ALLAH NE SHEDA HAUSA NOVEL

ALLAH NE SHEDA HAUSA NOVEL

anty meh kike so ne haka?

kuka tasaki ta rike hannun taslima tace’ kanwata yanxu haka Ina dauke da wani cikin a karo na6 kenan doctor ya tabbatar minda cewar cikin nan shima zubewa zaiyi kamar sauran saboda inada matsala kuguna(marata) bazata iya daukar Dan mutum ba mafita daya ce!
mene ne mafitar aunty?

dole saidai acire kwayoyin halitta na asaka a cikin wata indai anaso su rayu! taslima ki taimake ni, Ina rokon ki, ki amince a cire kwayoyin halitta na asama ki kirainar min su,ki haifarmin ki bani, taslima kinsan burina bai wuce Inga jini na ba, kuma inaji a jikina bawani dadewa zanyi a duniya ba,

jin maganar antyn tayi kamar saukar aradu ina bazai yiwuba, inzama bazawarar karfi da yaji alhalin bantaba yin aure ba,kuma idan mutane suka ganni da Cikin meh zance musu, mezan cewa ummana? baba da Inna suyi mana dariya a kunyata ni a idon duniya domin duk Wanda zancewa ba cikina, bane bazai yarda ba,ko a gaban ummana naje banida wata sheda,duk Wanda xancewa banyi zina ba kuma banyi aure ba,bazai yadda ba tunda dai ciki ba’a shansa a ruwa ko a shaka a iska kowa cewa zaiyi waye shaidata, to ni kuma ai nasan ALLAH NE SHAIDA sai kuma ita antyn, gaskiya bazan yarda ba,wannan ai ganganci ne da rayuwa da kuma farin cikina, take so inyi, tawani bangaren kuwa Ina tausayawa Mata matuka Ina kuma tuna alkairinta a gareni sosai,,,,
taslima kinyi shiru’ kallonta nayi nace’AUNTYYYYYY!!!!
Murmushi Antyn tayi tace’taslima? Fadamin abunda ke ranki,
A kasalance tace”anty na amince, da sauri tauhida ta rungumeta tana fadin nagode kanwata ki shirya gobe muje mucewa ummanki zamuyi tafiya zamu Dade, sannan kuma namiki alkawarin babu Wanda zaisan maganar nan dagani sai ke sai ALLAH to anty! Ta fadi ita dai kam duk jikinta a maceh yake tana tsoron al’amarin,

Washe gari suka shirya suka dauki hanyar kauyensu ita kam duk batada walwala domin abun yana bata tsoro,a haka sukaje Umma taji dadin ganin su barinma dataga harda tauhida,
Tauhida da kanta tayiwa ummar bayani fatan alkairi tai musu suka kwana daya suka dawo gida, ranar da za’ayi aikin sosai tauhida ta kwantarwa taslima da hankali inda taji tadan samu relief, a ranar doctor yai musu aikin, aka cire kwayoyin halittar daga jikin tauhida aka sakawa taslima, 1week sukai a hospital sika dawo gida a lokacin kuma su taslima suka fara zana jarabawar waec,
Ita kanta tana mamakin yadda Antyn ta tah take kulada ita Dan yanxu ko ruwan wanka ita take hada mata, Dan haka ta fara sakin jiki da al’amarin dukda sabon yanayi datake taji a jikinta, a haka ciki ya fara mikawa kuma sungama exam da haka tacigaba da zama domin yanxu boyeta anty takeyi a kullum tana fadin taslima’ ki saki jikin ki, kinji babu Wanda zaisan wannan sirrin dagani saike sai Allah ko mijina bazai saniba har sai zuwa bayan kin haihu zan sanar masa gaskiya kinji,

To but anty inda Allah yasa ni kuma nasamu miji nayi aure yagane baisame ni a budurwa bafa mezance masa,anty kinsan duk macen data haihu to sai tazama disvargin.
Hakane amma ke aina xaba miki miji kicire wannan shima a ranki kinji nayi miki miji nagari, yanxu ki kwanta ki huta bari inshiga kitchen mezan girka miki?
Ummmmm! Dan daga Kai tayi Rana’ nazari tace’ tuwon dawa miyar kuka tsanwa shar kar’asamata manja! Kuma bana son asaka tarugu ko kayan miya, so nake asaka sansamin yaji a miyar,
Dariya anty tayi’ tace to angama,

Kullum abunda take so take ci a gidannan Dan haka batada matsala saita tunanin haihuwa!
A haka har cikinta yakai wata 6 ciki fa yafara tsufa domin yafito sosai, har gida doctor yake zuwa yana dubata, ya kuma tabbatar musu yan’biyu ne namiji da mace’ Allah sarki anty harda kukan dadi tayi yanxu a duniya babu abunda tafi so kamar cikin nan, Dan haka kullum cikin addu’ar Allah yasauki taslima lapiya take,

Around 10pm na dare kwance take tana wayada tauhid tace’namesake kasan mene ne?
Gyara kwanciyar sa yayi tareda shafa sajensa yace’ a.a namecy saikin fadi,

Namesake Allah inada ciki,

Zabura yayi yace’sure, habibaty are you serious?
Am serious inada ciki harna tsawon wata shida6,
What you said 6month?
Yes 6months amma fa baya jikina wllh,
Shiru yayi yana nazarin maganar ta tah banda yasanta lapiyarta lau, da ace wani ne yai maganar da yace’ lallai bayada hankali,shi baigane wannan bahaguwar maganar ba wai tanada ciki na6 months amma a jikin wani kajifa wani sabon salon hauka kuma,

Shirun dataji yayi yasa’tace wallahi mijina da gaske nake kashirya ka kusa zama uba,
Jiyayi ta Kara rikita masa kwakwalwa yace’ ke tauhida karfa kibari son haihuwa ya haukata ki yakike min wani zance haka,
Dariya tayi tace’shikenan saika dawo zanmaka bayani duk yadda lamarin yake, kuma kashirya idan kadawo zanmaka aure Allah kuwa,
Oh! Shoooooooot! Ya fada yana dafe kansa yace’karki rikita min kwalwa da shirmen ki na yau kinji ki kwanta saida safe ki kulada kanki i love you ya fadi tareda manno Mata wani dogon kiss ya kashe wayarsa.
Dariya abun yabata ta tashi tashige bathroom ta dauro alwala ta tada nafila.

Shafin kune wannan @GOLDEN’S WRITES ASDOCIATION@ godiya mai tarin yawa Allah yakara hada kanmu,

Shi kuwa tauhid yana kashe wayar tsoki yayi tareda fadin xai nemi Dama a gurin aikin subarshi yaje’ Nigeria yakai tauhida a duba masa kwakwalwarta da haka yayi baccin sa,

Tauhida kuwa bayan tayi nafila alqur’ani tadauko tacigaba da karantawa kallon agogo tayi taga har daya da rabi na dare tati 1:30am Dan haka ta rufe tareda yin dogayen addu’o’i taje gefen taslima dake kan gado kwance Dan yanxu daki daya suke kwana, shafa cikin tayi taji sai motsi yake murmushi tati’ tareda mannawa cikin kiss ta kwanta bacci yadauketa,

Kiran sallar asubh ne yatayar da taslima bayan tayi sallah harta gama ta juya taga yadda tabar tauhida a haka tasameta murmushi tayi’ tace’ waih! Yau wacce Rana antyna da lattin sallah, aikuwa Bari inmiki wayau yauni Zan hada mana breakfast Dan haka, ta nufi kitchen around 8am ta gama ta nufo dakin again thanks a bata tashiba, Dan haka ta nufota tana antyna! Antyna!! Kitashi kiyi sallah, shirun dataji yasa ta tabata tace’anty!anty!! Jitayi babu alamar numfashi a rikice ta daga hannunta tasaki taga yafadi yaraf! Kallonta tayi taga idanunta ya kalli sama kuma farine kawai da wata Kara tasaki da guru ta nufi waje a garden inda maigadi da driver suke sai ganinta sukai da gudu ga katon ciki, da mamaki suke kallonta ciki kuma, karasawo tai tana fadin kutaimake ni antyna!!!
Tanata nuna cikin gidan binta sukai har dakin baba maigadi ne yaduba tareda dogon salallami yace’ hajiya ta rasu!
Wani ihu taslima tasaki tareda sulalewa kasa a someh! Wannan yayi dai’dai da shigowar doctor dake dubata,



Sai wajen sha biyu ta farfado inda taganta a gidansu tauhida wato gidan iyayen tauhid, juyawa tayi gefenta taga gawar tauhida tasauri ta nufi gurin aka janyeta, tanaji tana gani aka fita da gawar tauhida domin kaita masaukinta na gaskiya wani kuka tasaki tana fadin anty karki tafi kibarni anty zaki barni cikin matsalar rayuwa kece shaidata sannan kuma ALLAH NE SHAIDA kidawo anty!!!
A haka aka mayarda taslima wani daki daban, tacigaba da surutun ta, tana kuka haka ta wuni a dakin har dare, salloli kawai takeyi ko abinci bataci yadda taga dare haka taga safe a haka tai rayuwa harta 3days akayi addu’an sadakan3 ummi ce(mahaifiyar su tauhid)’ ta shigo fuskar nan a murtuke ke! ta fada cikin tsawa!
A firgice taslima ta juyo ta dubeta jikinta na rawa, dubanta tayi ‘tace” ke kuma a gidan ubanwa kika samo wannan katon cikin?
Hawaye suka zubo mata tace’wallahi hajiya na rantse da Allah ba cikina bane, cikin anty tauhida ne wallahi Allah ne shaida itama kuma shaida ce, bantaba zinaba wallahi tallahi cikinta ne,

Previous page 1 2 3Next page

Leave a Reply

Back to top button