HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Aikuwa yana yin zafi ya sheƙo da ruwan zafin kasancewar babu inda zai zuba tunda bata tara cup ba hakanne yasa ya biyu ta jikin drawern sai sakin ƙara tayi kawai.

Saurin juyowa yayi don ganin abunda ya faru da sauri ya ƙarasa ya riƙo ta yana kallon ƙafar ta inda ruwan coffe ɗin ya zubar mata.

Kamota yayi ya zaunar da ita akan kujerar dining ɗin gurin wanda gurin zaman mutum biyu ne kawai.

Ɗayar kujerar yaja ya zauna ya kalle ta yace ; “Azizateyy!”.

Voice ɗin da yayi amfani da shi wajen kiran ta Azizateyyn shi yasa ta ɗago lumsassun idanun ta ta kalle shi.

Bece mata komai ba ya ya buɗe firdge ya ɗakko ƙanƙara ya ɗora mata akai.

Lumshe ido tayi saboda yadda sanyin ya shiga jikin ta, tattare gurin yayi ya goge sannan ya haɗa sabon coffee ɗin ya ɗakko babban cup ya tara a gurin ai kuwa yana tafasa ya zubo da ruwan, murmushi tayi tana faɗin “Haka akeyi kenan?”.

“Eh haka akeyi, village girl”. Ya faɗa yana murmushi.

Saurin kallon shi tayi don bata zata maganar da tayi ya fito ba, ɗan tunzura bakin ta gaba tayi tace; “Allah ni ba villager bace”.

Hancin ta yaja yace ; “oya lunch is ready gyara zama kici abinci”.
Juyowa tayi ta kalle shi tana sakin murmushi, tana son shi sosai da sosai ta san zai kula da ita zai bata duk wani jin daɗin rayuwa, zai share mata hawayen ta zai tsaya mata, amma still bata yi shiryawar da za su fara irin wannan soyayyar ba amma tana roƙon Allah ya kawo mata lokacin da zata kula da shi ta bashi full kulawanta.

 

Nigeria, kano.

Zainab tunda taji zancen dawowar su Ahmad hankalin ta ya tashi sosai, take ji inama ace zata iya binsu amma ina babu dama bata isa ba.Kullun cikin kuka take babu dare babu rana wai ita a kaita gurin yaya Ahmad ita ya Ahmad take so.

Ganin hakan ne yasa maman ta ta fara musu wani shiri kan za su je gurin wani malami sai an fitar da Suhaila a gidan Ahmad kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Zainab, da haka ta kwantar mata da hankali.

Abba kuwa kullum sai ya kira su yaji ya suke.

Suhaila ma haka tana kiran Abbu taji yadda kowa yake haka zalika ma tana kiran Ammi amma sai dai tafi kiran Abbun nata.

New york

A ɓangaren Suhaila kuwa yau kwanan su biyar amma ko kaɗan bata bawa Ahmad fuskar da zai taɓa ta ba,bata so ko kusa da ita yazo sai dai Kuma suna zaune lafiya zaije aiki ya dawo ya tarar ta gyara ko ina ta kuma yi mishi girki.

Yauma kamar kullun bayan ya dawo daga aiki yayi wanka sunci abinci suka shiga ɗaki don kwantawa bacci wata doguwar riga mara nauyi ta ɗakko ta saka a jikin ta yayin da shi kuma yake zaune a bakin gado daga shi sai 3 quarter sai faman aiki yake a computer, warmer ta kunna musu sannan ta haye gado tace mai sai da safe, bece mata komai ba ya cigaba da aikin shi bayan ya kammalla, ya sauka ƙasa ya ɗakko musu ruwan sha ya ajiye akan bed side ko wani a cikin su zai sha da daddare.

Kashe wutar ɗakin yayi sannan ya kunna musu bed lamp, matsawa yayi can kusa da ita kuma duk tana jin shi, ita kanta tasan abunda take mai be kama ta ba amma kuma she is not ready yet.

Matsawa ya daɗa yi ya jawota jikin shi ya rungume ta yana sauke numfashi.

Bakin shi ya kai saitin kunnenta, cikin sanyin muryar shi yace ; “Nasan idon ki biyu ba bacci kike ba, me yasa kike mun haka ne? Me ya kike nesanta kanki dani? Me nayi miki? Ko har yanzu fushi kike dani? Ko kuma wani abu ke damun ki? wallahi duk abunda kika ji na faɗawa Zainab ba haka bane ki fahimce ni please”.

Lumshe idon ta tayi saboda yadda take jin wani iri a jikin ta, she needs him too amma baza ta iya ba sam.

Jin ta mai shiru yasa ya juyowa ta ta fuskance shi kuma haryanzu idon ta a rufe suke.

Peck yayi mata a forehead ɗin ta yace; “Wallahi i love you with all my heart, ba widow ba ko menene i don’t care ni ke nake so ba wani abu naki ba, wallahi duk abunda kike so a duniyar nan zan miki shi duk wani farin ciki da kike nema zan baki shi”.

Sam baza ta iya ɗaukan kalaman nashi ba hakan ne yasa ta buɗe idonta da suka ɗan canza kala ta zuba su a cikin nashi idon.

Gyaɗa mata kai yayi, sannan yasa hannun shi ya goge hawayen da ya zubo mata yanzu.

“Menene?”

Bata bashi amsa ba ta shige cikin jikin shi tana ƙara sakin wani kukan kamar wata ƙaramar yarinya.

“Shhhh”. ya faɗa yana shafa bayanta.

“Am sorry, am sorry ya Ahmad amma bazan iya ba, bazan iya kasancewa da kai ba yanzu ka yafe ni kar ka dinga fushi dani ballantana mala’iku su tsine mun please na roƙe ka”.

Lumshe idon shi yayi yana jin sonta na ƙara shiga cikin jikin shi, shi kanshi yasan akwai abunda yake damun ta amma taƙi ta sanar da shi zai bata duk lokacin da take buƙata bazai taɓa yi mata dole ba.

Kissing gashin kanta yayi yace ; “Ki ɗauki duk lokacin da kike buƙata zan jira ki domin bazan taɓa miki dole ba, amma please za mu dinga bacci a haka?”

Gyaɗa mai kai tayi tana me ƙara ƙanƙame shi.

 

Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa tsakanin Ahmad da Suhaila baya taɓa mata dole, amma kuma tana kula da shi duk wani abu za tayi mai haka ma idan aiki yayi mai zafi tana ƙoƙarin taya shi bincike.

 

Zaune take akan kujera sai faman washe baki take tana kallon waya, sai da na matsa kusa da ita sannan naga ashe video call take yi da Surayya.

Daga cen ɓangren Surayya tace ; “Wai har yanzu baki da ciki ne? biki kusan wata huɗu amma shiru muke ji, ko dai shi ɗin be iya harka bane?”

Dariya kawai Suhaila tayi tace ;” Uhmm Allah ya shirya ki, ni kam ai kin fi ƙarfi na, ina zan sani ƴar rainin hankali, kedai kiji da Isyakun ki, koda yaushe ana neman abun faranta mai”.

“Aff ki tsaya wasa karuwan garin nan su ƙwace miki shi wallahi”.

Dummmm taji gabanta ya faɗi dumin kuwa bata taɓa kawo haka a ranta ba.

“Surayya hakan zai iya faruwa fa ko?”

“Sosai ma kuwa yarinya”.

“Na shiga uku, bafa abunda ya taɓa shiga tsakanina da shi wallahi”.

Wani irin buɗe baki Surayya tayi tana fito da idanu waje tace “Kin gani ba caɓɓ kina da aiki kuwa, to bari kiji yadda zaki jawo hankalin shi zuwa kanki, don masu jajayen fatar nan ƴan iska ne wallahi.

Kafin Suhaila tayi magana Surayya tace” Kalle ni ki gani, kina ji na? ”

Ta ƙarashe maganar bakin ta na rawa tsabar son tayi magana.

Gyaɗa mata kai Suhaila tayi tana kallon ta.

 

” Namiji alwaya loves yarinta,so act like that don ki ja hankalin shi.
2..Ko wani namiji yana son voice ɗin matar shi, make good use of it, ki karya murya kiyi fari sai ya kalle ki wallahi.
3..He loves to be respected always remember that, zai ƙara miki daraja a idon shi.
4..nasan ki dai you are hilarious idan ba yanzu ki ƙara canzawa ba, so maza loves kind of fun, keep it up.
5..learn to be appropriative of every thing he does, express it to him, make efforts to show how much you appreciate, zaki ga har wani langwaɓar dakai yake tsabar jin daɗi.
6..kin san duk wani favorite food ɗin shi lokaci bayan lokaci ki dinga mai, kina ji ba?”

Gyaɗa mata kai Suhaila tayi tana jin duk abunda take faɗa yana shiga jikin ta sai dai matsalar ba ga shi bane itace da matsalar amma duk da haka za tayi trying.

Katse mata tunanin tayi da ta cigaba da magana.

” 7..He is a man always be his woman to your full potential, ki bashi duk wata kulawa ki biya mai buƙatar shi.
8..kince yana son waƙa, so, dedicate a time for just that, kiyi mai har sai yayi bacci, ke idan da dama ma ki haɗa harda rawa.
9..You are more than a woman to him, maintain that, prove it.
10..Namiji loves shagwaɓa, and he gave you full license of that idan kina da ciki, so you better conceive ki dena wani tunani idan ma kina yi. Ga 10 tips nan na baki idan har kika yi amfani da su kika kyautata mai, believe me babu wacce da zata ƙwace miki shi, na barki lafiya my Habibi ya kusa dawo wa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button