ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Da sauri ya ƙarasa yana ɗago ta yaji jikin wani irin mugun zafi wanda be taɓa ji ba tunda yake, kallon ta kawai yake ba tare da yasan me zaiyi ba, gashi su ba asibiti ba kuma idan ya taso su yanzu me za suyi mai.
“Ya… Ya… Ah..ma..d sanyi zan mutu ka temakeni ka kaini asibiti”.
“Shhh baza ki mutu ba you will be fine”. Ya faɗa yana shafa forehead ɗin ta zuwa Saman gashin ta.
Cire zanin yayi ya zame ƙyalen dake kanta ya janyo ƙwaryar da suka kawo mai ruwa a ciki ya tsoma ɗankwalin nata a ciki, ya fara shafa mata, yana daɗa matsewa amma duk haka akwai zafi sosai sai dai ya rago ba kamar da ba.
Ganin wannan baya working ya rasa ya zai mata, ko yaje ya taso su ne, har yayi hanyar ƙofa zai buɗe ƙofar karar sai kuma ya dawo yana kallon ta sai rawa jikin ta yake yi.
Da sauri ya dawo yace ; “Baza ki mutu ba we will be together ummmm” Ya ƙarashe maganar yana cire rigar jikin shi ya kwanta a kusa da ita ya jawo ta jikin shi ya ƙanƙame ta kamar wani zai ƙwace mai ita, itama ƙanƙame shin tayi tana ƙara shigewa jikin shi kamar za a ƙwace mata shi.
Ɗan kuka take yi na zazzaɓi yayin da shi kuma yake shafa bayan ta yana bata haƙuri, haɗe da ƙara shigewa jikin ta.
Washegari da safe wajen 7 ita ta fara farkawa taji ta jikin mutum ya wani ƙanƙame ta itama ta ƙanƙame shi, kallon innocent face ɗin shi tayi tana sakin murmushi kafin ta ɗan ɗaga kanta don ganin a wani guri suke haka, ganin bukka ce yasa tayi murmushi tana ƙara kallon fuskar shi, motsawa tayi zata tashi, ya ƙara janyota jikin shi, yana ƴan maganganu cikin bacci ba tare da taji me yake cewa ba. A lokacin ne taji a wani irin yanayi take, wani irin kunya ne ya lalluɓe ta ta ƙara shigewa jikin shi don bata jin zata iya tashi a haka, taje ya farka ya ganta.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi hakan ne yasa ya ɗan buɗe idon shi, ita kuma tayi luff kamar bata farka ba, saurin tashi yayi yana runtse ido, kafin ya nemo rigar shi ya saka sannan itama ya saka mata rigar ta, ya ɗaura mata ɗanƙwali ya rufa mata zani sannan ya tashi daga kan gadon karar nata ya koma gefe yanajin wani irin kunya na rufe shi don ma Allah yasa bata farka ba.
Buɗe ƙofar yayi a hankali ya fita yayo alwala sannan yazo yayi sallah, yaje yana taɓa jikin ta a hankali ko da akwai sauran zafi.
********
_*Asalama alaikum, faɗma Ahmad*_
[8/26, 2:56 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Watpad@cynosure*
*Page7️⃣9️⃣to8️⃣0️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Abin Da Musulmi Zai ce Idan ya zo yabon wani Musulmi:*
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Idan har daya daga cikinku ba makawa sai ya yabi abokinsa, to ya ce; Ina zaton wane – Allah dai Shi ne makiyayinsa, Mai yi masa hisabi, kuma ni ba na tsarkake kowa ga Allah – ina zato shi kaza-da-kaza ne, idan dai ya san hakan game da shi.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
_*Forest*_
Ƙasa suka umarci kowa yayi, ai kuwa ba musu duk suka zube a ƙasa jikin su na kyarma. Shi kuwa Ahmad har ya fara tunanin yadda zai yi musu saboda sun shammace su ba kaɗan ba gashi babu damar motsawa don sun saka wa mazan bindiga, Daddy kuwa yana gefe kanshi sai zubar da jini yake, don sosai suka buge shi da ƙasan bindigar. Wani daga cikin su yayi musu nuni da hannu nan suka finciko Suhaila, wani irin faɗuwa gaban ta yayi yayin da Ahmad da Jibril suka ji komai ya tsaya musu ba irin Ahmad ma,ɗaya daga cikin su ne yace; “Kai, shegen, kai amma zaka more wallahi”.
Sai kuma ya fincike mayafin da ke jikin Suhailan, wani irin yunƙura Ahmad yayi, wanda yake bayan shi ya buga mai bindida a kafaɗa tuni ya koma ya durƙusa akan ƙafafun shi, wanda ya fincikewa Suhaila mayafi ne ya saka dariya yace; “Kai amma fa duk da haka bata da wani kaya, akwai hips dai amma babu saman”.
Ya ƙarashe maganar yana pointing chest ɗin ta, ita kuwa Suhaila gabanta sai faɗuwa yake duk tayi experiencing rape case amma idan aka ƙara raping ɗin ta bata san yadda za tayi da rayuwar ta ba.
Janta sukayi, nan ta saki wani uban ihu, tana basu haƙuri, Ummi ma kuka ta fara yi inda Kausar ta kasa magana saboda tsabar yadda ta tsorata saboda bata taɓa ganin abu irin wannan ba, shi kuwa Jibril yama rasa yadda zai yi gashi da tsoron bala’i, Ahmad kuwa tunanin ta inda zai fara kawai yake yi don suna da yawa.
Waɗanda suka fito daga cikin daji ne suka ƙaraso nan suka fara hargagin a basu kuɗi, shiga lalubensu sukayi suka kwashe duk kuɗin dake jikin su suka kuma haɗa da wayoyin su duka ba abunda suka bar musu.
Wani daga cikin su ne, ya finciko Kausar yana shinshinata yace; “Kai Baabaa wannan gaskiya za tayi daɗi, kuma fresh ce daga ganin ba a farke ta a leda ba”.
Wani ihu Suhaila tayi tace; “Don Allah ku rabu da ita wallahi na yarda duk wanda zai yi, yayi da ni amma please kar ku taɓa ta na roƙe ku don Allah, don Allah ba don ni ba please”.
Ahmad da yake durƙushe idon shi yayi ja yace; “Malama ki rufe mana baki ba abunda zai samu ɗaya daga cikin ku”.
Wanda yake gefe tuntuni da beyi magana bane ya ƙaraso ya ɗauke shi da mari, sannan yace; “Ai kuwa yau sai kayi kuka da idanun ka saboda yadda zamuci matar ka, sai kaji duk duniyar nan babu wanda ka tsana sama da ita, a take a gurin nan zaka mata saki uku, saboda yadda zamu mata fata-fata ko moruwa baza ta sake yi ba, ka kalle mu ka gani mu takwas ne kuma kowa sai ya sha gyaran amaryarka”.
Suhaila ce tayi wani irin ƙamewa, don ko daga bacci aka taso ta taji wannan muryar sai ta gane ta ballantana kuma idon ta biyu.
“Ku shigar da su mota waɗannan tunda mun gama da su mun karɓi kuɗi, su jira su kafin mu gama aiki, shi kuma ku kamo mun shi don a gaban shi zamu yi komai kuma babu abunda ya isa yayi wallahi”.
Wani daga cikin su ne yace; “Haka ne don dare be riga yayi ba duk da hanyar ba a fiya bi ba amma wani zubin ƴan iskan ma’ikatan nan suna yawo wallahi”.
“Hakane fa”. Wanda yake kan Ahmad ya faɗa.
Kallon Jibril yayi yace ; “ku gyara parking zuwa gefan titi da kyau ku shiga mota kuyi tsit, kuna motsawa wallahi sai na fasa kan ɗan uwanka”.
Saurin gyaɗa kai yayi sannan ya tashi ya fara ƙoƙarin jan Daddy zuwa cikin mota, Ummi kuwa sai kuka take yi kamar ranta zai fita, tana kiran sunan Ahmad da Suhaila da aka ja su zuwa cikin dajin dake gurin amma ta farko farko, kafin su Shige Ahmad ya juyo ya kalli Jibril yayi mai alama, sunkuyar da kai Jibril yayi, ƙara jadadda mai kai Ahmad yayi kafin aka shige da su.