HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

وَحَدَّثَنَاهُ قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ وَأَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ وَعَمْرٌو النَّاقِدُ وَزُهَيْرُ بْنُ حَرْبٍ – وَاللَّفْظُ لِقُتَيْبَةَ – قَالُوا حَدَّثَنَا سُفْيَانُ بْنُ عُيَيْنَةَ عَنِ الزُّهْرِىِّ عَنْ سَعِيدِ بْنِ الْمُسَيَّبِ عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ قَالَ جَاءَ رَجُلٌ مِنْ بَنِى فَزَارَةَ إِلَى النَّبِىِّ -صلى الله عليه وسلم- فَقَالَ إِنَّ امْرَأَتِى وَلَدَتْ غُلاَمًا أَسْوَدَ. فَقَالَ النَّبِىُّ -صلى الله عليه وسلم- « هَلْ لَكَ مِنْ إِبِلٍ ». قَالَ نَعَمْ. قَالَ « فَمَا أَلْوَانُهَا ». قَالَ حُمْرٌ. قَالَ « هَلْ فِيهَا مِنْ أَوْرَقَ ». قَالَ إِنَّ فِيهَا لَوُرْقًا. قَالَ « فَأَنَّى أَتَاهَا ذَلِكَ ». قَالَ عَسَى أَنْ يَكُونَ نَزَعَهُ عِرْقٌ. قَالَ « وَهَذَا عَسَى أَنْ يَكُونَ نَزَعَهُ عِرْقٌ ».

*It was narrated that Abu Hurairah said: “A man from Banu Fazarah came to the Prophet (s.a.w) and said: `My wife has given birth to a black boy.` The Prophet (s.a.w) said: `Do you have camels?` He said: `Yes.` He said: `What are their colors?` He said: `Red.` He said: `Are there any dusky ones among them?` He said: `There are dusky ones among them.` He said: `Where does that come from?` He said: `Perhaps it is an inherited trait.` He said: `And perhaps this is an inherited trait.`”*

Sahih Muslim

*This page is dedicated to Umar ɗalha, Allah ya baku lafiya ya sa kaffara, Aunty Ummi Allah yasa kaffara da ke da shamsiyya…..*

 

*_The Wedding_*

 

Da sauri Jibril ya bi bayan ta yana tambayar ta me ya faru, Ahmad kuwa cire Zainab yayi a jikin shi yaja hannun ta suka bar gurin.

Fitowa waje suka yi suma, inda ya fara mata magana kan me zata rungume shi cikin mutane ita ko kunya ma bata ji.

A dai-dai lokacin kuma ya haɗa ido da Jibril, ɗan ƙarasawa yayi kusa da shi ya rungume shi yace; “Oh bro, saukar yaushe? Sannun ku da zuwa ai munyi ta jiran ka da ango baka ƙaraso da wuri ba, ko ka tsaya kaduna ne?”

Kallon Ahmad ɗin ya tsaya yi ba tare da yace mai komai ba, Ahmad ɗin ne ya ɗan kalli Suhaila sai kuma ya juyo da kallon shi kan Jibril yace;” Kar dai kace mun itace amaryar tamu?”

Nan ma shiru yayi mai be amsa mai ba, sai kuma ya kalli Suhaila yace ;” Allah sarki, sannu fa ya gida? Kin san be taɓa nuna mun koda hoton ki bane”.

Kallon mamaki tayi mai tana tunanin me yasa yake behaving haka me ya faru da shi.

Katse mata tunani yayi da faɗin “Sai anjima na barku lafiya”.

Bata san sanda bakin ta ya furta”Ahmad me ke damun ka ne? Why are you behaving like this are you okay?”.

Juyowa yayi ya ƙara ɗaga mata hannu ba tare da yace komai ba, Zainab kuma ta take mai baya.

Suhaila kuwa hankalin ta ya tashi sosai, don wani wutar son shi ne taji yana daɗa rurar mata a cikin zuciya.

Jibril ne yazo yi mata magana ta ɗaga mai hannu tana shiga cikin hall ɗin.

Ummi da take zaune kamar butun mutumi tayiwa sallama sannan ta kama hannun Surayya suka fita a cikin gurin.

Suna fita wajen gurin ta saka kuka tana rungume Surayyan.

“Wallahi Surayya ina son shi, ina son shi sosai, kinga yadda yayi kamar be sanni ba, ya wani share yayi banza da ni yana pretending dama cewa da yayi yana so na duk ƙarya ne”.

Kallom ikon Allah Surayya ta tsaya yi.

“Yau naga ikon Allah, ke kin nuna mai kina son shi ne? Naga cewa su Abba kika yi su Jibril za su turo basu Ahmad ba, yanzu kuma zaki zo kina blaming ɗin shi, kinga ki nutsu ki san wanda zaki aura yauwa, ni wallahi har kin fara sani ciwon kai, banza kawai, me ruwan ido, dalla kwace, ni bani hanya na wuce ko abinci bamu ci ba kika taso mu”.

Goge fuskarta tayi tabi bayan Surayyan da ta fara ƙoƙarin tsare masu napep, babu wani ɓata lokaci suka samu suka wuce gida.

Jibril da yake biye da su a baya yaji duk abunda suka faɗa hankalin shi ba ƙaramun tashi yayi ba jin Suhailan tace tana son Ahmad.

Hakan ne yasa washegari, bayan anyi ɗaurin aure ya sanar da Daddy yana so washegari suje don ayi maganar bikin ayi ta taƙare, haka kuwa aka yi, suka je har aka saka rana bayan sallah da sati uku, don a nan za su yi Sallah amma sun koma abuja.

Yau ta kama aka ɗauki azumi inda kowa yake cikin hidima yake kuma tunanin da me zai sha ruwa kasancewar yau aka fara.

Bayan ansha ruwa jiki duk yayi yaushi suna zaune a palo wayar Suhaila ta fara ƙara, bata ɓata lokaci ba gurin ɗaukar wayar saboda number ne, ɗauka tayi tana karawa a kunne jin muryar Ahmad yasa gabanta yayi muguwar faɗuwa.

Kalamai ya dinga faɗa mata na soyayya inda ita kuma ta ɗaure fuska kamar tana ganin shi ta buga tsaki sannan ta kashe wayar ta tana sakin murmushin jin daɗi, tunowa da tayi an saka ranar ta da Jibril shi ya saka ta ta dawo cikin hayyacin ta.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Jibril yake nan-nan da ita kamar ƙwai, baya so yaji tace zata je wani gurin, yayin da hankalin ta gaba ɗaya yake kan Ahmad shi kuwa tun ranar da suka yi waya ya kuma ji an saka ranar su da Jibril be sake kiran ta ba.

 

Yau take sallah inda gari ya ɗau hayaniya kowa burin shi yayi wanka ya tafi massallaci don kar ya rasa sallar idi.

A ɓangaren gidan su Suhialan ma hakan take saboda kowa ya shirya cikin kayan shi inda matan suka ci hijabi sky blue har ƙasa, dadduma suka ɗauka suka fito daga gida , direct massallaci suka wuce suka yi sallar su, bayan sun gama kuma aka ɗau hotuna sannan suka ɗau hanyar komawa a gida, a nan fa suka haɗu da Suarayya nan hira ta ɓarke don Abba ma tafiya yayi ya barsu abun shi.

Ɗungumowa suka yi suka fito daga harabar massallacin suna tafiya cikin nutsuwa, ga gurin babu lefi har yanzu da ragowar mutane.

Wata motace ta taho da gudun gaske inda tana zuwa gurin da mutane suke da ɗan yawa ta taka wani ubun burki, lokacin kuma yayi dai-dai da ƙarasowar su kusa da su Suhaila inda wani ruwa ya taru a gurin, jikake banjamm, suka zuba musu ruwan a jikin su.

Wani irin uban ashar Farida ta saki tana bin jikin ta da kallo, Suhaila ma kallon jikin ta tayi tana kallon motar, Farida kam bata iya haƙuri ba taje ta buga musu glass kasancewar baƙin glass ne a jikin motar.

Ɗan winning glass ɗin aka yi drivern ya zuro kan shi yana faɗin”Ƴan mata kiyi haƙuri don Allah matsala aka samu”.

Zainab kuwa da duk ranta ya gama ɓaci tace; “Haba malam amma dai kunsan ba kuyiwa kan ku adalci ba ko, ya za ayi gurin nan da dandazon jama’a kuzo kuna gudu a layi kamar kun samu highway tsakani da Allah fa, ku dinga dubawa haba mana”.

Ɗayan da yake gefe a zaune ne ya buɗe murfin motar ya fito yana kallon ta yace; “Kiyi haƙuri munyi kuskure kinji ko, kallon Suhaila yayi da take cikin niqab yace;” Yayar mu kiyi haƙuri mun ɓata ku matsala aka samu”.

Wani irin juyowa tayi ta kalle shi jin muryar da ko tana bacci ne sai ta gane shi.

Lulu eyes ɗin ta ta zuba mai tana kallon shi tayi missing ɗin shi sosai da sosai amma baza ta taɓa nuna mai ba,ballantana ma da yasa ran da za ta buɗe fuskar ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button