ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Hakan yasa ya yanke shawar zuwa gidan nasu ko Allah zai bashi sa’ar ganin ta, amma ina yadda yazo haka ya faka motar shi a gurin sai dai hange daga nesa amma ya kasa ɗaga ko da ƙafar shi ce guda ɗaya.
A ɓangaren Suhaila kuwa tana zaune suna hira da Kasaur haɗe da ƙarasa shirye-shiryen su kiran Fatima ya shigo wayar ta, nan ta ɗaga suka gaisa, ita dai Kausar bata san me akace mata sai gani tayi Suhaila ta saki wayar tata ta zame zuwa jikin cinyar ta Allah yaso ma a zaune take.
Nan da nan hawaye suka shiga zubo mata.
Cikin wani irin yanayi Kausar ta jefo mata tambayar meke damun ta, kallon ta tayi sannan ta ɗauke kai kafin ta miƙe tsaye zata fita a ɗakin, Kausar ce ta riƙe mata hannu, tace ; “Haba Suhaila me ya faru ne ki faɗa mun don Allah”.
Kallon ta Suhaila tayi idon ta yana daɗa cika da hawaye kafin tace; “Am sorry Kausar ki ɗan barni, inason kasancewa ni kaɗai kar ki biyo ni”.
Gyaɗa mata kai tayi ba tare da ta sake ce mata komai ba.
Sanye take cikin duguwar riga, irin ta baccin nan amma cotton ce ba transparent ba, sai rigar sanyi irin ta ƙulun nan kanta kuma role yake da mayafi, kafarta kuwa ko safa babu ga wani irin sanyi da yake kaɗawa, direct ta fito daga cikin gidan ta nufi hanyar waje don bata ma san inda zata je ba.
Finally dai yau Abbun ta ya saki Ammin ta shikenan komai ya ƙare, babu wani abu yanzu abunda suka ga yafi musu kenan.
Shi kuwa Ahmad ganin bazai iya shiga cikin gidan nasu ba yasa ya juya jikin shi duk yayi sanyi ya buɗe murfin motar shi ya shige ciki, yana jin zuciyar shi na mishi zafin rashin ganin masoyiyar tashi, haɗa kanshi yayi da sitiyarin motar.
Kamar daga sama yaji anbuɗe ƙofar gidan nasu. Wani irin ɗagowa yayi don ganin me fitowa ko zai iya bashi saƙo ya faɗawa Suhaila, ganin itace yasa ya tsaya yana kallon ta babu ko ƙiftawa.
Ganin tana kuka yasa hankalin shi yayi mugun tashi, kallon ta yayi from head to toe, yaga ko kayan arziƙi babu a jikin ta, bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta fara tafiya, tayar da motar shi yayi ya dinga bin bayan ta a hankali, tayi tafiyar kusan 30 minutes kafin ta samu wani bus stop ta zauna a kan kujerar gurin tana sakin wani kuka me cin zuciya. Tafi 10 minutes tana kukan sai da yaga tayi me isar ta sannan ya fito daga cikin motar yazo ya zauna a kusa da ita ya miƙa mata handkerchief ɗin dake hannun shi.
Kallon hannun tayi don ita tayi tunanin masu hawa bus ne, da sauri ta ɗago kai ta kalle shi, shima kallon ta yake, sai da suka ɗau ɗan seconds a hakan kafin ya sauke idon shi ya juya ya kalli titi, cikin sanyin muryar shi yace; “Yanzu da kika fito da daddaren nan idan kika haɗu da bad guys ɗin garin nan fa me zaki ce ummm? Bakya jin tsoro kwata-kwata shiyasa kika fito a wannan lokacin ko, ba da ke muka je gurin therapy ba, me yasa baza ki iya danne abunda kike ji ba, me yasa baza ki iya controlling kanki ba, ko ma menene ya faru addu’a ya kamata kiyi baki fito daga gida kizo ki zauna a nan kina kuka ba Suhaila, me yasa bakya kula da kanki?”
Kallon shi tayi ba tare da tace mai komai ba hawaye na daɗa zubo mata.
Bata san lokacin da bakin ta ya buɗe ba ta fara magana; “Ya Ahmad ya za ayi ace Abbu ya kasa sabawa da halin Ammi? ya Ahmad me yasa Ammi baza ta taɓa canzawa ba? me yasa Ammi take da wannan halin ne? Na rasa me yake damun ta, na rasa wani kalar daɗi take ji idan ta ɓatawa Abba na, indai don saboda ni ne ai na bar gidan ko, sai ta barshi ya huta, amma ina har saida ta ja ya sake ta, yanzu wa gari ya waya, am sure tana can tana regreting abunda ta aikata, ya Fatima tace mun wai tace baza ta bar gidan ba,ya zanyi ne? Ya Ahmad ina mutanen nan suke so na saka rayuwa ta ne? Da matsalar su zanji ko da tawa matsalar? ”
Nan da nan yaji idon shi ya ciko da ƙwalla, be ce mata komai ba ya kalle ta yana daɗa dai-dai ta kanshi don kar ya bari hawayen dake cikin idon shi su samu nasarar zubowa.
Handgloves ɗin dake hannun shi ya cire, ya kamo hannun ta ya saka mata, sannan ya cire coat ɗin dake saman kayan shi ya saka mata.
Kallon shi tayi da mamaki kafin tace; “Kai kuma fa?”
Murmushi yayi mata ya cire mofular dake maƙale ajikin wuyan shi ya saka ya nannaɗe hannun shi dashi yana ɗaga mata kaɗa.
“Yanzu kice inallillahi waina ilaihi rajiun, am sure baki faɗa ba da aka gaya miki wannan maganar”.
Gyaɗa mai kai tayi sannan ta faɗi abunda ya faɗa ya.
“Good giril, Allahummaajirni fi musibati wa aklifni khairan minha”.
Sake gyaɗa mai kai tayi sannan itama ta mai-maita abunda ya faɗa.
Kallon ta yayi yace; “Now, how are you feeling?”
“Much better”. Ta faɗa tana kallon shi”.
“Good zo muje na kaiki wani guri”.
Tashi tayi babu musu ta bishi suka shiga cikin mota. Be Parka a ko ina ba sai Hilton, fitowa sukayi a tare suka shiga sai bin gurin take da kallo kamar wata ƴar ƙwaye,escalater suka zo za su hau ta tsaya tana kallon shi alamar bata iya hawa ba, don tanajin tsoro sosai koda suka je silver bird a abuja bata yarda ta hau ba, sai elevator ta hau saboda wannan yana bata tsoro farkon hawa gani take kamar zai tafi da ƙafarta ne.
Ni kuwa a nace Suhaila sha sha’anin ki don ko nima nayi wannan ƙauyancin.????????????????????????
Dariya yayi ya kama hannun ta suka hau, farkon saka ƙafar ta sai taji kamar zata shige ciki, da aka cigaba da tafiya kuma sai taji dai-dai, ko da suka zo ƙarshe ma saida ya jata suka sauka.
Wani restaurants dake cikin gurin haka suka shiga yayi musu ordering abinci, suka zauna suka ci, shi dai yaci babu lefi amma ita kam hankalin ta na kano so take kawai ta koma gida ta gaji irin sosai ɗin nan.
Haɗa ido suka yi taga yadda yake kallon ta kamar zai cinye ta, lallai rayuwa ta canza wai itace yau namiji ya ɗakko ta ya kawo ta restaurants suka ci abinci tare, yau itace sanye cikin doguwar rigar ba tare da long hijab ɗin ta da niqab ɗin da safar ta ba, taɓɓ lallai, gaskiya baza ta iya cigaba da rayuwa a haka ba, gaba ɗaya imanin mutum ya tafi, sai kayi da gaske ka cize ka daure sannan zaka iya yaƙi da sheɗan, lallai Amminta ta cuceta ba kaɗan ba wallahi, duk da bata san ko wani dalilin ne yasa tazo garin ba, amma tabbas tana jin baƙin cikin yadda ta maida kanta a halin da take ciki, wai a haka ma tana ƙoƙari.
Saukar da idanun ta tayi tace; “Inaso zan tafi gida ka kaini gida please”.
“Okay bari mu gama sai na kaiki, gurin da na sauka a nan kusa ne, so don haka ba da mota zan kaiki ba bus zamu hau ko?”
Gyaɗa mai kai tayi ba tare da ta sake magana ba.
Bayan sun gama cin abincin suka fito ya samar musu bus suka hau har sai da ya kaita bus stop ɗin kusa da gidan su sannan suka sauka.
” Thanks”. Ta Faɗa tana kallon shi.
“Jibi zamu wuce Nigeria, thank you for everything saduwar alkhairi, take care of yourself and eat well, ka dena tunani, ka manta da komai, sannan kuma ka dinga addu’a don ita ce maganin komai, am gonna miss you, my hilarious yaya”.
Ta faɗa tana kallon face ɗin shi “Am gonna miss you too my hanoona, ki gaishe da su Abbu, su Ammi, Farida Ahmad, Surayya, Najwa baby, kowa da kowa dai, sannan kuma ki cigaba da yiwa su Ammin ki addua don itace maganin komai a rayuwa, ki dena saka kanki cikin damuwa, sannan kuma ki dena tunanin komai saboda ke ya faru, ba haka bane, kaddarar auren su kenan su kuma, don haka addu’ar ki gare su Allah ya basu ikon cin jarabawowin su ummm, sai mun haɗu a kano may be ma na riga ku sauka bye”.