ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Ki faɗawa Ammi ma ki nemi shawarar ta itama ko?
” Ahan in sha Allah. Ma’asalam”.
“Bissalam……..
*******
*_Hihihihi Suhaila Suhaila????_*
*_Ohhhhh!!! i don’t have to say it_*
*_Follow me on wattpad@cynosure3,drop a comment and vote please….._*
_*Assalama alaikum*_????????
*Faɗma Ahmad*✍️
*????????SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*page* 5️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
*~We are bearer’s of so golden pen????~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*
_*Habib 2 and the crisis*_….
Suhaila ta daɗe a inda take tana juya maganar da Surayya ta sanar da ita. Ta ina ma zata fara idan ya kira me zata faɗa mishi, ta san dai Surayya baza ta taɓa cutar da ita ba, kuma idan da ace yana da wasu halaye da ta sanar da ita, kuma baza ta taɓa yarda ta amsa mishi ba ballantana ma har ta kai ga sanar da ita.
Haka dai tayi ta tunani har lokacin sallah yayi.
Bayan ta idar da sallah ne ta yanke shawarar kiran fatima taji ko sunyi nisa sosai daga nan sai ta sanar da ita, don ji take baza ta iya bari har sai ta isa gida ba, gudun kar ya kira ta kuma bata san me zata ce mai ba.
“Assalama alaikum”.
“Wa alaikum Salam, Suhaila ya dai nace lafiya dai ko?
” Yes lafiya lau wallahi, Amma akwai maganar da zan sanar da ke please ki bani shawara yanzu”.
“To ina jin ki Suhaila”.
“Ina Uncle ɗin Surayya, wanda jiya naje gaida shi a gurin convocation”.
“Uhmm ina jin ki me ya faru da shi?
” Cewa yayi wai yana so na shine nake tunanin idan ya kira ni a waya wacce amsa zan bashi”.
“Hmm Allah ya shirya ki dai wallahi, ki ce mai go to hell kawai”.
“Haba ya Fatima don Allah fa”.
“To Suhaila idan banda abunki, abunda ake nema ya samu har ki tsaya kina sanya ma”.
“Am just scared wallahi, tunda ta faɗa mun sai naji hankali na sam be kwanta da abun ba wallahi”.
“Anya kuwa baki da aljanu Suhaila?
Sai da Suhaila ta tunzuro baki gaba kamar Fatima na kallon ta kafin ta ce” Ni wallahi lafiya ta lau babu abunda yake damu na, kawai naji be yi mun bane”.
“To ai shikenan sai ki yanke duk hukuncin da yayi miki, kuma dama ba shawara kike nema ba kin bugo ne kawai ki bani labari”.
“To shikenan bari zanyi istikara mu gani, abunda Allah yayi ai shikenan”.
“Okk ki gaida Ammi”
“Zata ji. Kunyi nisa ne? Kun kai ina yanzu?
” Hmm sai da kika gama faɗar buƙatar ki tukunna. Gamu a zariya mun kusa shiga Kaduna”.
“Ayya ki gaida mun babies ɗina please”.
“Ahan, ma’asalam”.
“Bissalam”.
*****
After Suhaila tayi sallar isha’i ta shiga gurin Ammi don sanar da ita halin da ake ciki nan ta same ta itama akan prayer mat daga gani bada daɗe da idar da sallah ba.
“Ammi barka da dare”.
“Barka dai, ya aka yi?
Sai da Suhaila ta tattaro duk wata nutsuwar ta, ta sunkuyar da kai ƙasa kamar me neman gafara kafin ta fara magana a hankali.
” Ammi dama Surayya ce ta kira ni ɗazu take ce mun wai akwai wani ƙanin maman ta da yazo taron mu na jiya shine ya ce ayi mun magana, zai zo ya ganni”.
“Tofa! Ikon Allah, ni kuma kinga ban ganshi ba wallahi, amma ai babu komai idan yazo munga yana yin shi ko”.
“To Ammi dama cewa nayi bari na sanar da ke”.
“Ai kuwa kin kyauta sosai, Allah ya muku albarka”.
******
Habib tunda ya koma gida ya ke tunanin ta inda zai fara kiran Suhaila da ya ɗakko wayar zai yi dealing sai kuma ya mayar aljihu, duk ya bi ya wani rikice kamar wani wanda zai yi magana da ƴar governor ko kuma president…
_Ni kuwa nace ko dai tayi mai kwarjini ne ba kamar irin ƴan matan da ya saba kulawa ba_.
Yanzu ma zaune yake akan 1 seater kujera a cikin ɗakin da ko da yaushe idan yazo a nan yake sauka, waya ce riƙe a hanun shi sai juyawa yake yana tunanin da me zai fara idan ya kira ta. Sai dai ya sauke dogon numfashi kafin ya danna kiran nata.
Suhaila tana zaune a bakin gadon su tana aiki a system kiran shi ya shigo wayar ta.
A hankali ta ɗaga kanta tare da kallon screen ɗin wayar nan ta ga unknown number amma kuma through caller ɗin ta sai ta rubuta mata Habib Mansur.
Ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi, ita bata san me yasa idan ta tuna da zancen Habib ɗin gabanta yake faɗuwa ba. Itama sai da ta sauke numfashi wanda yafi nashi ma kafin ta ɗaga wayar.
“Salama alaikum”.
Cikin sanyayyar murya ta amsa da “Wa alaikum salam”.
“Kin wuni lafiya?
” Lafiya lau Alhamdullilah, ya aiki?
“Lafiya lau wallahi, ammmm nace ba, Habib ne uncle ɗin Surayya”.
“Ayya, ai na gane mun yi magana da ita Surayyan ɗazu da rana”.
“To Masha Allah, amma naji daɗi sosai da ta rigani sanar da ke”.
“Ayya babu komai ai”.
Ɗan shiru suka yi kamar 5 seconds basu ce komai ba har sai da ta cire wayar a kunnen ta tana tunani ko wayar katsewa tayi ashe shima shiru yayi kamar yadda tayi shirun itama.
“Hello! Habib ya sake faɗa a karo na biyu.
” Inajin ka”.
“Da gaske nake ba wasa ba, don ni bana so ma a ja abun wallahi. Da fatan dai zan karɓu babu wanda ya riga ni ko?
” Uhmm babu wanda ya riga ka, amma plss zanyi istikara kaima kaje kayi sai muga abunda Allah ya ajiye mana”.
Ɗan shiru yayi yana tunani cikin ranshi kafin yace mata “To shikenan babu komai in sha Allahu zanyi hakan, Allah ya tabbatar mana da alheri”.
“Amin ya Allah, sai anjima”. Ta faɗa tana ƙatse wayar.
“Kai amma wannan yarinyar da tsirfa take, ni yaushe rabo na da yin wani istikara”.
Data ya kunna ya ɗakko application na azkar a nan ne ya gano addu’ar sannan ya tayar da haddar da akayi tun ana zuwa islamiyya may be ma tun be fi 18 ba zuwa 20,don su yawancin maza da sun kai shekarun gama secodary to tare fa za a dena zuwa da islamiyya su gani suke kamar sun girma da shiga aji.
_Ni kuwa nace ka ga ko yanzu Suhaila ta temaka, ka yayyafa wa hardar da ta kwanta ruwa don ya taso ta_
Daren ranar kuwa haka Habib yayi raka’ar shi biyu haɗe da yin addu’ar istikara, itama kuma Suhaila ana ta ɓangaren haka ne.
Sai da suka yi kwana biyu suna yin haka, sunyi sau biyu-biyu kenan.
Shi dai Suhail ji yayi son ta yana ƙara shigar shi while ita kuma Suhaila bata jin komai, ita dai gata nan, ta dena jin ta tsani abun sannan kuma yanzu gabanta ya dena faɗuwa.
Bayan sati ɗaya Habib yazo suka gaisa da Ammi sannan kuma suka ƙara fahimtar juna da Suhaila, a nan ne kuma yake sanar da ita ai washegari zai wuce Kaduna.
Bayan tafiyar Habib Ammi ta tayar da ɓallin wani irin aiki shi Habib ɗin yake yi, nan Suhaila take sanar da ita ai yanzu a kasuwa yake, kuma political science ya karanta a nan A.B.U zariya ana sa ran samun aiki nan kusa, dan ma yanayin ƙasar tamu ce sai wanda yake da hanya tukunna da shi ake damawa.
Buɗar bakin Ammi sai cewa tayi”Ina! gaskiya bana jin wannan abu zai yiwu, au wai dama ba aikin gomnati yake ba?
“A’a Ammi me zai hana, ai a hakan ma yana samu, tunda gashi har mutar kanshi yana da ita”.
“Hmm Suhaila kenan baza ki gane abunda nake ji miki ba,ki je ki sake tunani gaskiya don ni ganin shi ma da nayi sai naji gaba ɗaya jiki na yayi sanyi be yi mun ba sam”.
“A’a Ammi don Allah kar ki ce haka, mu dai kawai mu yi ta addu’a Allah ya zaɓi abunda yafi alkhairi”.
“To ai shikenan, Amin”.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda su Suhaila har sun kai project nasu kuma Alhamdullilah shima B suka samu, yanzu kuma an fara registration na N.Y.S.C don haka tuni har sunje sunyi abun su, jira suke kawai a fara posting, fatan su ma Allah yasa sune fast batch.