ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Wani irin kuka ta saka tana ƙanƙame Ahmad, shima kukan yake yi, yana bata kiss a duk inda yaci karo da shi a jikin nata, riƙe ta yayi tsam-tsam kamar za a raba shi da ita, wani irin son ta ne yake ƙara mamaye zuciyar shi ba irin yanzu ma da ya ƙara jin abunda ya faru da ita amma duk da haka tana behaving kamar wani abu be taɓa faru da ita ba.
Ɗago fuskar ta yayi yasa hannun shi ya share mata duk wani hawayeb fuskarta.
Cikin muryar kuka ta cigaba da cewa”Abbu na da ƙyar ya ƙaraso inda nake ya ɗago nikamar wata gawa, ya rasa inda zai saka ni ga wani uban jini da nake zubarwa kamar wacce ta haihu, Hijabi na kaɗai ya iya saka mun a jiki na sannan ya shiga cikin ɗaki ya kwanto Ammi, tana ganin irin halin da nake ciki ta yo kaina da gudu gaba ɗaya na canza kamanni kamar ba ni ba, ido a kunbure baki, fuska ta kamar an hura ta, baki na kuwa ba a cewa komai. Acikin wannan daren suka kaini asibiti jikin kowa a cikin su rawa yake, asibitin ma da kyar suka karɓe ni wai ina police sai da Abba ya dinga haɗa su da Allah yana su ceci rayuwa ta sannan, koda suka duba ni cewa suka yi baza su iya ba a kaini Aminu kano teaching hospital basu saniba ko mahaifata ta taɓu, babu musu kuwa aka kawo ni nan, ya Ahmad saida aka mun ɗinki ɗauri bakwai tukunna don sosai suka farka ni irin abunda suka mun babu wanda ya zaci zan rayu, likitan ma cewa yayi don ina da sauran kwanaki ne shiyasa kawai ban mutu ba domin kusan har ta ciki sai da aka mun ɗin ki, kusan wata na biyu a hospital ban dawo dai-dai ba har sai da na zama kamar me taɓun hankali ina zaune kawai sai dai na tashi na zura a guje, da Addu’a da temakon Allah na samu na ɗan fara dawowa cikin nutsuwa ta amma fa komai ya canza domin kuwa magana ma da ƙyar nake iya ta, na zama sam bani son ganin komai nidai kawai na zauna ni kaɗai, ganin hakan ne yasa likita yace a dena bari na ni kaɗai ko kuwa na ɓuƙaci hakan, ya Fatima kuwa itama zama tayi kusan iri na don ko magana bata fiya yi ba itama a lokacin, cikin ikon Allah na samu sauƙi sosai aka dawo dani da gida, a haka-haka har nasamu sauƙi sosai na fara taka ƙafata babu lefi, bayan an kwana biyu na fara dawowa dai-dai har ma ina ɗan zuwa islamiyya, da temakon Suarayya komai ya fara dawomun dai-dai. Bayan an kwana biyu sosai Fatima ta bani wani agogo wai bayan anyi rapping ɗina tana gyaran gado ta ganshi akan gadon, ina ganin agogon naji gaba na yayi mugun faɗuwa domin kuwa nasan ko na wanene agogon karɓa nayi batare da nace mata ƙala ba, washegari naje gidan su na cilla mai agogon shi, na kuma sanar da Umma cewar ranar da akayi mun fyaɗe aka bar agogon kowa ya san nashi ne babu wanda be sani ba, sanar da ita nayi sai na faɗawa police kuma bazan taɓa yafewa ba, hakan ne yasa ta kira Ammi ta sanar da ita halin da ake ciki be ko ji tsoro ba ya amsa shine yayi mun hakan saboda nace bazan aure shi ba shiyasa yace bari yayi mun hakan sai yaga wanda zai aure ni idan ba shi ba. Duk sun sha mamaki inda Umma ta dinga bani haƙuri harda durƙusawa wai shikenan mata ɗan ta namiji in rufa mata asiri haka ta dinga bawa Ammi haƙuri tana kuka, ko da nace sai na gayawa Abbu hana ni tayi tace wai ai lefi na ne me yasa nayi mai rashin kunya Allah sheƙara maganina kenan, gwara ma da Allah yasa ni akayiwa ba Fatima ba ko Farida kuma na sake na faɗawa Abbu bani babu ita don haka an binne maganar tsakanin ni da Umman sheka, da kuma shi Ja’afar, ba wani abu yasa na bar zancen ba sai irin kalaman Ammi wai gwara da Allah yasa ni akayiwa ba sauran ƴaƴan ta ba, hakan ne yasa nasan da cewar bani da wani ragowar gata tunda har uwa ta da ra san irin walahar da nasha amma kuma ta goyi bayan wai a rabu da case ɗin karma na taso da shi, haka aka barshi ko kaɗan ba a taɓa reporting ba har shekaru suka ja. Surayya ce tayi mana ƙoƙari da kuma ƙwarin gwiwar da Abbu yake bani har na sake jamb na fara zuwa makaranta, tunda na fara makaranta kuma sai na rage damuwa sosai daga baya ma nazo na fara manta komai sai dai lokaci bayan lokaci idan na tuna”.
Shiru tayi tana sauke numfashi da ƙyar.
Ta buɗe baki zata sake magana kenan y haɗe bakin su waje ɗaya, sai da yayi kusan 10 minutes sannan ya saketa ya kwantar da ita yace; “Ya isa haka kwanta Kiyi bacci, am really sorry na tuna miki abunda be kamata na tuna miki ba sorry Azizateyy”.
Gyaɗa mai kai tayi sannan ta lumshe ido tana daɗa dunƙulewa guri guda dama bacci take ji sosai.
Bayan tayi bacci Ahmad yaje yayi alwala yazo ya kabbara sallah, yayi ta musu addu’a Sanna ya kwanta after 3.
Washegari da safe…
Nigeria, kano..
*My people na janye amma gaskiya ku sake dagewa, comments na mun kaɗan musamman ƴan wattpad*
_*Ma’asalam, Faɗma Ahmad*_.
[8/31, 10:43 PM] fatima boi/isc: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page8️⃣7️⃣to8️⃣8️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Addu’a Idan Mutum Ya ga wani abu mai ban Mamaki, ko na farin ciki*
سُبْحَانَ اللهِ!
Subhanal-lah!.
Tsarki ya tabbata ga Allah.
اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar
Allah ne mafi girma.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*_Finding Solutions_*
Nigeria, Kano.
Da misalin ƙarfe 9 na safe Umma da Zainab suka gama shiri don zuwa wajen wani malami, babu ɓata lokaci suka ɗau hanya sai da suka yi tafiya me nisa sosai sannan suka isa don a ƙalla sunyi kusan 1hour a hanya, wani ɗan daji suka shiga wanda ba shi da wani duhu sosai don daga nan ma kana iya hango ƙauyikan dake gefan gurin, a hankali suka taka zuwa cikin ɗakin dake gurin babu ko sallama suka danna kai, ita kuwa Zainab sai zare ido take kamar an farauci ɓera, wani gwalangwace nasu na bokaye yayi musu hakanne yasa cikin Zainab yayi mugun ƙullewa, kallon ta mamanta tayi alamar ta kwantar da hankalin ta babu wata matsala.
“Me ke tafe daku?”.
Muryar Bokan ya daki kunnen su, cikin dagiya da jarumtar Umma wanda dama daga gani ta saba zuwa tace; “Boka wata yarinya ce ta tsaya mana a hanya, ta hana mu rawar gaban hantsi shine muke so a mana maganin ta, ta kowace hanya mudai fatan mu kawai Zainab ta auri Ahmad”.
“So kuke a kashe ta kenan!?”
Zainab ce tayi saurin girgiza kai”A’a ina so a batta a raye idan son samu ne ma, ta zama ƴar aikin gida na sai abunda nace”.
Dariya bokan yayi yace; “To ai aikin ki ma me mugun sauƙi ne kuma anfi saurin samun nasara, zaki aure shi kuma zata zama a ƙarƙashin ki sai abunda kika ce za ayi”.