ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Da sauri ya ƙarasa yana ɗago ta yaji jikin wani irin mugun zafi wanda be taɓa ji ba tunda yake, kallon ta kawai yake ba tare da yasan me zaiyi ba, gashi su ba asibiti ba kuma idan ya taso su yanzu me za suyi mai.
“Ya… Ya… Ah..ma..d sanyi zan mutu ka temakeni ka kaini asibiti”.
“Shhh baza ki mutu ba you will be fine”. Ya faɗa yana shafa forehead ɗin ta zuwa Saman gashin ta.
Cire zanin yayi ya zame ƙyalen dake kanta ya janyo ƙwaryar da suka kawo mai ruwa a ciki ya tsoma ɗankwalin nata a ciki, ya fara shafa mata, yana daɗa matsewa amma duk haka akwai zafi sosai sai dai ya rago ba kamar da ba.
Ganin wannan baya working ya rasa ya zai mata, ko yaje ya taso su ne, har yayi hanyar ƙofa zai buɗe ƙofar karar sai kuma ya dawo yana kallon ta sai rawa jikin ta yake yi.
Da sauri ya dawo yace ; “Baza ki mutu ba we will be together ummmm” Ya ƙarashe maganar yana cire rigar jikin shi ya kwanta a kusa da ita ya jawo ta jikin shi ya ƙanƙame ta kamar wani zai ƙwace mai ita, itama ƙanƙame shin tayi tana ƙara shigewa jikin shi kamar za a ƙwace mata shi.
Ɗan kuka take yi na zazzaɓi yayin da shi kuma yake shafa bayan ta yana bata haƙuri, haɗe da ƙara shigewa jikin ta.
Washegari da safe wajen 7 ita ta fara farkawa taji ta jikin mutum ya wani ƙanƙame ta itama ta ƙanƙame shi, kallon innocent face ɗin shi tayi tana sakin murmushi kafin ta ɗan ɗaga kanta don ganin a wani guri suke haka, ganin bukka ce yasa tayi murmushi tana ƙara kallon fuskar shi, motsawa tayi zata tashi, ya ƙara janyota jikin shi, yana ƴan maganganu cikin bacci ba tare da taji me yake cewa ba. A lokacin ne taji a wani irin yanayi take, wani irin kunya ne ya lalluɓe ta ta ƙara shigewa jikin shi don bata jin zata iya tashi a haka, taje ya farka ya ganta.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi hakan ne yasa ya ɗan buɗe idon shi, ita kuma tayi luff kamar bata farka ba, saurin tashi yayi yana runtse ido, kafin ya nemo rigar shi ya saka sannan itama ya saka mata rigar ta, ya ɗaura mata ɗanƙwali ya rufa mata zani sannan ya tashi daga kan gadon karar nata ya koma gefe yanajin wani irin kunya na rufe shi don ma Allah yasa bata farka ba.
Buɗe ƙofar yayi a hankali ya fita yayo alwala sannan yazo yayi sallah, yaje yana taɓa jikin ta a hankali ko da akwai sauran zafi.
********
_*Asalama alaikum, faɗma Ahmad*_
[8/26, 2:56 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Watpad@cynosure*
*Page7️⃣9️⃣to8️⃣0️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:*
“Allah Almighty has said:
‘The son of Adam denied Me and he had no right to do so. And he reviled Me and he had no right to do so. As for his denying Me, it is his saying: ‘He will not remake me as He made me at first’ (1) – and the initial creation [of him] is no easier for Me than remaking him. As for his reviling Me, it is his saying: ‘Allah has taken to Himself a son,’ while I am the One, the Everlasting Refuge. I begot not nor was I begotten, and there is none comparable to Me.’”
(1) i.e., bring me back to life after death.
[Bukhari (also by an-Nasa’i).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: كَذَّبَنِي ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، وَشَتَمَنِي وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: لَنْ يُعِيدَنِي كَمَا بَدَأَنِي، وَلَيْسَ أَوَّلُ الْخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَيَّ مِنْ إِعَادَتِهِ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا، وَأَنَا الْأَحَدُ الصَّمَدُ، لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لِي كُفُوًا أَحَدٌ رواه البخاري (وكذلك النسائي)
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
_*Home*_
Yana ɗora hannun shi a kan soft skin ɗin ta, a nan take ya ji wani irin shock ya jashi, saurin cire hannun shi yayi yana me runtse idanun shi. Duk da ba wannan ne karo na farko da ya fara taɓa mace ba, amma sai yaji wannan is different, ƙara kai hannun shi yayi a karo na biyu ya ɗan dinga taɓa hannun ta a hankali, ganin shirun da tayi hakan yasa ya ɗan ƙara matsawa kusa da ita ya cigaba da tattaɓa hannun ta, nan da nan idon su ya sarƙe a cikin na juna, wani irin kallon so yake mata, yayin da ita kuma take ji idan babu shi baza ta iya rayuwa ba.
Saurin janye idonta tayi tana ƙoƙarin tashi, yayin da ya kamo kafaɗunta domin ya taya ta tashi zaune tana ɗan riƙe kanta.
“Are you okay?” ya faɗa cikin sanyin murya.
Gyaɗa mai kai tayi alamar “Eh”.
“Je kiyi sallah lokaci ya tafi da yawa”.
Tashi tayi a hankali tana ɗan dafa bango saboda har yanzu bawai ta gama warwarewa gaba ɗaya bane, ganin tana tafiya da ƙyar yasa ya tashi ya kamata, a hankali suka fito waje,sanyin iskar da ya daki fuskanta ne yasa ta lumshe ido.
Ruwa ya zuba mata tayi alwala sannan ya ruƙo hannun ta suka dawo cikin daƙin.
Abunda yayi sallah da shi ya saka mata itama tayi sallah, bayan ta idar sannan tayi azkar ta koma ta ɗan jingina da jikin bango.
Kamar daga sama yaji tace; “Ya jikin naka? Da fatan babu inda yake maka ciwo ko?”.
Girgiza mata kai yayi, kafin yace; “Kefa?”
“Babu ko ina, sai jiri kaɗan”.
Gyaɗa mata kanshi yayi ba tare da yace mata komai ba.
Suna cikin haka sai ga Musa da fatsima sun shigo cikin ɗakin, sannu suka yi musu inda Fatsima take tambayar sunan Suhaila nan take faɗa mata, abun kari aka kawo musu inda suka basu guri don su karya.
Kaɗan ya iya shan kunun tsayamin da suka kawo musu sai ƙosai da yaci guda biyu ya ture,ita kuwa Suhaila ko a jikin ta dama wata muguwar yunwa take ji, sakin jikin ta tayi ta sha sosai, sai da tayi ƙat sannan ta dena ci.
“Dama kin taɓa ci?”
Ya faɗa cikin sanyin murya.
“Eh mana, kai baka taɓa ci bane?”
“Umm to gaskiya ban sani ba, i don’t think na taɓa ci, sai dai ko ina yaro”.
Gyaɗa mai kai tayi ta koma kan abun kwanciyar ta ba tare da ta sake furta ko a ba.
Kamar daga sama taji yace; “Gobe zamu shiga cikin babban garin ƙauyen nan, Allah ya temaka wallet ɗina na jiki na so, id cards ɗina da ATM cards ɗina duk suna ciki, zan ciro kuɗi inyaso zuwa jibi ko gata sai mu hau motar da zata shigar da mu cikin abuja sai mu nemi su Ummi ko”.
Gyaɗa mishi kai tayi ba tare da tace ƙala ba.
Kamar daga sama taji wani bahagon tambayen shi ya daki dodon kunnenta”Suwaye mutanen jiya? because am sure sun sanki sosai tunda har suka ambaci sunan ki”.