HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Murmushi Zainab tayi tana riƙe hannun Umman ta alamar za su samu nasara.

Wani surutu yayi akan wani ruwa sai ga hoton Ahmad da Suhaila ya bayyana a cikin ruwan, kwance suke a kan gado sai bacci suke kowa ya shige jikin ɗan uwan shi.

Wani irin murmushi Hajiya tayi yayin da Zainab ta haɗe rai ganin su a haka.

“Kar ki ji haushi ƴan mata har yanzu be kusance ta ba”.

Muryar bokan ya daki dodon kunnen Zainab.

“Yauwa haka nake so don Allah kar a barshi ko kusa da ita yaje”.

Surutu ya cigaba da yi idon shi a rufe, sai da ya ɗau kusan 20 minutes a haka sannan ya buɗe idon shi da ya kaɗa yayi jajur, kallon Hajiya yayi yace; “An samu matsala aikin bashi da wahala amma yana da wahala gaskiya saboda suna da tsari sosai a jikin su don haka sai ansha wahala kafin abun ya kamasu yanzu haka ma na tura wani baƙin aljani amma sai dawowa yayi”.

“Amma shi ɗin za a iya aiki a kanshi ina tunani don ya fita rauni”.

Zainab ce tayi saurin cewa”A’a gaskiya kar a taɓa shi don na fison ya aure ni yana cikin hayyacin shi, a samo dai wata mafitar”.

“Mafita biyu ce”. Bokan ya faɗa.

Umma ce tace; “Uhmm munajin ka”.

“ko a kashe ta, ko kuma a hanasu haihuwa daga nan kuma sai a saka mai sha’awar ƙara aure, kinga sai ya aure ki kawai”.

Murmushin jin daɗi Zainab tayi tace; “Mun ɗauki na ƙarshen”.

Umma kuwa wani kallo ta watsawa Zainab alamar baki da hankali.

“Me zai hana kawai a kashe ta”.
Umma ta faɗa.

Zainab ce tayi saurin cewa”Umma gaskiya banda kisa”.

“Ya isa haka ba a mun haka a gurin nan, za a miki aikin ki kuma zai fara daga yanzu, baza su haihu ba har sai sanda muka gadama”.

Biyan shi suka yi kuɗin aikin shi sannan suka fito zaso wuce gida, ita kuwa Umma sai harar Zainab take har suka isa gida.

A ɓangaren su Daddy kuwa tun ranar da su Ahmad suka tafi Ummi bata ƙara zuwa hospital ba, Jibril ke kula da Daddy sai Kausar da take kai musu abinci. Sunyi trying sunyi trying number Suhaila amma baya shiga sam haka ma na Ahmad ɗin, sun shiga damuwa ba kaɗan ba har Jibril, shi kanshi Daddy har yanzu be dena mamakin abunda Ahmad yayi mai ba, gashi shima duk hankalin shi yayi kanshi yana ta tunanin ko a wani hali suke oho.

New york.

Da wuri ya tashi yayi sallar asuba ya ƙara musu addu’a yayi azkar sannan ya taɓa karatun ƙur’ani kafin ya koma ya janyo Suhaila zuwa jikin shi ya lumshe idon shi don wani mugun bacci ne yake fizgar shi, jinshi ya dawo yasa itama ta ƙara shigewa jikin shi, nan fa suka cigaba da baccin su me daɗin gaske.

Sai after 10 sannan ya tashi a hankali ya zare jikin shi a nata ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shafa mai a jikin shi ya fesa turare sannan ya shiga gurin kayan shi ya ɗakko wani white boxer short ɗin shi ya saka sannan ya saka wata armless riga, kallon kanshi yayi a mudubi yaga gashib kanshi ya ɗan yi yawa saboda baya son ganin gashi ko kaɗan a kanshi, juyowa yayi yaga sai bacci take hankalin ta kwance, murmushi yayi sannan yaje ya buɗe curtain ɗin jikin window nan fa haske ya ƙara gauraye ɗaƙin. Ɗan motsawa tayi sannan tayi miƙa a hankali kafin ta buɗe idonta, tsaye ta hango shi jikin windown ya riƙe ƙugu yana sakar mata murmushin shi, mayar da idon tayi ta rufe ganin shi babu wani kayan arziƙi a jikin shi.

Saman gadon ya hayo ya yaye duvet ɗin yace; “Oya tashi kije kiyi wanka, don ba kya sallah shine kike ta bacci ko?”

Ya ƙarashe maganar yana jan hancin ta, amma ko motsawa bata yi ba, ganin haka yasa ya ɗauke ta cakk ya shigar da ita toilet, ya ajiye ta bakin bathtube ya cillo mata towel sannan ya rufe ƙofar yana faɗin” Idan kin gama halin fulanin rugan da muka baro a can Nigeria kiyi wanka sai ki sakko ƙasa muyi breakfast zan ajiye miki kaya akan gado”.

Murmushi tayi ta ɗauki towel ɗin sannan ta fara wanka, bayan ta gama wanka ta fito ta ɗauki pad ɗin ta ta koma ta saka, ta dawo ta ɗaga kayan da ya ajiye mata, wata ƙatuwar rigar shi ce da ta kawo mata har saman knee ɗin ta, murmushi tayi tana faɗin “Allah ya shiryi cynosure wai wannan ne kaya”.

Bata daɗe ba ta shirya ta feshe jikin ta da turare ta saka hula sannan ta sakko ƙasa.

Ko da fito bata ganshi ba a cikin Palo, kuma baya inda suke girki.

Guri ta samu ta zauna a tunanin ta ko ya fita ne, ga ƙamshin girki tana ji alamar yayi abinci amma ko kaɗan bata ganshi ba kuma babu abinci a dining.

Shigowa yayi ya tsaya yana kallon ta, itama kallon shi tayi sai kuma ta ɗauke kanta, don kallon shi a haka ba ƙaramun kunya take ji ba.

Hannun ta ya kamo suka fita wajen gidan nan taga yayi musu shimfiɗa daga cen gefe ya shirya komai, zaunar da ita yayi sannan ya zuba musu abinci, a baki ya dinga bata har sai da ta ƙoshi, bayan sun gama kuma ya dawo ya janyo ta jikin ya sata in between legs ɗin shi ya ɗaura haɓar shi saman kanta sannan yace; “Jiya baki ƙarasa bani labari ba na saki bacci”.

Murmushi tayi ta ɗago kai ta kalle shi tace; “Me kake so kaji kuma?”

“Labarin Habib zaki bani”.

Mayar da kanta tayi kan cinyar shi sannan ta bashi labarin yadda suka fara haɗuwa da Habib har suka yi aure.

Kanta ya shafa yace; “Allah ya isa na, yaje ya samu virgin wacce zata cu uban shi wallahi, ban san meyasa wasu mazan basu san yadda za su zaɓi abokiyar zama ba, wani zubin da virgin ɗin ba gwara wacce tayi auren ba, virginity fa bashi ne mata ba, ka samu mata me hankali, me haƙuri, me ilimin addini da na boko dai-dai gwargwado me ladabi da biyayya da sanin ya kamata itace mata amma sai mu tsaya muna ta shirme saboda ruwan ido, wasu mazan suna tunanin sex shine kaɗai rayuwar aure kuma ba haka bane”.

Jin ya dage yana ta masifa yasa ta ɗago tana kallon shi.

“Uhmmm, kalle ni da kyau Allah ya bani haushi wawa kawai, amma kuma nagode mishi da har ya sake ki ni kuma na samu”.

“Yanzu ma dai mu bar zancen shi. Ya zamu yi da case ɗin Ja’afar?”

Saurin tashi tayi zaune tana kallon fuskar shi duk idonta ya ciko da ƙwalla.

Kamo hannun shi tayi tace; “Ta ya za a taso da abunda ya wuce for more than six years umm? Beside ko reporting ba a taɓa yi ba, taya zamu buɗe case ɗin? Ta ya zamu fara? Tun shekarun baya ba mu kai ƙara ba sai yanzu wa kake tunani zai karɓi wannan case ɗin namu han?”

Lumshe idon shi yayi sai kuma ya rungumo ta, shi kanshi yasan baza su iya buɗe case ɗin ba tunda an ɗibi shekaru ba ayi reporting ba, so yanzu kam hakan bashi da amfani.

Ɗago fuskakar ta yayi yace; ” Na sani, amma ba da wannan zamu yi accusing nashi ba, da robbery ɗin da suka mana zamu kama su daga nan kuma sai a tado da case ɗin ki ko?”

Shiru tayi sai kuma tace; “To amma ta yaya zamu samu evidence ummm, kasan dai bamu da wani clue ko?”

“Yes i know, kin manta mijin ki criminologist ne?”

“Ban manta ba, please cynosure for my sake, tunda muna lafiya lau kuma bama tare da su don Allah ka bar zancen nan kaji ko, for my sake please”.

Ganin zata mai rigima yasa yace mata “Okay ooo, amma fa sai naga kin canza, kin koma normal life ɗin ki kamar yanzu kika fara rayuwa kamar ba abunda ya taɓa faruwa dake, kamar baki da wani sad story”.

Gyaɗa mai kai tayi sannan ta rungume shi tana sakin kuka, ita kam bata san inda zata saka kanta ba Allah ya bata wanda yake sonta ba don komai nata ba, ba don kyaun ta ba wanda dama ba wani kyaun azo a gani gare ta ba, ba kuma jikin ta yake so ba, ba komai nata ba, kawai haka nan ta rasa me yasa ma yake sonta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button