Allon Sihiri 6HAUSA NOVEL

Allon Sihiri 6

 

Tamkar bata taba wanzuwa ba awajen.
Bayan shudewan wasu ‘yan dakiku ne su jaruma
suhailat sukaga sarkokin da aka dauresu dashi
sun bace bat!! Tamkar basu taba wanzuwa ba
Sannan sukaji karfin jikinsu yadawo dakuma
kuzaharinsu yadawo tamkar wani Abu bai taba
samunsuba.
Cikin hanzari jaruma suhailat mike tsaye zumbur!
Tacire rawanin dayake kanta tayi jifa dashi.
Alokacinne dogon gashin kanta ya zubu izuwa
gadon bayanta yana sheki da walwali.
Jaruma suhailat ta cire babban rigan da ke jikinta
doguwa ta tsargeta da hannayenta biyu tayi jifa
da ita saiga gaba daya surorin jikinta sun fito.
Koda sarauniya Akisatul sauwara da sarki darmaz
sukayi Arba da wannan baiwa ta kyau wacce
Allah yayiwa jaruma suhailat saisuka dimauce
suka fita a haiyacinsu alokacin idanuwansu suka
kafe, jikinsu ya Kame suka kuramata idanu
kawai.
Ita kuwa sai ta durfafosu saida tazo dafda su
sannan ta tsaya fusakrta a murtuke.
Susana SUHAILAT BINTU AFUWAN, kuma nafitone
daga wata nahiya Mai Nisa, daban da taku ba,
Acikin wata kasa da ake Kira DARUL ILMUN.
Bakokai ne yakawoni nayiyarku ba face jaddada
ADDINiNA Wanda shine Addinin gaskia a bautawa
Allah shikadai Wanda bashida Abokin tarayya,
wato ADDININ MUSULUNCI!
Lallai saina tabbatarwa da sarakunanku da kuma
Bokayenku cewa bautar gumaka da tsafin da
kukeyi duk karyace, kuma hanyace ta bata
mabaiyani.
idan har na’isa login bahar imfal da taimakon
ubangijina nayi nutso acikinsa na tsunto Dan
itatuwar da yarima lubainu zaisha ya warke daga
asirin da yarima mangul Yamar dolene su yarda
da Addinin tunda sun tabbar babu Wanda yataba
yin hakan, kuma babu Wanda zai iya.
Kosani cewa koda Allon sihiri na wajenmu ko
bayanan zamu isa kogin bahar imfal nabiyawa
yarima Lubainu bukatarsa Da izinin ubangijin
musulunci.
Sa’adda jaruma suhailat tazo nan azancenta sai
sarauniya akisatul sauwara da sarki darmaz suka
dawo haiyacinsu sunamasuyin doguwar ajiyan
nunfashi, sannan sai sarki darmaz yadubi jaruma
suhailat cikin fushi yace, to mu meye Amfanin mu
cigaba da binku acikin wannan tafiyan tunda
Arrabaki da Allunan na sihiri?
tayaya zaki iya dauko wannan makarun maganin
da akayiwa trains lubainu Alhalin babu ALLON
SIHIRI awajenki?
koda jin wannan Batu sai jaruma suhailat tace,
tunda imaninku ya karkata akan sai da ALLON
SIHIRI?! Za’a aiwatar dashi, to shiekenan zan
karbo muku ALLON SIHIRIN daga hannun wannan
Aljana da tazo tasaceshi.
ALLON SIHIRI
Littafi na shida (6)
Part D
Kusani cewa sakaci ne yasa har tasamu dama ta
shammaceni kuma bansan da batuntaba, Amma a
yanzu Dana Dani duk inda take saina bita na
karbo ALLON SIHIRIN naku da iznin ubangijina.
Kusani cewa wannan buri na banza da kuke son
MALLAKAN DUNIYA da abun cikinta shirme ne
kuma nadaukeshi tamkar tatsuniya, wato Abunda
bazai taba faruwa ba, Saboda shi tsafi karyane
kuma batane.
Da idanunku kunga dai Abubuwa da dama danayi
na Al’ajabi cikin jarumtaka cikin taimakon
ubangijin gaskiya kokuwa har yanzu zukatanku
suna yaudarar ku??
Sa’adda jaruma suhailat tazo daidai nan a
zancenta sai dadin muryanta yasake dimauta
Sarki darmaz, yadubi sarauniya Akisatul sauwara
sai sukakamayin in’ina suka kasacewa komai.
Koda ganin haka sai jaruma suhailat ta yafito
yarima lubainu da hannunta tajashi can gefe daya
inda baza’aji abunda suke tattaunawa ba, suka
kamayin maganganu.
Koda ganin haka sai KISHI yakama Sarki darmaz
da Dan wada dazyan, domin kowannensu jiyayi
inama shine yakadaita da jaruma sulailat haka
yana kallon kyakkyawar fuskarta kuma Yana ka
sauraron naganarta Mai zaki wacce ita kadai
zatasa mutum yayi bacci kokuma ta kwantar
masa da hankali a lokacin da yasamu kansa cikin
bakin ciki ko damuwa.
Ita kuwa Akisatul sauwara wani tunanine yafado
mata nan take Wanda ya dugunzuma hankalinta
tarasa Abinda yake mata dadi.
Dafarko dai sa’adda taga yarima lubainu da
jaruma suhailat sun koma gefe sun tsaya dabda
juna suna magana saita kuramusu idanu Tana
Lura da irin kallon da sujeyiwa junansu, kawai so
take ta gano shin Akwai soyayyane a tsakaninsu?
To idanma Akwai soyayya ai saidai idan ayanzu
take aka farata tunda dai shi baitaba ganin
fuskartaba sai a yanzu.
Tun a ranan da Sarauniya akisatul sauwara tafara
ganin yarima lubainu taji ya kwanta mata aria
domin yanada duk abunda takeso ga namijin da
zaizamo abokin rayuwarta.
Abu nafarko dai shine, yanada tsananin kyau,
kuma gashi basarake ne, sannan jarumin maza.
Wadannan abubuwa uku sune samarin da suke
nemanta suka kasa hadawa duk, kuma shine
dalilin dayasa itama taki karbar soyayyarsu.
Daga ranan da tahadu da yarima lubainu taga
Ashe Allah yakawo mata karshen laluben da
takeyi.
A yanzu kuma dataga jaruma suhailat tare da
yarima lubainu, saitaji wani irin BAKIN KISHI ya
turnuketa, saboda…. KUYI HAKURI BABU PAGE
DAYA missing 27 page.
Sarauniya akisatul sauwara sai taji kamar Tasa
kafarta tayi tamaula dashi, tunda tsawonsa gaba
daya baiyuce tsayin guiwartaba.
Dan wada dazyan yayi shiru ga barin yin dariyan
sannan yadubi sarauniya akisatul sauwara yace,
dafarko dai kisani cewa ban isa na fadi komai
akan shugabata face sai da izninta saboda bin
umarninta.
Abu na biyu danakeso na tunamiki shine, yarima
lubainu yanada mata wacce tunima Andaura
musu Aureda ita, kuma saboda itane yafito
neman maganin lalurarsa.
Shin tayaya kike tsammanin zaibada soyayyarta
take tsawon shekaru izuwa wata macen daya
hadu da ita acikin kankanin lokaci?
Idan kema kinji kinfara kamuwane da soyyar
yarima lubainu inamai shawartarki da ki gaggauta
ki shafeshi acikin Kundin rayuwarki don kada
yabada miki kasa…..
Kafin Dan wada dazyan yagama fadin abunda ke
bakinsa tuni sarauniya akisatul sauwara ta daka
masa tsawa.
Al’amarin dayasa yarazanane har hantar cikinsa
ta kada yadan ja da baya a firgice.
Sarauniya Akisatul sauwara ta dubeshi a fusace
tace, waccer Shugaba taka babu wani Abu da da
namiji bazata iya saye zuciyarshiba saboda
kyawunta, koda kuwa shine Wanda ya kirkiri
soyayya a duniya.
Ni kaina danake ‘ya mace kuma kyakkyawa abar
kwatance ayanzu Dana ganta saida na Raya a
Raina cewa imani ni namiji ne Dana mallaketa
Amatsayin Matata.
Kasani shi SO ba karya bane gaskiyane kuma
nasani cewa yarima lubainu yanada matar da
yakeso, Amma shin mainene tabbacin zaisake
saduwa da ita Alhalin rayuwarta nacan acikin
mugun hadari?
Kai! Ni tuni ma nayi bincike acikin tsafina nagano
cewa gimbiya yazirina da yarima lubainu baza su
tabayin zaman mata da miji ba, Dan haka babu
abunda zaisa nadaina sonsa.
kuma kasani cewa nice nafara haduwa da yarima
lubainu har nabaro kasata, mulkina da jama’ata
domin na taimakeshi.
kaikanka kasan cewa idan babu SO da KAUNA
babu yadda za’ayi Nabaro wadannan Abubuwa
uku, na sallama rayuwata kawai Dan biyan
bukatarsa.
Caraf! Sai dazyan yatari mumfashin Akisatul
sauwara yace Ai badon bukatarsa kadai kema
kika fitoba sai domin kema ki samu daman hada
Allunan sihiri guda uku.
sarauniya Akisatul sauwara tayi murmushi tace,
maiyasa tuntuni banyi wukurin Nemo wadannan
Allunan sihiri ba guda biyu tunda nasan A inda
suke sai ayanzu da yarima lubainu yazo gareni?
Kai! Dakata nagaya maka gaskia, karfin soyayya
yafi dukkan karfi, domin so yana iya sakawa
mutum yadaina tsoron abunda yake tsoro,
Saboda soyayya ta mantar dashi baya ganinsa.
SO yana sakawa mutum ya fansar da rayuwarsa,
kuma duk Wanda yayi yunkurin rabani da Abunda
nake kauna shima zarrabashi da rayuwarsa!!!
Ko ka sanar da shugabarka wannan ko baka
sanar ba wannan ba matsalata bace, Amma zaifi
kyau kagaya mata, domin ta nisanta kanta da
yarima lubainu domin nawane ni kadai.””
koda fadin haka sai Sarauniya akisatul sauwara
tajuya da nufin ta koma inda tabaro sarki
darmas,Amma sai Dan wada dazyan yayi saurin
kiran sunanta sai tajuyo ta dubeshi sannan yace,
Babu yadda za’ayi ta nisanta da yarima lubaino
saboda ahalin yanzu yazama tamkar Dan uwanta
najini tunda yakarbi Addininta, wato Addinin
musulunci.
koda jin haka sai habkalin sarauniya Akisatul
sauwara ya dugunzuma fiye da ko yaushe, tayi
shiru Tana Mai sunkuyadda kanta kasa, inda
tafada cikin kogin tunani Mai zurfi.
Tana cikin tunanin ne taga yarima lubainu ya
baru inda jaruna suhailat take ya durfafo inda
suke, Dan haka saita kura masa idanu Tana Mai
murmushi..
da isawarsa inda suke yadubeta sannan yadubi
sarki darmaz yace, jagorar tafiyarmu tace nasanar
daku cewa anan zamu kwana tunda Rana ta fadi
sai gobe mucigaba da tafiya.
Kodajin wannan Batu sai Sarauniya Akisatul
sauwara tadubi yarima lubainu cikin fushi tace,
waishin akan wane dalili zamucigaba da bin
jagorancinta Alhalin tanaji Tana gani akazo aka
kwace mana ababan dogaranmu aka tafi dasu??
Ai wannan alamune na gazawa, waishin yanzu
tasan inda zamuga Aljana badi’atul sauwara ne
bare har muje mu risketa a fafata KAZAMIN YAKI
Don kwato kayanmu.
to kasani Aljana badi’atul sauwara bakamar
hatsabibiya bace,
Sarkin wannan Birni na Istanbul saurayine
kyakkyawan gaske, kuma sadauki Mai TARWATSA
MAZA a FILIN DAGA!!
A duniya kaf! Awannan lokaci babu Wanda yafishi
tarun dukiya, girman sarauta da kwarjini.
wannan daliline kowace kasa ke shakkarsa, domin
yatara mayaka ‘yan gaban gani kasheni masu
tsananin karfi da horon yaki na ban Al’ajabi.
Ana kiran wannan sarki na Birnin Istanbul da suna
SHA’AFARAN IBN AUHID.
Khamis Idris Muhammad
ALLON SIHIRI
Littafi na shida (6)
Part E
Babu wani jindadi Wanda Allah baibawa sarki
Lubainu ba face Abu guda daya jal!!
Bakomai bane face Rashin lafiyar maza kuta!!!
Tundaga balagar sarki lubainu har yacika shekara
talatin da uku baisan wani Abu waishi Sha’awa
ba akan ‘ya mace, baitaba yin wata mu’amala
dawata mace ba hasalima ko kuyangi basa masa
yidima saboda sanin baya bukatarsu a rayuwarsa.
Duk wata hidima tasa maza ne ke masa, dafarko
boye matsalarsa yayi Sai akafara zargin ko yana
harkan banzane da maza Amma da’aka gano
baya wannan harkan Sai akagano bashida lapia
ne, saboda tunda yake arayuwarsa baitaba yin
soyayya ba, kuma baitaba tunanin koda yin Aure
ba.
Akaf duniya babu abunda Allah yajarrabi sarki
lubainu yakeso sama da kananan yara ‘yan
shekara hudu zuwa kasa.
A kullim yanasa adebomasa kananan da yammaci
acikin lambunsa azauna acikinsu yaita wasa dasu
har magariba tayi sannan za’araba musu kayan
wasanni iri iri da kayan zaki sannan ya
sallamesu.
Duk sa’ilin da sarki lubainu ya kurawa wa’yannan
yaran idanu ASA ilin da suke wannan wasa Sai
yafara zubda kwalla saboda takaicin sanin
bashida haiwuwa bare yasamu magaji na har
Abada!
Babban abun bakinciki ma agareshi shine, shine
zuri’a na karshe a wannan gidan sarauta, dazarar
ya mutu shikenan sarautar tabar Ahalin gidansu
takoma kan wata zuri’a sannu ahankali
za’amanta da zuri’arsu ma gaba daya a doron
kasa.
Bisa wannan daliline yabaza yaransa afadin
duniya suna ziyartar bokaye da manyan likitoci
har tsawon shekara uku domin asamo masa
magani Amma ba’adaceba,kuma Duk wajen
bokan da akaje saiyace indai sarki Lubainu yanso
yasamu lafiya irinta da namiji toko saidai yaje
birnin Hindu yayi tsirata a gaban sarauniya
Mauzuratul shardila ya fadi bukatarsa bayan
yayimata yanka sannan ne bukatarsa zata biya
shikuwa sarki Lubainu yace bazai taba kaskantar
da Kansa irin haka ba ace har mutane suga
tsiraicinsa don kawai biyan bukata Lallai daya
Aikata haka gwara yamutu babu haihuwa.
Dukkanin samoyan sarki Lubainu da
makusantanshi da Aminansa babu Wanda
baibashi shawari akan yaje gaban sarauniya
mauzuratul shardila baya Aikata abunda aka
uwarceshi domin yasamu Haihuwa, Amma Sai
yaki.
Duk Wanda yamatsamar akan yaje karshenta
batawa sukeyi da shi yadaina kulashi, dukkuwa
kusancin dake tsakaninsu dashi.
Haka dai sarki Lubainu yaci gaba da tayuwa
haryacika shekara sha biyar akan mulki bayatare
dayasamu da ba bare jika.
Kwatsam! Sarki Lubainu wata rana yayi sha’awar
yafita daji yayi farauta, don haka saiyadibi
dakarunsa mutum shida kacal! Domin suyi masa
rakiya, sukayi shiri irin na mafarauta suka shiga
daji.s
A farkon yammaci sarki Lubainu yafito wannan
farutan, alokacin da rana tayi sanyi launin garin
sunyi shudi, alokacin anayin wata iska mai sanyi
atakaice dai yanayin da akeciki yanayine mai
dadi, uanayin da yakesa mutum nishadi da
farinciki.
Duk da sarki Lubainu ya kasance sadauki, kuma
GORZON MAYAKI mai TATWATSA MAZA a FILIN
DAGA Amma Sau uku kacal yataba fita farauta a
rayuwarsa, don haka baisan sirrin dajiba sosai,
kuma baisan sirrin dabbobin daji ba.
Sai da sarki Lubainu suka shafe kusan sa’a biyu
da rabi a daji suna yawon farauta Amma ko zomo
basu kamoba.
Hatta ysuntsayen da suke Yawo asararin
samaniya sunkasa hatbo ko guda daya.
Al’amarin da ya fusata sarki Lubainu kenan
yadubi wa’yannan dakaru guda shida a fusace ya
daka musu tsawa sannan yace, Amma tur! Da Ku!
Tabbas kunji kunya!! Nazaboku ne saboda
dukkanku kunkasance ‘ya’yan manyan mafarauta,
Amma kunkasa farauto koda Kwaro ballantana
dabbar daji ko tsuntsayen da suke giftawa ta
saman knmu.
Towai shin sokuke mukoma gida cikin Abun
kunya agammu babu komai a hannunmu ko
yaya ??
Koda jin haka Sai babban cikinsu Wanda shine
Dan sarkin mafarauta na garin yarisina Ga sarki
Lubainu yace, agaskia Akwai matsalar da tafaru
akan wannan lamarin.
Yau kusan sati uku kenan dazuzzukan dake
yankin birnnan namu sun zama wayam!
Duk dabbobin dake cikinsa sun face bat! Tamkar
Anyi ruwan sama Andauke.
Amma mahaifina yace yanaganin wasu bakin
mafarautane suka gifta ta wannan dajin kuma
suna da yawan gaske, Ayari ne guda, yana zaton
sune suka kwashe mana komai.””
Kodajij wannan batu Sai ran sarki Lubainu ya
baci, zuciyarsa tayi bakikkirin sayake dakawa Dan
sarki mafarauta tsawa har said a hantarsa ta
kada yace, yanzu daman Ansan da wannan
matsalar ba’azo an sanar daniba??
Dan sarki mafarautan yasake risinawa yace, ya
shigabana mahaifina ya sanar da waziri, kuma
waziri yasa Ana bincike akan lamarin, nayi
tsammanin Sai abun yafi karfinsa ne zai sanar
dakai””.
Koda sarki Lubainu yaji haka Sai yayi kwafa
yacije lebe sannan yace, aikuwa idan nakama
wa’yannan bakin mafarauta Sai sun biya duk
abunda akarasa acikin dazuzzukanmu kokuma su
fanshi laifin su da rayukansu,,,,,””
Kafin sarki Lubainu yagama rufe bakinsa Sai
sukaga giftawar wani mutum cikin wani
azabebben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya
ya wuce fit! Tagabansu ya bausa cikin daji , kafin
giftawar ido yabace bat! Aikuwa Sai sarki Lubainu
ya sakatwa dokinsa linzami yabi wannan mutum,
cikin hanzari suma dakarun suka rufa masa baya.
Sarki Lubainu uacigaba da baiwa dokinsa kaimi
yanamai irin wani azabebben gudu tamkar zai
tashi sama, Amma Dakar ya iya hango mutumin
daya gotasu a can gaba nesa dashi.
Ashe ma macece acikin shigar kayan fatar
damisa.
Koda sarki Lubainu ya hango wannan mace tana
faman wannan azabebben gudu na ban Al’ajabi
kuma yaga Ashe dawata damisa suke tsere.
Damisar gudu take iya karfinta domin ta ceci
ranta Amma tazarar dake tsakaninsu da wannan
macen baiwuce taku biyar ba, Ako yaushe za’aiya
cimma damisar, Nan take sarki Lubainu yacika da
tsananin mamaki kuma ya dimauce sakamokon
dalilai biyu.
Dalili na farko shine, Duk da cewa bayan wannan
macen yake hangowa mai kyan kira da siffa
kamar ta ba. Gashin kanta kadai ya isa mutum
yasa ya dimauce saboda ya zubo harkan kasan
kugunta saboda tsawonsa.
Duk da cewa an tartare gashinne a gadon
bayanta Sai tarwatsewa yakeyi acikin iska saboda
yawansa ya kasance yanada tsananin baki gami
da kyalkyali da hasken da mutum zai iya gamin
fuskarsa akansa tamkar madubi.
Dalili na biyu kuwa shine, sarki Lubainu baitaba
ganin bil’adama ba mai karfin gudun wannan
mace ba wacce take kokarin kurewa damisa gudu.
Nan da nan zuciyarsa ta Aiyyana masa
tambayoyi.
KUMA WAI SHIN ITA WANNAN JARUMA MACE
WACE IRIN SHAIDANIYACE ITA HAR DA WANNAN
KATUWAR DAMISAR ZATA GUJE MATA. KOKUWA
TA KASANCE ALJANA BA MUTUM BA.??
Sarki Lubainu yabaiwa kansa Amsar da yayiwa
kansa wannan tambaya kawai saiyaga wannan
mace ma’abociyar kyau tayi sufa tafadi cahn gefe
ta chapo wuyan namisar suka kama kokawa a
kasa.
Kawai Sai jarumar ta miki tsaye ta rike makoshin
damisar da hannu daya tayiwa damisar hajijiya
Asama say uku ta fyadata da kasa ta takemata
wuya da kafarta guda.
Nan fa damisar tafara kakakin Mutuwa inbanda
jelarta da kafarta babu abunda take iya motsawa
kafin sarki shahran ya iso garesu tuni damisar
tazama gawa.
Koda wannan jarumar taji sukuwar dawakai
abayanta sai tajuyo saita kurawa sarki Lubainu
idanu batare da tayi wani motsiba ko taji wani
tsoro ba.
Sarki Lubainu yadira a gabanta yajuyo yana mai
yimata nuni da tabashi wannan damisar.
Jarumar ta wunkura kamar zata mikamasa
wannan damisar. Amma Sai itama ta daka tsalle
sama cikin shammata takaimasa duka da kafarta
a girjinsa.
Duk da tsananin karfi irin na sarki Lubainu said a
yayi baya taga taga kamar zai fadi, yzamana
suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da
kafa acikin tsananin zafin nama. Juriya da
bajinta.
Ai kuwa Anafara wannan gumurzu ne Sai sarki
Lubainu yacika da tsananin mamaki domin a iya
rayuwar gwagwarmayarsa baitaba haduwa da
jarumin da karfinsu na damtse yazo daya ba irin
wannan jaruma.
Komai karfin kato da iya fadansa akaron farko
yake gamawa da shi Amma gashi wai ‘ya mace
ya shafe ‘yan dakiku da ita. PAGE 46 IS MISSING.
Wannan bakuwar jaruma kasa, kuma ya kwace
wannan damisa dake hannunta ta kowane hali,
Idan ba hakaba kuwa ta karya Alkadarin
jarumtakarsa kuma ta bashi kunya agaban
dakarunsa.
TUNDA DAI TA’IYA FADA DA HANNU GASHI
HARMUNYI KUNNEN DOKI , BARIN GWADA IYA
YAKINTA DA MAKAMI NAGANI.
Koda Aiyana hakan acikin ransa Sai sarki Lubainu
yadubi jarumar a fusace yace, yake wannan
budurwa INA gargadinki da ki mika wuya agareni
na kamaki amatsayin mai laifi, kuma ki bani
wannan damisar dake hannunki inbahaka ba
kuwa zaki tilastani nayi Amfani da takobina
akanki, kuma banaso naragewa wannan
kyakkyawar sura naki kyawu.
Koda jin wannan batu Sai jarumar tayi wani dan
guntun murmushi Ga sarki Lubainu kuma tasake
murtuke fuskarta tace.
Ai ba’a sanin maci tuwo Sai miya takare!
Idan har kana ganin zaka iya samun nasara
akaina da karfin takobinta saika jarraba!!.
A India babu kasa Anan ake gardamar kokawa!!!
GA FILI GA MAI DOKI Mu zuba mugani!!!
Tana gama fadin haka tasa hannu ta zare
takobinta, Al’amarin dayayi matukar girgiza
dakarun sarki Lubainu kenan suka kamu da
tsananin mamaki kuma suka tausayawa wannan
jarumar domin inda tsan tsananin iya yakin sarki
Lubainu da batayi wannan ganaganciba duk da
cewa sums basusan iya NATA yakinba.
Koda yake makaho bayacewa ayi wasan jifa
saiyaga hoge, Amma kuma ai bakin rijiya bawajen
wasan makaho bane!!!
Koda sarki Lubainu yaga irin dakewar wannan
jarumar budurwa harms ta rigashi zare takobi Sai
ya sake cika da mamakinta, kuma yaji ta Dada
burgeshi Ainun,domin yanason mace mai zuciyar
maza wacce yakeganin itace kadai zata iya
dacewa da shi ,
Nan take sarki Lubainu ya sake ja da baya kamar
taku biyar sannan yatsaya tsaf yazare tasa
takobin yanamai bude hannayensa suka kurawa
juna idanu shida ita har izuwa wani Dan lokaci.
Kamar hadin Baku Sai duk su biyun suka Togo da
gudu izuwa kan junansu sunamasu kartan kasa
da takubbansu kaida gani kasan cewa idanu
akayiwa wannan haduwar komai zai iya faruwa.
Muhadu gobe in Allah yakaim

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button