Allon Sihiri 6

ALLON SIHIRI
Littafi na shida (6)
Part F
Koda yarage saura taku uku su hadu Sai suka
daka tsalle sama suka kaiwa jujansu mugun hari.
Shidai sarki Lubainu a wuya ya kaimata saran da
nufin ya tsizge mata kai, ita kuma Sai takaimasa
Sara a kafada da nufin ta zaftaremasa hannunsa
na hagu.
Cikin zafin nama kowannensu yakaucewa harin
da aka kawomasa Amma Sai wani abun Al’ajabi
yafaru a lokacin da suka duro a kasa a bayan
junansu a tare.
Abunda ya faru shine, sakaomakon da saran da
sarki Lubainu yakaiwa jarumar wuya ko shafar
jikinta baiyiba Amma Sai kaifin takofinsa ya
tumke wani Jan kyalle da ta daure gashin kanta
da shi, ya tsargeshi gida biyu ya fado kasa.
Ita kuwa kwalar rigar da ke jikinsa ta yanke ta
yanke tafadi kasa.
Ita dai wannan rigar ta sarki Lubainu mai
muguwar tsada domin ta zallar rigar Alhariri
akayita gami da zaren danyen zinare, musamman
yasa akaje birnin farisa aka dinkota.
Koda sarki Lubainu yaga An lalata masa wannan
Riga mai Daraja Sai ranshi ya baci Ainun.
Itama jarumar dataga An yanke mata wannan
Jan kyalle nata Sai tajuyo a fusace Ainun.
Ashe wannan kyalle shine matsayinta na
sarauniyar mafarauta a cikin gabilarsu.
Cikin tsananin bakin zafin nama sarki Lubainu da
wannan jarumar suka juyo a cikin fushi Sai suka
juyo izuwa kan junansu suka ruguntsume da
sabon masifeffen yaki yazamana cewa suna
kaiwa junansu mugayen harehare.
Nan fa karar haduwar takubbansu yacika dajin
gaba daya, motsinsu da hare harensu ya haifar
da tashin kura, kuma ya dugunzuma hankalin duk
wani Abu dayake kusa. Domin hatta yaran sarki
Lubainu Sai suka rinka ja da baya, wani
lokacimma har buya sukeyi a bayan bishiyoyi kar
tsautsayi ya hausu,Dan wata ‘Yar karamar
bishiya ma sarki Lubainu da jarumar Sara daya
sukeyi mata ta fadi kasa,a lokacin da suke
kaucewa harin junansu.
Nanfa dajin gaba daya ya hautsine, tsuntsaye ma
dake kan bishiyoyi babu shiri suka farayin yijira
dole suna sauya sheka.
Wannan tashin hankalin ne gami da karafkakiyar
yakuba na sarki Lubainu da jarumar ne yakai
izuwa kunnen ‘yan uwan jarumar dake can gefe
nesa kadan awani bangare a dajin, inda suke
yada sansani.
Adadin wadannan Ayari yakai na mutum dubu
uku da sittin da biyu, kuma dukkajinsu suna
karkashin wani mutum ne ma’abocin kwarjini da
kamala gami da kira Da SADAUKANTAKA Amma
girma yafara kamashi, domin ya haura shekara
sittin a duniya, Ana kiransa da suna ZAHAR BIN
AUDASI.
Sadauki zahar shine mahaifin waccer yarinyar da
take fafatawa da sarki Lubainu.
Koda sadauki zahar yajuyo karar takuban ‘yarsa
saiya zabura yafito ya fito da sauri daga cikin
tantinsa ya dubi gaba dayan dakarunsa wadanda
suka kasance maza da mata, kuma dukkaninsu
acikin shigar yaki suke irinta mafarauta yace, Ga
Sarauniyarmu can tana gunurzu, kuzo muje mukai
mata dauki tunda bamusan Adadin mutanen da
take yaki dasuba, kunsani cewa ‘yata daga nesa
da sarki Lubainu yaga wannan gagarumar
jarumtaka da jarumar tayi kuma ya kare mata
kallo yaga irin tsananin kyawun da Allah yayi
mata Sai yasake dimaucewa kuma nan take
akaron farko a rayuwarsa yaji yakamu da
tsananin son ‘YA MACE!!
Lokacin da wannan jarumar taga sarki Lubainu ya
kura mata idanu kuma ta kare masa kallo taga
yanayin shigarsa Sai tagane cewa mai mulki ne
Dom haka Sai ta turbine fuska tacigaba da
kallonsa kawai har ya iso daf da ita.
Dazuwansa Sai ya dubeta a fusace ya daka mata
tsawa yace, yake wannan bakuwar mafarauciya
wacece ke har da zaki shigu jejin kasata kiyi
farauta ba tare da izininaba?
Ina sauran ‘yan uwanki suke wadan sukamin
mummunar barna haka kuka kwashe mana duk
Amfanin cikin dazuzzukanmu??
Kisani cewa tunda na kamaki dolene Ku
dawomana da dukkanin abunda kuka kwashe
kokuma Ku biya da rayukanku tunda kun karya
doka.
Hatta wannan damisa da kika kashe yanzu
dolene ki bani ita.
Koda sarki Lubainu yazo nan a zancensa Sai
kyakkyawar jarumar ta kyalkyale da dariya, lokaci
guda kuma ta turbune fuskarta tace, Ai isace
takesawa akarya dokar sarki!
Munan daka gammu babu bangaren da bamuje ba
a duniya munyi FARAUTA, Kuma kasa ko birni ko
Alkaryar da muka zuwa muka nemi izinin wani
Wanda mukashiga yankinsa””.
Koda gama fadin haka Sai jarumar ta sunkuya
tadau wannan damisar ta saba ta kafadarta
taruga inda ‘yan uwanta suke, kawai Sai sarki
Lubainu ya daka tsalle sama dagakan dokinsa ya
shallaketa, sarki Lubainu yana gana Ayyana
hakan a ransa saiyaja da baya yadaina yakar
jarumar kamar zaiyi saran da Amma saiya
shammaci jarumar yaruga da gudu izuwa inda
damisar take.
Koda ganin haka Sai ita jarumar ta falfala da
wannan azabebben gudu nata tabi bayansa,
saigashi har tashi sama takeyi saboda tsananin
gudun, Amma duk da hakan dakyar ta riski sarki
Lubainu sukayi kafada da kafada, ahaka sukaci
gaba da kaiwa junansu naushi domin akai daya
kasa Amma abun yaki yiwuwa.
Koda sukaga saura baifi taku biyarba su isa inda
damisar take.Sai duk su biyun suka daka tsalle
suka kaiwa damisar cafka da Hannu daya.
Bisa rashin sa’a Sai sarki Lubainu ya damki
wuyan damisar, ita kuma Sai ta cafko kafadar
damisar.
Koda kowannensu ya yaja iya karfinsa Sai
damisar ta rabe gida biyu duk su biyun suka fadi
rike da tsagin damisar.
Kawai Sai yaran sarki Lubainu suka farayimusu
tafi sakamakon ganin gagarumar jarumtakar da
sukayi.
A daidai wannan lokaci ne zugar su sadauki
zahar ta karaso wajen a guje bisa dawakai
sukayiwa su sarki Lubainu KAWANYA.
Koda jarumar taga mahaifinta shima yaganta
kwance a kas rike da tsagin damisa kuma Ga jini
a hancinta da bakinta kuma yana diga Sai ya
dubi dakarunsa yamusu inkiya.
Take tadarun suka zaro kibiyoyi suka tana suka
ta6e zasu sakarwa sarki Lubainu da yaransa
harbi, Amma Sai jarumar tayi sauri yace ae
ba’abokin gaba bane, wannan shine sarkin
wannan birni da muke ciki””.
Koda jin haka Sai sadauki zahar ya dubeta a
fusace yace, idan ba abikin gaba ba to menene
yasa ya yakeki harya lalata naman farautarki?””
Koda jin wannan tambaya Sai tayi murmushi
tace, “‘ saboda munyi masa babbar barna mun
kore duk dabbobi da tsuntsayen dake cikin
dazuzzukan birninsa..
Yanada gaskia akan wannan Al’amari duk da
cewa shi daji na Allah ne bana kowa ba..yakai
Abbana abunda nakeso dakai shine, mu biya
wannan sarki duk abunda ya bukata dangane da
wannan barnan da muka masa, Amma ayau
dinnan nakeso mubar yankin kasar nan tasa mu
kara gaba.
Banason muyi yaki da wannan sarkin domin shine
jarumi na farko dana taba ganin iyada jarumtaka
irin taka””.. Koda jin wannan batu Sai mamaki
Yakama sadauki zahar da sauran jama’arsa.
Shi kuwa sarki Lubainu Sai hankalinsa ya dugun
Zuma Ainun bisa jin ayau su jarumar sukeson
subar kasarsa Alhalin ayanzu ma jiyake kamar
bazai iyayin rayuwa ba in baya ganin wannan
kyakkyawar sura tata. Nan take sarki Lubainu
yashiga tunanin dabarar da zaiyi ya hana
wadannan mafarauta barin kasarsa.
Ita kanta jarumar ta gano abinda ke cikin ran
sarki Lubainu domin ta lura da irin kallon da
yakeyimata run farkon haduwarsu kuma itama
jarumtakarsa ya burgeta.
To Amma Sai ta tambayi kanta a cikin zuciyarta
tace,
MEYASA WANNAN SARKI YA YAKENI DA
DUKKANIN KARFINSA DA NUFIN YA HALLAKANI
IDAN HAR WANNAN KALLO DAYAKE YININI NA
KAUNANE? WATA KILA DARAJARSA DA KIMARSA
AWAJEN YARANSA KOKUMA DOMIN YA JARRABI
JARUMTAKARSA AKAN TAWA””..
Shi kuwa sadauki zahar Sai ya sake doban ‘Yar
tasa yace, yake SUHAILAT, Nawa ne adadin kudin
da wannan sarki yakeso mu biyashi bisa wannan
barna da mukayimasa?
Koda jin wannan magana Sai jaruma suhailat ta
dubi sarki Lubainu tace, Ai waka abakin mai ita
tafi dadi, don haka Sai yayi mana bayani da
bakinsa muji.
Koda jin wannan batu Sai sarki Lubainu ya kara
fadawa kogin tunani.
Abu na farko dayayi shine,ya karewa wadannan
mafarauta kallo domin yaga ya Arzikinsu saboda
yasamusu kudi mai yawa wadda baza su iya biya
ba.
Amma Sai wata zuciyar tace dashi, Aisu kudi
basuda kama, kuma bisbisa ganin yadda
wadannan mutane sukeyin wannan gagarumar
farauta, Akwai alamun zasu iya Tara makudan
kudaden da ba’a zato””.
Koda jaruma suhaikat taga sarki Lubainu yayi
shiru Sai ta matso kusa da shi ta katsenmar
tunani tace Malam kana bata mana lokaci mu
mata fiyane ba mazauna ba!
Bamu gaba zama akowane gariba sama da
tsawon kwana bakwai ba Sai a wannan gari
naka””.
Koda jin wannan tambaya Sai sarki Lubainu yayi
murmushi yace, Ai wannan babbar barns da
kukayimin baza Ku iya biyanta da kudi ba domin
ni mawadacine na kudi, harma sunyi mini yawan
da babu abunda zanyi dasu. Idan kunaso Ku
biyani saidai mu shirya wata Gasa ta jarumta
tsakanin zakurkuran mayakanku mutum Ashirin
da nawa, kuma kullum mutum biyu ne kacal
zasuyi wannan gasar.
Abunda ake bukata a gasar kawai shine, akai
mutum kasa ba tare ta an illatashiba, idan
jama’atane suka lashe wannan gasa to dole Ku
zauna a birnina tsawon wadansu kwanaki Ashirin
din kunayimin Aikin bauta a cikin gidan sarautata.
Idan kuma kune muka lashe gasar a cikin kwana
ashirin din to shikenan kun biyani barnar da
kukayinin saikuyi tafiyarku””.
Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar da
jaruma suhailat Sai suka dubi junansu kawai Sai
sukayi shiru suna tunani.
Suma jama’ar tasu Sai suka kama kus kus suna
tattauna Al’amarin a cikin fargaba da damuwa.
Muhadu gobe in Allah yakaimu muji yadda
wannan Al’amari zai kasance
ALLON SIHIRI
Littafi na shida 6
Part G
Koda ganin haka Sai sadauki zahar Yakama
hanjun jaruma suhailat ya jata gefe daya ya
dubeta yace, ni Abunda na lura dashi shine,
wannan sarki bayason tafiyar mu kuma laifin da
muka masa mashine a gabansaba kece
matsalarsa.
Ga dukkan Alamu yafada irin tarkon da sauran
sarakai dayawa suka fada akanki””.
Sa’adda jaruma suhailat taji wannan batu Sai tayi
ajiyar zuciya cikin alamun damuwa tace, yakai
Abbana indai hakane kuwa bamuda wani zabi
Wanda yafi muyi wannan gasa, domin idanma
mukace zamu gudu nida kai ne kadai zamu iya
gudun da barlza acimmana ba, yazamuyi da
sauran jama’armu zamu barsu ne akamasu
Amatsayin bayi? Duk da cewar bamusan irin
jarumtakar dakarunsaba dolene muma a
bangarenmu muma mu ware namu jaruman
wadanda muka yarda dasu kuma dole ne muma
mushiga cikin gasar domin karawa namu jaruman
karfin gwuiwa””.
Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar ya
jinjina kai yace, “” tabbas bamuda wata mafita da
tahuce wannan””.
Koda gama fadin haka Sai sadauki zahar ya
matsa kusa da sarki Lubainu yadubeshi yace, “”
mun yadda zamuyi wannan gasa ta kwana
Ashirin a birninka, Amma bisa shatadi guda!!
Sharadin kuwa shine, cimmu da shammu da
masaukinmu yana hannunka Atsawon wannan
kwanaki dakuma tsaron lafiyarmu dakuma
rayukanmu tunda mu munfi kwarewa rayuwar daji
yanzu kuma kai kanaso muzauna a birninka tare
da jama’arka.
Idan rayuwar daya daga cikinmu ta tabu ko
lafiyarsa to zaka biya diyya mai darajar gaske,
shin ka Amince da wannan sharadin??””.
Lokacin da sarki Lubainu yaji wannan batu Sai
zuciyarsa takamu da farin ciki tayi fari kal, kawai
Sai yadubi sadauki zahar yace, “” Nima na
Amince da duk wannan sharadin naku “”.
Batare da wani bata lokaci ba sarki Lubainu da
dakarunsa shida suka wuce gaba da dakarun su
wannan tawagar su sadauki zahar suka rufa
masa baya aka nufi cikin BIRNIN ISTAMBUL.
Duk bayan kamar dakika goma Sai sarki Lubainu
ya dubi jaruma suhailat.
Koda taga kallon yayi yawa Sai ta dauko wani
shudin rawani ta rufawa kanta yazamana cewa
idanuntane kadai ake gani.
Koda ganin haka Sai sadauki zahar ya bushe da
dariya yace, dakyau ‘yata kinyi maganin ido
domin shi ido gubane!
Ina mai shawartarki da kija ajinki awajen wannan
sarki da dukkan jama’arsa, kuma ki kula da kanki
don inatsaron wadannan mutane suyi wani Abu
Wanda zai cutar da mu””,
Koda jin wannan batu Sai jaruma suhailat tayi
murmushi tace, ” kwantar da hankalinka yakai
Abbana, kayi sani Babu abunda zai samu
dayanmu a wannan gari, lafiya lau zamu gama
abummu acikinsu mutafi”..
Lokacin da sarki Lubainu ya iso gidan sarautar
akaganshi da wannan bakin mafarauta Sai aka
cika da tsananin mamaki,
Dafarko Sai dakarun suka taso danufin su tsare
bakin masarautar domin su azatonsu kama
sarkinsu Akayi, Amma Sai sarki ya musu inkiya
suka koma suka tsaitsaya a inda suke.
Nana take aka bude kofar masarautan take suka
kunnakai ciki.
Da zuwansu Sai akaga sarki Lubainu duk ya rude
yanata haba haba da wadannan bakin mafarauta,
domin da kansa yayi musu jagora izuwa
masaukinsu, kuma masauki mai Daraja yakaisu
inda ba’a saukar kananan mutane, daga manyan
sarakai Sai shahararrun Attajirai.
Nan take sarki Lubainu yabada umarnin
Ashiryawa bakinsa abinci mai Daraja.
Nana da nan kuwa akacika babban falon da aka
kaisu da kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri
birjik! Wadanda ma sunyi musu yawa, baza su iya
karar da su ba, duk da cewa adadinsu yahaura
dubu uku.
Dakin barcin da aka baiwa jaruma suhailat kuwa,
koda matar sarki ce iya abunda za’a shirya mata
Keenan acikin dakin,
Dakin yana hade da makewayi acikinsa. Shikansa
makewayin katone kuma bahon wankansama na
zallan lu’u lu’u ne.
Gadon da ke dakin kuwa Lumsheshene mai tarin
shimfidu masu taushin gaske.
Abinka da wadanda basusan komai ba Sai
rayuwar daji, kuma basu da dakujan kwana Sai
bukkoki da kogunan duwatsu da tanti, duk Sai
suka zama cikakkun ‘YAN KAUYE, don haka Sai
suka kasa Amfani da kayan kyale kyalen cikin
dakinnasu dole aka kawo kuyangi suka koyar
dasu.
Bayan jaruma suhailat taci abinci ta koshi Sai
kuyangi uku su ka kamata suka shigar da ita
kewaye domin suyi mata wanka.
Koda suka kwabe mata kayan jikinta suka yi
mata tum6ur! Sai suka rude suka dimauce
sakamakon kyawun da dirin da Allah yabata
dakuma kyawun da Allah yayiwa fatar jikinta
dakuma laushi, domin ko a TARIHI basu tabajin
An wassafa mace mai irin kyawun jikintaba.
Hakadai kuyangin suka shigar da jaruma suhailat
cikin bahon wankan suka shiga yi mata wanka
hannunsu na kyarma, jikinsu nata makyarkyata
saboda tsananin Al’ajabi.
Bayan Angama yiwa jaruma suhailat wankan aka
shafeta da mai dakuma turare Sai aka je Aka
kwantar da ita bisa wannan lumsheshshen gadon.
Koda taji laushin gadon kuma ta duba kayan
kawan dake cikin dakin Sai fuskarta ta fadada da
murmushi da Annuri gami da kurawa rufin dakin
idanu tana mai cewa acikin ranta.
WAI SHIN YAUSHENE NIDA MAHAIFINA DA
JAMA’ARMU ZAMUSAMU NUTSUWA DA DAULA
IRIN WANNAN?
A IYA RAYUWAR DA NA TASO NA RAYU ACIKIN
DAJI, YAKA MATA ACE YANZU NE ZAN HUTA
NASAMU MIJIN DA ZAN AURA UBAN ‘YA’YANA.
BANIDA BURIN DAYAWUCE IDAN NAYI AURE
NASAMU DA KO ‘YA WACCE ZATA GADONI A
JARUMTAKA DA KYAU, KUMA TACI GABA DA
SHUGABANTAR KABILARMU!””
Koda jaruma suhailat tazo nan a zancen zucinta
Sai hawaye ya zubo mata, saboda bataga ranar
da wannan buri nata zaizo ba saboda
amatsayinta na shugabar kabilarsu kafin abaya
tashugabancin saida tayi rantsuwa akan har
abada bazata taba nisantar jama’arsuba kuma
zata ci gaba da shugabantarsu izuwa tafiye tafiye
donyin farauta akowane bangare na duniya har
izuwa karshen rayuwarta.haka Sai suhailat taci
gaba dayin wannan tunani har bacci yasaceta
bata sani ba.
AL’AMARIN Sarki Lubainu kuwa, tunda yaga
Anbaiwa su suhailat masauki da abinci mai kyau
Sai yatafi izuwa turakarsa cikin tsananin farinciki.
A wannan ranadai saida gaba dayan fadawansa
da hafiman gidan sarautar sukasan cewa lallai
yana cikin farinciki, domin saida halayensa suka
sauya nan take,
Kawai Sai Yakama yiwa mutane kyauta taban
mamaki da bazato, sannan ya ‘yanta bayi tamkar
yasamu waraka daga lalurar da ta addabi
rayuwarsa.
Kai awannan ranadai sarki Lubainu kasa bacci
yayi domin duk sa’inda ya runtse idanunsa domin
yayi baccin saidai yaga fuskar jaruma suhailat na
yi nasa murmushi. Atakaice Sai yadda sarki
Lubainu yaga rana haka yaga dare a wannan
ranar.
Ita kuwa jaruma suhailat baccinta tayi ta more
hadda munshari.
Koda ta farka da safe saitaji zuciyarta na faman
bugawa alamar cewa Akwai wani Abu dake shirin
faruwa marar dadi agareta kokuma Ga jama’arta.
Koda gama aiyana hakan acikin zuciyarta Sai
hankalinta ya zugunzuma ainun.
Bisa wannan daliline ta dauko madubin tsafinta
ta shafashi da hannun hagu tashiga bincike.
Nan take taga duk abunda yafaru Ga sarki
Lubainu agaba dayan rayuwarsa da matsalar da
ta Addabi rayuwar harda baccin da yakasayi
sakamokon kamuwa da sonta da begenta.
Koda ganin wannan Abu Sai nan take taji takamu
da tsananin tausayin sarki Lubainu akaron farko
dataji sonsa yadan digu cikin zuciyarta. Jaruma
suhailat taci gaba da bincike akan rayuwarta da
sarki Lubainu, Aikuwa Sai taga wani babban abin
tashin hankali Wanda indai tana Raye da sarki
Lubainu Sai ya faru.
Ba komai ne wadannan abunba face mugayen
yake yake Wanda za’ayi miliyoyin rayuka da
dukiya dakuma tsananin wahala ta gaban
kwatance.
Koda ganin haka Sai jaruma suhailat ta Aiyana
aranta cewa bazata taba baiwa sarki Lubainu
fuskar da zasuyi soyayya ba. Abunda zatayi
kokarin yi shine, ta tabbatar da cewa itada
jarumansu sun sami nasara acikin wannan gasa
da sarki Lubainu ya shirya.
Bayan jaruma suhailat ta gama yanke wannan
hukunci ne Sai ta mike da sauri taje tayi wanka
da kanta domin wannan karon kuyangin basuzoba
tunda sun koya mata yadda akeyin wankan.
Koda tafito daga kewayenta tashiga dakin barcin
domin tasanya tufafinta na fita farauta Sai tayi
Arba da wasu tufafi masu kyawun gaske irin nasu
na mata visa kan gadon nata wata kuyangan
sarki na tsaye agefe daya.
Koda kuyangar taga jaruma suhailat tashigo
dakin saita zube kasa gabanta tayi gaisuwa
sannan ta dago kanta ta dubeta tace, ya
shugabata sarki ne ya turoni nasa miki wannan
tufafi saboda ya gaiyaceku izuwa fadarsa keda
mahaifinki, koma Akwai manyan bakin sarakuna
da sukazo halattan wani biki da akasabayi a
wannan gari namu arana irinta yau””.
Koda jin wannan batu Sai jaruma tadubi wannan
kuyanga da’alamun mamaki tace, Wane irin biki
ne wannan haka?”
Kuyangar tace, gasa ne na Raye Raye da kade
kade gami da wake wake.
Wanda duk yalashe gasar sarakuna nabashi
kyaututtuka wani ma Sai yasamu sarkin dazai
bashi kwangila ta daukemasa kewa har izuwa
karshen rayuwarsa yana biyanshi Albashi mai
tsoka.” Koda jin wannan batu Sai suhailat takamu
da murna saboda a rayuwarta tanson kallon
abubuwan nishadi irin haka.
Batare da wata matsalaba ta Amince akasanya
mata wannan Riga mai Daraja akayimata kwalliya
ta gani afada.
Koda kuyangar takaita gaban madubi suka tsaya
takalli kanta Sai tacika da tsananin mamaki, da
farko razana tadanyi taja da baga don zato tayi
wata Al’jana ce me kamarta a jikin madubin.
Saida ta shafa hannunta ajikin madubin sannan
ta tabbatar hotonta ne ajikin madubin ba Al’jana
ba. Cikin murmushi suhailat tadubi kuyangar tace,
“Kaini masaukin mahaifina”, Nan take kuyangar
tahuce gaba jaruma suhailat na biye da ita.
MUHADU A LITTAFI NA GABA WATO NA BAKWAI
(7) DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN
KASAITACCEN LABARI.
DAGA MAI DEBE MUKE KEWA A KULLUM A KO
YAUSHE. KING OF ADVENTURE STORY.
ABDUL’AZEZ SANI MADAKIN GINI.
NI NAKU HAR KULLUM KHAMIS IDRIS
MUHAMMAD NAKE CEWA MUGANA A GABA NAN
BADA JIMAWABA INSHA ALLAH.