HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Jinjina mai kai kawai Abba yayi ba tare da yayi magana ba, nan aka bada sadaki dubu ɗari aka ƙarasa addu’a kowa ga watse, tunda ya fito mutane suke mai barka-barka.

Shi kuwa Jibril abokanan shi na can kaduna sun kasa gane ya abun yake faruwa a haka, a iya sanin su bikin shi ne yanzu kuma ya koma na wan shi to me ya faru kenan.

Haka dai kowa ya tafi gida da magana a ranshi amma babu damar tambaya close friend ɗin shi ne ma ya faɗa Musu abunda ya faru.

A ɓangaren gidan su Suhaila kuwa sai hidima akeyi ana ta jiran angwaye su ƙaraso amma shiru har sai after asur tukunna suka shigo gidan inda aka fara raɗeraɗin sunan Ahmad aka ji ba na Jibril ba, Jibril dai yazo gidan akaci abinci aka sha amma Ahmad ko kaɗan be je ba sai ma kanshi da yake mai ciwo saboda ya kasa gane abunda ya faru sam.

Suhaila kuwa tunda ta ji an faɗi maganar nan gabanta yake faɗuwa amma babu damar ta tambaya ko tayi magana, da yamma ne ma da akayi zancen kai amarya suka ce a bari tukunna akwai abunda za su yi solving zuwa washegari ko kuma ɗayan washegari. Haka nan dai aka bari amma fa ita hankalin ta be kwanta ba har dare saboda tayi ta kiran Jibril be ɗaga ba haka ma Kausar tunda ta tafi da safe bata dawo ba.

 

A can gidan su Ahmad kuwa taro aka haɗa shi sosai don harda su Umman su Zainab aka haɗo and other close relatives, kowa yayi zuru-zuru da ido kawai jiran Abba suke suji me zai faɗa musu.

Abba ne yayi gyaran murya sannan ya kalli Jibril yace; “Buɗe mana taro da addu’a”.

Ɗagowa yayi ya kalle shi sai kuma ya sunkuyar da kanshi, a hankali ya fara buɗe musu taron duk jikin shi a sanyaye.

Bayan ya buɗe taron Abba ya kalli Daddy yace ; “Umar dama nayi niyar haɗa wannan taron saboda kai, to sai kuma Jibril shima ya ƙara ɓullo da wani abun wanda dole ne a zauna a warware wa jama’a su fahimta da kyau yadda ya kamata, amma duk da haka ta kanka zan fara. Meye dalilin ka na korar ɗan ka Ahmad a gida shekaru kusan shida da suka wuce? wanda yazo daga bayan nan ma ka ƙara da cewa ko ganin shi baka son yi ya tafi can ya shiga duniya”.

Shiru Daddy yayi ba tare da yayi magana ba.

Abba ne ya sake cewa”Kaifa muke sauraro”.

“Yaya tundai abunda ya faru tsakanin shi da ƴar gidan Rukayya ne”.

“Shine da bayan shi babu wani abun kuma?”

“Eh babu, sai kuma kwanakin baya da muka sake kama shi da matar da Jibril zai aura wacce ka aurawa Ahmad ɗin a yau”.

“To, to naji, amma ka gyara zancen ka wacce ɗan uwan sa ya aura mai ita kenan, don ba dole akayi mai ba shi yazo ya sameni ya sanar da ni kan cewar ya barwa Ahmad ɗin, amma kafin muzo wannan zancen bari mu fara da matsalar ka tukunna”.

“Umar, ka saurare ni da kyau, bayan wannan abun ya faru bance maka komai ya wuce ba iye, asa musali ma yayi mata faɗen kai ba mai iya yafe mai bane ballan tana kuma hakan be faru ba, kasan sahihin abunda ya faru ne? What if kuma haɗawa akayi kuma? Me zaka ce mai idan ka gano gaskiya? yanzu Umar yaron nan idan be lalace ba yaje ya lalace kuma fa? tunda yace baya son Zainabu dole ne sai ya aure ta, baka san idan ya aure ta baya sonta ba duk abunda ya faru lefin ka ne ba, sannan kuma daga baya yace maka zai aure ta duk don komai ya wuce amma baka bashi dama ba”.

“Amma yay….

” Dakata mun bangama magana ba Umar, kenan haka yana nuni da har yanzu wannan ƙiyayyar bata bar ranka ba kenan? ka manta abunda inna ta faɗa maka kafin ta rasu kenan, ko dan ita baka yi kara ba, wani irin haƙuri ne Kulthum batayi da kai ba? wallahi idan wata matar ce ko kaɗan baza ta ɗau wannan abun ba, ita yanzu ba abunda abokiyar zamanta ta nema a gurin ta bane yasa ta kasa yada ƴaƴan ta, Aisha ko tana nuna muku wani banbanci ne? ”

Saurin girgiza mai kai tayi tana ƙasa da kanta.

” Uhmm kaji ko? To yanzu mai kake yi kenan? wanda kake nunawa son da nuna mai yafi ɗan uwan shi da fifita shi akan ɗan uwan shi, sanna kasa ya raina shi yau gashj ya barmai wadda yake so yake ji kuma bazai iya rayuwa da ita ba, sai kace me ummm?”

Sunkuyar da kai Daddy yayi ba tare da yayi magana ba.

” To wallahi ka kiyayi kan ka sannan kuma ka haɗa kan ƴaƴan ka idan ba haka ba zaka ji kunya a nan gaba, ni ba ruwa na da shiga harkar mata kuma bani da wani strong evidence amma ka sani wata rana gaskiya za tayi halin ta, ƴaƴa nawa ne suke shaye-shaye harkar mata luwaɗi kuma da sanin iyayen su amma sunyi haƙuri, to ka godewa Allah sannan kuma kasan halin da kake ciki ka gyara iyalin ka abunda zance maka kenan, bayan haka bani buƙatar wani bayanin ka don wannan ba hujja bace na wulaƙanta da halin ko ikula da kake wa Ahmad, yaro me tarbiyya da haƙuri”.

“Na gama wannan maganar kuma, Jibril na dawo kanka, yau nasan kowa a wajen ɗaurin auren nan yaji sunan Ahmad wanda bashi bane angon hakan ya faru ne da yardar ɗan uwan shi, jiya da yamma ina zaune yazo ya same ni a ɗaki akan ya fasa auren ita Suhailan shi a lallai ya barma Ahmad amma fa yana son ta, na tambaye shi meye dalili sai yace mun ai ita yarinyar Ahmad take so bashi ba, kawai dai tana la’kari da shi ya fara sonta idan ta zaɓi Ahmad kamar tayi mai butulci ne, kuma ko anyi auren hankalin ta zai zama yana kan Ahmad ɗin shiyasa ya yanke wannan hukuncin, nayi-nayi da shi ya sake tunani yace mun ai kawai ya haƙura kuma baya so na faɗa maka karma nayi zancen da kowa ballantana ma a hana hakan faruwa, to kundai ji yadda aka yi kuma ya sanar mun da kaima kana sonta Ahmad shiyasa ma na yarda aka ɗaura auren”.

Kowa shiru yayi ba tare da yace a ba, sai Zainab dake gefe tana ta kuka don ta san duk gurun babu sa’anta don haka baza tayi magana ba, Umman ta ce ta miƙe tsaye tace ; “To ni kuma ƴa ta yaya za ayi da ita kenan? Ahmad ne fa ya lalata ta kuma dole shi zai aure ta gaskiya yaya baka mun adalci ba wallahi”.

Ta ƙarashe maganar tana sauke numfashi tsabar masifa.

Abba ne yace; ” dakata Rukayya kin san ni ba Umar bane kuma bazan ɗauki wanan iskancin naki ba, da kike cewa ya lalata ta a ina ya lalata tan ummm? Sannan kuma namiji mijin mace huɗu ne sai ta nemi soyayyar ta a gurin Ahmad idan yana sonta ya aure ta idan kuma baya sonta ni bazan mishi dole ba”.

Daddy ne yace ; “Amma fa yaya gaskiya kana ɗaurewa yaron nan gidi fa, ai duk sai ya raina mutane gaskiya”.

“Oho ku kuka sani bani da lokacin ku, kun ji ko don bazan goyi bayan rashin gaskiya ba, nasan dai irin tarbiyar da muka bawa yaran mu, da zai raina ka da tuntuni yayi hakan”.

Zainab ce ta saki wani uban kuka tana ihu, da gudu ta tashi ta bar gurin itama Umman ta ta rufa mata baya.

Taɓe baki Abba yayi ya kalli babban ɗan shi wanda aka ɗaurawa aure kafin sallah yace ya rufe musu taro da addu’a.

Addu’a yayi musu aka shafa sannan kowa ya watse ana maganganu masu jin daɗi nayi masu baƙin ciki nayi.

Bayan an fita waje Ahmad yayi saurin riƙo hannun Jibril yaja shi gefe, duk da yana cikin farin cikin samun Suhaila amma son zuciyar shi be kai nan ba, beso Jibril ɗin yayi hakan ba.

Kallon Jibril ɗin yayi yace; “Me yasa ka aikata hakan bayan kana sonta? wallahi da zuciya ɗaya na bar maka ita saboda tana sonka Jibril me yasa zaka sadaukar mun da Suhaila?”

Ɗan murmushi yayi me ciwo yace; “Saboda kai take so shiyasa nayi hakan kuma nasan ko munyi aure baza ta taɓa mantawa da kai ba, shiyasa kawai nayi hakan,kuma kasan kai kowa yake so ko a family ne ni kuwa ko oho, ko da yaushe kai kake ƙwace mun duk abunda na mallaka ko nake son na mallaka, me nayiwa mutane ne? ka gaya mun abunda zanyi kowa yaso ni”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button