HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ita da Habib kuwa babu lefi sun saba sosai don yanzu soyyayar su suke yi babu lefi.

Ita kuwa Ammi yanzu ma ta fara daru don cewa tayi Suhaila baza ta Auri Habib ba saboda ba sa’an auren ta bane.

Amma fa ba wanda yake kula ta abubuwan su suke yi kawai ita da Abbun ta don sun ce ma turowa za su yi ayi maganar kawo sadaki da kuma saka ranar biki.

Wannan kenan….

****

Suhaila ce zaune a palon su ita kaɗai gidan yayi shiru da alama duk mutanen gidan basa nan sai ita kaɗai.

Ƙarar wayar ta dake gefan ta shi ya dawo da ita cikin hankalin ta dumin kuwa ta ba da hankalin ta gaba ɗaya kan laptop ɗin ta tana kallon wani korean film me suna moorim school.

“Hello ya Fatima”.

“Na’am Suhaila ya kike? Ya su Ammi?

” Duk lafiya lau wallahi, yasu Nihla?

“Suna lafiya lau wallahi. Hmmm Farida ta kira ni ai jiya ta faɗa mun duk abunda yake faruwa a gidan, shine baki gaya mun ba ko?

” Hmm bana son tayar miki da hankali ne kawai wallahi shiyasa, amma ba wani abu bane ba fa kawai dai rigimar Ammi ne kuma kin san in sha Allah we will sort things out umm kar ki damu”.

“Amma gaskiya Ammi bata kyauta ba sam, ana neman mijin nan, kuma yanzu gashi yazo sai wani complain take wai baya aikin gomnati da dai sauran su”.

“Idan banda abun Ammi ai ɗan kasuwa ma idan ya kafu yafi wani me aikin gomnatin wallahi”.

“Hmm kedai ki bari kawai sai dai addu’a, Amma kin sani sarai idan rigimar Ammi ya tashi, kuma dama na faɗa miki idan na samo miji sai tace be yi mata ba”.

“To ai shikenan, zan kira Abbu na faɗa mai kar ya biye mata duk abunda za tayi”.

“Ina faɗa mai ai kullum.ki gaida babies ɗi na please “.

“Okkk in sha Allah, Assslama alaikum”.

“Wa alaikum salam”.

*****

Habib ne zaune a sit ɗin driver while wani matashin saurayi wanda nake tunanin za su yi age ɗaya kuma a gefan shi.

“Mustapha wallahi ina sonta sosai da sosai, nifa na matsu ayi maganar auren nan Allah kuwa”.

“Hmmm ai ni kaina ina mamakin yadda wannan ustaziyar yarinyar ta gigita ka, duk ƴan matan ka amma wai ita zaka aura”.

“Hmm ai dama haka Allah yake lamarin shi, ni kuma a haka na ganta kuma nake son ta”.

“Ni baka taɓa nuna mun hotan ta ba ma, kullum cikin niqab nake ganin ta a wayar ka”.

“Ai ina da hotunan ta a system saboda irin ku shiyasa ban sa a waya ta ba”.

“Sai dai idan na shiga gida na kalli kaya na”.

“Hmm Allah ya kyauta tau”.

“Amin”.

**********

Bayan sati ɗaya….

Tun daga wajen gidan kafin na kai ga ƙarasawa nake jiyo muryar hajiya Asiya sai zazzaga bala’i take kamar zata tashi gidan, duk da dai sai dai hayaniyar amma bana jin abunda take faɗa sosai sai da na kai ga shiga cikin gidan.

“Wallahi baka isa ba, ni ƴata baza ta auri wannan abun ba! Gwara ma ka kira su ka sanar da su karma su zo”.

Abbu da yake zaune akan 1 sitter ko kollon inda take be yi ba ya cigaba da cin abincij shi.

Ganin be kula ta ba yasa ta ɗauke abincin a gaban shi tare da faɗin”Ai ni na dafa abincin! tunda baza ka kula ni ba ka maidani mahaukaciya wallahi baza ka ci ba”.

Tashi yayi tsam zai shiga cikin ɗaki ta tare mai hanya tana girgiza.

“Wallahi baka isa ba ka tsaya muyi magana kawai!!!

Kallon ta yayi cikin ɓacin rai amma ina bata ma san yana yi ba ƙara karkaɗa jiki take.

” Asiya ki bani hanya na wuce don Allah tunda ke duk wani kwanciyar hankali ba kya son shi”.

“Ai Suhailan ni na haife ta ba kai ba don haka sai abunda nake so za tayi, ni wannan yaron be yi mun ba sam wallahi”.

“To Asiya ya kike so ayi? kin dame ta akan ta fitar da miji, yanzu gashi ta fitar kince be yi ba”.

“Eh haka na ce saboda be yin bane”.

“Don Allah ki bani hanya na wuce”.

“Babu inda zaka shiga wallahi”.

Ta faɗa tana ƙara tare bakin ƙofar.

Kallon ta kawai ya tsaya yi don ya rasa abunda zai yi mata ya huce.

Hanyar fita daga gidan ya nufa, nan ma ta ƙara tare mai hanya tare da faɗin babu inda zai je.

Shi kuwa da takaici ya kama shi ya kwaɗa mata mari tare da ture ta gefe zai shige cikin ɗakin.

Suhaila da Farida da suke cikin ɗaki suna kuka suka yi saurin fitowa daga ɗakin kamar an jefo su.

Da gudu tayi gurin Ammin nasu tana ɗaga ta amma ta ture ta gefe.

“Kar ki taɓa ni ki tafi can gurin uban ki dama kin fi son shi”.

“Ammi ba haka bane don Allah ku bari don Allah”.

Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.

“Abbu ka kira su Habib ka sanar musu suyi haƙuri don Allah, wallahi bana son wannan tashin hankalin sam Abbu don Allah”.

“Wallahi na rantse da girman Allah bata isa ba Suhaila! Ai ba duk abunda take so zamu yi ba a cikin gidan na, fisabilillahi ace duk abunda take so shi muke yi a cikin gidan nan, wannan karan kam ko zata bar gidan wallahi bazan fasa abunda nayi niyya ba”.

Ya faɗa yana banging ƙofar ɗakin su…

Suhaila ce ta juya gurin Ammin ta tace”Ammi wallahi idan ta ni ne na haƙura saboda bana son tashin hankali. Amma don Allah kiyi haƙuri duk saboda ni hakan ta faru”.

Ita dai Ammi bata sake cewa komai ba itama ta shige cikin ɗakin…….

******

 

_*Tofa! Tirƙashi yau Ammin mu ta sha mari*_

_*Who is ready for the next page? ya ɗaga hannu please, amma fa ba a nan ba a fagen comment*_

_*I love u all*_????????

*faɗma Ahmad*✍️

 

*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page6️⃣to7️⃣*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~We are bearer’s of so golden pen????~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*

_*You have to know the secret*_…..

 

Bayan Ammi ta shiga ɗaki Farida ta kama hannun Suhaila suka koma cikin ɗakin su, cikin faɗaɗa ta ce”Haba ya Suhaila you have to wake up mana! ki farka daga baccin da kike, do you think a haka zaki cigaba da rayuwar ki? A haka zaki yi building gidan ki? Sai yaushe zaki yi auren idan baki yi yanzu ba ummm ya Suhaila? Haka zaki cigaba da biyewa Ammi kina mata biyyaya amma bata gani sam, am tired of wa’inan abubuwan gaskiya, na gaji da yin shiru. Sannan kuma kar ki sake shiga tsakanin Abba da Ammi ba ruwan ki, ki barshi ya ɗau matakin da ya ɗauka kawai”.

Suhaila tana zaune a kan gode sai kuka take idanun ta sunyi jawur kamar an kaɗa gauta, veins ɗin kanta gaba ɗaya sun tashi, babu abunda kake ji a ɗakin sai shashsheƙar kukanta da ajiyar zuciya.

With her red eyes ta kalli Farida ta ce”Then tell me Farida ya zanyi? Me kike so na ce mata ummm? I should argue her ko me kike nufi?

“Just stick to your position, kar ki shiga sabgar su ki barta da Abbu he will handle her ummm”.

Farida ta faɗa tana rungume Suhaila a jikin ta wanda har yanzu bata dena kukan ba.

Zamewa tayi daga kafaɗar Farida ta tashi tsaye sai zagaye ɗakin take,sai da tayi kamar kusan 5 round kafin ta tsaya ta riƙe kanta tana rubbing kamar zata cire goshin ta.

Kallon Farida tayi ta ce”Ya zanyi wa Ammi Farida? She always hide my secret, tace may be ma shiyasa bazan yi aure ba kuma bayan bata bari kowa ya san da hakan ba, tace nauyin jini ne da ni kamar dangin Abba, ta takura dole sai na samo mijn aure yanzu kuma gashi na samu tace be yi mata ba, ya zanyi ne? Ina zan saka rayuwa ta? Wayyo Allah na ka kawo mun ɗauki, ya Allah ka sauƙaƙa mun”.

Farida ce ta matsa kusa da ita ta share mata hawayen fuskar ta, ta ƙara janyo ta jikin ta ta rungume ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button