YANA TAFE bisa wani ingarman doki sanye da tufafi na alfarma ya ratso ta cikin Birnin. Duk inda ya wuce saidai kaga jama’a nata kallonsa saboda kwararan dalilai guda uku. Dalili na farko shine,tufafin dake sanye a jikinsa wanda babu mai iya sanyasu face shahararren ATTAJIRI ko kasaitaccen BASARAKE mai amsa sunansa. Dalili na biyu kuma ya kasance kyakkyawan saurayi na kwatance wanda dole ‘yanmata su yaba. Dalili na uku kuwa shine ya kasance GWARZON NAMIJI mai kirar sadaukai. Kash!rashin sani yafi dare duhu,inda ‘yan mata sun san matsalar wannan kyakkyawan sauarayi da sunce akai kasuwa.Haka dai wannan saurayi yaci gaba da tafiya a cikin babban birnin da ya shigo mai suna RAUHUL BAHADAR yana tambayar hanyar da zata kaishi izuwa fadar birnin ana nuna masa harya iso. Fadace kasaitacciya ta gani ta fada domin an kashe dukiya mai yawan gaske wajen ginata.Kaida gani kasan cewa an shirya Aljannar duniya a cikin wannan gidan sarautar. SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA na zaune bisa karagar mulki fadawanta sun kewayeta kuma fadar ta cika makil da jama’a ana gudanar da harkokin mulki,sai ga wannan bakon saurayi an shigo dashi dakaru kimanin su goma na zagaye dashi don tabbatar da tsaro.Ba’a bari wannan bakon saurayi ya kusanci inda karagar take ba har saida aka je aka gaya mata cewar yazo ne yana son ganinta sannnan ta bayar da izinin a gabatar dashi,aka rako shi aka gurfanar dashi da tazarar kimanin taku goma a tsakaninsu da ita. Bayan dukkanin dakarun dake cikin fadar sun tsaida hankalinsu a kansa kuma sun dafe kufen takubbansu suna jiran ko ta kwana. Saurayin ya zube kasa bisa guiwoyinsa a gaban sarauniya Akisatul Sauwar cikin biyayya ya kwashi gaisuwa.Cikin murmushi da annuri fuskar Akisatul Sauwar ta karbi gaisuwar sannan tace,ya kai wannan bakon saurayi ma’abocin kwarjini mene ne ya kawika kasata kuma menene dalilin dayasa kake son ka gana dani? Lokacin da saurayin yaji wannan tambaya sai ya sake risinawa cikin ladabi yace,ya shugabata ni dai sunana YARIMA LUBAINU IBIN SALLUR.Mahaifin a shine Sarkin wani babban birni da ake kira ZAMRUL a can wata nahiya dake yammacin wannan nahiya taku. Ba wani abu bane yasa na baro kasarmu ba face neman inda kogin BAHAR IMFAL yake.Koda jin wannan batu sai gaba daya mutanen dake fadar suka bude baki suna kallonsa cikin tsananin al’ajabi kuma suna yi masa kallon mahaukaci. Ba komai ne ya janyi hakan ba face sanin cewa babu wanda zai bukaci zuwa inda kogin Bahar Imfal yake ba face wanda ya gaji da duniyar yake neman ajalinsa. Duk da cewar Yarima Lubainu ya lura da irin kallon da jama’a keyi masa a cikin fadar sai ya basar ya sake duban sarauniya Akisatul Sauwara yace,Na sami labari cewa akwai cikakken tarihin kogin bahar imfal a wannan masarauta taki. Akwai wani magani da nake so naje na samo a cikin kogin Bahar Imfal kuma bokaye sun tabbatar mini da cewa saina sami cikakken tarihin kogin idan ina son na sami nasarar riskar inda yake har ma na sami nasarar shiga cikinsa na debo maganin danake nema. Koda Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara da dukkanin fadawanta da sauran jama’ar dake cikin fadar suka bushe da dariya. Al’amarin dayai mutukar bashi mamaki kenan ya rinka kallon kowa da kowa. Daga can sai kuma sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta tsuke bakinta ta hade fuska tana mai duba Lubainu a cikin nutsuwa tace,Yakai wanna dan Sarki kayi sani cewa abinda kake nema daidai yake da neman jaki mai kaho.Tabbas akwai tarihin kogon Bahar Imfal a cikin gidan sarautar nan,amma wani sashi ne daga cikin tarihin ba gaba dayansa bane. Mahaifina kafin mutuwarsa ya tabbatar mini da cewa duk abinda mutum yake nema a cikin Kogin Bahar Imfal ba zai sameshi ba face ya karance gaba daya rubutaccen tarihin kogin.Shidai wannan tarihi an rubutashi ne a jikin wani Allo wanda aka rabashi gida uku.Akan wannan Allo anyi yake yake marasa adadi,kuma milyoyin rayuka sun salwanta.A yanzu haka kaso daya na wannan Allo ne a hannuna,kaso na biyu yana hannun Sarki DARMASU na birnin Kimras. Daya kason kuwa na uku yana hannun wani takadirin boka wanda ake kira Da suna SARYANU IBINI DAUMUR. Lokacin da sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai Hankalin Yarima Lubainu ya DUGUNZUMA ainun ya rasa abinda yake masa dadi a duniya,cikin alamun damuwa ya dubi Sarauniya yace,Ya shugabata mene ne asalin tarihin wannan Allo mai dauke da tarihin Kogon Bahar Imfal,kuma yaya akayi ya rarrabu har kaso uku? Koda jin wannan tambya sai Sarauniya Akisatu Sauwar tayi murmushi tace,zan baka amsar wannan tambaya taka amma nima sai ka gaya min maganin da kake son ka debo a cikin kogin Bahar Imfal. Dajin haka sai hankalin Yarima Lubainu ya sake dugunzuma fiye da farko ya kama kallon jama’a ya kasa cewa komai. Daga can sai ya dubi Sarauniya yace,yake wannan sarauniya mai adalci kiyi sani cewa kin tambayeni wani babban sirri na rayuwata wanda bazan iya sanar dakeshiba anan cikin taro.Lallai akwai bukatar mu kebe kuma bazan iya gaya miki sirrin ba face kinyi alkawarin taimakona bisa tawa bukatar.Sa’adda sarauniya Akisatul Sauwara taji wanna jawabi na Yarima Lubainu sai itama jikinta yayi sanyi ta rasa abinda zatace,tayi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku,dagan can kuma saita dago kai ta dubi Yarima Lubainu tace,akwai bukatar nayi tunanin da nazari zuwa gobe,yanzu zan saka a kaika masaukin ka. Kafin Yarima Lubainu ya gama rufe bakinsa tuni Sarauniya ta kirawo wani hadiminta ta umarceshi daya tafi da Lubainu izuwa masauki. Tana gama fadin hakan ta mike tsaye daga kan karagar mulkinta ta juya ta shige izuwa cikin gidan sarautar,dakaru da kuyangi na take mata baya ana buga tambura ana busa algaita. Lokacin da aka kai Yarima Lubainu masaukinsa sai aka karrama shi ainun aka kaishi cikin wani daki na alfarma wanda ya kawatu ainun kuma aka kawo masa irin abincinsu na alfarma. Bayan Yarima Lubainu yayi wanka ya huce yar gajiyar dake jikinsa saiya zauna domin ya ci wannan abinci.Koda ya dauko lomar farko yakai bakinsa sai tunanin gida ya fado masa,nan take idanunsa suka ciki da kwalla ya kamu da tsananin bakin ciki har hawaye ya zubo masa.Bisa ba komai bane ya fado masa a rai ba face tunowa da masoyiyarsa YAZARINA…. pls Like nd comments……ALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 2 A can birnin Zamral Yazarina ta kasance tauraruwar mata wacce babu kamarta a fagen kyau,kuma tun suna yara ita da Yarima Lubainu jininsu ya hadu sosai har suka fara girma suka kama soyayya.Rana tsaka Yarima MANGUL da ga Sarki Alkas dake mulkin kasar dake makwabtaka da birnin Zamrul yaga Yazarina ya rude kuma ya dimauce a cikin begenta da kaunarta.Bisa wannan dalili ne mahaifinsa sarki Alkasa ya taso da kansa yazo har Birnin Zamrul ya nemawa dansa auren Yazarina a wajen mahaifinta wanda ake kira da ABU YAZARINA.Shi dai Abu Yazarina ya kasance gawurtaccen Attajiri a Birnin Zamral wanda babu kamarsa a nahiyar,kuma duk sarakunan dake nahiyar abokan kasuwancinsa ne.Lokacin da Sarki Alkas yazo birnin Zamral ya kadaita da Attajiri Abu Yazarina sai ya dubeshi yace,ya kai tsohon abokina kayi sani cewa dana Yarima Mangul ya kyallara ido yaga ‘yarka yayin da taje bikin cin kasuwar birnina wacce aka saba yi duk shekara.Ina mai sanar dakai cewa tun daga wannan rana sai Yarima ya susuce tamkar wanda ya zautu,ya zamana cewa dare da rana bashi da wani aiki face ambaton sunan ‘yarka.Kai sai datakai cewa ya daina ci da sha face anyi masa hirar Yazarina an koda ta ana baiyana masa irin siffofinta.Yakai abokina nazone neman alfarmar ka amince a daura auren ‘dana da ‘yarka cikin gaggawa domin ina tsoron cewa ‘dana zai iya rasa lafiyarsa ko rayuwarsa muddin bai mallaki Yazarina ba a matsayin matar aure Koda Sarki Alkas yazo nan a zancensa sai hankalin Attajiri Abu Yazarina ya DUGUNZUMA ainun domin an sashi cikin TSAKA MAI WUYA.Abu na farko dai Sarki Alkas da Sarki Sailur duk abokansa ne kuma aminansa tun yarinta,babu wanda zai nemi alfarma a wajensa ya hanashi.Abu na biyu shine ya san cewa ‘yarsa Yazarina da Yarima Lubainu sun dade suna soyayya tun suna yara kuma ya sance cewa Yazarina tana tsananin son Lubainu rabata dashi ba karamin aiki bane.Bayan Abu Yazarina yayi tunani na tsawon ‘yan dakiku sai ya dago kai ya dubi Sarki Alkas fuskarsa cike da dumbin damuwa yana mai ajiyar zuciya sannan yace,yakai abokina kayi sani cewa ‘yata Yazarina da Yarima Lubainu sunfi shekara goma sha daya suna soyayya kuma gashi rana daya danka ya ganta yana SO.Ka da sarki Sailur aminaine kamar yadda muke nida kai kaga bana son abinda zai kawo lalacewar zumunci a tsakaninmu.Hakika na tausaywa danka mutuka bisa halin daya shiga saboda nasan illar soyayya gami da sharrinta domin kuwa kwatankwancin hakan ya sameni a lokacin danake neman auren mahaifiyar Yazarina.Abinda nake ganin za’ayi yanzu shi ka labartawa Sarki Sailur wannan al’amari? Koda jin wannan tambya sai Sarki Alkas ya gyada kai yace,kawai ce masa zanyi nazone akan harkokin kasuwancinmu nida kai.Abu Yazarina ya gyada kai yace,ba za’ayi haka ba domin nan gaba wani abu ya faru sai yayi zaton munyi masa duk munafunci.Abinda za’ayi yanzu shine ka tashi muje fada musa ayi mana iso a wajen sarki mu fito zahiri mu baiyana masa duk abinda ke faruwa dominmu hada basirarmu waje guda mu yanke hukuncin da zai fi dacewa bisa adalci.Ba tare da gardamar komai ba kuwa Sarki Alkas ya amince da wannan shawara.Na take Attajiri Abu Yazarina yasa aka fito da keken doki suka hau aka tafi dasu izuwa fada.Da isarsu fadar suka tura akayi mus iso a wajen sarki.Na take Sarki yasa aka shigar dasu har cikin turakarsa saboda aminci.Bayan sun gaisa sai Attajiri Abu Yazarina ya zaiyane masa koma dangane da abinda ya kawoso.Koda Sarki Sailur yaji jawabinsa sai shima Hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun fiye da nasu.Saida ya jima yana tunani har ya mike tsaye ya kama kai kawo yana ta tunanin mafita.Daga can kuma ya dawo ya zauna ya fuskancesu su biyun yace,ni inda tason raina ne zan iya tilastawa Yarima Lubainu akan ya hakura ya barwa Yarima Mangul Yazarina amma idan akayi masa haka ba ayi masa adalci ba tunda ya riga Mangul son Yazarina,asali ma sun shafe shekaru masu yawa suna yin soyayar.Ni a nawa tunanin shawarar dana yanke a cikin zuciya itace kawai a shirya musu gasa wanda ya lashe shine zai aureta.Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Alkasa dana Attajiri Abu Yazarina Ya DUGUNZUMA.Cikin kaduwa Abu Yazarina ya dubi Sarki Sailur yace,wace irin gasa kenan za’a shirya musu? Sarki Sailur yace,tunda dai duk su biyun sun kasance GAWURTATTUN JARUMAI masu TARWATSA MAZA a filin daga kawai suyi yaki da junansu wanda duk ya kashe wani Yazarina ta zama tasa.Kafin Sailur ya gama rufe bakinsa tuni Sarki Alkasa ya daka masa tsawa yace,ashe ka sami tabin hankali ban sani ba? Ta yaya zamu sa ‘ya’yanmu suyi gasar kashe junansu akan soyayyar ‘ya mace alhalin su kadai garemu? Na sani cewa a duniya babu abinda kake so sama da danka Yarima Lubainu kamar yadda nima nake tsananin son Yarima Mangul.Menene hujjarka ta yanke wannan hukuncin? Koda jin wannan tambaya sai idanun sarki Sailur suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa sannan ya dubi sarki Alkas yace,yakai abokina kayi sani cewa mutum na iya rasa ‘da ya sami wani amma zumuncin daya kullu a tsawon shekara da shekaru a tsakaninmu idan ya zube ba zai taba debuwa ba har abada.Na gama yanke hukunci don haka ka koma gida ka shaidawa danka cewa idan har son da yake yiwa Yazarina na gaskiya ne to yayi shiri yazo nan birnin domin suyi gasar kashe juna nan da ranar karshe ta wannan watan,kaga kenan bai wuce kwanaki goma sha hudu ba masu zuwa.Ina maka fadan komawa gida lafiya.Koda gama fadin haka sai Sarki Sailur ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ya barsu su biyu a zaune cikin tsananin kaduwa da mamaki.Nan dai suma suka mike tsaye jikinsu a sanyaye suka fice daga cikin turakar….Like nd comments pls 10 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 3 Da la’asar sakaliya Sarki Sailur ya tura aka kirawo Yarima Lubainu suka kadaita a wani wuri na musamman acikin gidan sarautar inda sarke ke shakatwa.Bayan Yarima Lubainu ya zube kasa a gaban sarki Sailur ya kwashi gaisuwa sai sarki ya dubeshi fuskarsa a daure yace,yakai dana kayi sani cewa kai ba rago bane,kuma baka kasance matsoraciba.Baya ga haka ban taba umartarka dayin wani abu ka kasa yi ba,saboda haka yanzu na shirya gasar yaki tsakanin da Yarima Mangul akan soyayar da kuke yiwa Yazarina.Wanda duk ya sami nasarar kashe wani a cikinku shine zai auri Yazarina.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya cika da tsananin mamaki kuma hankalinsa ya DUGUNZUMA ainun ya dubi sarki cikin kaduwa yace,yakai Abbana ina dalilin yanke wannan danyen hukunci dakayi? Koda jin wannan tambaya sai sarki Sailur ya kwashe duk abinda ya faru tsakaninsu dasu Attajiri Abu Yazarina da kuma hujjarsa ta yanke wannan hukunci.Dajin haka sai jikin Lubainu yayi sanyi yayi shiru izuwa tsohon ‘yan dakiku,daga can sai kuma hawaye ya zubo masa yace,yakai Abbana kayi sani cewa Yarima Mangul abokinane tun yarinta bazan iya kashe shi ba da hannuna amma kuma ba zan kaucewa umarninka ba.Lallai zanyi wannan gasa.Koda jin wannan batu sai Sarki ya fusata ainun ya dakawa Lubainu tsawa yace,idan har kaki yin wannan yaki da dukkan karfinka da jarumtakarka a bakacin auren mahaifiyarka!Yana gama fadin haka ya mike tsaye yayi tafiyarsa yabar Yarima Lubainu a zaune cikin tsananin damuwa da tashin hankali saboda yasan halin mahaifin nasa baya magana biyu.Saida Yarima Lubainu ya dade a zaune a wannan wuri yana kukan takaici.Yana cikin wanann hali ne yaji an dafa kafadarsa ta baya.Cikin firgici ya waigo da sauri kawai sai yaga she mahaifiyarsa ce ZUHAIMA tsaye a kansa tana zubar da hawaye.Cikin hanzari Yarima Lubainu ya mike tsaye suka rungume juna kuma suka cigaba da kuka tare.Daga can sai Zuhaima ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna ta dubeshi cikin nutsuwa da murmushi tace,yakai ‘dana na sanka tun kana yaro karami duk abinda kasa a gabanka saikayi nasara.Nasani cewa ko kadan baka sin yin wannan gasa da abokinka Yarima Mangul amma ya zama dole kayi ta tunda baka da wani zabin.Lallai kayi wannan gasa da dukkan karfinka da jarumtakarka kamar yadda mahaifinka ya umarceka domin bana son na rasaka.Idan kuwa na rasaka nima bazan dade ba a cikin wannan duniya.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya kara kankame jikin Zuhaima yacigaba da kuka yana mai cewa lallai bazan yadda ki rasani ba domin nafi kaunarki fiye da komai a wannan duniya hatta Yazarina kuwa.Wannan shine abinda ya faru a birnin Zamral. ¤¤¤••••••••••••••••••••¤¤¤ A can birnin DARUL HUNZUL kuwa lokacin. da sarki Alkas ya isa gida sai ya kirawo Yarima Mangul da mahaifiyarsa tare da dukkan fadawansa ya sanar dasu irin hukuncin da sarki Sailur ya yanke bisa neman auren kyakkyawa Yazarina dayaje nemawa Yarima.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma ainun shi kuwa Yarima Mangul farinciki ne ya lullubeshi ya kama ihu da murna domin yana ganin cewa tamkar ya mallaki Yazarina ne.Duk dacewa yana kaunar Yarima Lubainu tsawon shekaru amma a yanzu sai yaji ya tsaneshi kamar yadda ya tsani mutuwarsa.Daga wannan rana Yarima Mangul ya shiga shirye shiryen tafiya wannan kasa ya zamana cewa kullum da safe da yam2tnma a cikin baiwa kansa horon yaki yake kuma ya rinka ziyartar bokaye suna bashi sa’a gami da mugayen lakanunnuka don ganin bayan Yarima Lubainu.Daga cikin bokayen ne aka sami wani gawurtacce kuma maketacin gaske wanda ya baiwa Yarima Mangul wani sihiri yace dashi koda Yarima Lubainu ya sami nasara akanka to har abada shima bazai taba sani Yazarina ‘Ya Mace ba.Abinda zakayi kawai shine kafin ku fara gasar ka tabbatar da cewa ka bashi hannunka kun gaisa.Na take bokan ya kama hannun Yarima Mangul na dama ya fidda wani garin magani ya shafa akan tafin hannunsa,sannan yace da zarar hannun Yarima Lubainu da hannunka sun hadu shikenan ya rasa darajarsa ta ‘da namiji domin bazai sake jin sha’awar mace ba kuma bazai iya zaman aure ba,kaga kenan shi da mace duk daya.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta yace,da kyau yakai boka Mugaru hakika ka bani babban abin dogaro wanda ko dana mutu a wannan gasa bani da wata nadama ko bakin ciki amma inda tambaya guda daya.Naji daga bakin bokaye da yawa cewar dukkan cuta tana da magani.Menen makarin wannan sihiri dazan yiwa Yarima Lubainu?Fatana shi ne idan ya cinye ni a wannan gasa ya karasa rayuwarsa a cikin wannan hali har abada.Koda jin wannan tambaya sai boko Mugaru ya bushe da dariyar mugunta sannan yace,ai nemo makarin wannan sihiri daidai yake da mutum ya tafi FARAUTAR AJALINsa domin dole ne yaje kogin Bahar Imfal yayi nutso a karkashinsa ya tsunko tsuron wata itaciya ta aljanu da ake kira Saumul Asraru.Har yau har gobe babu wanda yasan a inda kogin Bahar Imfal yake walau a cikin mutane ko aljanu sannan kuma babu mahalukin da ya isa ya gano inda kogin yake har sai ya sami damar zuwa wajen ya shiga cikinsa face ya hada ALLON SIHIRI wanda aka rabashi gida uku.Hada wannan Allon Sihiri daidai yake da neman jaki mai ‘kaho ko kuma ince mutum ya tunkari gaba dayan mutanen wannan duniya da yaki,saboda wadanda ke da mallakin allunan sunfi wuta zafi kuma sunfi ruwa sanyi.Mutum na farko mao rike da bari guda na allon Sarauniya Akisatul Sauwara ce mai mulkin Birnin Rauhul Bagadar.A yanzu haka wannan barin allo yana nan a ajiye a gidan tarihin Birnin cikin wata akwatun gilashi ta sihiri.Duk duniya babu wanda ya isa ya bude wannan akwati face Sarauniya Akisatul Sauwara ko Kuma Wanda ya gaji sarautar ta Wanda ya kasance jin in gidan……pls Like and comments is necessaryALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 4 Mutum na biyu mai mallakin barin Allon shine Sarki Darmasu na birnin Kimrasa,sai kuma barin Allo na uku dake hannun boka Saryanu Ibn Daumur.Karbar wadannan barikan alluna guda uku a hannun wadannan mutane daidai yake da tashin matacce ya zama rayayye saboda kowanne a cikin bashi da burin da yafi ya sami ragowar barikan biyun da nashi dasu ya hada nasa domin zama sarkin duniya,ya kasance komai da kowa na karkashin mulkinsa.Lokacin da boka Mugaru yazo nan a zancensa sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta.Nan take ya kawo alheri mai yawa ya baiwa boka Mugaru sannan sukayi sallama ya tafi. Daga sannanne Yarima Mangul ma ya dage da baiwa kansa horon yaki dare da rana kafin cikar lokacin ranar gasar ya gama shirinsa tsaf.Na take kuwa yayi shiri shi da mahaifinsa Sarki Alkas suka durfafi Birnin Zamral tare da dakaru masu yawa suna take musu baya. Ba isowarsu Birnin Zamral suka iske cewa garin ya cike makil da baki daga kowanne bangare na nahiyar. Ba komai ne ya haddasa wannan cikowa ba face anzo kallon gasar kisan juna da za’ayi tsakanin Yarima Mangul da Yarima Lubainu kan kyakkyawa Yazarina.Kai tsaye sarki Alkas tare da dansa yarima Mangul suka wuce fada.Tun kafin su karasa sarki Sailur ya fito kofar fadar ya tsaya tare da fadawansa suna jiransu. Ai kuwa da zuwansu sai Sarki Sailur ya karbesu cikin tsananin farinciki ya rungume sarki Alkas yana mai cewa lale marhaban da babban abokina.Hakika nayi mutukar farinciki dakuka amsa wannan gaiyata tawa. Abinda ya daurewa su Yarima Mangul kai shine basu ga Yarima Lubainu ba a wajen taryarsu.Nan take sarki Sailur ya kama hannun Sarki Alkas ya jashi izuwa cikin fada inda aka zauna gaba daya tare da dukkan jama’arsu.A sannanne kuyangi da hadimai sukai ta kawo abinci,ruwan inibi,ruwan sha kowa ya kimtsa kansa ana ta hira da dariya masu shewa nayi saboda santi. A wannan lokaci Yazarina da Yarima Lubainu nacan a zaune cikin lambun gidan attajiri Abu Yazarina suna hira irin ta ma’abota soyayya inda Yazarina ta dubi Lubainu a lokacin da hawaye ya zubo mata tace,yakai masoyina kayi sani cewa tun daga ranar dana sami labarin wannan gasa da mahaifinka ya shirya na rasa sukuni kuma na kasa yin bacci a kullum idan na kwanta akan gadona,har ya zamana cewa ina tayin mugayen mafarkai akan wannan gasa da zakuyi don haka ko yaushe zuciyata a cikin bugawa da karfi take.Bani da abinyi sai kuka saboda fargabar zuwan wannan rana gashi kuwa rana bata karya saidai uwar ‘ya taji kunya tunda gobene za’ayi wannan gasa. Lokacin da Yazarina tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi murmushi kuma yasa tafin hannunsa biyu ya share mata hawayen a lokacin da ya dago habarta suka dubi juna yace,ki kwantar da hankalin yake abar kaunata kiyi sani cewa nine da nasara a cikin wannan gasa lallai da izinin gunki Salhat babu abinda zai sameni. Koda jin wannan batu sai Yazarina taji dan sanyi har murmushi ya subuce mata amma sai ta sake hade rai ta dubi Lubainu cikin alamun damuwa tace,yakai masoyina waishin menene dalilin da yasa mahaifinka ya shirya wannan gasa ne alhalin na tabbatar da cewa yana tsananin kaunarka fiye da komai.Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Yazarina yace,sau tari sarki yakan dannen son zuciyarsa domin ya nemawa kansa martaba da kima a idanun talakawa.Wannan shine abinda ake kira sarauta,kuma shine abinda sarki yayi domin ya kawar da rashin jituwa tsakaninsa da tsohon abokinsa kuma ya kawar da tsegumi da kace nace tsakanin al’ummar kasashenmu.Idan kin Fahimci wannan bayani nawa zaki gane cewa sarki yayi daidai bisa wannan hukunci daya yanke.Lallai ina son ki kwantar da hankalin kawai ki cigaba da yimin fatan sa’a da nasara.Haka dai Yarima Lubainu Da Yazarina suka cigaba da hira har izuwa lokacin mai tsawon gaske . Da zarar yayi mata sallama zai tafi sai ta bijiro masa da wata sabuwar hirar da hillatar da zance mai dadi saboda bata son su rabu.Yarima Lubainu dai bai ankaraba sai gani yayi dare ya soma kuma gashi yana son yaje yayi shirin karshe na gasar fadan da za’ayi gobe.Kawai sai ya mike zumbur ya ruga waje da gudu yana mai cewa sai gobe da safe su hadu a filin fada wajen gasa.Yazarina ta bishi da kallo kawai tana mai zub da hawaye cikin tsananin fargabar ganin wayewar gari,domin babu abinda ta tsana sama da wannan gasa da za’ayi da Yarima Mangul saboda da gasa ce wadda babu wanda yake da yakinin ya fadi zakaranta.Har Yazarina ta juya zata koma izuwa bangaren da turakarta take sai ta hango mahaifinta ya shigo cikin gidan tare da wani bakon mutum ma’abocin haiba da kwarjini a cikin shiga ta kamala.Ga dukkan alamu dai bafatake ne.Cikin biyayya Lazarina ta risina ta gaishe da bakon a sannane Abu Yazarina ya gabatar da bakon nasa a gareta yace,Wanna shine Abdul Nasiri Ibn Hamza daga birnin Misra.Mai gidana ne a kasuwanci domin shine mutum na farko daya fara aminta dani yabani tsabar kudi dinare dubu dari a rayuwata,kuma wannan kudi daya bani sune silar arzikina da nake kai yanzu.Koda jin wannan batu sai Yazarina ta sake dukawa cikin girmamawa tayi gaisuwa a karona biyu.Cikin murmushi attajiri Abdul Nasir ya dubi Yazarina sannan yadubi Abu Yazarina yace tabbas kyan ‘da ya gaji ubansa,hakika wannan yarinya tana mutukar kama da kai.Koda jin wannan batu sai Attajiri Abu Yazarina ya bushe da dariya yace,Hakika kayi gaskiya mai gida.Na take Abu Yazarina yace da Yazarina taje tasa kuyangi su shiryawa Attajiri Abdul Nasir abinci na musamman kuma ya gargadeta da kada a dafa masa abincin da nama sai kifi.Koda jin wannan umarni sai Yazarina ta cika da mamaki domin bata san dalilin dayasa aka bayar da umarnin ba amma sai ta kudurce a ranta cewar zata tambayi mahaifinta dalilin. Nan take Abu Yazarina yaja Abdul Nasir suka tafi izuwa turakarsa suka zauna,ita kuwa Yazarina ta tafi izuwa madafar gidan ta baiwa kuyangi umarnin abinda zasu dafawa babban bako kamar yadda mahaifinta ya umarceta,daga na ta wuce izuwa cikin turakarta taje ta kwanta domin tayi barci amma sai ta kasa.Ga abincinta na dare an kawo an ajiye amma ko kallonsa batayiba.Har dare ya raba Yazarina bata rintsa ba.Koda taga tunani ya hanata bacci sai ta mike tsam daga kan gadonta ta fito izuwa cikin harabar gidan ta kama tattaki.Koda tazo zata gifta ta gaban turakar da aka sauki bako Abdul Nasir saita hangoshi a tsaye yana nafila.Al’amarin dayai matukar bata mamaki kenan domin bata taba ganin irin wannan ibada dayake yiba,bata ma san irin addinin da yake yiba.Kawai sai ta kura masa idanu har saida ya idar da nafilar yayi ‘yan addu’oinsa ya shafa.Koda ya mike tsaye da nufin ya nade sallayarsa sai ya hango Yazarina a tsaye acan gefe daya ta zubo masa idanu.Al’amarin dayai matukar girgiza shi kenan ya bashi mamaki,kawai sai ya fito daga cikin dakin ya taho gareta ya dubeta yace,yake Yazarina lafiya kike kai kawo a gida cikin wannan dare haka? Ga dukkan alamun akwai wani abu da yaje damunki domin na lura yanayin da kike ciki a farkon zuwana gidannan.Sa’adda Yazarina taji wannan tambaya sai ta sunkuyar da kanta kasa cikin alamun tsananin damuwa sannan tace,yakai wannan attajiri kayi sani cewa hakika ina cikin damuwa matsananciya wacce ta hanani barci da sukuni.Nan take Yazarina ta kwashe labarin gasar aurenta da za’ayi gobe da safe a fada tsakanin Yarima Lubainu da Yarima Mangul. ALLHAUSA NOVELSTV kuma ta jaddada masa irin tsananin soyayyarta ga Yarima Lubainu.Koda jin wannan batu sai Attajiri Abdul Nasir yakamu da tausayin Yazarina ya dubeta yace,yake ‘yata ki kwantar da hankalinki zanyi wata addu’a ta musamman a daren nan domin na nemi sanin sirrin abin dake cikin wannan gasa da za’ayi gobe da safen domin na sanar dake abinda Yarima Lubainu zaiyi don kare kansa daga sharrin abokin hamaiyarsa.Saidai nifa da safen zan bar garin nan na wuce izuwa birnin Kisra don haka bazan sami damar halattar wannan gasa ba.Lallai da safe bayan na gama kimtsawa sai kizo na sanar dake wannan sirri.Yayin da Yazarina taji wannan batu sai ta kamu da tsananin farin ciki tayi godiya ga Attajiri Abdul Nasir sannan kuma ta dubeshi tace,ni kuwa ina son nayi maka wata tambaya in bazaka damu ba.Abdul Nasir yayi murmushi yace,ai matambayi baya laifi domin yana neman ilmine,fadi abinda kikeso ki sani yake ‘yata .Yazarina tayi gyaran murya sannan tace,dazu naga kanayin wata irin ibada wacce ban taba ganiba,shin ko zaka iya yi min bayani akanta? Koda jin wanann batu sai Attajiri Abduil Nasir yayi murmushi yace,Kiyi hakuri bai kamata nayi miki wannan bayani ba ayanzu saboda wasu dalilai,amma bayan angama gasa zaki iya tambayar mahaifinki wannan tambya da kika yi min,lallai zai baki cikakkiyar amsa amma zaifi kyau ki bari sai bayan an gama wannan gasa ta neman aurenki.Saida safe ina mai saurarin zuwanki kafin in tafi. Koda gama fadin hakan sai Attajiri Abdul Nasir ya juya ya koma izuwa cikin dakinsa ya rufo kofa.Itama Yazarina sai ta juya da sauri ta koma turakarta zuciyarta cike da farin cikin wannan bushara wacce Attajiri Abdul Nasir yayi mata domin ji take kamar ta sami cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali.washe gari kuwa da sassafe fadar sarki Sailur ta cika ta batse da jama’a,duk inda mutum ya hanga babu abinda zai gani face kawunan bil’adama rututu.Abinda ya daurewa jama’a kai shine sarki Sailur da Yarima Lubainu ne suka fara zuwa filin fadar tun kafin jama’a su cika sannan sai ga Yarima Mangul Da sarki Alkas sun shigo fadar,Yarima Mangul yayi gagarumar shigar yaki ta jan sulke,hatta kufen takobinsa,hular karfen da yasa da takalman karfen dake kafafunsa duk jajaye ne.Shi kuwa Yarima Lubainu shigar fararen sulke yayi,farar takobi gami da farar garkuwa mai hoton zaki a jikinta.Koda shigowar su Yarima Mangul cikin fadar sai jama’a suka kaure da shewa da tafi.Maroka kuwa suka kama kirari,makada da masu busa suka kama aikinsu. Acan gidan Attajiri Abu Yazarina kuwa hankalin Yazarina a DUGUNZUMe yake domin tun da Asuba tayi wanka ta kimtsa ta tafi kofar dakin bako Abdul Nasir domin taji sakamakon abinda ya gani wansa yayi alkawarin sanar da ita amma sai ta iske dakin a kulle yana barci bai farka ba.Nan fa hankalinta ya kara dugunzuma ainun ta kama kai kawo a kofar dakin zuciyarta na bugawa da karfi saboda tana tsoron kada Yarima Lubainu da Yarima Mangul su fara gasar kafin ta isa can filin fadar.Tana cikin wannan haline Abu Yazarina ya fito daga cikin tasa turakar cikin shirin tafiya fada.Koda yaga Yazarina a tsaye a kofar dakin bako Abdul Nasir sai ya cika da mamaki yace,me kike yi anan alhalin ana jiranmu acan fada kinsani cewa saboda ke ake yin taron yau.Cikin yanayin damuwa Yazarina ta dubeshi tace,yaka Abbana ina da alkawari mai girma da wannan bako naka.Yace zai bani wani taimako akan masoyina Yarima Lubainu.Koda jin haka Sai Abu Yazarina ya girgiza kai cikin alamun damuwa yace,ai kuwa mun makara,na sani cewa Abdul Nasir baya barci da dare yana yawan ibadarsa,yanzu ne yake samun damar yin bacci bai kamata mu tasheshi ba.Gama fadin haka keda wuya sai sukaji an turo kofar dakin bako Abdul Nasir.Cikin matukar farin ciki Yazarina ta ruga izuwa bakin kofar ta tari Abdul Nasir,kafin ta budi baki tuni Abdul Nasir ya tari numfashinta yana mai cewa maza ki ruga izuwa fada ki gayawa Yarima Lubainu cewa kada ya kuskura ya baiwa Yarima Mangul Hannunsa su gaisa.Kafin Abdul Nasir ya gama rufe bakinsa tuni Yazarina ta juya da gudu ta nufi inda bargar dawaki take.Koda sauraron bawan dake kula da bargar batayi ba ta shiga ciki ta kwanto doki guda da hannunta.Ba tare da ta tsaya dauwara dokin siddi ba tayi tsalle ta haye kansa sannan ta zabureshi da gudu ta fice daga cikin gidan.Nan dai Abdul Nasir ya yiwa Abu Yazarina bankwana ya tafi sannan shima Abu Yazarina ya tafi izuwa fadar cikin sauri.A can fada kuwa bayan maroka da makada sunyi hayaniyarsu tsawon dan lokaci sai aka kirawo Yarima Lubainu da Yarima Mangul suka shigo cikin tsakiyar filin fadar suka tsaya suna masu fuskantar juna. Alkalin gasar ya dubesu yace,sai ku fara gaisawa bisa ka’idar kowace irin gasa ka akeyi a birnin nan. Adaidai wannan lokaci ne Yazarina ta shigo filin fadar a sukwane bisa dokin kuma a sannanne fadar ta sake rudewa da hayaniya da shewar mutane bisa ganin jaruman biyu sun tsaya a tsakiyar filin sun fuskanci juna.Koda Yazarina ta hango Yarima Mangul ya durfafi Yarima Lubainu yana mika masa hannu zasu gaisa sai ta kama kwalawa Lubainu kira domin ta hanashi gaisawa da Mangul,amma saboda iface ifacen daya kaure a filin ko kadan Lubainu bai jio kiran nataba.Tana isowa daf da kofar filin gasar ne ta hango gaisawar Yarima Lubainu da Yarima Mangul.Nan take ta kamu da tsananin bakin ciki har hawaye ya zubo mata.Cikin sanyi jiki da karayar zuciya ta sauko daga kan dokin nata ta tsaya cak ruke da linzamin dokin nata ta zuba ido izuwa cikin filin gasar domin taga yadda gumurzun zai kasance.Sarki Sailur da Sarki Alkas nacan sama bisa wani gini mai tudu inda aka ajiye kujeru na alfarma na sarakai da attajirai. Ai kuwa saiga Attajiri Abu Yazarina ma ya iso yazo ya zauna a kusa da su Sarki Sailur suka gaisa.Kwatsam sai akaji an buga tambarin fara gasa nan fa filin yayi tsit tamkar babu abu mai rai a wajen,baka jin sautin komai face sautin iskar dake kadawa.A lokacinne Jaruman Biyu suka zare takubbansu suka fara zagaya juna kowannansu ya fara nazarin dan’uwansa.Daga can sai suka fara ja da baya baya kamar bazasuyi yakinba,kuma sai suka rugo da gudu suka kacame da AZABABBEN YAKI,ya zama cewa suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin ZAFIN NAMA,JURIYA DA BAJINTA.Nan fadar ta sake rudewa da sowa kowa nayiwa gwaninsa jinjina.Ita kuwa Yazarina saita fashe da kuka taci gaba da kallon gumurzun a haka tamkar an tilasta ta da yin kallon.Saida jaruman biyu suka shafe rabin sa’a suna bakin gumurzu amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar dayan ba domin fadan ya nuna cewar karfinsu da kwarewarsu a iya yaki tazo daya.Bisa dole su biyun suka ja da baya suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna tamkar zakaru.Bayan yan dakiku kowannansu ya gama nazarin irin salon fadan da zai sauya sai suka sake rugowa da gudu izuwa kan juna.Koda ya rage saura baifi taku uku ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama cikin shammace yakai hari.Cikin sa’a kuwa Yarima Mangul ya yanki Lubainu a damtsen hannunsa na hagu,shi kuma Lubainu ya sami nasarar yankarsa a cinyar dama.Duk su biyun suka kwalla ihu sakamakon jin tsananin zafi da zugi kuma suka rikito kasa a galabaice a lokacin da jini yayi tsartuwa daga cikin jikinsu,amma saboda juriya da jarumtaka sai ko wannan su ya tsaya akan kafafunsa.Kamar hadin baki sai ko wannansu ya cire kyallan daya daura a goshinsa ya daure rauninsa don tsaida jini.Saida suka sake zagaya juna sau uku sannan suka kacame da sabin azababben yaki cikin tsananin fushi da kunar rai.Wannan karon dai sai yaki nasu ya zamo abin tsoro domin sun sauya salo sosai sun hada da tsalle tsalle a sama da kasa gami da kaiwa juna sara da suka da hannu da kafa.Ai kuwa sai kowannansu ya fara raina kansa domin na take suka fara hadawa juna jini da majina.Kuma kafin cikar wata rabin sa’ar sun sake yankar juna sau biyar biyar.Nanfa jiri ya fara dibarsi suka kama layi,amma saboda naci da taurin kai basu fasa ci gaba da yakinba.Nanfa jikin sarki Sailur dana Sarki Alkas yayi sanyi kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun domin babu wanda yake da tabbacin cewar dansa zai sami nasara.Ana cikin hakane Yarima Mangul ya shammaci Yarima Lubainu ya danki kasa ya watsa masa a ido.Kafin Lubainu ya mitstsike idon nasa tuni Mangul ya soka masa takobi a gefen ciki.Lubainu yayi ihu kuma yayi sauri ya rike takobinsa da hannunsa a lokacin da Mangul ke kokarin danna takobin ta nutse a cikin ta faso ta baya.Cikin tsananin Jarumtaka Lubainu yasa hannunsa na hagu ya gabzawa Mangul naushi a fuska.Saboda karfin naushin saida Mangul yayi katantanwa sau uku a tsaye sannan ya zube kasa a mutukar galabaice. A sannan ne Yarima Lubainu ya zare takobin daga cikinsa ya yanke jiki ya fadi kasa magashiyan. Koda Yazarina taga abinda ya faru ga Lubainu sai ta kurma ihu ta sulale kasa sumammiya.Ai kuwa Attajiri Abu Yazarina bai san sa’adda ya mike tsaye ba ya ruga izuwa inda Yazarina take ya kama yi mata firfita don ta farfado.A wannan lokaci Lubainu ya baje kasa yana dafe da raunin cikin nasa wanda jini ke bulbulowa daga cikinsa,jikinsa na tsuma kuma idanunsa na lumshewa.Kawai Sai Yarima Mangul ya mike tsaye yana mai kyalkyala daritar mugunta da farincikin domin ya tabbatar dacewar ya gama samun nasara a wannan gasa.Mangul yazo kan Yarima Lubainu ya tsaya ya tofa masa yawu a fuska yace,burina ya cika akanka.Yanzu zan karasa kashe ka kuma na auri masoyiyar taka.Gata can ta suma saboda ganin nasarar dana samu akanka.Ko domin na cusa mata bakin cikina har abada saina karasa kasheka.Koda jin wannan batu sai Lubainu yaji zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone.Duk irin tsananin ciwon da yakeji a cikin nasa sai yaji kamar an zare masa shi saboda fishi.Koda Mangul ya dago takobinsa sama da nufin ya datse masa kai sai ya mirgina can gefe daya cikin zafin nama,takobin Mangul ya karci kasa.Ai kuwa sai fadar ta rude da shewa. Sarki Sailur kuwa baisan sa’adda kwallar farin ciki tazo masa ba.Kafin Mangul ya juyo ya sake kawo masa wani harin tuni Lubainu ya suri tasa takobin ya daka tsalle sama ya sare hannun Mangul mai ruke da takobi.Take hannun ya gutsure ya fadi can gefe daya.Mangul ya kwarara uban ihu a lokacin da jini ya kama feshi daga cikin dungulmin hannun nasa,kawai saiya sulalae kasa sumamme.Shima Yarima Lubainu sai jiri ya sake dibarsa shima ya zube kasan sumamme.Nan take dakaru suka rugo da gudu izuwa kansu,aka daukesu aka shigar dasu izuwa cikin gidan sarautar aka kirawo lokitici suka dukufa a kansu.A wannan lokacin gardama ta sarke a tsakanin Alkalan wannan gasa akan tantance wanda ya lashe gasar tsakanin Yarima Lubainu da Yarima Mangul.A karshe dai aka tabbatar da cewar Yarima Lubainu ne ya lashe wannan gasa.Lokacin da likitoci suka sami nasarar ceto rayuwar Yarima Lubainu da ta Yarima Mangul sai duk su biyun suka farfado lokaci guda,sukayi arba da iyayensu tsaye a kansu wato Sarki Sailur da Sarki Alkas.Koda Yarima Mangul yaga bashi da hannu daya saiya fashe da kukan bakin ciki ya kurma ihu sannan ya dubi Lubainu yace,Yakai abokin hamayya ta ka cuce ni da baka kashe ni ba,ka mayar dani masaki alhalin na tabbatar da cewa kai za’a bawa zakaran wannan gasa.Koda jin wannan batu sai Yaruma Lubainu ya bushe da dariya kuma ya murtuke fuskab yace,nikam burina ya gama cika tunda yanzu nine na zami angon Yazarina.Kafin Lubainu ya gama rufe bakinsa tuni Yarima Mangul ya bushe da mahaukaciyar dariya.Al’amarin da yai mutukar baiwa Yarima Lubainu Dasu Sarki Alkas mamaki kenan. Mangul yacigada kyakyata dariyar kamar bazai daina ba har izuwa lokaci mai tsawo,daga can kuma sai ya hade fuska ya dubi Lubainu yace,hakika ka lashe wannan gasa kuma zaka auri Yazarina amma ka sani cewa har abada baza ka taba tarayya da itaba,domin yanzu dakai da ‘ya mace duk daya ne,ka tashi daga matsayin ‘da namiji. A dazu kafin mu fara gasar nan na baka hannuna mun gaisa,a wannan gaisawa da mukayi na goga maka wani sihiri wanda shikenan ka zama mara amfani.Wannan asiri danayu maka duk duniya babu mai iya karyashi domin kuwa neman maganinsa daidai yake da neman jaki mai kaho ko kuma mutum ya tafi farautar Ajalinsa. Koda Mangul yazo nan a zancensa sai ya sake bushewa da dariyar mugunta. Like and cmmntALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 5 Koda Mangul yazo nan a zancensa sai ya sake bushewa da dariyar mugunta. A”amarin daya DUGUNZUMA hankalin Yarima Mangul da sarki Sailur kenan.Cikin bakinciki da takaici Sarki Alkas ya dubi Yarima Mangul ya daka masa tsawa yace,kaiconka ya kai dana,hakika kaci amanar abokantakar dake tsakaninmu da sarki Sailur domin babu maganar sihiri a cikin wannan gasa.Hakika baka yiwa Lubainu adalci ba,ka sani cewa ba karamin adalci Sarki Sailur yayi maka ba daya shirya muku wannan gasa saboda kada ni na zargeshi da rashin kyautata maka bisa zabin zuciyarka.To ka sani cewa wannan cin amana dakayi babu hukuncin da ka dace shi face na goge matsayinka na ‘da a zahiri da badini,kuma indai ina numfashi a doron kasa bazaka hau karagar mulkina ba.Koda gama fadin haka sai hawaye ya zubowa sarki Alkas ya juya ya fice daga cikin dakin yana mai tsananin bakinciki.Shi kuwa sarki Sailur sai ya sa ka dauke Yarima Lubainu aka kaishi can turakarsa sannan ya tura aka gaiyato babban Bokan kasar wanda ake kira Shalkar Ibini Madusa ya zaiyana masa abinda Yarima Mangul yace yayiwa Yarima Lubainu.Nan take boka shalkar yayi bincike ya tabbatar da faruwar hakan kuma ya sanar da sarki cewa babu yadda za’ayi Yarima Lubainu ya sami lafiyarsa ta cikkakken ‘da namiji face yaje Kogon Bahar Imfal ya tsinko dam itaciya da ake bukata,sannan ya baiyana masa irin matakan da zaibi na nemo sassan wannan Allon Sihiri guda uku wanda dole sai an karanta bayanin dake jikinsa sannan za’a iya izuwa Kogon Bahar Imfal.Koda Boka Shalkar yazo nan a jawabinsa sai Sarki Sailur ya fashe da kukan bakin ciki yana mai cewa ai kuwa indai haka ne wanann cuta batada magani kenan tunda ban ga ta yadda za’a iya samo wannan maganin ba. Lokacin da Yarima Lubainu yaga mahaifinsa ya fashe da kuka yana wanann jawabi sai ya yunkura cikin matukar karfin hali yace,ya kai Abbana shin ka manta ne cewar ka taba gaya min cewa dukkan CUTA tanada MAGANINTA? Nikam ban taba cire rai da samun wannan magani ba,don haka yanzu bayan na gama jinyar wannan ciwo nawa zanyi shiri na bazama cikin duniya neman wannan magani don haka baza’a daura aurena ba da Yazarina har sai na samo wannan magani. CUTA DA MAGANI ko yaushe suna tare da juna saidai rashin sani. Koda jin haka sai hawaye ya zubowa sarki Sailur ya jinjina kai yana mai dafa kafadar Lubainu yace,da kyau ‘dana ina alfahari dakai saboda baka karaya bisa duk abinda baka sa a gabanka,saboda haka na amince wannan shawara daka yanke. washe gari da safe sarki Alkas ya dauki dansa Yarima Mangul wanda ya zama nakasasshe mai hannu daya suka tafi izuwa nasu birnin. Al-amarin Yazarina kuwa lokacin data farfado taji cewar Lubainu bai mutu ba saita kamu da tsananin farin ciki ta mike zumbur ta ruga izuwa cikin gidan sarautar ta wuce kai tsaye izuwa cikin turakar Yarima Lubainu.Tana shiga ta iske Yarima zaune akan gadonsa likita na bashi magani a kofi yana sha.Yazarina ta karasa cikin farin ciki ta zauna a gefen gadon daf dashi ta dubeshi cikin murmushi tana mai ajiyar zuciya tace,ya kai masoyina inda ka tafi ka barni da nima bakin cikin rashinka ne zai kashe ni.Koda jun haka sai Yarima Lubainu yayi murmushi ya sallami Likitan sannan ya zaiyana mata duk abinda ya faru a filin gasar tun daga lokacin da ta fadi ta suma kawo izuwa sa’adda boka Shalkar ya tabbatarwa da Sarki Sailur asirin da aka yiwa Lubainu bisa cutar data sameshi da kuma yadda za’a samo maganinta.Koda jin wannan labari sai Yazarina ta dora hannayenta aka ta kurma uban ihu kuma ta fashe da matsanancin kuka domin tasan cewa murna ta koma ciki,kuma idan Yarima Lubainu ya tafi neman wannan maganin abu ne mayuwaci ya dawo gida a raye.Koda Yarima Lubainu yaga Yazarina ta fashe da wannan kuka sai ya shiga rarrashinta yana mai kwantar mata da hankali gami da nuna mata cewa lallai idan ya tafi neman wannan magani sai ya sameshi.Da Kyar da sidin goshi Lubainu ya samo kan Yazarina ta daina kuka amma sai tace da shi lallai bazai yi wannan tafiya ba sai an daura aurensu duk da cewar ya sami wannan lalura domin burinta shine mutuwa ta rabasu tana dauke da igiyar aurensa.koda Lubainu yaga ran Yazarina zai baci ainun idan bai amince da bukatarta ba kuma zata iya shiga cikin matsanancindamu wa sai ya amince da hakan.Saida Yarima Lubainu ya shafe wata shida a kwance yana jinyar wannan rauni na cikinsa sanann ya warke sumul.A ranar dayazo zaiyi bankwana da Yazarina sai da suka shafe sa’a daya a tsaye rungume da juna suna kuka.Daga karshe ne Yazarina ta janye jikinta daga cikin nasa suka fuskanci juna suna masu zubar da hawaye tace,yakai mijina kayi sani cewa daga yau bani da sauran sukuni da kwanciyar hankali a rayuwata.Komai dandanon abinci daci zaiyi a bakina komai kyan sutura bazata burgeni ba har sai gaka ka dawo gareni a raye koda kuwa baka sami nasarar samo maganin daka tafi nemowa ba.Na yarda na zauna dakai a cikin halin da kake ciki har izuwa karshen rayuwa ta. Koda Yarima Lubainu yaji wannan batu daga bakin Yazarina sai yaji tausayinta ya kamashi ainun bai san sa’adda ya rungumeta ba suka dada kankame juna suna masu fashewa da sabon kuka. Da kyar ya janye jikinsa daga cikin nata ya juya mata baya ya nufi inda dokinsa yake.Sai kawai yaga Sarki Sailur tsaye kusa da dokin nasa ya kura masa idanu kawai idanunsa sun kada sunyi jawur. Nan take Yarima Lubainu ya ruga izuwa ga sarki Sailur suka rungume juna. Tsawon ‘yan dakiku suna manne sannan sarki Sailur ya janye jikinsa daga cikin nasa ya fuskanceshi yace,Ya kai dana guzurin kudi kona abinci dazan baka bashi ne abinda zai taimake ba a cikin wannan tafiya da zakayi har ka kai ga samun nasara.Yanzu zan baka babban guzuri wanda aminina Abdul Nasir Ibini Hamza ya bani,kuma ya shawarceni dana dinga amfani da shi a duk sa’adda tafiya ta kamani.Tabbas na jarraba amfani da wannan guzuri har sau uku kuma ya fidda ni daga cikin mugayen masifun da suka gagareni,wanann guzuri dai ba komai bane face, GASKIYA, AMANA da cika ALKAWARI. Tabbas idan ka ruke wadannan abubuwa guda uku babu wata masifa da zata taso ta afka masa.Babu irin tsautsayin da bazaka shallake shiba kuma duk abinda kasa a gabanka sai ka sami nasararsa. Lokacin da Sarki Sailur yazo nan a zancesa sai Yarima Lubainu ya kamu da tsananin mamaki yace yakai Abbana kayi sani cewa Yazarina ta bani Labarin amininka Abdul Nasir da abinda ya gaya mata akan asirin da Yarima Mangul yayi mini,kuma akwai tambayar datayi masa yace kaine wanda zaka bata amsar wannan tambaya.Na duskanci cewar ka aminta dashi dari bisa dari,amma kuma gashi ba addininmu daya ba.To menene dalilin da yasa baka karbi addininsa ba? Koda jin wannnan batu sai Sarki Sailur ya murmushi yace,yakai dana kayi sani cewa komai da lokacinsa,tabbas na yarda da Abdul Nasir kuma na yarda da addininsa har cikin zuciyata amma ina jiran lokacin da zan karbeshi Koda gama fadin haka sai Sarki Sailur ya juya ya nufi cikin gidan sarautar yana mai zub da hawaye ba tare daya sake waigowa ba har ya kule. Nan take Yarima Lubainu ya kama dokinsa ya hau ya nufi kofar fita daga cikin gidan sarautar. Ita kuwa Yazarina sai ta bishi da kallo kawai tana kuka.Lubainu bai sake dubanta ba don kada zuciyarsa ta karaya har ya bace ma ta da gani.. Wannan shine asalin yadda Yarima Lubainu ya baro kasar su ya taho izuwa nan birnin Rauhul Rauhul domin neman maganin cutar da Yarima Mangul yayi masa asiri.Lokacin da Yarima Lubainu yazo daidai nan a tunanin zucin abubuwan da suka faru ga rayuwarsa a baya sai hankalinsa ya sake dugunzuma ainun,musamman daya tuno da maganganun da sarauniya Akisatul Sauwara ta gaya masa bisa irin tsananin tashin hankalin dake cikon daha wannan Allon Sihiri dake hannun mutane uku don karanta bayanin dake cikinsa sannan a tafi neman abokan tafiya kogin Bahar Imfal har mutum uku kuma aketa ta cikin wadannan mugayen dazuzzuka guda uku.Nan take Yarima Lubainu yaji zuciyarsa tasake karaya fiye da ko yaushe.Ya fara tunanin cewa ya kamata ya hakura da wannan bukata tasa kawai ya tafi izuwa wani bigiren dabam na duniya inda zai karasa sauran rayuwarsa ya kuma hakura da masoyiyar tasa.Amma da ya tuno da guzurin da sarki Sailur ya bashi sai kuma yaji guiwarsa ta kara karfi akan tafiyarsa. Haka dai ya wanzu yana mai ta sake saken zuci har barci ya sace shi bai sani baALLON SIHIRI Littafi na daya(1) Part 6 Al’amarin sarauniya Akisatul Sauwara kuwa lokacin data shiga cikin gidan sarautar ta isa turakarta sai ta kasa zaune ko tsaye ta kama kaikawo a cikin turakar tana tunani da zancen zuci.Koda taga hakan ba zai fissheta ba sai ta tura aka kirawo tsohuwa Dulaiba.Tsohuwa Dulaiba ta kasance mahaifiyar kakan mahaifin sarauniya Akisatul Sauwara,don haka a fadin birnin Rauhul Bagadar babu mai yawan shekarunta,domin shekarunta sun kai dari da sittin,amma kuma Allah ya bata lafiya,idanunta garau tana gani sosai,hakoranta duka suna nan reras daya bai fadi ba,kuma tana iya jure tafiyar yini guda ba tare da gajiya ba.Tsohuwa Dulaiba tana da kaifin basira gami da hangen nesa,don haka duk sarakunan da akayi a birnin Rauhul Bagadar basu da wani abokin shawara sama da ita,kuma bata taba bayar da shawara akabi akayi nadama ba.Lokacin da sarauniya Akisatul Sauwara ta kadaita da tsohuwa Dulaiba a cikin turakarta sai ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninta da Yarima Lubainu ta zayyane mata,kuma ta nemi shawararta bisa abinda ya kamata tayi.Koda jin wannan batu sai tsohuwa Dulaiba ta kyalkyale da dariya.Al’amarin dayai mutukar baiwa Akisatul Sauwara namaki kenan ta dubeta cikin mamaki tace,yake Dulaiba ina dalilin wannan dariya taki?Koda Dulaiba taji wannan tambaya sai ta nutsu tace,ki karbi wannan bako hannu biyu,kiyi masa duk abinda yake so,domin a sanadinsa ne zamu cika burin da kakanninki suka kasa cikawa tun kafin a haifeni ni kaina.Ki sani cewa wannan barin Allon sihiri dake cikin gidan tarihin garin nan wanda aka sanya shi a cikin kwalba ya zamana cewa duk duniya ke kadaice zaki iya fito da shi to duk ranar da aka samo ragowar barinka biyun aka hadashi aka dora allon akan gunkin dake tsakiyar fadarki sai Birninmu ya sami daukaka da arzikin da babu wata kasa dazata kaishi kuma har abada baza a cimu da yaki ba har sai mun mallake gaba dayan kasashen duniya sun dawo karkashin mulkinmu.Wannan shine burin da iyayenki da kakannink suka kasa cikawa amma yanzu ke kin sami babbar dama ta cika wannan buri.Abinda zakiyi shine ki dauko wannan Allon Sihiri amma kada ki damkawa Yarima Lubainu a hannunsa.Ki boyeshi a tare dake dare da rana kuma ki bishi kuyi wannan tafiya tare har izuwa sauran kasashen biyu inda za’a sami ragowar barikan Allon biyu.Da zarar an samo su saiki shammaci Lubainu ki kwashe Allunan ki bace.Na san cewa ke gagarumar jaruma ce kuma mayakiya mai tarin sirrikan tsafi don haka ko gaba da gaba zakiyi dashi sai kin sami nasarar hallakashi.Idan ya tambayeki dalilin dayasa kike son ki bishi kuyi tafiyar tare kice dashi saboda a rayuwarki babu abinda kike so sama da tafiya.Koda tsohuwa Dulaiba tazo nan a zancenta sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta gamu da tsananin farin ciki kuma ta sami nutsuwa gami da kwanciyar hankali. washe gari kuwa da safe sai sarauniya Akisatul Sauwara ta tura aka zo da Yarima Lubainu har cikin turakarya in ya riske a kishingide bisa wata doguwar kujera ta alfarma tana shan ruwan inibi a cikin wani kofin zinare.A wannan lokacin tana sanye da wata jar riga mai shara shara wacce take bayyana dukkan surar jikinta.Koda Yarima Lubainu yayi arba da Akisatul Sauwara cikin wannan hali sai zuciyarsa ta buga da karfi,yayi sauri ya sunkui da kansa kas.Ba komai ne yasa shi hakan ba face gani yayi kamar masoyiyarsa ce Yazarina zaune a wajen saboda komai irin na surar jikin Akisatul Sauwara yazo iri daya sak dana Yazarina tamkar Hassana da Hussaina suke. Kawai a kamannin fuska ne suka bambanta.Tabbas Sarauniya Akisatul Sauwara ta cika kyakkyawar mace abin kwatance,To wai shin mene ne abinda ya hana wannan kyakyawar sarauniya yin aure alhalin tana cikin kuruciyarta don baza takai shekara ashirin ba a duniya?Wannan itace tambayar da Yarima Lubainu ya yiwa kansa kuma ya kasa bada amsarta.Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara taga Yarima Lubainu yayi saurin kawar da idanunsa ga barin kallonta ya sunkui da kansa sai ta kyalkyale da dariya sannan ta dago hannunta guda tana mai yiwa gaba daya kuyangin dake dakin inkiya dasu fita su basu wuri.Nan take kuyangin suka cika umarni. Fitarsu ke da wuya sai Akisatul Sauwara ta dauki wata abaya irin tasu ta saraunta ta yafa a jikinta,wato ta suturce tsiraicinta sannan ta dauko tambula na ruwan inibi gami da wani kofin zinare tazo daf da inda Lubainu ke tsaye ta kusanceshi ainun yadda har suna iya jin numfashin juna,sannan ta zuba masa ruwan inibin a kofin ta mika masa.Ba tare da tsoron komai ba Lubainu ya karbi kofin ya kurba.A sannan ne ta kama hannunsa taja shi izuwa kan waccan doguwar kujera suka zauna tare ta dubeshi fuskarta cike da annuri da murmushi tace,yakai wannan ‘dan Sarki kayi sani cewa kai ne da namiji na farko wanda ya taba shigowa har nan cikin turakata yasha ruwan inibina,kuma har hannuna mai daraja ya taba nasa.Ka sani cewa ba komai ne yasa ka sami wannan matsayi ba face saboda kazo min da babban al’amari wanda na dade ina jiransa a rayuwata.Kafin nayi maka wani cikakken bayani ina son ka sanar dani sirrin da yasa kazo kasata neman barin Allon Sihiri ni kuma nayi maka alkawarin zan dauko maka Allon Sihirin dake hannuna amma bisa sharadi guda biyu.Sharadi na farko shine tafiyar da zakayi tare dani za’a tafi har a gama hada Allon Sihirin uku.Sharadi na biyu kuma shine zan ajiye nawa allon a hannuna bazan baka ba har sai bayan an samo ragowar barikan biyu.Nasan zakayi mamaki bisa dalilin dayasa na kafa maka wadannan sharuddai to ka sani ba wani dalili bane face kawai ni a rayuwata babu abinda nake so sama da yin tafiya domin naga abubuwan al’ajabi,kuma nayi gami da mugayen dabbobi da tsuntsaye don na gano iyakar jarumtaka da sadaukantaka ta. Lokacin da Akisatul Sauwara tazo nan a jawabinta sai Yarima Lubainu yayi shiru yana tunanin da mamaki,kawai har izuwa tsawon yan dakiku,daga can sai yayi ajiyar zuciya yace shike nan na amince da wadannan sharudai naki.Nan take Yarima Lubainu ya kwashe labarin rayuwarsa kaf ya zaiyane mata ba tare da ya boye komai ba.Ai kuwa yana gama bata labarin jikinta yayi sanyi don har saida idanunta suka ciko da kwallah.Nan take taji zuciyarta ta kama wasi wasi akan cewar bai kamata ta yaudari Yarima Lubainu ba ta gudu da Allon Sihiri bayan sun hadashi.Zaifi kyau ta rakashi har izuwa kogin Bahar Imfal in yaso bayan bukatarsa ta biya sai ta dawo gida da Allon Sihirin ta cika nata burin.Wata zuciyar kuma sai tace da ita,idan kikayi haka kinyi babban kuskure tunda baki da tabbacin zaki iya wucewa lafiya kuma a raye ta cikin wadannan mugayen dazuzzuka guda uku kafin a isa kogin Bahar Imfal.Kawai sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta dago kai ta dubi Yarima Lubainu cikin alamun tausayawa tace,ka kwantar da hankalinka yakai Lubainu,hakika na tausaya maka mutuka bisa kaddarar daka tsinci kanka a ciki,kuma nayi maka alkawari cewar zan taimaka maka da raina da jikina da dukiyata har izuwa lokacin da bukatarka zata biya.Ina so ka gama dukkan shirye shiryenka a yau din nan amma zan shiga nawa shirin kuma yanzu zamuje dakin da wannan Allon Sihiri yake na daukoshi in yaso gobe da sassafe a lokacin da alfijir ya keto zamu bar garin nan mu durfafi BIRNIN KIMRAS domin mu gana da SARKI DARMASU mu sanar dashi bukatarmu ta barin wannan Allon Sihiri dake hannunsa.Kayi sani cewa bana tunanin cewa Sarki Darmasu zai amince ya bamu wannan barin Allo dake hannunsa domin yau shekara kusan bakwai kenan muna yaki a tsakanin kasashenmu akan mallakar Allon Sihirin amma abun ya gagari kowanne bangare.Idan har kaga ya amince da fito da Allon Sihirin dake hannunsa saidai idan shima yana da wata bukatar dabam.Babban abinda yake bani tsoro shine kamar yadda nake da tsaro akan nawa Allon Sihirin haka shima Sarki Darmasu yake da tsaro akan nasa,kuma bazamu iya rabashi da Allon ba da karfin damtse kona yaki da tsafi.Sa’adda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a zancenta sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ya rasa abinda yake masa dadi,kawai sai ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,nikam bani da wani zabi wanda yafi na jarrabata sa’ata kawai don haka babu gudu babu ja da baya a cikin wannan tafiya.Koda jin haka sai fuskar sarauniya Akisatul Sauwara ta fadada da murmushi tace biyoni muje.Tana gama fadin hakan ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuma saiya bita da sauri a baya. SHIN YARIMA LUBAINU ZAI SAMI NASARAR SAMO ABINDA YA FITO NEMA? A WANNE HALI YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA SUKE CIKI? INA LABARIN MATAR YARIMA LUBAINU (YAZARINA) DA MAHAIFINSA? ME ZAI FARU TSAKANIN SARKI DARMASU NA BIRNIN KIMRAS DASU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ITA DA YARIMA LUBAINU YAYIN DA SUKA JE GARESHI DON KARBAR BARIN ALLON SIHIRIN HANNUNSA? SHIN ZAI AMINTA YA BASU WANNAN BARIN ALLON SIHIRIN? Mu hadu a ALLON SIHIRI 2 don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Post navigation [ad_2]