ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

*Addu’ar Tsayuwa a Kan Dutsen Safa da Na Marwa*
Jabir, Allah ya yarda da shi ya ce, yayin da yake siffanta hajjin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; yayin da ya kusanto dutsen Safa sai ya karanta:
إِنَّ الصَّفَا وَالْمَرْوَةَ مِنْ شَعَائِرِ اللهِ.
أَبْدَأُ بِمَا بَدَأَ اللهُ بِهِ.
Bers Safa: Innas safa wal marwata min sha’a’irillah
Abda’u bima bada’al lahu bihi.
Hakika Dutdsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)”.
Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi.
Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai da ya hango dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce;
اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar.
Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma.
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، اَللهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدُهُ، وَهَزَمَ اْلأَحْزَابُ وَحْدَهُ.
Bers la Ka’aba: La ilha illallahu, allahu akbar, La ilaha illal lahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay’in kadirun. La ilaha illal lahu wahdahu. Anjaza wa’adahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata a gare shi, kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.
Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin addu’a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*Wannan page ɗin naku ne my 3 Fatimas, Fatima Batula (Mrs Balarabe), Fatima Aminu Baba (My besty), Fatima Aliyu(Oum Insaf) kuyi yadda kuke so da shi.*
_*The awaiting secret*_
Ranar hankalin Ahmad be kwanta ba sai da yayi musu booking tickets sannan hankalin shi ya kwanta washegari suka ɗaga zuwa London. Ko gida basu isa ba suka wuce hospital ɗin, irin yanayin da suka ga Daddy shi ya ɗaga musu hankali saboda yaji jiki sosai ya karye a ƙafa ga kuma raunuka duk a jikin shi.
Ummi hankalin ta ya tashi sosai idan banda kuka babu abunda take kuma har yanzu be farfaɗo ba.
Bayan kwana biyu Daddy ya farka nan fa kowa ya shiga cikin farin ciki sai murna ake,Ahmad ne ya shigo cikin ɗakin ya gaida Daddy ya mai sannu da jiki babu yabo ba fallasa ya amsa mai, ganin Daddyn ya ɗan sake hakan ne yasa ya zauna aka ɗan yi hira da shi.
Suna zaune sai ga Jibril ya shigo ya miƙawa Daddy wasu files, kowa kallon shi ya tsaya yana yi ko me zai yi da files yana asibiti oho.
Ahmad ya miƙawa file ɗin yace ya duba, babu musu kuwa ya fara dubawa sai da ya kammala tasss sannan yace ; “Daddy na gani kamar takardun company ɗin ka ne na can Abuja ko?”
“Eh sune”. Daddyn ya faɗa yana kallon shi.
“Me zanyi da shi?”
“Naka ne na baka a matsayin gadonka, koda na mutu na riga da na baka abunda zan baka ba sai an raba da kai ba”.
Da sauri kowa na ɗakin ya ɗago ya kalle shi, shi kuwa Ahmad wani malolo ne yaji ya tsaya mai a wuya.
Ummi ce tace ; “Haba mana ka taɓa ganin inda akayi haka akan me!? Akan wani dalili? Gaskiya na gaji da abunda kake mun, sam baka kyauta mun ba kuma ka yi mun kara, fisabillahi duk abunda nake maka, shirun da nake yi maka fa ba yana nufin bana son shi bane, and wannan hukuncin naka babu me karɓar shi bari kaji”.
“Jibril samo mun takarda nayi rubutu”.
“A’a Daddy please kar kayi haka kayi haƙuri don Allah ka bar maganar nan don girman Allah”.
“Ka bani nace maka ko!”
Har Jibril ya juya zai fita Ahmad ya dakatar da shi yana faɗin”Ba sai ka ɗakko ba, ko baka yi rubutu ba in sha Allahu indai ka mutu bazan taɓa karɓar gado na ba na barwa ƴan uwa na tun yanzu tunda haka kake so, amma inaso ka sani kuma kayi haƙuri da abunda zan faɗa maka yau, idan nine na zalunce ka kuma naƙi bin umarnin ka, ya Allah kasa kar na gama da duniya lafiya amma idan har kaine ka zalumce ni ka shiga haƙƙina ba tare da ka fahimta ba kuma ka janye ƙudurin ka ba wallahi bazan taɓa yafe maka ba”.
Ya ƙare maganar yana zubda hawaye.
Wani irin mari Ummi ta zabga mai, ta ɗago hannu zata ƙara mai wani ya riƙe hannun ta haɗe da girgiza mata kai sannan ya saki hannun nata, juyawa yayi zai ƙara magana Suhaila ta riƙe hannun shi tana girgiza mai kai.
Wani irin cilli yayi da ita sannan ya nuna ta da hannu yace ; “Idan kika ƙara taɓa ni sai ranki yayi mugun ɓaci so, ki zauna a inda Allah ya barki kar ki shiga wannan maganar”.
Kausar ce tace; “Ya Ahmad!”
Afusace ya juyo yace ; “Yaushe na fara wasa da ke han? Ina magana kina magana”.
Juyowa yayi ya cigaba da faɗin”And waƴanan files ɗin babu abunda zanyi da su, gasu nan”. ya faɗa yana watsa su a ɗakin nan ko wanne yayi hanyar shi, ko wace takarda da inda ta nufa.
“And kamar yadda na faɗa a baya babu ni babu ku bani da wani family da yake da sunan ku, har ke Ummi, tunda kin san gaskiya amma kin kasa ƙwatar mun ƴanci na saboda kina son shi, ni kuma ko oho”.
Sake ɗauke shi da mari tayi tana zubar da ƙwalla a idon ta.
Matsawa kusa da ita yayi yana faɗin “Dake ni, dake ni yadda kike so Ummi ki kashe ni kawai ki huta”.
Da sauri Suhaila ta ƙaraso ta riƙe shi ta janye shi a gurin sai fuzgewa yake kamar wani mahaukaci, da ƙyar ta samu ta fitar da shi a ɗakin.
Ummi da Kausar sai kuka suke, yayin da Jibril ya kasa motsawa, shi kanshi Daddy yau yayi mamakin yadda Ahmad yayi behaving.
Da ƙyar ta saka shi a taxy suka wuce gida, suna isa ya haɗa kayan shi ya ɗau tickets nashi ya sanar da ita za su wuje.
Bata yi mai musu ba saboda tasan tana magana ta shiga uku.
6 na yamma suka sauka a New York cikin fushi ya shiga cikin gida yayi wanka ya canza kaya ya fice a gidan ko ƙala bece mata ba.
Ranar kuwa taga banu domin kuwa har 2:00 na dare tana jiran shi be dawo ba.
Tana zaune a kujeran da take zama ko da yaushe tajira shi ya dawo, tana ɗan rubutu a journal ɗin ta don ta rage tunani taji ya buga bell, da gudu ta tashi ta buɗe mai don tasan shine.
Turus tayi ganin shi a bai-bai kaca-kaca kamar bashi ba.
Coat ɗin shi a hannu, bottom ɗin rigar shi duk a buɗe, links ɗin hannun rigar duk a cire, igiyan takalmun shi a buɗe, rigar kuma gaba a ciki baya a buɗe.
Doso ta yayi zai shigo taji wani wari ya dake ta wanda bata san ko na menene ba.
Ganin yana tangaɗi hakan ya tabbatar mata da giya yasha.
Wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, da sauri da taro shi suka hau sama tana tallabe da shi yana tangaɗi.