ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ya faɗa yana juyawa.
“Your jacket”.
“Na bar miki” yayi maganar ba tare da ya juyowa ba, kallon shi tayi ta yi har sai da ya ɓace mata, Allah sarki yaya Ahmad ɗin ta ga addini amma rayuwa ta canza masa komai, juyawa tayi zata shiga cikin gida su kayi ido haɗu da Jibril, ji tayi gaban ta yayi mugun faɗuwa ai ko ba komai tasan zai ji babu daɗi kuma ko itace baza ta ji daɗi ba, amma sai ta haɗe girar sama da ƙasa ta canza hanya zata shige cikin gidan.
Wani irin fizgo ta yayi wanda har sai da ta faɗa jikin shi, ya riƙeta gam yaƙi sakin ta duk yadda taso da ta ƙwace jikin ta a nashi kasawa tayi.
Wani irin ihu ta saka a kan layin nasu tana kukan ya sake ta amma ina saima rungume ta da yayi tsam a jikin shi babu kukan da ba tayi ba amma yaƙi sakin ta.
“Suhaila i love you, i love you so much duk ranar dana ƙara ganin ki da ya Ahmad irin haka zuciya ta bugawa zata y…..
Be ƙarasa faɗan abunda zai faɗa yaji an fizge Suhaila a jikin shi, kamar tana jira kuwa tayi bayan shi tana kiran sunan shi” Ya Ahmad kayi mai magana bana son abunda yake mun bana so”.
“Jibril meye hakan!? Kana da hankali kuwa!? Kasan me kakae aikatawa kuwa!? Yanda tayi ihun nan idan wani yaji ya kira police kasan da cewa rape case a garin nan ba wasa bane ba ko, don ana ganin ka cewa za ayi raping ɗin ta kawai za kayi”.
Be jira Ahmad ɗin ya ƙarasa ba ya kai mai naushi, dama Jibril zuciyar shi ita ke ja mai saboda yana da zuciya sosai da sosai.
Ahmad ma naushin ya kai mai nan aka fara dambe, tayi ihun tayi ihun amma ina babu wanda yake jinta a cikin su.
Ni kuwa nace faɗan masoyiya ai baza su ji ba.
Buga gate tayi me gadi ya fito ya fara raba su da ƙyar ya ɓanɓare su a jikin junan su.
Kowa ya koma gefe yana maida numfashi, bin su tayi ta bawa kowa mari ta ƙara da faɗin “I hate you, you guys na tsane ku na tsane ku, ya Ahmad kasan halin da nake ciki me yasa zaka biye mai kuyi faɗa haka han? A kaina, to indai haka ne kaima Jibril na fasa auren ka shikenan”.
Ta faɗa tana shigewa cikin gidan. Jibril ne yabi bayan ta yana bata haƙuri.
Shi kuma Ahmad yace ; “Suhaila! I love you, i love you so much, and indai kina so na i will do anything just to have you”.
Ko da take cikin fushi sai da ta juyo ta kalle shi tana mamakin kalaman shi sannan ta shige cikin gida.
Jibril kuwa ji yayi kamar ya shaƙe mai wuya, haka suka shiga cikin gida ba tare da ta saurare shi ba.
Haka kowa a cikin su yaje yayi jinya don sun dambatu har da su fasa baki, shi kuwa Ahmad washegari yayi Nigeria, infa Suhaila har ranar da za su tafi babu wani walwala a tattare da ita.
Bayan sun isa Nigeria a birnin tarayya abuja suka sauka sai washe gari ne suka fara shirin zuwa kano, ɗayan washegarin kuma suka ɗau hanya, inda suka sauka a gidan wan Abban nasu da za ayi bikin ɗan shi, Zainab kuwa ta dawo wani iri don ko Umman ta ma taga yadda ta canza duk tayi yaushi, hankalin ta be kwanta ba sai da ta sanar da ita cewar akwai wani malami can za su je dole Abba ya amince da auren nasu.
Ita kuwa Suhaila ko kwana bata yi ba ta wuce gidan su zo ku ga murna da jin daɗi wajen Mubarak da Farida kamar su cinye ta, ita kanta Ammi tayi mamakin canzawar ƴar tata, don cikin ɗauki ta rungume ta kamar ba Ammin da ta sani ba. Bayan magrib Abba ya dawo shima yayi murna da ganin maman tashi yadda ta canza kamar ba ita ba.
A ranar dai tayi ta musu nasiha da janyo musu ayoyi da hadithi kan abunda suke aikatawa musamman ma Ammin, kamar gaske ta marairaice fuska har dai Abbu yace ya mayar da ita ɗakin ta.
Surayya kuwa bata iya haƙuri ba sai da tazo wajen rabin ranta, sunyi farin cikin ganin juna kamar ba a rabu ba inda suka sha hira, tayi ta bata labarin Ahmad da Jibril, ita kanta Surayya taji tausayin Ahmad amma baza ta iya cemata ta auri Ahmad ba saboda ko ba komai Jibril ɗin ya rigashi sannan kuma shima duk abunda yayi saboda yana son ta ne,ce mata tayi zaɓi ya rage gare ta.
Itama kanta tasan cewar Jibril ɗin yayi mata adalci tunda shi yasan ita bazawara ce Ahmad kuwa koda wasa be taɓa sani ba.
Dangi kuwa sun sha tsaraba a gurin ta inda Ja’afar yake ta mata isgilancin yayi aure harda ƴa ita kuwa tana ta yawo gidan aikatau a gidajen masu kuɗi, bata tanka mai ba saboda ba ƙaramun tsoran shi da tsanar shi take ji ba.
Abba yayi magana da Suhaila inda tace mai ai su Jibril ɗin bayan sun kammala bikin su za su zo ayi magana don kafin su koma suke so ayi bikin, tunda ba wani abu za a tsaya yi ba.
Bayan kwana biyu Suhaila da Surayya suka shirya don zuwa bikin gidan su Kausar.
Wani arnen lace, pitch da Marron Suhaila ta ɗinka yaci style me shegen kyaun gaske, mayafi ta yafa pitch ta saka takalmin ta maroon sai ƴar ƙaramar jaka itama maroon, babu wani make up ɗin kirki, ta fito tayi kyau sosai abunta, tunda ta shiga cikin girin ake kallon ta inda Kasaur tana gano ta ta taho da gudu ta rungume ta, Ummi ma taji daɗin ganin yadda Suhailan tayi kyau kamar ba ita ba.
Jibril yana kallon su hakan ne yasa ya taso ya ƙaraso zuwa gurin yana sunkuyar da kai.
Gabatar da shi tayi gurin Surayya suka gaisa sannan suka nemi guri suka zauna, amarya da ango ne suka shigo, inda abokan su da ƙawayen amarya suke take musu baya, nan fa guri ya ɗauki hayaniya kowa burin shi ya ɗauke su hoto, amma sai dai aka hana, aka sanar da kowa babu ɗaukar hoto za ayi video kowa ya gani idan aka bashi.
Suna zaune babban abokin ango ya fito ya bada biography ɗin sa, bayan ya gama kuma na hango wani matashi meji da cikar haiba, nutsuwa tattare da kamala, ga kwarjini ga kuma kyau, yana doso stage ɗin, sanye yake cikin wata golden gezna wanda taji aiki shaɓe shaɓe a jikin ta, ya dasa hular sa zannabukar, ga wani shegen agogo sanye a hannun shi, sai takalmi brown da kuma kwaliyar coffe dake sanye a ƙafar shi, loudspeaker ya karɓa ya fara bayani da turancin shi wanda kana ji kasan ba na nan Nigeria bane, nan kallo ya koma kanshi.
Nan da nan Ummi taji gabanta yayi mugun faɗuwa don dama daurewa kawai take yi, bata taɓa zaton zata ga Ahmad ba yanzu.
“Ya Ahmad” Suhaila ta furta inda Kausar itama ta karɓa. Kallon su tayi ganin yadda hankalin su ya tashi su duka ukun musamman ma Ummi da Suhaila, don maganar da yayi mata ta zaci wasa yake mata.
Bayan ya gama bayanin yana sakkowa da gudu Zainab ta taho daga mazaunin ta tana rungume shi haɗe da fasa kuka, nan fa kallo ya daɗa komawa kansu.
Ita kuwa Suhaila bata san sanda ta miƙe ta fice a gurin ba tanajin zuciyar ta kamar zata faɗo ƙasa tsabar yadda take bugawa….
*****
*_Tofa! Ku biyo ni don jin yadda zata kaya…_*
*_Assalama alaikum, Faɗma Ahmad_✍????✍????*
[8/16, 1:04 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page7️⃣1️⃣to7️⃣2️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*