HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Da sauri suka ƙaraso gurin suna kallon ikon Allah, nan wasu ma suka fara fitowa, wani ne yace a temake su, wani kuma yace wa ya san daga inda suke, kuma me ya kawosu ƙoyen nasu.

Haka dai suka yi ta mahawara har daga ƙarshe iyayen yaron suka ɗauke su zuwa ɗayar bukkar su, nan aka fara basu temakon gaggawa ana kawo magunguna, Ahmad targaɗe biyu yayi a kafaɗar shi, sai kuma ciwo da yaji a ƙafafun shi duka biyun.

Sai bayan shi da yake ciwo saboda goyon da yayiwa Suhaila.

Itama tana da targaɗe a ƙafa sai kuma zazzaɓi mai zafi da kuma ƙananun ciwuka da ba a rasa ba.

 

Haka bayin Allahn nan suka kula da su na kwana biyu amma cikin su babu wanda ya farfaɗo.

A ɓangarem Ummi kuwa kullum cikin kuka take tana roƙon Allah ya bayyanar mata da su, Kausar kuwa tunda ta farfaɗo take tambayar su, tunda taji ance ba a gansu ba shikenan ta koma wata iri, bata magana, bata komai abinci ma sai Ummi ta ɗura mata, Daddy ma ya farfaɗo ba wanda yake tambaya sai ya Kausar take amma dai basu mata komai ba ko, be lalata mai ƴa ba haka dai yayi ta surutai har sai da Jibril ya faɗa mai abunda ya faru, ya sanar da shi kuma har yanzu ba a ga su Ahmad ba, hankalin shi ya tashi sosai amma sai be nuna musu ba yace Allah ya bayyana su kawai.

 

Ummi ce ta kira can gidan su Suhaila ta sanar da su abunda ya faru, ta kuma gaya Abba.

Irin tashin hankalin da Abbu ya shiga ba maganar shi, Ammi kuwa kamar zata tayi ɗanƙaramun hauka, sai cewa take wai sun siyar mata da ƴa, Farida da mubarak da Fatima kuwa sunyi kuka sunyi kuka har sun gaji, sun Umman sheka ma duk ba a barsu a baya ba.

 

Zainab kuwa ba abunda take sai Allah yasa Suhaila ta mutu Ahmad ya dawo shi kaɗai.

Both Family ɗin babu abunda suke yi sai addu’a dare da rana Allah ya bayyana musu ƴaƴan su, Abbu kuwa har wani ramewa yayi saboda yana son Suhaila ba kaɗan ba, duk cikin ƴaƴan shi babu wacce yake so kamar ta.

 

Kwance suke a kan gadon kara su duka biyun sai dai kowa da nashi gurin, Ahmad ne ya fara buɗe idon shi a hankali yana kallon inda yake, kanshi ne yaji yayi mugun yi mai nauyi ga jikin shi da yake kamar an ɗaure mai shi, da ƙyar ya samu idon ya fara gani da kyau, hankalin shi kuma ya fara dawowa jikin shi, duk ya rame kai baka ce shine Ahmad ɗin New York ba????.

 

Tunowa da abunda ya faru yasa yayi saurin tashi yana bin ɗakin da kallo, da sauri ya yunƙura zai tashi sai kuma ya koma ya zauna saboda jin shi da yayi kamar a ɗaure babu damar motsawa, jikin nashi gaba ɗaya sai a hankali ba irin kafaɗun shi da yake ji kamar ba a jikin ba.

 

Gefan shi ya hango ta amma ya kasa ƙarasawa gurin, inda hankalin shi ya kwanta da yaga tana numfashi, sai kallon ta yake daga ita sai rigar fulani an ɗaura mata zani a kai kanta kuma an rufe mata shi da ƙyallan kayan jikin ta, kamar ko farka shi su kayi suka mata ɗankwali dai.

Yana zaune a haka bafulatanin ya shigo cikin ɗakin, ganin shi ya tashi yasa yayi saurin komawa yana kiran wani da yake jin hausa wanda shi yafi fita cikin gari kiwo a cikin su.

Suna shigowa suka ƙarasa inda yake suna mai sannu.

Ɗago kai yayi shima ya musu sannu yana gaishe su haɗe da yi musu godiya, yayin da ɗayan yake fassara musu, shi kuwa sai kallon ikon Alah yake wai basu jin hausa.

“Masha Allah, mun godewa Allah da yasa ka farfaɗo, wannan wacce kuke tare da ita,itama zuwa anjima ko da dare zata tashi Allah ya baku lafiya, Amma me ya same ku haka har kuka shigo wannan dajin a haka?”

Ɗan murmushi Ahmad yayi saboda shi kanshi wanda yake jin hausan abun dariya ne yadda yake magana.

Basu labari yayi from a to z, inda sukayi ta salati, ɗaya daga cikin su ne yace ; ” Dama daga can kudancin su an fara raɗeraɗin akwai sansanin ƴan fashi a gurin.

Nan dai su kayi ta maida zance, shi kuwa yana gefe amma hankalin shi gaba ɗaya yana kan sahibar shi.

Wani ne yace a barsu su huta, nan aka kawo mai fura me daɗin gaske da fiyo nono, sai tuwan dawa miyar karkashi, gwara ma fura ya santa amma wannan abun shi kam baya jin zai iya ci, ga miyar koriya shar ga uban yauƙi kamar mai.

Furar dai ya ɗauka ya kai baki saboda yadda yake jin yunwa, ga mamakin shi kuma sai yaji tayi mai daɗi, tass ya shanye ba tare da ya rage komai ba ya ajiye ƙwaryar yasha ruwan da suka ajiye mai.

Hamdala yayi ya rufe tuwon ya jashi gefe, matar bafulatanin ce ta shi go ta gaishe shi tayi mai sannu ta duba Suhaila sannan ta fita a ɗakin.

Can da yamma mijin fatsima ya shigo ɗakin don ya sake duba shi, a lokacin ne yake faɗa mai ai shi sunan shi musa maƙocin shi kuma wanda ya kira sunan shi Adamu,, haka dai yayi mai gwaranci Ahmad ɗin dai ya gane me yake nufi.

Kiran Adamu yayi don ya tambayi Ahmad me yasa beci towon ba.

Murmushi yayi yace mai”A’a kuyi haƙuri amma bazan iya ci ba, gwara ɗayan abun fura da nono ko? ”

Gyaɗa mai kai suka yi adamu yace anjima sun nemo mai wani abunda zai ci tunda baya cin tuwan su me daɗin gaske.

Dariya sukayi su duka sannan suka fice a ɗakin.

Ruwa yasa ɗan fulanin ya kawo mishi yayi alwala sannan ya fara jero sallolin da suka wuce shi yana daga zaune.

Bayan ya idar yayi godiya ga Allah, sannan ya musu addu’ar ƙara samun sauƙi.

Bayan yayi sallar isha’i ya samu ya ɗan matsa zuwa kusa da Suhailan yana kallon fuskar ta, har yanzu bakin ta da ragowar kumburi, ga cizon da wannan mutumin yayi mata, runtse ido yayi yana tuna abunda ya faru, duk inda yaga wannan mutumin ba abunda zai hana ya harbe shi, amma sai dai yasan hakan da kamar wuya tunda ko fuskar shi be gani ba, sannan kuma yana mamakin yadda yaji ya kira sunan Suhaila which means ya santa kenan.

Yana zaune suka kawo mai gurasa da balango wanda suka siyo a kasuwar cikin garin.

Karɓa yayi ya ƙara musu godewa sannan ya ajiye a gefe.

Adamu ne yace mai”Kar ka damu zata tashi itama kamar yadda ka tashi, ta samu zazzaɓi ne me zafin gaske sannan ga tsoro da fargaba amma in sha Allahu zata tashi”.

Godiya ya musu suka fice a gurin.

Bayan ya ɗan ci gurasar ba yawa ya sha ruwa sannan ya koma kan gadon shi na kara ya ɗakko ɗan zanin da aka rufa mai ya ƙara mata a kan nata saboda yana ganin yadda take ɗan motsawa alamar tana jin sanyi sosai.

 

 

A ɓangaren su Abbu kuwa hankalin shi be kwanta ba sai da yaje garin Abuja amma ina duk da haka babu koda labarin su ne, haka sukayi ta fafutuka amma a banza don ko police ma sunyi iya yin su amma babu wani labari, kowa jikin shi yayi sanyi, Ummi kuwa koda yaushe cikin kuka take.

Abbu ne yace; ” Kiyi haƙuri hajiya addu’a zamu cigaba da musu in Allah ya yarda za su bayyana da yardar Allah”.

“To Allah yasa, Abban Suhaila amma abun ne abun tsoro yau muna kwana na uku fa amma ko labarin su babu abun ya fara bani tsoro”.

Jibril ne ya rungume ta ya share mata hawaye yace; “Haba Ummin mu, kefa ya kamata ace kina kula da mu kina bamu haƙuri amma sai mune muke dauriyar muke kwantar miki da hankali”.

Kallon shi tayi ta gyaɗa mai kai sannan ta share hawayen ta tana kallon Kausar da babu umm ko Ammamm kawai dai gata nan sai dai ka ga hawaye na bin kuncin ta kawai.

Da misalin ƙarfe 1 na dare Suhaila ta farfaɗo amma sai dai da wani irin mugun zazzaɓi ta tashi, don saboda tsabar sanyi da take ji haƙwaranta har wani haɗewa suke yi.

Kamar daga sama cikin bacci yaji tana kiran sunan shi cikin sarƙewar murya,firgit kuwa ya tashi ya hangota jikin ta sai kyarma yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button