HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Oily eyes ɗin ta wanda suka fito waje ta zuba mai a cikin nashi idon. Tabbas abunda yake zarki haka ne ta sansu, tun maganar shi ta farko ta gane muryanshi amma baza ta taɓa iya gayamai ba, tasan da cewa be san rape case ɗin ta ba, so bata son yin maganar ma.

“Ban san su ba, amma wata ƙila su sun sanni”.

Kallon yanayin ta yayi har zai sake jefo mata wata tambayar sai kuma ya basar kawai, zai ajiye tambayoyin shi ba yanzu ba, ya ɗaukarwa kanshi alƙawarin ko su ubanwaye ne sai ya binciko su.

Washegari da wuri suka fita cikin garin dake gaba da rugar tasu inda suka samu wani ƙaramun Atm a gurin 30k kaɗai ya samu, sannan suka dawo gida.

Ganin bata cikin ɗakin yasa ya tambayi yaron Fatsima ko tana ina.

“Suna rafi” ya faɗa cikin fulatancin shi, be gane abunda ya faɗa ba hakanne yasa yaja hannun shi suka je gurin.

Suna zuwa Fatsima tayi mai sannu da zuwa sannan ta basu guri tana kama hannun ɗan nata suka bar wajen.

Kallon shi tayi tace ; “Sannu da zuwa”.

“Yauwa”. ya faɗa yana matsawa kusa da ita.

“Mun samu 30k kawai, zan basu 10k tunda ba a samu da yawa ba, inyaso sai mu shiga cikin gari da 20k,Allah yasa ta ishe mu”.

“Amin” ta amsa mai tana kallon shi.

Kallon ta yayi yaga damuwa ƙarara a cikin idanun ta,gashi ta zama wata sukuku da ita, gaba ɗaya canji ya gani a tattare da ita, bazai iya ganin ta haka ba, hakan ne yasa ya matsa kusa da ita ya rungumota zuwa jikin shi yana kallon yadda ruwan rafin yake tafiya a hankali, shigewa jikin shi tayi tana sakin kuka me cin zuciya ita kaɗai take da masaniyar abunda ke damun ta, wanda a can baya ta manta, amma abun nan da ya faru yasa komai ya dawo mata sabo fil.

“Shhhh”. ya faɗa yana shafo gefan fuskanta, yana da tambayoyi da yawa amma yasan yanzu ba lokacin da zai mata wainnan tambayoyin bane.

Sun ɗauki kusan 30 minutes a haka, jin sanyi-sanyi yana shigar sa yasa ya ɗaga ta cak yana kamo gefan kafaɗar ta suka bar gurin, bayan sun shiga cikin bukkar ya kwantar da ita inda yasaka kanta akan cinyar shi ya zame ɗankwalin kanta yana shafa ɗan madaidaicin baƙin gashin ta wanda ya sakko zuwa ƙasan wuyan ta,cikin mintuna ƙalilan bacci yayi awan gaba da ita, jin ta fara sauke numfashi yasa ya kalle ta nan yaga tayi bacci innocent face ɗin ta ya kalla, a hankali ya saka hannun ya shafa saman lips ɗin ta, yayi alƙawarin duk wani wanda yake da hannu a cikin abunda ya faru sai yayi maganin shi ko waye shi, duk wanda yake da hannu wajen dakushewar farin cikin ta bazai taɓa yafe mai ba.

Haka ya gama tunanin tana me bashi tausayi.

Washegari da safe da wuri suka tashi suka yi wanka suka shirya, inda suka ƙara yiwa su Adamu godiya suka kuma basu 10k, da ƙyar da suɗin goshi suka karɓa wanda da ace sun samu kuɗin da yawa zai iya basu 100k amma hakan be samu ba.

Tafiya sukayi na kamar 20 minutes sannan suka iso asalin cikin garin inda a nan ne suka yi sallama suna ƙara musu godewa.

Tunda suka hau motar take kallon window kamar wacce take kallon titi amma a zahirin gaskiya tunanine fal a cikin ziciyar ta,kula da hakan da yayi ne yasa ya juyo da fuskar ta, ta kalle shi, gira ya ɗaga mata alamar menene, amma sai ta girgiza masa kai alamar babu komai.

Be wani jira abunda zata ce ba ya janyo ta jikin shi yayiwa kanta masauki a chest ɗin shi, babu musu kuwa tayi luf don dama haka take da buƙata.

Sunyi kusan tafiya 40 minutes sannan suka iso wani gari wanda a nan ne za su hau motar da zata shigo da su cikin garin Abuja.

Tunda suka shiga babu wanda yace da ɗan uwanshi ƙala sai bacci da tayi, ganin kanta na lilo yasa ya kwantar da ita akan shoulder ɗin shi.

Tafiyar kusan 4 hours sukayi sannan suka iso cikin Abuja, inda ya tare musu taxi ya sanar da shi inda zai kaisu.

Cikin minutes da basu wuce 30 ba suka shigo area 1 inda me motar yayi parking a gaban wani makeken gida, a hankali ya sakko da ita ya biya kuɗin taxi ɗin sannan ya riƙo hannun ra, tura ƙofar gate ɗin yayi megadi yana ganin hakan yayi saurin miƙewa yana mai kallon mamaki.

“Masha Allah, Allah ya kuɓutar da ku Alhaji” megadin ya faɗa yana me washe bakin shi.

Gyaɗa mai kai Ahmad yayi don ba ko ina ya fiya son yin magana ba.

Direct cikin gidan suka shiga inda sanyin Ac haɗe da wani silent ƙanshi ya daki hancin su.

Kausar dake zaune akan sofa tayi shiru kamar ba ita ba taji sallamar su, wani zabura tayi wanda tunda abun ya faru bata yi wani ƙwaƙwaran motsi irin wannan ba.

Da sauri ta tashi tsaye tana kallon su haɗe da nuna su da hannu.

Ita kam Suhaila bata jira ba ta cire hannun ta a cikin nashi ta ƙarasa da gudu tana rungume Kausar wanda har yanzu akwai ɗan tabon ciwo a bakin ta.

Wani ihu Kausar tayi itama tana rungume ta wanda wannan dalili ne yasa Ummi da take kitchen tana girki tayi saurin leƙowa don ganin abunda ya samu Kausar ɗin.da sauri itama ta taho, tana zuwa ta rungume Ahnad tace ; Allah sarki Ahmad Allah ya kuɓutar mana daku, Allah abun godiya, ya Allah ka ƙara tsare mun zuri’a ta”.

Ta ƙarshe maganar tana sakin kuka me cin zuciya,rungume ta yayi shima yace ; “Haba Ummi ba gamu ba cikin kwanciyar hankali ga kuma lafiya Allah ya bamu sai mu godewa Allah”.

Jibril da yake shigowa cikin palon ne ya tsaya kamar statue yana kallon su sai kuma ya taho da gudu ya rungume Ahmad ƙwalla na zubowa daga cikin idanun shi.

Ummi ce ta kamo hannun Suhaila tace ; “Daughter da fatan babu inda yake miki ciwo ko?”

Gyaɗa mata kai tayi tana faɗawa jikin Ummin.

Nan fa kowa ya shiga farinciki inda aka kammala lunch suka ci, Ahmad sai da ya cika cikin shi tafff saboda ya kwana biyi Beci abinci ba, kafin ya wuce part ɗin su yayi wanka, itama Suhaila wanka tayi ta saka riga da siket na atamfa wanda ya karɓi jikin ta sosai.

Nan fa aka hallara a palo inda Ahmad ya mayar musu da duk abunda ya faru, babu wanda be musu kuka ba, Ummi ma ta sanar da su abunda ya faru da Kausar, wani irin juyowa Suhaila tayi ta kalle ta don tasan experiencing irin wannan abun babu daɗi sam, rungume juna suka yi yayin da Suhaila ta saka kuka tana shafa fuskar Kausar ɗin tana kuma ƙara godewa Allah da yasa babu abunda ya faru da su.

 

Koda Daddy ya fito bece musu komai ba sai Allah ya ƙara kiyaye gaba,inda Ahmad ko a jikin shi don yasan inda ya ajiye Daddyn nashi yanzu.

Daga ɓangaren dangin su Suhaila kuwa washegari 12 a garin Abuja tayi musu don gaba ɗaya suka taho harda Ammi, ta ɗan nuna kulawa ga Suhailan inda Mubarak yake liƙe da ita baya zuwa ko ina ita kuwa Farida wani irin daɗi take ji Allah ya kuɓutar da yayarta a kashi na biyu.

Kwanan su biyu suka koma bayan nan kuma Fatima tazo daga Kaduna ta duba ta, Surayya kuwa bata samu zuwa ba amma kullum suna cikin video call, da kewar junan su.

Bayan sati biyu kome ya warware hakan ne yasa suka fara shirin komawa London inda Ahmad da Suhaila da Kausar da Jibril za su fara zuwa Saudiyya suyi Umara kafin su koma can London ɗin.

Ummi da Daddy ne suka fara tafiya bayan kwana biyu suma jirkin su ya ɗaga zuwa saudiyya. Sunyi ibada sosai inda Suhaila bata da wani addu’a sai Allah ya yaye mata abunda ke damun ta ya basu zaman lafiya me ɗorewa ita da mijin ta, ya kuma shirya mata Ammin ta don bata so ta tafi a wannan halin nata.

 

Satin su biyu suka koma London inda har yanzu Suhaila bata dawo dai-dai ba ko da yaushe cikin damuwa take, shi kuwa Ahmad yana ankare da ita, burin shi kawai su isa London ya wuce da ita can America gidan su yadda zai kula da ita da kyau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button