ALLAH NE SHEDA HAUSA NOVEL

ALLAH NE SHEDA HAUSA NOVEL

💞💞💞💞💞💞💞💞
alhamdulillah my fans this is my new book,Ina godiya ga Allah sannan kuma Ina godiya a gareku masoya na, nagode.

💕💞💕💞💕
ALLAH NE SHEDA!
💕💞💕💞💕

@GOLDEN’S WRITERS ASSOCIATION@writing by’xee”abu safana
mrs’salihu Bamalli my ustax!

</</</</<//Allah ne sheda!

Ayyah taslima kinga ajiye aikin nan kije xan karasa girkin nan kinji kinga kinyi latti xuwa school, to anty dakin bari na karasa miki kawai na kusafa,
a’a kije driver yashirya ke yake jira ki fito kawai,jeki kanwata Zan karasa ki maida hankali ayi karatu saikin dawo!
to antyna nagode saina dawo’to kanwata.
dasauri tashirya cikin school uniform dinta ta dauki baskect dinta ta fice, harga Allah tana kaunar anty tauhida saboda yadda take sonta kai kace’ wata kanwarta ce alhalin kuwa babu dangin uwa bare na uba, hasalima taslima yar aikinta ce’zakuyi mamaki idan nace’muku yar aikinta ce, takewa wannan gatan harta sakata makaranta domin a lokacin da aka dauko Mata taslima a matsayin yar aiki dama tun a kauyensu ita tana karatu hakan yasa tauhida(anty) ta mayarda ita ta kuma jawota a jiki kamar wata kanwarta wacce suka fito gida daya, komai yimata takeyi, shi yasa suka shaku matuka,
around 1:30pm tashigo gidan ta kwalla Kira “antyna! antyna!!
shirun dataji yasa ta nufi bedroom din tauhida a kwance take’ tana xubarda kwallar data Saba,
shiru tayi’a lokacin data sameta a wannan yanayin zama tayi a gefenta tareda dafa kafadarta tace ‘antyna’
dasauri tauhida ta dago tana share kwalla tace’taslima yaushe kika dawo,banji dawo war ki bane,

anty dama bazakiji dawowa ta nasani tunda kina nan kina abunda kika Saba,ban San har zuwa yaushe ne zaki daina tunani da kukan nan ba,Allah yasani bana son ganinki cikin wannan yanayin ko kadan domin hankalina yana matukar tashi,
Allah sarki kanwata kiyi hakuri, kinfi kowa sanin Abunda yake damuna banida burin daya wuce naganni da dana! ko diyata a duniya sai dai kuma Allah bai bani ba, shekata6 kenan da aure taslima Dana samu cikin saiya zube baya zama munyi maganin asibitin munyi na Islamic din but kin daiga shiru taslima Ina tsoron Karna mutu banga,iri na ba a duniya nasan idan na mutu taslima kowa zai manta dani ne, a duniya tunda kinsan banida iyaye na,mamana da babana duk sun rasu dama ni kadai suka Haifa a duniya sai kuma suka rasu,hakan yasa na tashi a hannun wan mahaifina wato baban tauhed mijina Wanda shida matarsa suka rike ni tamkar yarsu yaransu kuwa babu wani banbanci a tsakanin mu,tin Ina karamata tauhed yake hidima dani,harna girma inda hakan yazama soyayya aka hadamu aure nida shi, so da kauna da kula babu Wanda bana samu a gurin tauhid daga baya yanayin aikinsa ne yasa baya xama a gida kinsan cewar soja ne,kuma babba Ana tura shi kasashe yayo watanni inda yake Nuna min damuwar sa akan barina dayake yi ni kuwa na nuna masa babu matsala na kuma Kara masa kwarin gwiwa akan aikin nasa,shi yasa yake alfahari dani,

rashin haihuwata ni yafi tayarma da hankali domin shi yake rarrashina, akan hakan Ina son haihuwa matuka a haka muka cigaba da addu’a akoda yaushe muna Neman zabin ubangiji a family ma duk su suke kwantar Minda hankali, haka nacigaba da rayuwa idan yayi tafiya sai kannensa suxo su tayani xama domin su ukku iyayensu suka Haifa shine babba tauhed sai saudat da muhsina, yanayin karatun su yasa na nemi a samo min yar aiki shine aka kawo min ke,naji dadin zama dake saboda kirkin ki tarbiyar ki,nutsuwa kamala da sauran su,shi yasa nake jinki kamar jinina kuma kece kika zamo mai share min hawaye a duk lokacin da suka xubo, kece madadin tauhed…….

💕💞💕💞💕💞💕💞💕ðŸ

wannan shafin kune members of Sirrinki Alkhairin ki group and Matan aure group godiya da sadaukarwa a gareku.

Allah ne sheda! by xee’abu safana

hakane anty dukda haka kisa hakuri a ranki kinji komai lokaci ne, kuma haihuwa nufin Allah ne kiyi hakuri kinji antyna!
to taslima nagode kinji Allah yai miki Albarka kije watsa ruwa kiyi sallah saiki zo muci abinci,
yawwa antyna ta uncle dina ko kefa harnaji dadi’murmushi kawai tai batace komai ba,
kwance take tana waya da tauhed yace’namesake (domin haka suke kiran junansu tace’ Na”am namesake Dina,

kinga wallahi nayi kewar ki Ina so inzo inganki gaskiya ni,
dariya tayi domin cikin shaqwaba yayi maganar tace’ soja mazan aiki karka tada hankalin ka Ina lapiya kuma Ina kular maka da kaina sosai da sosai, bana so kadamu kanka harkaje ka fara ramewa,
smilen yayi tareda shafa lallausan sajen sa yace’Allah sarki iyalina Allah yabrmu tare’amin mijina nakaina,

a haka suka cigaba da wayarsu taslima dake zaune, bayan tauhida ta kashe wayar tayi’dariya tare da fadin Kai Ana shan love a gurin nan anty wallahi kina son uncle dayawa shima kuma yana sonki, kuna burge ni wallahi,

Allah ko kanwata to kema zancigaba da miki addu’a Allah yabaki miji nagari kamar ki domin mata tagari ita tafi dacewa da miji nagari, shi isanya nakewa uncle dinki addu’a ko bayan ba raina Allah yabashi Mata tagari wacce zata kula dashi fiyeda ni,
haba anty ai dake zai kare rayuwar sa, insha Allah.

ohni! wai kuna bani mamaki kunsan fa rayuwar nan batada tabbas ba madawwa miya bace’ tadan wani lokaci ne,
dukda haka dai anty’to shikenan ina fatan kinshirya kayanki Dan kinsan gobe ne,kikace zakije kauye gurin umma, haba anty aikin san yadda nake dokin ganin ummana yau ai bazanyi baccin kirki ba, kinsani ummana Allah sarki,
au wato taki ce ke kadai ma ko?

au sorry ummanmu!
washe gari tunda safe taslima da driver suka dauki hanyar kauyen nasu da akwai nisa hakan yasa sai karfe3 na yamma suka shiga kauyen sukayi parking a kofar gida da gudu tashiga gidan tana kwalawa ummar ta tah Kira,
ummar datake duke tana hada itace a murhu tace’ wah nakeji kamar taslima, kafinta karasa taji an rungemeta dukkan su farin ciki suke kara ra, a fuskokin su,

daki suka nufa driver kuwa shigowa yayi da kayan bayan sungaisa da umma yasha ruwa yace’xai wuce.

Inna kuwa tanajin xuwan taslima ta dauko tabarma ta shinfida a tsakar gida tanata habaici da maganganu anje karuwanci andawo shine za’a shige daka a bawa uwa Dan abunda aka samo Ana karyar aiki akaje to aidai maji magani,
tundaga umma har task in a babu Wanda ya kulata, taslima ta fito da 20k dinda anty tauhida ta bada akawo wa umman da kuma tsaraba da kayan abinci da sutura, sosai umma ke godiya tana sawa tauhida albarka sannan takara yiwa taslima nasiha ta rike mutuncin ta tabama marar da kunya,

satin ta daya amma jitayi kamar tana kurkuku saboda axabar bakaken maganganu da mugun fata irin nasu baba da inna Dan haka 1week tayi tadawo kano,tacigaba da karatun ta DA kuma aikinta,,,,,,

💞💕💞💕💞💕💞
Allah ne shaida!

xee’abu safana mrs’Bamalli

this is your page safiyya lamba Ina godiya da nuna kulawa da kaunar littatafai na jinjina yar mutanen sakwatawa,

¶¶¶¶¶

cikin kula tauhida ta dubeta tace’taslima alfarma naxo nema a gurinki?

alfarma kuma ni anty,ai babu abunda zaki nema a gurina ki rasa shi, meh kike so anty!

aikine mai wahalar gaske taslima, aikine kuma na sirri sonake yazama sirri tsakanin na dake,sai Wanda xaiyi aikin?

1 2 3Next page

Leave a Reply

Back to top button