HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Dafa kafaɗar shi Ahmad yayi yace ; “Ba wanda ya tsane ka, kowa da irin farin jinin shi Jibril sannan kuma dama can kai ba me shiga mutane bane, baka saba da mutane ba shiyasa amma ba wai don an tsane ka bane, ka fahimta? ka sakewa mutane kowa ya zama naka zaka ga yadda mutane za su so ka, sannan kuma na gode sosai da bani Suhaila da kayi wallahi bazan taɓa mantawa ba kuma na maka alƙawarin kula da ita”.

Rungume shi yayi kamar zai maida shi jikin shi, shima Jibril ya rungume Ahmad yace ; “Yaya am sorry for everything, thank you”.

“Ni baka mun komai ba Jibril, Allah ya haɗa ka da wacce take son ka duniya da lahira, Amin ya amsa mai da shi sannan suka bar wajen cikin farin ciki.

Shi kuwa Daddy babu abunda ya ragu a ranshi na tsanar Ahmad da yayi sai zazzaga bala’i yake yi yana cika yana batsewa shi kaɗai.

Koda Jibril yaje gurin Abba sai bala’i yake mishi wai kan me yasa zai bar mai Suhaila, yayi-yayi mai bayani amma ya kasa ganewa sam.

A gidan su Suhaila kuwa hankalin ta duk a tashe yake su Surayya da Fatima suna ta kwantar mata da hankali, ana cikin haka ne Jibril ya kira ta jikin ta yana rawa ta ɗaga ta kara a kunnen ta.

“Hello nayi ta kiran ka baka ɗauka ba me yasa? me ya faru? wani magana naji da gaske ne ko kuwa?”

“Suhaila duk abunda kika ji da gaske ne, saboda nasan Ya Ahmad kike so shiyasa kawai na haƙura na bar miki shi, so kiyi haƙuri don Allah, kuma tun jiya Abba ya sanar da Abbu komai bayan an ɗaura auren amma yace kada ya sanar da ke a cikin jama’a shiyasa be faɗa miki ba”.

“Wa ya gaya maka ina son shi ni bana son shi idan banda tsanar shi babu abunda yake raina kuma bazan taɓa mantawa da abunda yayi ba”.

“Suhaila naji abunda kika faɗa ranar bikin Abubakar fa, sannan kuma shekarnjiya duk abunda kuka tattauna keda Surayya duk a kenne na ne so please ki dena damun kan ki, sannan kuma koda baki son shi, shi yana son ki zai kula da ke ballantana kuma kina sonshi sai dai idan baki sani ba, so daga yau babu abunda yake tsakani na dake sai a matsayin matar wa na na ɗauke ki, fatan alheri a rayuwar ki nagode sosai da sosai Allah yasa ki samu farin cikin da kika rasa a baya,sai anjima”.

Be jira ta bakin ta ba ya kashe wayar yana sakin kuka me cin zuciya.

Itama kunkan tayi kuma bana komai bane sai na tausayin shi don tasan daurewa yayi kawai. Shi kuwa Ahmad ko kiran ta beyi ba, don yace sai ta nuna mai tana sonshi ta kuma dena mai duk wani faleƙen banza, a cewar shi sai ya rama abunda tayi mai.

Ni kuwa nace lallai Ahmad ta ka same ta ko. ????????

Da ƙyar Suhaila ta dena kuka har sai da Ammi taci mata tukunna, washegari kuma aka zo da motoci guda huɗu aka ɗau amarya aka kaita gidan Abba sai kuka take yi, kuma ba kukan komai bane sai maganganun da Ja’afar ya faɗa mata na baza ta taɓa jin daɗin aure ba kuma yayi mata wannan alƙawarin sai ya tozarta ta, gashi tana bala’in tsoranshi duk don ta ƙi auren shi, sai da Umman sheka taci mai tukunna sannan ya rabu da ita.

Cikin mutuntawa suka karɓi amarya aka sauke ta a wani part da yake cikin gidan inda su Ummi suka sauka, babu wanda yakai Ummi farin ciki ranar bakin ta har kunne sai ɗauki take yi yau burin ta ya cika, Kausar kuwa kamar ta meda ta ciki haka take ji.

Bayan ƴan kai amarya sun tafi Ummi ta shigo cikin ɗakin ta same ta har yanzu bata dena kuka ba, zama tayi kusa da ita tace; “Daughter me akayi miki ne sai kuka kike yi haka? ko har yanzu missing ɗin Abban ne don ace mun da ƙyar kika sake shi aka saki a mota”.

Ummi ta ƙarashe maganar tana dariya.

Rumgume ta tayi ta buɗe fuskar ta ta share mata hawaye sannan ta zuba mata abincin da aka shigo da shi ta fara ɗebowa a hankali zata kai bakin ta.

Saurin riƙe hannun ta tayi ta karɓi cokalin don ko da wasa bata jin Ammi ta taɓa yi mata haka shiyasa taji abun wani banbarakwai.

“A’a Ummi ki bari zanci da kaina, nagode sosai”.

“To ai shikenan daughter bari na barki kar na takura miki ga akwatunan ki nan idan kin gama kiyi wanka sai ki kwanta ki huta ko, Allah ya miki albarka”.

Amin ta amsa mata dashi sannan ta cigaba da cin abincin bayan ta gama tayi wanka ta saka wata riga mara nauyi sannan ta ɗau mayafin ta ta yafa ta kwanta bacci abunta don ta gaji sosai ba na wasa ba.

Ummi ce zaune a palo ta sa aka kira mata Jibril, bayan ya shigo sun gaisa ta fara godiyar abunda yayiwa ɗan uwanshi don taji daɗi sosai.

Tashi yayi ya runguma ta yace; “Allah ya kiyaye ace Ummi nace take mun godiya kan abunda ban fi ƙarfin shi ba don Allah ki bari, sannan kuma kiyi haƙuri akan abunda ya faru a baya nayi tunanin ba kya so na ne kin fison Ya Ahmad”.

“Haba Jibril ya zaka ce haka, banfi son kowa ba duk ina son ku don haka ka bari kaji ko”.

Gyaɗa mata kai yayi ya ƙara shigewa jikin ta yana kuka.

Bayan kamar ƙarfe shaɗaya kowa ya kwanta bacci, Ahmad ya shigo cikin part ɗin nasu kamar wani ɓarawo, ya buɗe ɗakin da Suhaila take ciki, turus yayi ganin Kausar a gefan ta sai bacci suke hankalin su a kwance.

Naɗe hannun shi yayi a ƙirji yana kallon ta, murmushi yayi yace; “Silly girl har yanzu bata bar bacci da wannan abun ba”.

A hankali ya taka ya zauna saitin da take ya warware mayafin a hankali ya koma kan pillow amma babu damar zare shi gaba ɗaya saboda ta kwanta a kan shi.

“Ko zafi bata ji” sai kuma ya kalli Ac ɗankin yaga basu kunna ba.

A hankali ya kai bakin shi cikin kunne ta yayi whispering “Azizateey”. Amma bata motsa ba tsabar baccin da yake kanta ga kuma gajiya, daɗa whispering yayi amma bata motsa ba.

Hannun sa yasa saman girar ta ya shafa girar yace “Ki tashi kiga mijin ki ya biyo dare don ya ganki”.

Kamar a mafarki taji maganan nashi amma bata motsa ba ta daɗa gyara kwanciyar harda kamo hannun shi.

“Malama sakar mun hannu na” yayi whispering cikin kunnen ta.

Saurin buɗe idon ta tayi tana zuba su cikin nashi idon, wani irin yunƙura tayi zata tashi yayi saurin maida ta yace; “Shhhhh ba wani abu nazo yi ba nazo ganin fuskar mata na ne kawai, so karki mun ihu ballantana ki tashi Kausar don cewa zanyi ke kika kirani nazo.

Kallon shi tayi tana wani haɗe rai” ka tafi please kaji ko bama son damuwa inajin bacci”.

“Idan anaso na tafi a mun goodnight kiss kinji ko sai na tafi”.

Wani kullo ta watsa mai sannan ta mayar da idon ta rufe. Jin kanshi a saman cikin, ya kwanta yasa ta buɗe ido.

“Ya Ahmad please ka tafi mene hakan?”

“Har sai kin mun abunda nace sannan zan tafi”.

Jin Kausar ta motsa yasa tayi saurin tashi, shi kuma ya bar jikin ta yana kallon ta, saurin yi mai peck tayi a baki tace;”Oya go, go kafin ta tashi ka rufa mun asiri please”.

Dariya yayi ya tashi yana ɗaga mata hannu ya fita a ɗakin.

Murmishi tayi tana lumshe ido , sai jin ƙarar buɗe ƙofa ta ƙara yi tana buɗe ido ta ƙara ganin shi, murmushi ya mata yace; “Good night Azizateey bye”.

Ɗaga mai hannun tayi alamar bye, sannan ya rufe ƙofar ya tafi, murmushi ta ƙara yi sannan ta koma bacci.

Bayan sati ɗaya suka fara shirin tafiya can gidan su na abuja inda Suhaila da Ahmad har yanzu ba abunda ya shiga tsakanin su shine me binta dama kuma shima tunda yaga wulaƙancin yayi yawa ya rabu da ita yasan idan suka je gidan su, su kaɗai duk zata sauke komai ma.

Yau kam sai shirin tafiya suke inda Suhaila tuni taje gida sunyi sallama, Abba kuma ya jawa Daddy kunne kan cewar ko da wasa kar yaji ance ya ƙara korar Ahmad a gidan shi, Zainab kuwa kamar za tayi hauka don bada ita za a koma ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button