yayin da hankalin ta yayi matuƙar tashi, ace tuntuni Abba be saki Umma ba sai yanzu da ta girma sannan zata ja abunda har zai sake ta, ita kam saboda tsabar baƙin ciki ko takanta ma bata bi ba sai Abba da takira tayi ta bashi haƙuri akan ya mayar da ita, ba abunda ya iya ce mata sai zai yi tunani kawai.
Umman sheka ma da taji abun ranta ba ƙaramun ɓaci yayi ba, saboda tasan basu da iyaye ina zata je gidan ƙanin mahaifin su ko ina, ta rasa meye matsalar ƙanwar tata kwata-kwata.
*London…*
Yau saura kwana uku mutanen London su sauka a Nigeria, masoyan guda huɗu kowa da abunda yake ranshi, Zainab gani take baza ta iya rayuwa idan babu Ahmad ba, saboda tana son shi sosai, haka zalika ma Jibril yasan idan har Suhaila ta rabu da shi to babu makawa saboda Ahmad ne, shi kuwa Ahmad so yake ya tabbatar da Suhaila tana son shi to a lokacin ne zai fara yaƙi da Jibril ɗin, ita kuwa Suhaila kanta yana duhu don duk cikin su babu wanda bata so, idan tace ga wanda take so ta aura ma tayi ƙarya, hakan yasa ta kira Surayya ta fara gaya mata halin da take ciki kafin ta isa Nigerian, itama bata wani bata amsa ba tace sai tazo sunyi shawara.
8:30pm…
Zaune yake a cikin ɗakin hotel ɗin da ya sauka bayan isowar shi daga Washington don yana so yayi sallama da Suhaila kafin ya wuce Nigeria, tunda yake America duk ya gama wani shirye-shiryen sa gida kawai zai wuce.