HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Har Surayya za tayi magana don ta gane Ahmad ɗin tayi saurin riƙe mata hannu sannan tace; “Ba komai mun gode”.

Juyawa tayi zata tafi yayi saurin tsayar da ita da faɗin”Haba matar Jibril nan da zuwa sati uku, kina tunanin bazan iya gane muryar ki bane, Allah ya baki haƙuri ba faɗa me ya kawo gaba kuma, ai shikenan mun haɗe ranar biki to tunda ba a son yi mun magana”.

Irin yanayin da ta tsinci kanta a ciki ɓata lokaci ne wajen faɗar shi don ba ƙaramun faɗuwa gabanta yayi ba.

Gaba tayi ba tare ta sake magana ba idon ta na cikowa da ƙwalla.

Bayan ta su Farida suka bi ba tare da sun sake magana ba.

Tunda ta koma gida ta kasa nutsuwa haka zalika shima Ahmad ɗin don ya riga da ya haƙura tunda Jibril take so.

Haka kwanaki suka cigaba da tafiya ana ta shirye-shirye ita da Kausar kuwa ba a cewa komai don komai tare suke yi, ga Surayya kuma aminiya.

Tun biki saura sati ɗaya Fatima ta duro daga kaduna, bayan kwana uku kuwa gida ya sake ɗinkewa ƴan uwa suka cika gidan, kai harma yafi auren ta na farko.

Wannan karan dai Ammi ta kwanatar da hankalin ta ana ta abun arziƙi da ita babu wani rigima, ko don Abba ya ɗan bata saki ɗaya ne Oho.. ????????

Amarya taci gyara, an gyare ta tsaf duk wasu magunguna masu kyau anyi mata su musamman na sanyi ma, gyaran jiki kuwa ba a magana sai glowing take kamar ba ita ba duk ta canza, amma fa kana kallon ta kasan tana cikin damuwa ba kaɗan ba.

Walima kaɗai dama suka yi za su yi sai ɗan abunda ba a rasa ba.

Ana gobe walima mutanen abuja suka iso inda suka sauka a gidan wan Daddy nan fa gida ya ɗauka aka yi ta tsokanar ango.

A nan kuma Daddy da Ahmad suka haɗu be wani nuna akwai wani abu a tsakanin su ba ya tsugana har ƙasa ya gaishe shi ya gaida Ammi sannan ya rungume Jibril yana kiran ango ango.

Kallon wan Daddy yayi yace; “Abba ka ga yadda ango ya canza ko, ana ramewa shi har wani ƙiba ma naga yayi wallahi”.

Dariya Abba yayi yace; “Ga alama na gani kam”.

Daddy da ya gama ƙuluwa da abunda Ahmad yayi yace; “Yaya wai me wannan ɗan iskan yaron yake yi a gidan nan ne?, tun a bikin Abubakar na ganshi me yake yi har yanzu?”

“Dakata mun Umar dama inason mu zauna da kai bayan bikin Jibril, yaron nan a gida na yake ba a gidan ka ba don haka babu ruwan ka da shi, sannan kuma duk wannan baƙin ran naka da ka kasa ajiye shi zan saka dole ka ajiye tunda naga har yanzu da sauran ka baka gama sanin inda yake maka ciwo ba, ina da meeting tabbas bayan auren nan”.

“Kai kuma Jibril wallahi ko da wasa naji ance wani abu ya faru tsakanin ka da Ahmad sai ran ka yayi masifar ɓaci saboda baka da ɗan uwa irin shi duk duniyar nan, na faɗa maka kasan halin da kake ciki, ka godewa Allah ma da ya baka ɗan uwa irin shi”.

“To Abba in sha Allahu zq a kiyaye”.

Haka aka cigaba da shirye-shirye cikin farin ciki kai baka ce akwai wani abu ba, amma fa kowa da abunda yake ƙasan ranshi.

Bayan anyi walima ana gobe ɗaurin aure suna zaune a ɗakin su Suhaila Jibril ya kira ta suka gama wayar su, bayan sun yi sallama ta jefar da wayar ba tare da kashe ba tana ƙuncin rai.

Surayya ce ta kalle ta tace; “Me ya faru ne, wai me yasa kike yin irin haka ne, bawan Allahn nan fa ke kika ce kina son shi ba dole za ayi miki ba, tunda kika tashi kike ƙunci kin san baki son shi me yasa zaki aure shi, kar dai kije a mai-mai ta abunda ya faru a baya ki zo kina danasani kamar yadda uncle Habib yake cikin danasani, duk da yayi aure amma har yanzu complain yake, saboda bata mai biyayya kamar yadda kika mai, sai abunda take so shi take yi, to kingani da ki zo kina danasani gwara kawai ki san halin da kike ciki”.

Deep breath ta sauke tace ; “Bawai bana son shi bane Surayya, A’a ina son shi sannan kuma inajin tausayin Ahmad sosai sosai wallahi kuma shima ina son shi kowa abun dubawa ne a cikin su, amma yanzu gaskiya Ahmad yana bani tausayi sosai bashi da kowa, babu wanda ya tsaya mai, har mahaifiyar shi ta zaɓi farin cikin Jibril a kan nashi, to kin gani, shi kuma Jibril saboda halarcin da yayi mun bazan taɓa iya cewa bazan aure shi ba, amma kuma hankali na yana kan Ahmad”.

“To ai shikenan tunda kin kasa sanin wanda kike so a cikin su har yanzu sai kiyi haƙuri ki dena mana ƙunci malama”.

Jibril da ya gama jin hirar su jikin shi yayi sanyi sosai, ya ajiye wayar, ya haɗa kanshi da gwiwa yana jin ƙwalla na cika mishi ido.

Haka ya wuni ranar babu wani walwalar arziƙi a tattare da shi.

Shi kuwa Ahmad duk da yana cikin damuwa be fasa sabgar gaban shi ba, a ranar ne kuma yasan Suhaila bazawara ce yayi mamaki sosai don ko a kamarni bata yi kama da bazarawa ba duk da kana kallon ta zaka san babbace ba yarinya ba.

Washegari da safe kowa ya tashi ya fara shiri za a tafi gurin ɗaurin aure, inda Angon babu wani walwalar arziƙi a tare da shi.

Haɗuwa suka yi da Kausar zata shige cikin gida ya riƙo hannun ta ya jata zuwa wani ɗan lungu, kallon ta yayi yace; “Tambayar ki zanyi ki kuma bani amsa”.

Gyaɗa mai kai tayi don bata ga alamun wasa a tattare da shi ba.

“Dama Suhaila tana son ya Ahmad?”.

Jin tambayar tayi kamar saukar aradu, saurin ɗaga mai kai tayi saboda yadda ya tsare ta a gurin.

Sakin ta yayi tayi gaba, cusa hannun shi yayi cikin gashin kan shi yace; “Damn it Suhaila, me yasa zaki so shi? Me yasa?”

Fita yayi a gurin ya koma cikin gida yaje ɗakin Abba ya same shi, sun yi kusan 30 minutes a ɗakin sannan suka fito.

Da misalin ƙarfe 2:30 aka ɗaura Auren *Suhaila Muhammad* da *Ahmad Umar meshadda* wanda ɗumbin jama’a suka halarci ɗaurin auren…

********

_*Ma’asalam, Fadma Ahmad*_

 

[8/22, 8:46 AM] Ya Umar: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure*

*Page7️⃣3️⃣to7️⃣4️⃣*

 

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Abin Da Musulmi Zai ce Idan ya zo yabon wani Musulmi:*

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Idan har daya daga cikinku ba makawa sai ya yabi abokinsa, to ya ce; Ina zaton wane – Allah dai Shi ne makiyayinsa, Mai yi masa hisabi, kuma ni ba na tsarkake kowa ga Allah – ina zato shi kaza-da-kaza ne, idan dai ya san hakan game da shi.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*Sorry for the late update abubuwane suka mun yawa kwana biyu*

 

_*You surprise me*_

 

 

Mutane ne suka ji abun wani iri musamman ma na cikin massallacin, shi kuwa Ahmad ji yayi komai ya dena tafiyar mai dai-dai, ɗan sunkuyar da kai yayi ya cewa Abba”Anya kuwa ba a samu matsala ba, suna na fa ya kira”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button