ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Bers Safa: Innas safa wal marwata min sha’a’irillah
Abda’u bima bada’al lahu bihi.
Hakika Dutdsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)”.
Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi.
Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai da ya hango dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce;
اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar.
Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma.
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، اَللهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدُهُ، وَهَزَمَ اْلأَحْزَابُ وَحْدَهُ.
Bers la Ka’aba: La ilha illallahu, allahu akbar, La ilaha illal lahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay’in kadirun. La ilaha illal lahu wahdahu. Anjaza wa’adahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata a gare shi, kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.
Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin addu’a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
_*There Home*_
Basu wani daɗe ba suka sauka a garin na New york, taxi suka ɗauka ya kaisu masaukin Ahmad ɗin.
Tunda suka shiga take kallon palon, ko ina zane, babu bangon da babu zane a jikin shi wani ya yi kyau sosai wani kuma beyi kyau ba wani rose flowers ne wani kuma sun flower.
Babban palo ne wanda ya ji furnitures masu shegen kyan gaske komai na gurin white and blue ne kama daga kujera curtain, rug da dai sauran kayan amfani, daga gefe kuma can wani ɗan guri ne wanda aka ƙawata shi da carbinet na kitchen masu kyan gaske gata fara ƙal, duk wani tools and equipment ɗin gurin red ne hakan ne yasa suka ƙara fito fa kyawun drawern gurin, idan tace gurin beyi kyau ba ta zabga ƙarya.
Ba tare da ya ce mata komai ba ya kama hannun ta suka bi wani ƙaramin stairs wanda ya kasance wooden ne, suna hawa sai gasu a wani ɗan corridor ƙofofi biyu ne a gurin, ta farko ya buɗe ya shigar da ita ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya koma ya kwaso musu kayan su, ganin bata cikin good mood yasa ya shige cikin toilet ba tare da yace mata ƙala ba, wanka yayi sosai saboda sai da ya jiƙa kanshi a cikin bathtube sannan ya dawo ya sakarwa kanshi shower yana tunanin meye matsalar matar tashi ne, anya kuwa babu wani babban al’amari da take ɓoye mai.
Haka ya gama tunanin shi ya fito daga toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugun shi wajen kayan shi ya nufa inda yana zugewa wani haɗaɗɗen guri ya bayyana kayan shi ne a cikin gurin, gurin kaya daban sai takalma daga gefe ɗayan gurin kuma agoguna ne da wasu manya-manya sarƙoƙin wuya na maza wanda ya ɗan daɗe be za su ba.
Suhaila kuwa kallon ikon Allah ta tsaya yi, dumin kuwa abun ya bata mamaki duk waƴan nan kayan na mutun ɗaya ne shi kaɗai.
Wata white riga ya ɗakko me ɗan shara-shara ya saka a jikin shi gaba ɗaya gaban rigar a buɗe yake, white trouser ya janyo ya saka a jikin shi sannan ya fito ya mayar da gurin ya rufe, jakar kayan shi ya ɗakko ya zaro turarukan shi ya jere su a kan mudubin gurin sannan ya ɗauki guda ɗaya a ciki ya feshe jikin shi.
Kallon shi ya mayar gare ta kafin cikin sanyi murya yace mata “Ki tashi kiyi wanka sai ki sakko ƙasa muci abinci”.
Kai kawai ta gyaɗa mai sannan ta miƙe tsaye, ko kaɗan bata son abunda take mai amma kuma she is not ready yet don haka baza ta iya mai duk romantic abu ba wanda zai sa taja hankalin shi zuwa gare ta amma tasan soon komai zai yi dai-dai.
Bayan ta fito daga wanka ta shafa kayan shafar shi da ya fito da su da fesa turare sannan ta jawo jakarta ta fara fiddo da kayan ta a ciki, wani lace ta ɗakko wanda yaji ɗinkin doguwar riga ta saka a jikin ta sai kallon kanta take ta cikin mudubi, duk ta rame komai nata ya faɗa har ƙirjin ta wanda dama ba wani abun arziƙi bane a gurin.
Inda taga ya buɗe nan ta shiga ta jera kayan ta sannan ta buɗe wani ɗan guri da ta gani a cikin gurin ta saka journal ɗin ta da duk inda zata je da shi take tafiya.
Wata sarƙar shi da ta tayi mata kyau sosai ta ɗauka ta saka a wuyan ta zallan chen ne babu komai a jiki amma kuma tayi kyau sosai da sosai.
Fitowa tayi ta tsaya a gaban mudubi ta ɗaura ɗankwalin ta, tayi kyau babu lefi, tana gamawa ta fice a ɗakin ta sauka ƙasa tun kafin ta ƙaraso take jin ƙamshi na tashi, hango shi tayi ya sanya apron a jikin shi sai aikin girki yake, bata wani yi ƙasa a gwiwa ba ta bi inda yake, tana ƙarasowa be ko kalle ta ba yace ; “Kinyi kyau sosai”.
Gyaɗa mai kai tayi tace ; ” Thanks” sannan ta nufi inda coffe maker yake kunnawa tayi ta zuba komai ta nemo two cups ta ajiye, sai dai abunda bata sani ba shine, wannan ba irin na gidan Ummi bane domin kuwa yana yi zai sheƙo da ruwan ba tare da ya jira ba.
Aikuwa yana yin zafi ya sheƙo da ruwan zafin kasancewar babu inda zai zuba tunda bata tara cup ba hakanne yasa ya biyu ta jikin drawern sai sakin ƙara tayi kawai.
Saurin juyowa yayi don ganin abunda ya faru da sauri ya ƙarasa ya riƙo ta yana kallon ƙafar ta inda ruwan coffe ɗin ya zubar mata.
Kamota yayi ya zaunar da ita akan kujerar dining ɗin gurin wanda gurin zaman mutum biyu ne kawai.
Ɗayar kujerar yaja ya zauna ya kalle ta yace ; “Azizateyy!”.
Voice ɗin da yayi amfani da shi wajen kiran ta Azizateyyn shi yasa ta ɗago lumsassun idanun ta ta kalle shi.
Bece mata komai ba ya ya buɗe firdge ya ɗakko ƙanƙara ya ɗora mata akai.
Lumshe ido tayi saboda yadda sanyin ya shiga jikin ta, tattare gurin yayi ya goge sannan ya haɗa sabon coffee ɗin ya ɗakko babban cup ya tara a gurin ai kuwa yana tafasa ya zubo da ruwan, murmushi tayi tana faɗin “Haka akeyi kenan?”.
“Eh haka akeyi, village girl”. Ya faɗa yana murmushi.
Saurin kallon shi tayi don bata zata maganar da tayi ya fito ba, ɗan tunzura bakin ta gaba tayi tace; “Allah ni ba villager bace”.
Hancin ta yaja yace ; “oya lunch is ready gyara zama kici abinci”.
Juyowa tayi ta kalle shi tana sakin murmushi, tana son shi sosai da sosai ta san zai kula da ita zai bata duk wani jin daɗin rayuwa, zai share mata hawayen ta zai tsaya mata, amma still bata yi shiryawar da za su fara irin wannan soyayyar ba amma tana roƙon Allah ya kawo mata lokacin da zata kula da shi ta bashi full kulawanta.