ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Cikin maganar ta da take fita da ƙyar tace; “Ya Ahmad ka tafi ka barni bazan iya tafiya ba, gwara kai da sauran ƙarfin ka kuma za su iya ganin mu a koda yaushe kuma ka ga dajin nan za a iya samun mucize wallahi, kar wani abu ya same ka saboda ni, don ni nasan mutuwa zanyi”.
“Shhhh” ya faɗa yana ƙara ƙanƙame ta haɗe da kissing kanta.
“Ba abunda zai faru, nayi going through abunda yafi wannan ma, so karki damu we will be fine, kidai kawai ki daure mu bar gurin nan ko yaya ne na gaji bazan iya ɗaukan ki ba, please, idan kika barni yaya zanyi don Allah ki tashi, I know my Azizateyy zaki iya abunda yafi wannan ma so please ki tashi mu tafi ummm, may be yanzu 12 yayi da sunga asuba ya kawo kai za su dena bin mu please”.
Kallon shi tayi ta girgiza mai kai duk da bata ganin shi yadda ya kamata, amma haka ta lalubashi tayi kissing nashi tace; “Am sorry for everything, ka tafi kawai ya Ahmad, i love you, and you are my reall cynosure, i love you so very much, the very first day i meet you i know you have to be the one, i can smell you all over even when we are not together, my husband my cynosure, my hanoon, my Azizeyy, my habibi, my ruhalbi, uhibuka kaseeran-kaseeran, am going to miss you, and am sorry for everything just leave, but i still hate you”. Ta faɗa tana saka forehead ɗin ta a saman haɓar shi, rungune ta ya ƙara yi ya ɗaga ta ba tare da yace mata komai ba ya fara janta a hankali amma ta kasa fara tafiya kuma shima da ƙyar yake tafiya ganin hasken fitilar na ƙara doso su yasa ya tsaya, ya zame ɗankwalin kanta da ya rage mata ya ɗaure mata baki ya tsugunar da ita ya kamo ƙafar da ƙarfi ya ja ta don alamar targaɗe ne, wani irin ihu ta saki amma babu ƙara, nan da nan kuma ƙafar tayi ƙara, janta yayi da ƙarfi suka bar gurin ta fara takawa ba tare da ta shirya ba haka yayi ta janta tana kuka ga uban ƙulli da ya rufe mata baki babu damar ihu, su kuwa da suka gano su suka fara bin bayan su amma duk da haka basu cin musu ba……
Su Daddy kuwa suna shiga garin Abuja ko gida basu isa ba suka nufi asibiti, kafin suje Ummi ta mayarwa da Kausar kayan jikin ta sannan ta fito da ita da ƙyar, shima Jibril da ƙyar ya jawo Daddy amma sai da aka temaka mai, shigar da su ciki akayi inda Kausar har yanzu bata san inda kanta yake ba, saboda ta firgita sosai.
Ni kuwa nace tun ba ayi me duka ba……….
*******
_*Ma’asalam Faɗmah Ahmad*_
[8/25, 9:52 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page7️⃣7️⃣to7️⃣8️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta hhhh a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*_The escape_*
Daddy aka fara shigwar emergency inda likitoci suka fara bashi temakwan gaggawa, Kausar kuma wasu nurses ne suka karɓe ta aka kaita ɗaki sannan suka kira likita tazo da dubuta ta saka mata drip don ƙarfin jikin ta ya dawo sannan ta kalli Ummi tace ; “Hajiya ki dena damuwa ba abunda ya samu ƴar ki, she will be fine zuwa gobe da safe, amma ki dinga mata addu’a don naga kamar tana firgita sosai”.
Jinjina mata kai Ummi tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuwa Jibril yana gefe yayi wani fiƙi-fiƙi da ido kamar an jijjaga ɓera a buta har wani rama yayi na ɗan lokacin.
Shima Daddy ba a daɗe ba aka fito da shi bayan an gama mai ɗinki a kan nashi aka kawo shi ɗakin hutu, nan fa Ummi da Jibril suka rankaya yawan dubo jikin shi.
Bayan sun fito Jibril yace bari yaje ya shigar da cass ɗin su yaya Ahmad ko Allah zai sa a samu wani abun, haka kuwa akayi yaje police station ya sanar da su duk abunda ya faru, suka ce za su yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ceto rayuka biyun.
Ummi kuwa tunda ta dawo gurin Kausar tayi Alwala take ta sallah tana addu’a Allah ya bayyanar da su Ahmad ya bawa Daddy da Kausar lafiya.
A ɓangaren su Ahmad kuwa gajiya suka yi suka zauna a jikin wata bishiya suna hutawa, sai maida numfashi suke ba ƙaƙƙautawa, ba irin Suhaila da take jin numafashin ta kamar zai ɗauke ga wani rawa da jikin ta yake tsabar sanyi, daga gani asuba ta gabato shiyasa wata iska me sanyin gaske take kaɗa ga bishiyun gurin sai hooo, hooo suke fitarwa.
Faɗawa tayi jikin shi tana kiran”Sanyi ya Ahmad zan mutu, wayyo ƙafa ta, ciki na, kai na, innnalillahi wa’inna ilaihi rajiun, allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha”.
Rungume ta yayi yace ; “Ba abunda zai same mu in sha Allahu we are safe, in Allah ya yarda zamu samu temako kinji ko, ki dena cewa zaki mutu”.
“Ya Ahmad baza ka gane abunda nake ji ban……
Bata ƙarasa faɗan abunda zata faɗa ba ta zube a jikin shi sumammiya, jin jikin ta ya sake ya sa ya ɗagota yana shafa fuskar ta haɗe da kiran sunan ta” Suhaila! Suhaila!! “.
Ina bata jin shi, jijjaga ta yayi ya ɗan mari fuskarta, amma duk da haka bata motsa ba, kwantar ta ita yayi ya ɗora hannun shi akan ƙirjin ta yana dannawa amma a banza kamar ma bayi yake ba.
Bakin shi ya ɗora akan nata yana busa mata iska ko zata farfaɗo amma ko gezo, wani irin ɗagota yayi ya rungume ta a jikin yace ; “Wallahi baki isa ki mutu ki barni ba, don Allah ki tashi na roƙe ki don girman wanda ya hallice ki tashi Suhaila, yanzu fa muka fara rayuwa ko ince bamu fara ba ma, amma ki tafi ki barni don Allah ki tashi”.
Ya ƙarashe maganar yana fasa kuka sosai kamar wani ɗan ƙaramun yaro na goye.
Haka yayi ta girgiza ta amma ko kaɗan bata motsi.
“Suhaila ta baki mutu ba, tashi mu cigaba da tafiya mu samo temako don Allah kar ki barni, uhibbuki kaseeran, ma fini ish bidunik, inti hayati, (ina son ki sosai, bazan iya rayuwa idan babu ke ba, ke rayuwa ta ce) don Allah la tatirikini lahali, inti ahla kulla shai’i fi hazzadduniya, fa lausamahtyy, la taruh wa tatirikini lahli please Suhaila na roƙe ki don Allah, inti habibty, wa farhatyy,don Allah ki tashi”.
Ganin bata responding nashi yasa ya tashi da ƙyar ya goya ta ya cigaba da tafi da ƙyar da ƙyar, yayi kusan 30 minutes yana tafiya sannan ya fara hango wasu bukkoki, saboda gari ya fara haske daga can kuma yana hango gidajen ƙasa tsilli-tsilli.
Da ƙyar ya cigaba da tafiya yana ganin tara-tara shima, sai da ya kusa isa jikin wani garken shanu sannan ya zube a gurin shima ya sume.
Sai da gari ya waye tassss wani ɗan ƙaramun bafulatanin yaro yazo zai saki shanu su tafi kiwo ya gansu a zube a gurin kamar matattu, da gudu ya koma ya sanar da iyayen shi abunda ya gani.