NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 3) 23

RAINA KAMA…!!
              (Kaga gayya)
          Bilyn Abdull ce????????
_______
      ASSALAMU ALAIKUM
      Tabbas da nayi niyyar ajiye RAINA KAMA saboda sakkayar da wasunku sukaimin, bazanyi ALLAH ya isa ga Wanda yafara fidda hotuna da nufin niceba, amma lallai koda ace aunty Ruk’ayya

ce ko Ummi da muka fito ciki d’aya Na barsu da ALLAH,  kai koda ace nina haifeta, ai kowacece ita ba dabba bace, kusan abinda ya dace da Wanda bai daceba, ba hotona nazo talla a social media ba, ????kukuma masu gani da yad’awa jikinku Na rawa wlhy kushirya fidda hak’ina dake kanku a kotinda bakuda abin biyana sai ayyukanku, kunyi domin Ku tozartani saidai baku rageni da komaiba sai kanku, wannan abun yay matuk’ar 6atan rai fiye da zatonku, har yanzu idan Na tura raina Na 6aci, wlhy bazan zubar da hawayena a banzaba akan wannan abun, sai ALLAH ya fiddamin hak’ina akan kowacece ta fara turawa da masu cigaba da yad’awa????, Ku miyasa Baku tura baku hotunanba? Da kunga Abu jikinku narawa kuhau yad’awa, saikace social media gidankune, ai cikinku babu Wanda baya banbance dai-dai da akasinsa, saboda kawai ina son nayi suna a gareku saina turo hotona nace kuyad’a, kwana nawama bana online d’in, inacan da damuwar son Na k’arasa muku abinda Na fara Ku kunan kuna cutar dani????????????.

       Kosuwaye suje suda ALLAH, ALLAH kuma zai tozartasu suma fiye da Wanda suka aikata a gareni, Dan Na tabbata wlhy su ba masoyana bane, duk masoyina bazai aikata haka a gareniba,???? kai ALLAH dai ya gaggauta sakamin kawai, bikin sallar da kowanne bawan ALLAH yake tsintar kansa a farinciki ammani kuka 6ata nawa da 6acin ran da bansan mafariba????.
__________
BOOK 3 ????????22
……………..Bata d’agaba dan haka ya maida wayarsa a aljihu yanufi d’akin da Abie yake jinya.
★★★★★★★★★
        Zazza6in da innarmu ta tashi dashi yasaka mama Rabi’a zuwa dubata da iyalanta duka, kasantuwarmu waje d’aya a yau saiya bamu damar tuntu6ar sauran y’an uwanmu mizai hana mu tunkari iyayenmu da batin sanin asalinsu?.
    Damacan ya Marwan ne matsalarmu, danshi muke shakka, amma Alhmdllh Munubiya ta lalla6a manashi ya amince. Hasalima shine ya tunkaresu kai tsaye da maganar.
        Da farko shiru duk sukayi basu amsashiba.
       Saida ya Fadeel yace, “please iyayanmu Ku taimakemu Ku fiddamu daga wannan duhun, muma cike muke da shauk’in son sanin ina danginku suke, maybe hakan zai rage mana rad’ad’i da kewarsu, amma kuyi hak’uri idan mun Shiga hurumin daba namuba”.
  
     Innarmu ta sauke ajiyar zuya daga kwancen datake, ta kalli Mama Rabi’a datai k’asa dakai idonta cike da kwalla, tashi innarmu tayi zaune tana kallonmu d’aya bayan d’aya, ganin duk mun zuba musu idanu saita murmusa, cikin dakiya tace, “Nasan wannan tambayar ta dad’e tana cinku tsawon shekaru, dukda nuna mana da kuke Na buk’atar sanin su wanene mu amma muna sharewa, ina mai muku albishir da lallai wannan karon zaku samu dukkan amsoshinku daga garemu, amma ta hanya guda d’aya tak”.
        Kallon juna muka shigayi, kowa yana mamakin wace hanyace wannan?.
      Murmushi innarmu ta sakeyi, tana fad’in “karku zurfafa tunani, hanyar dai bata wuce shirya tafiya gaba d’ayanmu domin waiwayar ahalinmu ba, duk da kuwa su basa buk’atarmu a cikinsu, saboda kasantuwarmu jinsin da basa baraba dashi a tsarinsu, jinsin da basu shirya kar6aba saboda wani al’adar banza mara amfani da amfanarwa, sun mata dukkan saurinsu sai sunjira ALLAH. Munaya yanzu kece kad’ai matsalarmu, saboda bamusan ko mijinki zai aminceba, amma ki tambayesa, inhar ya amince to lallai k’arshen satin sama zamu tafi”.
         Gaba d’ayanmu farincikine ya baibayemu, kowa fuskarsa a washe, ya Marwan sarkin miskilanci ne kawai yay d’an murmushi, amma fuskarsa shima ta nuna alamar jin dad’in hakan.
      Farin cikin damuke ciki yasani bamma San Galadima ya kiraniba, saida Na d’auki wayar da nufin kiransa na fad’a masan zancen tafiyarmu ne sannan naga kiran, idanu Na waro waje, Na mik’e ina barin cikinsu Ayusher danma karsu isheni da hayaniya.
       Harta tsinke bai d’agaminba, nakuma kira nanma baiyi picking ba, sainaji duk babu dad’i, kardai fushi yayi?, k’ok’arin rubuta masa massege Na fara saiga kiransa ya shigo.
       ‘Dagawa nayi da sauke ajiyar zuciya, Galadima dake zaune bakin gado sanye da bathrobe Dan yana wanka taita kira. Murmushi yayi mai sauti har tana jiyoshi, cikin sanyin Murya yace, “wannan ajiyar zuciyarfa?”.
          Tsayuwa Munaya ta gyara, da y’ar shagwa6a tace, “Ba kaineba”.
       “Tofa, ni jikan Abubakar da Abdul-fatah, ni minayi kuma?”.
       “Shine naketa kira kak’i d’agawa”.
      “O, Na ramane nima. d’azun ban kiraki ba? Amma baki d’agaba, bakuma ki biyoniba, awa nawa kenan?”.
        “Kayi hak’uri My king, wlhy ban kulaba sai yanzu, hirace ta d’auke hankalina, Su Ayusher duk sunzo duba Innarmu”.
        “Humm, toya jikin inna?”.
      “Alhmdllh ai tama warware, yasu Momma da jikin Abie”.
        “Everything Alhmddllh, ina maganarmu ta tsaya?”.
         Dafe kai Munaya tayi, ta zauna saman katifar su Aryaan, tawani narke murya da shagwa6eta, “Haba yalla6ai miyasa kakeda son maida zance bayane? Ba mungama da wannaba?”.
        ‘Dan kausasa muryarsa yayi. Yace, “Munaaya! Nagaji da wannan yawo da hankalin, shin wai k kam bakida tausayine? Nifa ba dutse bane, ko har yanzu baki yafemin kuskurena bane ba?”.
        “Kayi hak’uri to, dama yanzu wata mafita Na samo, dan wlhy kunya nakeji, bazan iya tunkarar inna nace mata zan komo ba”.
      Kamar bazaiyi maganaba, harma Munaya ta fidda tsammani saikuma taji muryarsa a sanyaye yace, “Miye  mafitar?”.
          Kwanciya munaya ta gyara jin tafara samo Kansa, Dan burinta kawai ya amince suyi tafiyar, sauran zance saita dawo sayi.
   tace, “Yauwa Autan Momma bud’e kunnenka da k’yau kasha labari”.
        Murmusawa yay kawai yana zamewa ya kwanta shima, wayonta Na birgeshi, inhar zai 6ata rai akan Abu tasan hanyar da zatabi ta bashi nutsuwa. yace, “ina jinki”.
        A nutse tabashi labarin zuwansu Niger domin ganin danginsu inna, a salon data fahimtar da shid’in lallai ya fahimta, saidai amsa zai barta zuwane yad’anso yin gardama, saida ta kalallameshi da dad’in baki da magiya sannan ya amince akan shima zai biyo bayansu, daga nan zai d’akkota su taho. Kai tsaye tace ta amince. Yayi farin cikin da hakan, yabata labarin shima yanda sukayi da Dr Ajay.
      Yanda ta nuna tsantsar farin cikinta da murna akan lamarinne Yakuma saka masa nutsuwa akanta, soyayyar da takema mahaifansa da dukkan ahalinsa shine makamin farko data fara amfani dashi wajen bige dukkan yak’ininsa akan shirin Auren contract, takuma k’ara kima da daraja a idonsa.
       Daganan suka cigaba da hirarsu ta soyayya anutse, abin akwai birgewa. Yace saita sakashi yayi barci sannan zata kashe, wannan ne punishment d’inta.
    Babu yanda ta iya dole ta bishi yanda yakeso, har saida taji tsitt alamar yay barcin da gaske sannan ta kashe tana dariyar wannan shagwa6a ta Galadima, a yanzu Idan yamata wani abun takanyi mamakin dama haka yake?.
        Aiko data koma d’aki tasha tsiya wajensu Feena, sai banza tamusu sukayi mai isarsu.
********
          Kamar yanda shirye-shiryen tafiyarsu Munaya Niger ta kankama haka shirin kai Abie Kashmir wajen Doctor Erfan Fahad Sajaad ta kankama suma.
      Y’an gidansu Munaya dai ansamu abinyi, sai gulmace-gulmace da gugar zana sukeyi akan wannan tafiya, harda masu fad’in talauci da wahalane ya koro su inna, yanzu anga ansamu arzik’i za’a koma k’auye amusu iyayi da farfaganda.
       Duk abinda ke faruwa Inna naji kuma tana saurare, amma baiwar ALLAH sai dai tayi Murmushi kawai, takuma hana su Munaya cewa komai, har Innaro saida ta yaddama Inna habaici akan wannan tafiya. Su Maman ya Hameed akaita dariyar gatsatsa.
     Wannan abin da inna taga sunayi ya sakata rok’on Abba akan tafiyarnan yakamata ace Innaro ma aje da ita.
       Abba bai kawo komai a ransa ba ya amince, harma ya nuna mata farin cikinsa, yakuma shiga yima Innaro shiri itama
__________
      Dukkan shirin da ake buk’ata nakai Abie Kashmir ya mammala, Galadima da doctor Ajay da Dr Akash ne kawai zasuje, Anbar su Momma gida su huta, duk da taso binsu amma Galadima ya lalla6a ta dai ta zauna.
      Ta jirgi suka tafi, dukda bawani insane mai yawaba, to amma jikin Abie bayason yawan matsala da takurar zafi. Suna Isa Ambulance tazo ta d’aukesu.
           Asibitin bawani k’ato baneba, hasalima Wanda Abba ke ciki a new Delhi yafi wannan girma da k’ayatuwa, dukda shima wannan d’in ya had’u bakin gwargwado, sunkai 3hours zaune basu sami ganin doctor Erfan ba, dukda kuwa shine yabasu wannan date d’in domin ganinsa, andai shiga da Abie wani d’aki tun zuwansu.
    Ran Galadima ya fara 6aci, abinka da ba sabawa yay da hakan ba, zai fara k’orafi saiga doctor Erfan Fahad ya fito daga wani d’aki, da alama ma wani aikin yayi a ciki, su Galadima basuga fuskarsa ba harya shige Inda suke tunanin Office d’insane.
       Wajen 30minute’s da shigarsa sannan aka basu izinin shiga.
    Sai wani cika da batsewa Galadima yakeyi Na haushi, shi dai Dr Ajay yanata lallashinsa akan inhar zasu sami biyan buk’ata ai hakan ba komai baneba.
    K’ala dai Galadima bai ceba.
     Doctor Erfan Fahad Sajaad, matashin likita dabazai wuce sa’ar Galadima ba, k’yak’yk’yawan ba indiye mai tashe da lokacinsa, Wanda duniyace ke amfanuwa da fik’irarsa bawai India ko yankin Kashmir kawaiba.
      Kallo d’aya Galadima yamasa ya d’auke kansa, Dr Erfan ya ajiye file d’in Abie dayake dubawa yana fad’in “Kuyi hak’uri dani Brother’s, aikine babba ya dinkareni daga cika alk’awarin Dana muku, gashi kuma Na gaggawa”.
      Galadima ya juyo da nufin juye masa abinda ke ransa sai kawai doctor Erfan Fahad yad’anyi baya cikin mamaki. Yace, “Waishi wama nake gani a gabana kamar Muhammad Sameer Saifuddin?”.
       Galadima da mamaki ya kasheshi yace, “lallai shine, amma a ina kaimin wannan sanin haka?”.
      Wata dariya Dr Erfan Fahad yayi, yad’an bigi tebir d’in gabansa yana fad’in “Duniya labari, Muhammad Sameer Saifuddin kenan! Nikam kaga koda saida muka tsufa Na ganka saina ganeka wlhy, shin zaka iya tuna wani Wanda kukai karatun Addini shekaru 19 da suka shige a wajen Sheaik Mu’azzam Abdul’aziz khan?”.
      Shiru Galadima yay ya lula duniyar tunani, Dan a yanzu yad’an fara d’ago fuskar Dr Erfan Fahad d’in.
     Dr Erfan Fahad ya d’an daki kafad’arsa cikin dariya, “My friend mu ajiye wannan chapter d’in, tana buk’atar nata time d’in, amma lallai nayi farincikin ganinka bayan tsawon shekaru Dana d’auka wajen nemanka, kardai kacemin har yanzu Abie yana jinya?”.
      Ajiyar Zuciya Galadima ya sauke yana jinjina kai, danshikam tunanine dank’are a ransa gameda Dr Erfan Fahad Sajaad d’in.
      Dr Erfan Fahad yace, “Abie ne mutum Na farko daya fara fad’omin a rai bayan zamana cikakken likita kwararre ta fannin irin matsalarsa, sai dai duk tunanina shi yasamu lafiya, Ashe yanata ibadar ALLAH har yanzu, insha ALLAH matsalarsa tazo k’arshe kuwa, Doctor Ajay nadawo gareka, ina buk’atar k’arin bayani gameda magunguna da Abie yakesha?”.
     Dalla-dalla Dr Ajay ya shiga ma Dr Erfan Fahad bayani, Galadima dai Na saurarensu, dukda Rabin hankalinsa naga son tunano wanene Dr Erfan Fahad?.
        Bayan Dr Erfan Fahad yagama sauraren Dr Ajay, shima yaymusu bayani dalla-dalla akan alurai daza’a dungama Abie duk bayan wasu awanni. Allurarce zata zama makarin wannan ruwan guba daya gauraye dukkan jijiyoyinsa, ahankali zasu fara motsawa daga dakatar dasu aikin da akayi da wancan poison d’in, daga nan ga66an jikinsa saisu fara aiki insha ALLAH.
    Dukda nauyin tsadar wannan Allurai haka Galadima ya amsa, yasan tattalin arzik’insa ba k’aramar girgiza zaiyiba, Dan harma saiya had’a da saida wasu kadarori, bashida burin dayafi yaga Abie yasamu lafiya, koda ace dukkan dukiyarsa zata salwanta bazaiyi bak’in cikiba, fatanshima ALLAH yabashi ikon had’a dukkan kud’ad’en da ake buk’atar batareda ya dogara da taimakon kowaba.
          Masauki Na musamman Dr Erfan Fahad yabama su Galadima, dukda Akash yashiga gari ya sama musu, amma Dr Erfan Fahad yace Sam bazai yuwuba, a gidansa zasu sauka tilas.
    Bayan sun sami nutsuwa, Galadima yayi wanka ya kira Momma yamata bayani akan komai, hankalinta ya tashi kwarai da gaske, Dan kud’ine masu yawa, wad’anda tana k’yautata zaton dawuya ace Galadima yanadasu gaba d’aya.
     Amma jarumin naku saiya shiga kwantar mata da hankali akan Neman nasara da addu’arta.
      Fatan alkairi taita masa da fatan dacewa.
    Yana yanke wayar ya kira Baffi suka tattauna shima akan kaddarorinsa daya kamata a saida, danshima dai shine lauyan nasa.
    Sosai Baffi ya tausaya masa, Inda ace shid’in wanine tabbas daya taimakama Galadima da iya k’arfinsa, amma ina, a abinda ake buk’ata shiba komai baneba, Dan ko kud’in ruwan allura d’aya ba iya saya masa zaiyiba.
       Haka ya shiga shigi da fici akan dukkan abinda ya dace.
     A nanma Galadima ba zama yayba, washe gari yabaro Kashmir shida Akash suka dawo India, Dr Ajay kawai suka baro can, wasu kud’ad’en ya fara turawa dake hannunsa, Dr Erfan Fahad yafara treatment d’in Abie.
       
**********
     Busy da Galadima yayi yasaka shi da Munaya waya sai time to time sukeyinta, a koda yaushe kuma cikin kwantar masa da hankali take, a Daren da zasu wuce Niger nema suka d’anyi doguwar hira, yayta shinfid’a mata dokoki akan yaransa, ita dariyama abin yayta bata, ta dai danne da binsa da to Dan a zauna lafiya, ta d’ira da masa godiyar hidimar da yasaka Muftahu ya kawo musu da sunan tsaraba da dukkan abinda zasu buk’ata, wai ba sai sunje sunkaima mutane nauyiba.
      Washe gari suka Nufi Niger Republic cike da zumud’in son kasancewa da ahalin mahaifansu.
     Tafiyace da sukayi cikin isassun motoci babu takura, Dan Galadima motoci ya aiko musu har hud’u, wad’anda zasu iya jurar dukkan wata wahalar shiga sahara, tareda kwararrun driver’s da sukasan hanya. gashi basuda matsalar Abinci dan sun tanadi abinsu. Tafiyar sassafe sukayi. Dukda sakko da sukayi basu sami shiga Agadas ba a ranar, dole suka sami mafaka suka kwana, ranardai kam babu maganar waya da kowa dake Nigeria, balle kuma su Galadima. Sosai Munaya taji kewar mijinta, balle da taga su Munubiya nata soyewarsu, hasalima d’aki d’aya suka sauka a masaukin, itakam itada laraba saboda kula da yara.
     Ya Marwan kam shi ai gaba ta kaishi, dan wannan damar ya samu ya more amarcinsa, Dama an dad’e ba’a had’uba????.
     Dukda magiyar da Munubiya taita masa akan yabari saisun koma gida amma yace Sam bama ta isaba, yaudai saiya lasa, dole ta barshi yayi yanda yakeso harma da bashi gudunmawa, dan sunyi missing juna, saidaga baya taita masa zun6ure-zun6uren baki, shikam yayata mata tsiya da gwalo.
       Da safe Munaya yanayinta kawai ta kalla taita shek’a dariyar mugunta, harda Munubiya ta tsargu. Su Feena nata tambayar Miye?.
    Munaya tace, “kuma Ku gano da kanku, dan babu ruwana”.
       Su Ayusher dai basu fahimci komaiba, har Munaya tagama shak’iyancinta tayi shiru a motar.
     Yau d’inma dai sai yammaci lik’is suka isa Cikin Birnin Agadaz.
     Dan anata kiraye-kirayen sallar Magrib.
     Tunda suka shigo garin inna tai zugum tana tuna wasu shud’ad’d’un shekaru da abubuwa masu yawa suka faru, babu inda tagane saboda dad’ewar da sukai da barin tushensu, garama ita, mama Rabi’a ma bata fahimci komaiba ita, dan wayonta a wancan lokacin baikai Na inna ba.
       Kula da damuwar da inna take cikine ya sama Abba kama hannunta ya rumtse a nashi alamar lallashi. Batace dashi komaiba, sai d’ora kanta datai gefen kafad’arsa.
     Driver dake driving motar dasu innar suke ciki yace, “Hajiya ina muka dosa to?”.
     Shiru Inna tayi takasa magana, saboda kuka daya taho mata, tana fargabar ko zasu sami k’ar6a daga ahalin nasu kokuwa sa6ananin hakan, gashi harda uwar gayya sukayo.
      Mama Rabi’a ce tai k’arfin halin cewa “Zamuje masarautar garinne”.
      Daga Abba har Abbansu Feena kallonta sukayi da matuk’ar mamaki, mama Rabi’a dai tai k’asa da kanta, dan batada bakin amsa musu dukkan tuhumarsu. Inna kam ai saita fashe da kuka k’asa-k’asa.
     To Mudai bamusan ina aka dosaba, kallon gari kawaine namu, ni inata fama da Abdurraheem ma dake kukan gajiya, nasan wanka kawai suke buk’ata, shine zaimin bore, ALLAH ma ya soni Sauran basu d’auki amshiba, dan duk suna hannun su Feena da muke tare a motar.
      Innaro dai tanata baza ido da ta6e baki, burinta dai a Isa taga abinda yasa aka tasosu daga wata uwa duniya.
     ????innaronmu ta mutunci badai za’a canjaba kam.????????
        Duhun da dare ya farane yasa bamu fahimci inda muka iso ba, inna tasan baza’a ta6a barinsu shiga masarautarba kai tsaye, Dan haka ta fita daga motar, takai mintuna kusan 20 tana fama da masu tsaron k’ofar, amma sunk’i aminta da shigarsu, dukda kamaninta da suke hangowa dana ahalin masarautar.
     Ana cikin haka saiga wani matashin saurayi dabazai wuce sa’ansu Yaa Marwan ba. Yanda yake tafiya cikin tsari da Isa zai tabbatar maka shi jinin gidanne, masu tsaron k’ofar duk suka zube k’asa suna masa barka da fitowa, bai amsa musuba sai inna da yaketa faman bi da kallo, itama dai idonta na’a kansa.
     Kamannin mahaifinta take kallo tsaf tattare da saurayin, yayinda shima dai take masa tsananin kama da nasa ahalin, ya d’auke kai da nufin barin wajen batareda ya tankama innarba, murmushi tayi kawai, Dan shariya da Isar mulki wannan jinin gidansune, shiyyasa mafi yawan lokaci ba hak’urine kawai ke sakata share haukar y’an gidansuba, harda wannan halayyar data zama jinin jiki.
     Cikin harshen buzanci tamasa magana.
    Cak ya tsaya, kusan wasu seconds sai kuma ya juyo yana kallonta.
      Inna tace, “dukda banida hurumin tambayarka wanene kai a masarautar nan, domin yanayinka ya tabbatar min kasancewarka jinin gidan, ina rok’onka alfarmar tambaya da kuma taimako”.
     Nanma kallonta kawai yake, tamkar bazaiyi maganaba saikuma ya matso gabanta, alamar yana saurarenta.
      Sunayen mutum uku ta lissafo masa akan ko sunada rai.
       Da mamaki sosai yake kallonta, dukda yanayinta ya nuna ita buzuwace, amma ba mazauniyar wannan yankinba, Dan suturarta da wasu abubuwa da dama ya banbantata al’ummar yankin, gashi kuma ta lissafa masa sunayen manyan mutane masu daraja a masarautar.
     Shima cikin harshen buzancin hace, “baiwar ALLAH ked’in wacece?”.
        “ta hanyar shiga damu wannan gidan kawai zakasan wacece ni”.
     ‘Dan jim yay alamar tunani, zuwa can sai yace, “ina zuwa to”.
     Kai inna ta jinjina masa, ya koma ciki, inna kuma tadawo jikin motarsu tana bama su Abba hak’uri.
    Sukace karta damu, tabi ahankali.
      Kusan mintuna 30 saiga saurayinnan ya dawo tare da wasu tsoffi biyu, inna Na hangosu ta nufosu itama, bata ganesuba, amma haka ta risina tana gaishesu cikin yarensu.
       ‘Daya a cikinsu tamata wasu y’an tambayoyi, duk inna ta amsa mata kai tsaye, mamaki ya kamata, takuma jeho mata wata tambayar, nanma dai inna ta amsa.
      Tsohuwa tayi murmushi, sannan tabama masu tsaron k’ofar umarnin barin motocin su inna shiga cikin masarautar.
     Inna taji dad’i sosai, taita mata godiya.
          Shigarmu katafaren gidan mai yalwace da haske a ko inane yabamu mamaki, bayan driver’s d’in sun faka motocin inda aka nuna musu duk muka fito, mudai kallon kallo muka koma a tsakaninmu, Dan munga abinda ya girmi tunaninmu, hadimai sai kai kawo sukeyi dukda duhun dare.
      Iya abinda zamu iya buk’ata kawai aka fidda mana a motocinmu, tsaffinan da matashin saurayi daya maidamu television sukai mana iso wani Sashe, babu kowa amma cike yake da komai Na buk’atar rayuwa, yayinda kwanmu da kwarkwatarmu zai ishemu mu sakata mu wala.
      Mun gaida tsoffi nan dukda bamu da tabbacin sun iya Hausa, amma a mamakinmu duk sai suka amsa mana, suka kuma mana sannu da zuwa sannan suka fita, amma banda wannan saurayi daya koma gefe ya zubama dukkan wani motsinmu ido, musamman ma mu hud’unnan, Ni munubiya Ayusher Feena, bansan miyake kallo tattare damuba, nidai damun had’a ido dashi saina zuba masa harara, yakanyi murmushi ya d’auke kai, Ashe sauran y’an uwanama hakance ke faruwa a tsakaninsu dashi. Yaa Marwan da Fadeel kuma suna lura daduk abinda ke faruwa, amma suka k’i cewa uffan. Dan yak’ima kowa magana a cikin mu, shiyyasa muma duk mukayi watsi da lamarinsa, babu Wanda ya tanka masa.
        Babu jimawa saiga tsoffi nan sun dawo tare da wasu y’ammata kusan goma, kowacce abinda ke hannunta ta ajiye, sannan duk suka durk’usa suna gaishemu.
      Tsoffi suka sake zama muka gaisa, sannan suka nunamana d’akunan barci, dacewar mu huta zuwa safiya koma mikenan dai saji.
     Innaro dai bin kowa take da ido, ga gajiya Na cinta ga tambaya fal ranta, dasun had’a ido da inna saita sakar mata murmushi kawai, hakama Abba da abbansu Ayusher, saibin matan nasu suke da kallon tuhuma, amma su inna sunk’i bada dukkan k’ofar da kowa zai fahimci wani Abu.
       Saurayinan ya fice bai tankama kowaba, yana fita muka shiga ta6e baki. Amma bamuce uffanba dai.
     Nace, “Ni dai bata abincinnan nakeba, nasami ruwa nayi wanka shine matsalata”.
     Hararata mama Rabi’a tayi, tana fad’in “Baki da tausayi Munaya, wad’annan bayin ALLAHn ai suke buk’atar duk wannan bakeba, musamman Abdurraheem dashi baima son takura Na kula”.
      “Yo mama nidai kaina Na sani wlhy”.
     Rankwashi Yaa Fadeel ya zubamin akai, Na dafe wajen idona Na cikowa da kwalla, “Amma Yaa Fadeel da zafifa?”.
     “Ai dankiji zafin namiki”.
       Yanda nahau matsar kwalla duk sai suka haumin dariya, hardasu Abba, haushin hakan yasani tashi Na shige d’akin dake kusa da inda muke zaune.
     Kutt d’akine k’ato, d’auke da makeken wani irin gado mai k’yau, saida nayi bismilla sannan Na fad’a saman gadon, Dan tsayawa muku lissafin had’uwar d’akin 6ata lokacine, ahaka Ayusher ta shigo ta sameni, muka 6ararraje abinmu.
    
    Bayan awa 3
   Duk d’inmu kowa yayi wanka ya canja kayan barci, yaranma an musu, munci abincin dai sama-sama, Dan ba irin cimar da muka saba baceba, amma dayake akwai fruits dawasu abubuwan irin shigen abincinmu sai muka harhad’a mukai nak, garin dad’an sanyi gaskiya, aka nad’e su Ameen cikin kayan sanyi su duka,  kowa d’akin da yay wanka yakoma ya kwanta a matsayin masauki.
    Mudai tare da innaro da laraba muka kwana, saboda matsalar yara.
    To dayakema kowa gajiya taci k’aniyarsa lafiyar ALLAH mukasha barcinmu, amma wlhy akwai d’an karen sanyi, Dan zuwa asubahi harda wata iska mai azabar sanyi daban tsoro, ALLAH ma yasomu akwai manyan barguna a d’akunan, gakuma ko ina ruf an d’auki mataki, da alama sun saba da kayansu su dama.
      Tunda safe sosai aka kawo mana karin kumallo a kuloli masu k’yau.
       Mudai kam bama mu tashiba, saisu innarmu, koda hadiman dazasu mana gyaran sashe. Sukazo sai komawa sukayi, dan barci muke, su Abba ne kawai suka tashi dasu innarmu.
    
     Kusan awanni biyu da kawo abincin tsoffi nan sukazo kiran inna, sai suka tafi da mama Rabi’a, mu munatama barcinmu bamusan duk anayiba.
     Tunda suka fito idon Inna ya cika da hawaye, yau sune a mahaifarsu, bayan tsawon shekaru da suka d’auka basannan, sosai masarautar ta canja, an k’awatata fiye da da, abubuwan cigaba masu d’unbin yawa sun yalwatu a cikinta, ga gine-gine Na k’awa da akayiyyi cikin masarautar.
     Itama dai mama Rabi’a bata tuno komai dan sanda sukabar masarautar bama tasan kantaba.
       Sun isa wani Sashe mai girman gaske da k’awa, kamar yanda kowanne bango yake da hoton Rak’umi haka shima wannan, an k’awatashi da hoton rak’uma har Uku, hadimai sai mik’a gaisuwa suke gasu inna, nasudai d’aga hannu da murmushi, Dan ita inna ta mance abubuwan da yawa da suka shafi tsarin masarautar tasu, to bama wayaune da itaba awancan lokacin, sai y’an abubuwan daba’a rasaba.
     Sun Isa katafaren falon daya k’awatu da kayan alatu irin Na yankin nasu, basu tsaya ananba sai a wani dake gabansa.
     Buzuwar tsohuwa ce k’yak’yk’yawa, mai cike da d’umbin kamala da halin dattako, tana zaune bisa wata darduma ruwan goro, hadimai biyu namata hidima.
       Batako d’ago kai ta kalli kowaba, dukda tasan da shigowar su inna, Tsoffi nan guda biyu suka rissina suna sanar mata zuwan su inna.
         Mayafin dake yane da jikinta Na yadin lafaya irin kayan buzaye ta janye saboda rufe mata rabin fuska da tayi, ta d’ago kai tana kallonsu inna Wanda suma itad’in suke kallo.
       Wani Murmushi ta sakar musu Na musamman, yayinda idonta ke binsu da kallon k’urilla mai nuna alamun kallon kamannin wani a jikinsu.
     Cikin yarensu Na buzaye tama tsoffin da hadiman Umarnin ficewa.
     Saida suka fita sannan ta yafito su inna alamun su matso gareta.
     Inna da mama Rabi’a suka matsa inda take, ta kamo hannayensu ta rik’e a nata tana murzawa, kusan mintuna biyu, sudai su inna Na kallonta, tamusu nuni da subata tafin k’afarsu ma.
      Inna a ranta tana mamakin kenan har yanzu canfe-canfe da muguwar al’adar gidan Na nan dai?…..
     Tunaninta ya katse lokacin dataji hannun tsohuwarnan bisa fukarta, kallon juna sukayi itada mama Rabi’a, sannan suka maida kallonsu ga tsohuwar da idonta ke a rufe tana murmushi da cigaba da shafa fuskokinsu.
      Kusan mintuna biyu sannan ta bud’e ido akansu, race, “lallai kud’in ahalin wannan gidane Na gaskiya, masu tafe da babban abin al’ajab da ba’a ta6a samuba a wannan masarautar, barkabku da dawowa hamshak’iyar masarauta mai d’unbin tarihi da yalwar arzik’i, minene sunayenku?”.
       Cikin had’iye yawu inna tace, “Ni Ai’sha, itakuma Rabi’a ”.
      Tsohuwa tayi murmushi mai k’ayatarwa, sannan tajawo kaskon wuta dake cike da rushi gabanta, ta bud’e wani kasko mai k’yau ta zuba garwashi kusan bakwai sannan ta saka turare mai d’unbin yawa a ciki, dandanan wani k’amshi ya baibaye falon, gabansu inna ta tura kaskon, ta jawo wani mayafi ta mik’a musu da musu nuni su rufa dashi.
     Basuyi musuba, Dan ita inna duktasan hakan al’adar masarautar suce. Haka suka shige mayafin k’amshin yanata baibayesu, kusan mintuna biyar ta bud’esu da kanta.
     Babu Wanda yay magana tsakanin ita da su, saiga mutane sun fara shigowa d’ai-d’ai cikin falon.
     Kowacce cikin shiga ta alfarma irinta cikakkun Buzaye, hakama mazan, kowanne fuska a nad’e cikin rawani.
     Dukkan mai ruwa da tsaki saida yagama hallara, adadin wasu mintuna saikuma ga wani dattijo mai cike da tarin kamala ya fito ta wata k’ofa daban, a tare dashi da mata biyu suma cikin nutsuwa, kowa saida ya mik’e a falon har wannan tsohuwa.
    Dattijo ya zauna bisa kujera dake gefe, sannan kowama ya zauna, cikin risinawa sukaita gaisheshi, kansa kawai yake jinjina musu, hakanne yasakasu inna fahimtar lallai wannan shine Sarki mai mulki a wannan masarauta yanzu.
     A cikin nutsuwa yay magana, idonsa nakan mama Rabi’a da inna.
      “Lale marhabun da dawowarku wannan masarautar mai d’unbin tarihi da dattako, mai takaici dakuma dana sanin farrak’a mafi yawan ahalinta bisaga bahaguwar al’ada mai durk’usar da kowanne irin ahali”.
     Idon Inna cike da kwalla, da d’okantuwa da furucin wannan adalin Sarki mai kama da jirwayen nadamar kasatuwar abinda ya wanzu abaya dama Wanda basuda tabbacin faruwarsa ko dakatawarsa.
       “Muna godiya mai cike da girmamawa da farin cikin waiwayen bayanmu dukda muna tare da fargabar koza’a kar6emu, amma lallai an ciremu daga wannan fargabar da muka shigo da ita wannan yanki”.
       Dattijo ya jinjina kansa yana murmushi.
      Tsohuwar d’azunce ta kalli dattijon Sarki, ta buk’aci shigowar sauran tawagar bak’in dasu inna sukazo dasu.
       Kai tsaye yabada izini.
    Kwammu da kwarkwatarmu muka shigo, hardasu Aiyaan dasu Innaro, duk muna d’auke dasu Amaturrahman, nanma dai abin kallon muka gani da mamaki, tamkar yanda muka baro wasu abaya, mun kasa fahimtar inane su Innarmu suka kawomu kuma?.
     Gaisuwa mukaiyi irin wadda muka iya, hakama su Abbanmu da aka bama wajen zama Na musamman a gefen wannan dattijo.
     Duk sun kar6a mana a yanayin kallo da son sanin su waye mu?.
      Irin turaren da akaima su inna suma su Munaya saida aka musu, dukda su ba’a rufesuba, aiko su Meenal sukaita atishawa, mudai harma muka tsargu.
         Tsohuwar nan daice ta mik’e tana Neman sanin daga ina muke? Su waye kuma su inna?.
      Inna ta mik’e tsaye, cike da girmamawa ta maimaita musu sunanta, sannan tafara koro bayani kamar haka………………????
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button