Allon Sihiri 6

ALLON-SIHIRI,
Littafi na Shida (6)
Part A
Lokacin da aka ruguntsume da Azabebben yaki
tsakanin suhailat da wadannan samudawan
maridai su sarauniyya Akisatul sauwara suka fice
daga tsakiyar da’irar da’akeyin gumurzun suna
masuyin rarrafe tamkar kananun yara saboda
tsananin razana dasukayi,. Nanfa jaruma suhailat
tazamawa samudawan Alakakai yazamana cewa
Anrasa Wanda zaisamu daman koda lakutan
jikinta, haka itama takasa samun koda Kai guda
daya kasa acikinsu, alokacin dasu sarauniya
akisatul sauwara suka koma gefe duksu su ukun
suka takura jinkinsu suka zama ‘yan kallo, banda
muzurai da rawar jiki babu abunda sukeyi, kamar
Ace kyat!! Su fita da gudu. Saida akashafe kusan
sa’a biyu Ana wannan mummunan dauki ba dadi
ba tare da wani yasamu nasara ba Atsakanin
jaruma suhailat da wadannan samudawan
maridan. Al’amarin daya fusata samudawan
maridan Kenan, bashiri sukaja da baya sunamai
kurawa suhailat idanu suna huci da numfarfashi
kamar do Dodonni. Hakika wadannan halittar
sunyi matukar mamakin yadda wannan karamar
halitta ta gagaresu Alhali Tana yakarsune da
tsagoron KARFIN DAMTSENTA da iya takinta
batare da nau’in wani sihiri tsafi ba. Itakuwa
jaruma suhailat Ashe wannan ja da baya da
samudawan maridan sukayi, dama suka bata
takaranta Addu’ointa na neman tsari da sa’a.
Duk da cewa jaruma sulailat batasamu wata
nasara akansuba, Amma Sam zuciyarta bata
karaya ba, saboda ta dogara ga Allah, kuma
tasan cewa babu abunda zai gagareshi, nanfa
suhailat tafarayiwa Allah kirari acikin zuciyarta
Tana kiran sunsyensa tsarkaka guda Dari ba
daya. Tana cikin wannan Addu’o inne taga
samudawan sun hada kawunansu waje guda suna
kus kus! Kawai Sai suka rugo da guda gaba
dayansu izuwakan suhailat acikin sabon SALON
YAKI na musamman. Komai jarumtar mutum da
iya yakinsa idan yaga salon yakin da samudawan
sukazo dashi dole ya firgita, domin arike sukeda
hannunsu sunayin KAWANYA, sauran
hannayennasu na rike da makamai. Koda jaruma
suhailat taga sun durfafota acikin wannan salon
yakin sai nantake tagane nufinsu wato sosuke
lalle suyimata kuri a tsakiya yadda bazata taba
samun daman motsawa ba izuwa duk inda taga
dama, saidai sutakure awaje daya har yazamana
cewa tagaji sannan su samu lagonta. Koda
yarage saura baifi taku biyarba samudawan
maridan su cimmata sai tadaka tsalle sama ta
tsallakesu, kafin ta dira Achan bayansu saita
dako daya daga cikinsu. Take yarinjayi sauran
suka kife kasa.
Al’amarin dayi matukar baiwa maridan dasu
sarauniya Akisatul sauwara mamaki kenan bisa
ganin yadda jaruma suhailat tasami wannan
gagarumin wannan karfin. Cikin tsananin fushi
samudawan maridan suka miki zumbur! Suka
juyo da baya a fusace. Maimakon susake rike
hannun juna su rugo gareta sai suka tarwatse
kuma kowannensu yadako tsalle daga inda yake,
saigasu a sama tamkar tsuntsaye masu
fuka_fukai. Asamanne ko wannensu yazaro
makaminsa da nufin suyiwa jaruma suhailat
rubdugun SARA DA SUKA. Kafin kowannesu
yasamu daman Kai makaminsa jikinta tuni jaruma
suhailat tayi Dan tsalle sama tayi wata irin
katantanwa Sama tamkar An murza mazari ta
tarwatsasuTana Mai naushin fuskokinsu da
kafafunta dakuma hannayenta duk alokaci guda.
Kawai saigani akayi samudawan maridan suna
zuzzubewa kasa itakuma saitacigaba da
katantanwa Asaman kaman Anmurza mazari ta
tarwatsu Tana Mai naushin fuskokinsu da
kafafunta dakuma hannayenta duk a lokaci
guda.kawai saigani akayi suna zuzzubewa kasa,
itakuma tacigaba da katantanwa Asama har
izuwa ‘yan wasu dakiku ba tare da tafado kasaba
harsaida gaba daya samudawan maridan sukaje
Kasa sannan taduro kasa da kafafunta. Saboda
tsananin mamaki bisa ganin gagarumar wannan
jarumta da jaruma suhailat tayi Akisatul sauwara,
jarumi lubainu, sarki Darmaz da Dazyan basusan
sa’adda suka wangame bakinsuba sukazama
kamar gumaka domin ko giftawa basayi.
Mutara kokuma Anjima idan nasamu time gobe
Naku Khamis Idris Muhammad
Allon sihiri
littafi na 6 shida
Part B
Koda samudawan maridan sukaga abunda jaruma
suhailat tayi musu yazamana cewa duk ta
farfasamusu baki da hanci, sai suka fusata Ainun
suka taso mata da nufin su tarwatsata.
Koda ganin haka sai itama jaruma suhailat ta
fusata ta maida takobinta cikin kufenta ta taresu
Tana Mai karanta wasu Addu’a ta musamman
acikin ranta. Aikuwa suna riskarta sai sukaci
gaba da kaimata Sara da suka da manyan
miyagun makamansu, ita kuwa sai tawanzu Tana
Mai Kare duk hare harensu Tana Kama
hannayensu da kafafunsu Tana kakkaryasu.
Nanfa ihun samudawan maridan da kururuwarsu
tacika dajin gaba daya. Karar karyewan
kasusuwannasu kuwa tamkar karyewar
bishiyoyine Manya ke faduwa Kasa.
Kafin cikan dakika Dari bakwai da sittin gaba
daya samudawan naridan sun zube kasa
sunzama naka sassu sai koke-koke da ruri sukeyi
sakamakon tsananin zafi da zogin da sukeji.
A daidai wannan lokacin ne sarki Darmaz yadubi
sarauniya Akisatul sauwara yace, Tabbas wannan
jarumin ba mutum bane, Aljanine yazo garemu
domin ya yaudaremu. Saboda idan ba Aljani ba
banga wani mahaluki da zaizo yayi wannan
gagarumin jarumtakar ba.
Koda jin wannan Batu sai sarauniya Akisatul
sauwara tayi murmushi tace, Tabbas mutum ne
ba Aljan ba, domin inda Aljanine tun farkon
haduwarsu za’agane, saboda dukkan matsafi
yana gane Aljani adukkan shigar da yazomasa,
kawai kace hatsabibine kuma takadarin
BIL’adama Mai abubuwan Al’ajabi na gaban
kwatance,
Saidai Akwai wani Abu guda Dana kasa fahimta
akansa, har yanzu nakasa ganewa shin namiji ne
kokuma mace ne??
Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yadubi
sarauniya Akisatul sauwara afusace yace, wannan
wace irin maganan banza kikeyi yake wannan
sarauniya? Ina Mai tabbatar miki da cewa
maigidana namiji ne ba mace ba, saboda meye
kike tantama akan haka?
Koda jin haka sai itama sarauniya akisatul
sauwara ta dubi wada Dazyan afusace ta
dakamar tsawa tace, idan hard Mai gidan naka
namiji ne meyasa yakejin kunyan ya rube
agabana??
Tunda muka Fara wannan tafiyar babu Wanda ya
taba ganin gashin kansa bare cinyarsa.
Akan wane dalili yake boye komai na jikinsa?
Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yayi tsaki
yamiki daga cikinsu yatafi inda jaruma suhailat
take.
Shukuwa yarima Lubainu daman yana gefe daya
yana ganin ikon Allah.
Lokacin da Dan wada Dazyan yace wajen jaruma
suhailat sai ya sanar mata da duk abunda suke
fada akanta, sai hankalinta ya dugun zuma ainun,
tayi mamakin yadda har sarauniya akisatul
sauwara take kokarin gano haka.
Kawai sai ta dubi Dan wada Dazyan acikin YAREN
KURAME.
Karka damu da ita akan Hakan zargi takeyi
batada yakini akan hakan.
Gama fadin haka keda wuya sai jauma suhailat
ta juya gefen inda yarima lubainu yake tsaye.
Awannan lokaci samu dawan maridan da jaruma
suhailat ta bazar akasa sun Fara Jan jikinsu
akasa dakyar tamkar macijiyar da tayi babban
hadiya.
Kwatsam bazato ba tsammani sai sukaji wata
gagarumar iska a samansu.
Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri tun An
mammakesu.
Saboda karfin bugun da akayiwa kowannensu a
fuska, take suka zube kasa sumammu.
Lokacin da jaruma suhailat da yarima lubainu
suka farfado daga suman da sukayi sai suka
tsinci kansu a daddaure da wata murtukekiyar
sarka ajikin wata bishiya kuma duk gabobin
jikinsu a sanyaye suke ta yadda ko daga
hannunsu bazasu iyaba saboda rashin karfi da
kuzahari.
Acan gefe guda kuma sarauniya akisatul sauwara,
sarki Darmaz, Dan wada Dazyan ne suma acikin
mummunan Hali suyi darsham akasa kamar
yadda su jaruma suhailat suke na dauri.
Har izuwa wannan lokaci wannan iska bata daina
ba ta gabar da yamma kudu da Arewa.
Nanfa jaruma suhailat da Dan wada dazyan suke
kokarin bude bakinsu suyi Addu’oi Amma abun ya
gagara.
Al’amarin dayayi matukar dugun zuma hankalinsu
kenan suka rasa abunda keyimusu dadi, sabida
tamkar sunayin yakine da abunda basa ganinsa!
Kawai sai sukaji An bushe da wata mahaukaciyar
dariya wacce sautinta yacika dajin gava daya
karfinta yasa tantuna sukafara jijjiga kamar zasu
tumfuke sufadi Kasa.
Bazato ba tsammani sai halittar ta baiyana
tsulum! Agaban yarima lubainu ta yadda har
sunajin nunfashin junansu.
Bakowa bace wannan halittar face Aljana
badi’atul sauwara.
Cikin razana da mamaki yarima lubainu yaja da
baya yadubeta yace,
Kekuma waye ya kunceki acikin daurin Dana
baroki?
Koda jin haka sai Aljana badi’atul sauwara tasake
bushewa da dariya a Karo na biyu sannan ta
tsuke bakinta Tana Mai turfune fuska tace, Kai a
iya tunaninka ka dauren kana tunanin vazan taba
kubuta ba ko?
To kayi babban kuskure da kayi zaton haka,
saboda Mai RAI baya fidda tsammanin RABO face
yaba nunfashi a doron Kasa.
ALLON SIHIRI LITTAFI
NA SHIDA 6 PARTC
Tabbas yanzu ne zakayi babban nadama akan
rashin bani hadin Kai domin mugudu tare mu tsira
tare da Kai.
Aljana Badi’atul sauwara takauda kanta wajen
jaruma suhailat race,
Angaisheki BABBAR JARUMA! Hakika kin
yaimakeni kin gajarcemun duk wahalan da zansha
ta hada wannan ALLON SIHIRI guda uku, tunda
gashi yanzu gaba dayansu a Hannunki.
Kisani cewa wadanchan samudawan maridan da
kika yakesu bakowa bane ya turosu face Boka
darbusa, kuma har ynz baituromuku kaso goma
ba daga cikin dubun irin mugayen abubuwan da
yayi tanadi domin ku Akan wannan ALLON
SIHIRI”.
Lokacin da Aljana badi’atul sauwara tazo daidai
nan a zancenta sai Sarauniya Akisatul sauwara ta
wunkura cikin karfin Hali ta bushe da dariyar
farinciki sannan tace, yake wannan Aljana Mai
tsananin SA’A da RABO! Ina Mai godia a gareki
da kika fitar damu faga cikin duhun daya
baibayemu game da Abokanan tafiyarmu.
Tun a farkon tafiyar mu da wannan bakuwar
jarumar idanuna suka nunamin cewa wannan
MACE ce ita Name MIJI ba kamar yadda take
ikirari.
Shin yanzu ke mecece ribarki idan kika tafi kika
barmu awannan mawuyacin halin makiya sukazo
suka hallakamu tunda dai kinsami abunda kike
nema?
Sa’adda Aljana badi’atul sauwara taji wannan
Batu saita bushe da dariya tace, Ai shi makiyi
ba’a bashi dama komai kankantarta.
Ni banida makiyin da yawuce boka Darbusa a
duniya, shikuma awajensa kune manyan
makiyansa tunda kunzo har gidansa kurrabashi
da abunda yashafe shekara da shekaru yana
gadinsa Dan yacika burinsa na duniya.
Kusani cewa bayan na dauke Allunan sihiri da
suke wajenku yanzu, ina tafiya da tsawon dakiku
sarkokin Dana daureku zasu bace bat! Daga cikin
jikinku, kuma kuzaharinku zai dawo kamar yadda
kuke a da, Amma fa kusani boka darbusa bazai
taba barin kokarin hallakakuba tunda shi
azatonsa kuna tare da ALLON SIHIRI.
Nikuma daman zanyi Amfani da wannan ALLON
SIHIRIN Wanda daman asalinsa nawane tunda
mahaifinane yakerashi, kafin ku fita daga cikin
masifun da kuke ciki tuni nagama dukkanin shirye
shiryena na zama SARAUNIYAR DUNIYA acikin
kwanciyar hankali batare da na fuskanci wata
matsalaba.
Gama fadin haka keda wuya sai tajuwo ta dubi
yarima lubainu tadubeshi cikin wani irin
murmushi na mugunta tace, tabbas kasaki reshe
ka Kama ganye! Yanzu inda ace ka taimakeni ka
kunceni acikin daurin da boka darbusa yamin da
yanzu take Zan daukeka na doraka akan gadon
bayana natafi dakai Chan fadata.
Achanne zan karanta wannan ALLON SIHIRI
nagano inda KOGIN IMFAL yake nakaika Chan
kaciro saiwar da bishiyar da ake bukata wacce
zakasha ka warke daga lalurar da yarima mangul
ya sakamaka.
Yanzu gashi kayi biyu babu, domin bazaka warke
ba, kuma bazaka sake saduwa da matarkaba
GIMBIYA YAZIRINA har Abada, dimin a halin
yanzu suna Chan wani waje Mai mugun Nisa
acikin daji acikin mugun yanayi na rashin sanin
inda suke dama inda zasu dosa.
Kuma yarima mangul bazai daina farautarsuba
har saiya riskesu ya kashe SADAUKI RUHAISU
sannan ya dauke gimbiya yazarina”.
koda Aljana Badi’atul sauwara tazo nan a
zancenta saitakara Bushewa da dariya akaro na
biyu sannan tadubi yarima lubainu tace, shin
kanada wata wasiyya ne ga mahaifinka!?
tabbas zanyi maka wannan Alfarmar nakai
wannan wasiyyarka tunda nima Kayimin Alfarma
guda daya ta rufamin Asari baka sanar da
wannan BAKUWAR JARUMA Mai Rufe fuskarta da
jikinta labarina sa’adda ka ganni acikin gidan
boka darbusa da bansamu wannan damar yanzu
ba Dana shammaceku Dana sumar daku, kuma
nasanya muku wannan tsananin mutuwar jikin.
koda jin haka sai Aljana Bari’atul sauwara tasake
tuntsurewa da dariyar mugunta taita kyalkyalewa
kamar bazata dainaba ba.
daga can kuma saita tsuke bakinta tace,
Ai shi kenan nida Kai zanga Wanda zancensa zai
tabbata.
Tana Gama fadin haka sai ta bude fuka fukanta
saiga ALLON SIHIRI guda uku amakale a
hammatarta.
harta yunkura zata tashi sai yarima lubainu yace
yake wannan Aljana, waishin wanene ya kunceki
daga wannan daurin da boka darbusa yamiki?
Koda jin wannan tambaya sai Aljana badi’atul
sauwara tayi murmushi tace, babu Wanda ya
kunceni face ni kaina.
Kasan Ance Mai rai baya kasa motsi! Bayan kaki
kunceni katafi kabarni acikin wannan mawuyacin
Hali ina zubar da hawaye sainarinka buga kaina
ajikin bango saboda bakin ciki kuma narinka buga
kafafuwana a kasa.
Adalilin hakanne kafafuwan nawa suka rinka fasa
malalen kasan har suka haddasa rami Mai zurfi,
Ashe acikin kasan dakin danake aciki yake ajiye
Littatafai dayawa na sirrikan tsafin boka darbusa.
Dayake sarkar dayake daure Dani Mai tsawo ce
sosai, take nakarasa Burma ramin da kafafuna
sukayi nafada kasan dakin nashiga karanta
littatafan.
Acikin littatafanne naga sirrin yadda zan kwance
kaina daga sarkokin da boka darbusa ya daureni.
Nantake nakamu da tsananin farinciki dakuma
takaici ganin cewa sai a sannan ne nasan da
wannan damar bayan na shafe shekaru da dama
acikin kurkukun bakin ciki.
Da wannan furuci nakeyi muku bankwana na
karshe.
Koda Gama fadin haka sai Aljana badi’atul
sauwara tasake bude fukafukanta ta tashi sama.
kafin giftawar ido ta luluka acikin gajimare ta
bace bat!!