HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Sharafff ya baje a gado, kallon shi kawai take tana zubda hawaye, ita! mashayin giya, yau mijin ta ne ya sha giya ya dawo mata gida a buge, abunda take faɗawa Ja’afar na Allah ya kiyaye ta auri ɗan shaye-shaye shi ya faɗo mata.

Zaman dirshen tayi a ƙasa tana fasa kuka kamar ranta zai fita.

Jin kukan ta yasa ya ɗago, duk da baya cikin hayyacin shi amma sam kukan nata baya jin daɗin shi.

Sakkowa yayi ya kamo ta zuwa jikin shi, cikin muryar maye yace ; “Am sorry Azizateyy i don’t mean to hurt you, and nayi ƙoƙarin kar na sha Daniel yasa na sha, kiyi haƙuri please kinji ko”.

Duk da tana jin warin bakin shi hakan besa ko kaɗan taji haushin shi ba sai ma wani tasauyin shi ne da taji yana ratsa ilahirin jikin ta, rungume shi tayi itama tace ; “Am sorry too, amma kasan baza ka iya controlling kanka ba me yasa ka fita uhmm?”

“Bana son na miki wani abu ne, saboda idan ina cikin irin mood ɗin nan bana iya controlling kaina kiyi haƙuri Azizateyy, Abba ne baya kyauta mun sam, me nayi mai uhmmm? Baya sona kwatakwata bawai iya abunda ya faru tsakani na da Zainab bane dama can baya so na, har aiki na na bari duk don naje na duba shi amma ya wulaƙanta ni”.

“shhhhh, ya isa haka ka kwanta kayi bacci”.

Ba tare da yace mata komai ba ya zame zuwa cinyar ta ya kwanta abun shi.

“I love you Azizateyy”.

Ya faɗa cikin muryar bacci.

Murmushi tayi tace ; “I love you too cynosure!”

Da misalin 6:30 na safe shi ya fara buɗe idon shi, jin kanshi yayi nauyi sosai yasa ya riƙe kan nashi nan da nan abubuwa da suka faru suka shiga dawo mai.

“Inallilahi wainna ilaihi rajiun, ya Allah! Me na aikata jiya? Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha”.

Ɗagowa da yayi yaga fuskar ta, gata a zaune da alamun a haka ta kwana hakanne yasa wasu hawaye suka zubo mai.

Nan ya shiga da nasanin abunda ya aikata jiya, duk da ba a cikin hayyacin shi yake ba amma yasan sam be mata adalci ba yasan yabar wannan rayuwar a baya amma jiya ya aikata duk wani abu da yayi shi a baya.
Cikin lokaci ƙalilan ya fara zubda hawaye.

Ganin hakan ba mafita bane yasa ya tashi a hankali sannan ya ɗauke ta ya ɗora ta a gado kuma yayi alƙwarin bazai sake aikata abu irin haka ba.

Banɗaki ya shiga yayi wanka sanan yayi alwala ya fito yayi sallah ya tashe ta, sanar da shi tayi bata sallah hakanne yasa ya shiga bata haƙurin yadda ya dawo gida jiya ya kuma mata alƙawarin bazai sake ba, sannan ya sanar da ita ko wayar su Ummi kar ta sake ɗauka, be yadda da ita bama hakanne yasa ya danna su a block both chart da call sannan ya bata wayar ta.

Ƙasa ya sauka don ya haɗa musu breakfast, nan yaci karo da journal ɗin ta, saurin ɗauka yayi ya ɓoye shi sannan ya haɗa musu breakfast, kafin ya koma ɗakin har tayi wanka ta gyara ɗakin.

Fitowa suka yi nan take tambayar shi ɗayan ɗakin ina ne, don a rufe yake ko da yaushe.

“Library ne, kuma baki taɓa tambaya ba na manta ban buɗe ba tunda muka zo”.

Bayan sunyi breakfast ya wuce gurin aiki.

Ita kuwa kafin ya dawo, ta gyare gidan ta saka turare tayi girki me daɗin gaske, wanka tayi ta fara duba abunda zata saka a jikin ta, amma ta rasa, saboda duk ƙananun kayan nan basu gare ta ba.

Kayan shi ta fara dubawa nan taga light blue long-sleeve shirt ɗakkowa tayi tana kallon ta, duk da rigar maza ce amma kuma tayi kyau sosai, sakawa tayi a jikin ta sannan ta saka wani black pant ɗin shi na maza ya ɗan sakko mata kaɗan kuma ya kama ta babu lefi, wani Chen ta gani wanda ake ɗorawa a wuyan riga ta saka kallon kanta tayi taga komai na jikin ta ana gani saboda rigar shara-shara ce ana ganin komai.

Gyara kanta tayi ta saka stretcher tayi stretching kanta yayi kyau har da wani coil sannan ta ɗan yi kwalliya ta saka red lipstick ta saka kwalli da maskara da eyeliner nan fa tafito tayi kyau sosai looking very sexy.

Bata ɗora komai a kanta ba ta sakko tana duba journal ɗin ta amma bata ganshi ba, tasan a nan ta barshi amma bata ganshi ba.

Zama tayi a kujerar dining tana danna waya.

Jin ƙarar bell yasa taje ta buɗe ƙofar, wani irin kallo ya bita da shi yana mamakin shigar da tayi yau, Masha Allah kawai yake furtawa yana haɗiyar yawu ba irin ma yadda rigar tayi mata kyau kamar tata, pant ɗin shi ya kalla ya saki wani murmushi saboda mamaki.

Karɓar briefcase ɗin shi tayi tace ; “Sannu da zuwa”.

Kaɗa mata kai kawai yayi ba tare da yace komai ba.

Wanka yayi sannan ya sakko ƙasa suka ci abinci bayan sun kammallah suka shiga ɗakin don kwantawa bacci.

Riƙo hannun ta yayi yace; “Kinyi kyau sosai, amma kinsan ba kya sallah me yasa kika yi irin wannan kwalliyar baki tsoran nayi miki wani abu”.

Ɗan murmushi tayi tace; “Nasan baza ka mun komai ba miji na abun alfahari na, my dear cynosure”.

Rungume ta yayi yace ; “I love you so much Azizateyy”.

“I love you too cynosure”.

Ɗago da ita yayi yana zaro ido yace ; “Really?”

Ɗaga mai kai tayi tana sunkuyar dakanta ƙasa.

Tissue ya ɗakko ya goge mata make up ɗin fuskar gaba ɗaya sannan ya kaita bathroom ya wanke mata fuskar, hula ya ɗakko a drawer ya saka mata sannan ya ɗauke ta cakk zuwa gado ya kwantar da ita ya jawota jikin shi, ya kashe bed side lamp.

placing kanta yayi a ƙirjin shi yace; “Magana zamu yi and kuma bana son musu da ƙarya”.

Gyaɗa mai kai tayi ba tare da tace mai komai ba.

“Bayan kasancewar ki bazawara dama an taɓa yi miki fyaɗe? Kuma shine sanadin da yasa mijin ki ya sake ki?”

Ji tayi gaban ta yayi muguwar faɗuwa abunda take gudu ya faru yau, shikenan shima zai mata abunda Jibril yayi mata zai sake ta wayyo Allahn ta.

Kamar yasan abunda yake ranta hakkane yasa yace mata” Look karki ji tsoro, ni ba Habib bane kuma nasan me nake yi, ba jikin na aura ba i just want to know ne kawai”.

Gyaɗa mai kai tayi alamar “eh” tana mamakin inda yaji maganar nan.

Katse mata tunani yayi ta hanyar jefo mata wata tambayar wacce ta kusa ruguza mata lissafi.

“And who is Ja’afar? Ko shine guy ɗin da yayi attempting raping naki ranar? Who is he to you naga kamar kin san shi sosai”.

Da sauri ta tashi ta kunna bedside lamp ɗin tana kallon fuskar shi alamar a ina yasan duk wainnan labarukan don a iya sanin ta mutum uku ne kaɗai suka san wannan labarin wanda ko Abbun ta babu a ciki.

Janyo drawer yayi ya nuna mata journal ɗin ta.

“Kin temake ni da kanki ban wani sha wahalar bincike ba very simple don ma ban ƙarasa karantawa ba saboda bazan iya cigaba da jin yadda akayi raping naki ba, and meye dalilin ki na rubuta wannan abun ki ajiye?”

Sauka za tayi daga gadon idon ta duk ya ciko da ƙwalla ya fizgota ta dawo jikin shi, ƙara ƙoƙarin tashi tayi tana faɗin” Ka sake ni cynosure! Bana son wannan maganar”.

Ganin zata botsare mai yasa ya ƙara fizogata ya bata wani angry kiss, na kusan 15 seconds, sannan ya sake ta ya girgiza ta ya cillata tsakiyar gadon.

Ganin yadda idon shi ya koma ja yasa jikin ta ya fara kirma tana matsawa, ita dai tsoran ta kar yayi raping nata kuma gashi tana period.

Kamo kafaɗun ta yayi ya rungume ta tsam a jikin shi yana saka mata kuka kamar wani ƙaramun yaro.

“Zan sake nanatawa is he the one, shine wanda yayi attempting kashe ni ranar? Don da yayi raping naki mutuwa zanyi Suhaila”.

Cikin kuka ta ƙanƙame shi jin abunda yace, komawa tayi ta zauna sosai shima ya bita yana ƙara rungume ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button