ALLON SIHIRI Littafi na bakwai 7 A Duk Inda Suka Wuce Dakaru, Bayi, Barori Da Kuyangi Kamar Babu Mai Rai Acikinsu Sbd DuksuYazaunaKamar Gunki Suna Masu Quramusu Idanu, Bakomaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Tsananin Kyawun Jaruma Suhailat, Gashi Kuma Wannan Riga Datasaka Ba Qaramin Kyawu Tayi Mataba, Da Shigarsu Cikin Dakin Sai Suhailat Tasake Cika Da Mamaki, Ba Komaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Mahaifinta Sadauki Zahar Zaune Akan Kujera Cikin Tufafi Na Alfarma Tamkar Wani BASARAKE, Koda Sadauki Zahar Ya Hango Suhailat Acikin Wannan Kyakyawan Shiga Wace Taqara Fito Da Tsananin Kyawunta Da Kwarjininta Sai Ya Miqe Tsaye Cikin Matuqar Farin Ciki Ya Tareta Suka Rungume Juna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata Ya Dubeta Cikin Alamu Matuqar Damuwa Yace, Yake ‘yata Shin Kinada Lbrn Cewa Inda Zamuje Yanzu Taro Ne Na Sarakai Da Manyan Masu Fada”aji, Jaruma Suhailat Ta Gyada Kai Tace Nasani Ya Abbana, Kuma Ka Kwantar Da Hankalinka Babu Wani Sarki Ko Attajiri Wanda Ya Isa Ya Mallakeni Da Qarfin Arziqinsa, Na San Wannan Ce Damuwarka, Kodajin Hak Sai Sadauki Zahar Yayi Murmushi Yace Wannan Gsky Ne Yake ‘yata, To Amma Wane Mataki Zaki Dauka Don Kaucewa Hakan? Kisani Cewa Dazarar Sarakan Sun Ganki Zasu Dimauce Kuma Sufara Tunanin Hanyoyin Dazasubi Su Mallakeki Ta Kowanni Hali, Jaruma Suhailat Tasake Yin Murmushi Akaro Na2 Tace Kada Kadamu Yakai Abbana Domin Tuni Nadauki Mataki Akan Hakan, Kai Dai Kawai Kazuba Ido Kaga Abinda Zaifaru, Gama Fadin Hakan Keda Wuya Saiga Wani Hadimi Ya Shigo Cikin Turakar Da Sauri Ya Dubesu Yace, Sarkine Yaturoni Nayi Muku Jagora Izuwa Fada, Batare Da Bata Lkc Ba Jarumu Suhailat Da Sadauki Zahar Sukabi Bayan Wannan Hadimi Suka Nufi Fadar, Filin Fadar Yacika Ya Batse Da Bil’adama Duk Inda Mutum Yahanga Babu Abinda Zaigani Face Kawunan Mutane Rututu! An Kange Tsakiyar Filin Dawata Katangar Qarfe, Makada, Mawaqa Da ‘yan Rawa Sunjeru A Gefe Sahu Sahu Acan Sama Bisa Wani Gini Mai Tsawo Wanda Ke Dauke Da Matattakala Sarakai Ne A Zazzaune An Shirya Kayan Ciye Ciye Da Shaye Shaye Agabansu, Tuni A Wannan Lkc Anfara Gabatarda Sauran Jama’a Kuwa Sai Idanunsu Sakakafe Bakunansu Suka Wangame Sbd Kallon Kyakkyawar Surar Dake Wucewa Ta Cikin Tsakiyar Fadar Wato JARUMA SUHAILAT Tarada Muqarrabanta Nan Take Sarki Lubainu Da Dakkannin Sarakuna Dake Kewaye Dashi Suka Mimmiqe Tsaye Dao Tarbar Jaruma Suhailat Da Tawagarta, Sudai Sarakan Sunyi Zaton Cewa Suhailat Wata Shahararriyar Sarauniyace Daga Wani Bangare Na Duniya, Donhaka Basusan Sa’adda Sukakama Risinawa Ba A Gareta Suna Gaisheta, Shikansa Sadauki Zahar Anzata Cewa Sarkine Sbd Kwarjininsa Da Yanayin Shigar Dayayi Irinta Manyan Sarakai Ce, Cikin Hanzari Sarki Lubainu Yatarbi Jaruma Suhailat Da Mahaifin Sadauki Zahar Yarakasu Harzuwa Inda Aka Tanadarmusu Suka Zauna Sannan Shima Yakoma Gaban Karagarsa Yatsaya Ya Fuskanci Jama’a, Nanfa Fadar Tayi Tsit! Kamar Mutuwa Tagifta Aka Zubawa Sarki Lubainu Idanu Ana Sauraronsa Aji Bayanin Dazaiyi, Sarki Lubainu Yayi Gyaran Murya Sannan Yace Yaku Manyan Baqi Da Dukkanin Jama’a Dake Wannan Wurin, Ina Yimuku Barka Daxuwa Wannan Babban Taro Wanda Mukasabayi Aduk Shekara Awannan Birninamu Mai Albarka Na Istambul, Bayan Haka Inamaiyiwa Jama’a Busharada Cewa Wannan Tarona Banatarone Nadabam,kumanamusamman Wandabamutabayin Kamarsaba Sabodawannankaron Munada Wadansu Bakinamusamman Masu Dumbinbaiwada Darajakamar Yaddakukaga Shigowarsu Akarshe Izuwacikinwannantaro.Wannanmanyanbaki Sunzoda Zakwakuran Sadaukai Kuma Jarumaihar Gudaashirin Wadandazasu Yigasar Karfindantseda Dakarunbirnina,inamaiyiwa Jama,a Albishirdacewa Nimainacikin Jarumandazasuyi Wannan Gasarjarumtaka;kodasarki Lubainuyazo Nan Azancensa,saimutanesukarude.Dashewa,gami-datafi.Sabodasun,san.Irin Tsananin JARUMTAKARSA Da Sadaukantakarsa Don Hakasuna Son Kallon GUMUZUR, Al’amarin Jaruma Sahailat Da Mahaifinta Sadauki Zahar Kuwa Koda Sukaji Cewar Sarki Lubainu Mazai Shiga Wannan GASAR JARUMTAKA, Daza Ayi Sai Sukakamu Datsananin Mamaki Kuma Tsoro Yadarsu Acikin Zukatansu Domin Basu Taba Zaton Cewa Hakan Zatafaruba, Cikin Kaduwa Jaruma Suhailat Tadubi Zahar Cikin Qaramar Murya A Daidai Kunnensa Tace Yakai Abbana Yanzu Meye Abinyi? Idan Harmuka Bari Saski Lubainu Yashiga Wannan Gasa Muza A Cinye, Sadauki Zahar Yanumfasa Yace Maganarki Dutsece Donhaka Ina Ganin Cewa Nima Zanshiga Gasar Sbd Natareshi, Jaruma Suhailat Ta Girgiza Kai Tace A’a Bazaka Tareshiba Nice Dai Dai Dashi Domin KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA Yadda Yake Taqama Da Quruciya Daqarfi Nima Haka Nake Taqamadasu Kaikuwa Shekarunka Sunfara Nisa, Zai Iya Amfani Da Wannan Dama Yayi Saurin Galabaitar Dakai Donhaka Kawai Kabarni Dashi, Sarki Lubainu Yaci Gabada Bayani Yana Mecewa Yaku Jama’a Yanzu Batare Da Bata Lkb Ba Ina Kira Ga Wadannan Manyan Baqi Namu Dasu Fitoda Jaruman Gasarsu Guda Ashirin Su Gabatardasu A Tsakiyar Filh Sannan Muma Mu Gabatar Da Namu, Bayan Nan Za’ayi GASAR JARUMTAKA Guda Daya Jal! Awannan Rana Sannan A Cigaba Da GASAR NISHADI Koda Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yakoma Kan KARAGAR MULKINSA Yazauna. Muhadu gobe in Allah yakaimu. Naku khamis idris Muhammad [1/23, 00:53] +234 808 677 7945: e ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part B A Sannan Ne Sadauki Zahar Da Jaruma Suhailat Sukamiqe Tsaye Suka Kira Jama’arsu Suka Koma Gefe Daya Acikin Filin Fadar Sunaware Sadaukan Dazasuyi Wannan Gasa, Bayan Sungama Ware JARUMAI Goma Sha Takwas Sai Jaruma Suhailat Ta Sanya DAMARA Akan Rigar Dake Jikinta Takawo Takobi Ta Saqaleta A Kubin Cinyarta Ta Dam, Sannan Tariqe Garkuwa Ta Shiga Cikin Jaruman Gasar Ta Tsaya, Nan Take Shima Sarki Lubainu Yacire Alkyabbarsa Ya Sanya Damara Ya Dauko Tasa Takobin Da Garkuwa Sannan Yashiga Cikin Jaruman Gasar Yazamo Cikon Na Ashirin, Tuni A Wannan Lkc Sarakai Da Ragowar Jama’a Yan Kallo Sun Cika Da Tsananin Mamaki, Bakomai Ne Yabaiwa Mutane Mamaki Ba Face Ganin Yadda Wannan Mace Mai Tsananin Kyau Tashiga Cikin Wannan GASA TA JARUMTAKA Dakuma Dalilin Dayasa Shima Sarki Lubainu Yashiga Gasar Bayan Angama Ware Jaruman Gasar An Kawosu Tsakiyar Fili An Tsayar Domin A Fitarwa Da Kowannensu Abokin Gwaminsa Sai Zuciyar Jaruma Suhailat Tabuga Da Qarfin Gaske Bakomai Ne Ya Haddasa Hakan Ba Face Ganin Yadda Gaba Dayan Mutanen khamisidrismuhammad: Batu Sai Jama’a Suka Rude Da Shewa Gamida Tafi Sbd Basirar Da Aka Shirya A Wannan Gasa Tayi Ma’ana Sosai Nan Take Jaruman Gasar Su Ashirin A Bangaren Baqi Suka Balayi Daya Rak! Suka Rinqa Zuwa Gaban Wannan Akushi Sai Dai Kawai Abude Musu Akushin SuMuhammannu Su Dauko Dutse Take Sai A Duba Dutsen A Ga Sunan Wanda Ke Jiki A Bayyan A Matsayin Abokin Gwamin Wanda Ya Dauko Dutsen, Wani Ikon Allah Jaruma Suhailat Ce Ta Qarshe A Layin Kuma Sauran Jaruman Nasu Guda Goma Sha Tara Babu Wanda Ya Dauko Dutsen Mai Sunan Sarki Lubainu, Koda Akaga Jarumi Nasha Taran Bai Dauko Sunan Sarki Lubainu Ba Sai Filin Fadar Yarude Dashewa Gamida Kuwa Sbd Angane Cewa Lallai Sarki Lubainu Ne Abokin Gwamin Jaruma Suhailat Aikuwa Tana Dauko Dutsen Ana Dubawa Aka Ambaci Sunansa Koda Jaruma Suhailat Ta Waiga Inda Sarki Lubainu Yake Suka Hada Idanu Saita Ga Yayi Mata Murmushi Kuma Fuskarsa Acike Take Da Annuri Gami Da Farin Ciki Bisa Mamaki Sai Sarki Yaga Jaruma Suhailat Ta Maida Masa Martanin Murmushi, Al’amarin Daya Qara Jefashi Cikin Matsanaicin Farinciki Ke Nan Yaji Kamar Ya Fashe Da Kukan Murna. Su Kuwa Sauran Jama’a ‘yan Kallo Babban Bakin Cikinsu Shi Ne, Sarki Lubainu Da Jaruma Suhailat Ba Za Su Yi Wasansu Ba Sai a ranar karshe, amma sai aka ci burin wannan rana. Nan take aka buga gangar fara gasa, aka kirawo jarumi na farko daga cikin bakin jarumai mai suna FAIRUZ. A can bangaren jaruman Birnin Istambul Kuwa, Sai aka kirawo wani jarumi mai suna SAIHUF, Jaruman biyu suka fito tsakiyar fili suka fuskanci juna. Koda ‘yan kallo suka dubi fairuz da saihuf sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganin wani abin al’ajabi da aka gani a tare da su. Jaruman biyu dukkaninsu sun kasance samari matasa wadanda shekarunsa ba za su haura ashirin da biyar ba. Tsawonsu da kaurin jikinsu, kai! har da kamannin fuskokinsu ma ya kusan zuwa iri daya sak! kai kace hassan Matsanaicin F arinciki Ke Nan Yaji Kamar Ya Fashe Da Kukan Murna. Su Kuwa Sauran Jama’a ‘yan Kallo Babban Bakin Cikinsu Shi Ne, Sarki Lubainu Da Jaruma Suhailat Ba Za Su Yi Wasansu Ba Sai a ranar karshe, amma sai aka ci burin wannan rana. Nan take aka buga gangar fara gasa, aka kirawo jarumi na farko daga cikin bakin jarumai mai suna FAIRUZ. A can bangaren jaruman Birnin Istambul Kuwa, Sai aka kirawo wani jarumi mai suna SAIHUF, Jaruman biyu suka fito tsakiyar fili suka fuskanci juna. Koda ‘yan kallo suka dubi fairuz da saihuf sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganin wani abin al’ajabi da aka gani a tare da su. Jaruman biyu dukkaninsu sun kasance samari matasa wadanda shekarunsa ba za su haura ashirin da biyar ba. Tsawonsu da kaurin jikinsu, kai! har da kamannin fuskokinsu ma ya kusan zuwa iri daya sak! kai kace hassan da hussain Ne, Sukansu Jaruman Biyu Abin Yayi Matuqar Basu Mamaki, Basu San Sa’adda Suka Qurawa Junansu Idanu Ba Sunayin Murmushi, Ana Buga Gangar Fara Gasar Kuma Maimakon Sufara Dazare Makamansu Sai Suka Miqawa Juna Hannu Suka Gaisa Al’amarin Da Ya Burge ‘yan Kallo Kenan Aka Kama Yi Musu Tafi Gami Da Jinjina Bayan Fairuz Da Saihuf Sun Gaisa Sai Suka Saki Hannun Juna Sukaja Da Baya Taku Biyar Biyar Sannan Kowannensu Yazare Takobinsa Sukayi Kallon Kallo Na Tsawon Yan Daqiqu Kawai Sai Suka Rugo Izuwa Ga Juna Suka Kacame Da Azabbaben Yaqi Mai Matuqar Ban Al’ajabi Cikin Gagarumar Jarumtaka SARA DA SUKA Ba Sassauci Amma Sai Gashi Kowannensu Na Iya Kare Duk Hare Haren Da Dan Uwansa Kekai Masa, Babu Abinda Yaqara Daurewa Mutane Kai Face Ganin Yadda Yanayin Salon Yaqi Fairuz Da Saihuf Yazo Iri Daya Sak! Tamkar Wanda Ya Koya Musu Yaqi Mutum Daya Ne, Sai Da Saihuf Da Fairuz Suka Shafe Kusan Daqiqa Dari Hudu Da Tamanin Sunayin Azababben Yaqi Kuma Kowannensu Yanayin Yaqin Ne Da Dukkan Qarfinsa Dakuma Niyyar Kai Abokin Gwaminsa Qas Amma Sai Hakan Ta Gagara, Babu Shirisuka Jada Baya Suka Tsaya Suna Haki Sbd Tsananin Gajiya A Lbcn Da Kowannensu Yayi Sharkaf Da Gume, Kawai Saisuka Ji Anbuga Ganga Alamar Cewar Su Ajiye Makamansu Suyi Gumurzu Da Hannu Ai Kuwa Sai Kowannensu Ya Gyara Tsayuwarsa Suna Masu Dunqule Hannayensu, Koda Aka Aka Sake Buga Ganga Sai Suka Rugo Da Gudu Suka Sake Kacamema Da Sabon Azababben Yaqi Yazamana Cewa Suna Kaiwa Juna Naushi Da Bugu Hannu Daqafa Ba Sassauci, Kowannesu Na Karewa Iya Qoqarinsa Gami Damaida Martani, Wannan Karon Saida Fairuz Da Saihuf Suka Shafe Rabin Sa’a Cif! Suna Wannan Gumurzu Amma Dayansu Yakasa Kai Daya Qasa Kuma Sun Kasa Yiwa Juna Illah, Koda Ganin Haka Sai Suka Jada Baya A Karo Nabiyu Suka Yi Cirko Cirko Suna Kallon Junansu Kowannensu Yakama Yin Tunani Na Qarshe Akan Yadda Zai Sami Nasara Akan Dan Uwansa, Bayan Shudewar ‘yan Daqiqu Kadan Sai Suka Rugo Dagudu Izuwa Kan Juna, Koda Yarage Saura Taku Hudu Kacal Su Hadu Sai Kowannensu Yadaka Tsalle Sama, Aikuwa Suna Haduwa A Saman Sai Suka Doki Qirazansu Da Qafafunsu Take Duk Su Biyun Suka Fado Qasatim Suka Bugu Akan Qasa Da Gadon Bayansu Sukayi RAGAS Nanfa Filin Wasan Yarude Da Shewa Aka Kama Yimusu Jinjina Bisa Ganin Yadda Kowannensu Yayi Bajinta, Koda Saihuf Yamiqe Tsaye Sai Yaje Da Sauri Inda Fairuz Ke Zaune Yamiqa Masa Hannu Ya Tasheshi Tsaye Suka Dubi Juna Cikin Murmushi Yace Ashe Akwai Mai Kamata A Komai A Duniya? Kodajin Wannan Tambaya Sai Fairuz Yace, Nima Nayi Matuqar Mamaki Da Ganinka Yakai Wannan Sabon Aboki Nawa Kodajin Haka Sai Saihuf Ya Rungume Fairuz Yace Ina Godiya Ga Allah Da Yabani Aboki Na Farko A Rayuwata Wanda Yadace Dani, Ina Gayyatar Izuwa Gidanmu Yanzu Domin Muje Muci Abinci Tare, Kuma Muyi Hira Mu More Kodajin Wannan Batu Sai Fairuz Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Na Saihuf Yadubeshi Cikin Murmushi Yace Nakarbi Wannan Gayyata Taka Amma Kuma Shugabata, Dajin Wannan Batu Sai Saihuf Yadubi Fairuz Yace Yanzu Kana Nufin Kace Wannan Kyakkyawar Budurwa Yar Uwarka Cekuma Itace Shugabarku? Fairuz Yayi Murmushi Yace Wannan Gsky Ne Yar Khamis Idris Muhammad [1/23, 00:53] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi takes 8 Part D Khamis Idris Anan Cikin Gidaan Sarautar Kuwa Zamu Qara Matakan Tsaro Ninkin Nada, Duk Wanda Ya Kasance Baqone Kuma Bashida Wata Alaqa Da Cikin Gidan Sarautar Nan Baza A Barshi Yashigaba, Kaiko Ganinsa Akayi Yana Kai Kawo A Qofar Gidan Sarautar Za A Kamashi A Bincikeshi, In Bashida Gsky Akulleshi A Kurkuku Ko Kuma Akaishi Kotu Ayanke Masa Hukuncin Daya Dace Dasu, Nikaina Yanzu Zan Kasance Acikin Zakwaquran Dakarun Dakaru Hudun Daza A Zaba Wadanda Zasu Jagoranci Rundunoni Hudu Ta Mayaqa Izuwa Iyakokin Qasarmu Hudu, Koda Sarki Zairuf Yazonan A Zancensa Sai Kowa Yakamu Da Tsananin Mamaki Bisajin Cewa Sarki Zairuf Zai Bar Kan Karagar Mulkinsa Yabar Fada Yatafi Daji Domin Kare Qasarsa Da Jama’arsa, Nan Take Sarki Zairuf Ya Sallami Dukkan Mayaqan Bisa Yarjejeniyar Sun Amince Da Shawarar Dayakawo, Kowannensa Yatafi Cikin Nutsuwa Da Shawarar Da Sarki Zairuf Yakawo, Amma Banda Sadauki Ramazan, Domin Shiya Tafi Gidane Cikin Tsananin Baqin Ciki Da Tashin Hankali, Badon Komai Ba Sai Sbd Fiyeda Shekara Ashirin Baya Yan Qullace Da Sarki Da Sarki Lubainu Bisa Wani Hukunci Da Aka Yankewa Mahaifiyarsa Bisa Laifi Qarya Dokar Fatauci, A Lkcn Da Al’amarin Yafaru Sarki Lubainu Yana Da Kwana Shida Ne Kacal! Akan Karagar Mulki, Kuma Aranar Ne Sarki Lubainu Yakafa Sabbin Dokokinsa, Dokar Data Shafi Mahaifiyar Sadauki Ramazan Kuwa Itace, Ba A Yarda Bafatake Yakwashi Kayan Abincin Daya Haura Buhu Arba’in Baya Fita Dasu Izuwa Wata Qasar Sbd A Wannan Lkc Masu Hasashe Sun Gano Cewa Za’a Yi Fari A Shekarar, Aranar Da Aka Qafa Wannan Doka Neda Tsawon Rabin Sa’a Guda Kacal Aka Kama Mahaifiyar Sarkin Yaqi Ramazan Tafitar Da Keken Doki Shida Na Kayan Abinci A Sirrance Domin Takaisu Can Wani Gari Inda Ake Samun Kazamar Riba, Kayan Abincin Sun Kai Kusan Buhu Dari Biyu Da Arba’in Koda Aka Kama Masu Dauke Da Kayan Aka Matsasu Sai Suka Fadi Mai Kayan, Nan Take Sarki Lubainu Yatura Aka Kamo Babar Sarkin Yaqi Ramazan Aka Kaita Kurkuku Aka Kulle, Bayan Kwana Uku Da Faruwar Haka Sai Sarkin Qaqi Ramazan Yazo Fada Yafadi Gaban Sarki Lubainu Yaroqi Alfarmar Ayiwa Mahaifiyarsa Afuwa A Saketa, Kuma Abata Dukiyarta, Koda Sarki Lubainu Yaji Buqatar Sadauki Ramazan Sai Ransa Yabaci Ya Dubeshi Afusace Yace, Yakai Sarkin Yaqi Kayi Sani Cewa Duk Sarkin Dayake Son Yayi Mulki Na Adalci Dole Ne Yafara Nuna Misali Akansa Ko Zuri’arsa Kona Jikinsa, Idan Har Muka Yiwa Mahaifiyarka Afuwa Munbai Wa Sauran Mutane Irinta Qofar Aikata Irin Laifin Data Aikata, Kodajin Wannan Batu Sai Hankalin Sarki Yaqi Ramazan Ya Dugunzuma Ainun, Yazube Qasa Wanwar A Lkcn Da Idanunsa Suka Cikoda Kwallah Kamar Zai Yiwa Sarki Lubainu Sujjada Yace, Ya Shugabana Mahaifiyata Mace Ce Mai Tsananin Son Dukiya, Idan Harka Rabata Da Wannan Hajah Tata Zata Iya Hadiyar Zaciya Ta Mutu! Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Lubainu Yamiqe Tsaye Daga Kan Karagar Mulkinsa Yajuyawa Sarki Yaqi Ramazan Baya Sannan Yace, Na Rantse Da Darajar Abin Bautarmu Ko Uwata Tace Ta Aikata Wannan Laifi In Dai Tana Raye A Doron Kasa Ba Zan Yi Mata Afuwa Ba Lallai Dole Ne A Kwace Wannan Dukiya Ta Mahaifiyarka Kuma Dole Ne Tayi Zaman Kurkuku Na Tsawon Wata Shida! Koda Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yajuya Yafice Daga Cikin Fadar Gaba Daya Yabar Sarki Yaqi Ramazan Tsugunne Aqasa Cikin Tsananin Baqin Ciki Yana Mai Zubar Da Hawaye, Kamar Yadda Sarki Lubainu Yafada Haka Al’amarin Ya Kasance, Wato Saida Aka Kwace Dukiyar Mahaifiyar Sarkin Yaqi Ramazan Gaba Daya, Kuma Aka Yanke Mata Hukuncin Zaman Wata Shida A Gidan Yari, Kodajin Irin Wannan Hukunci Da Aka Yanke Mata, Nan Take Ta Hadiyi Zuciya Tazube Qasa Matacciya, A Wannan Rana Sarkin Yayi Kuka Kamar Ransa Yafita, Domin Har Dare Yaraba Yana Tsugunne Agaban Kabarin Mahaifiyar Tasa Yana Kuka, Saida Yadawo Cikin Hayyacinsa Sannan Yaqurawa Kabarin Idanu A Lkc Da Fuskarsa Ta Murtuke Izuwa Tsananin Fishi Dabaqin Ciki Mara Misaltuwa Yace, Yake Ummina Na Rantse Da Darajar Jininki Dake Cikin Nawa Bazan Taba Yafewa Sarki Lubainu Ba, Lallai Komai Dadewa Sai Na Dauki Fansar Ranki Akansa, Saina Rushe Daular Mulkinsa Na Jefashi Cikin Mugun Baqin Ciki Makamancin Wanda Ya Jefani Daga Wannan Rana Sarkin Yagi Ramazan Ya Cigaba Da Qullatar Sarki Lubainu Acikin Ransa Yana Tunanin Hanyoyin Dazaibi Ya Dauki Fansa Akansa, Amma Har Akazo Wannan Lkc Da Sarki Lubainu Yakamu Da Wannan Cuta Bai Samu Mafitaba, Koda Yaga Sarki Lubainu Yakwanta Ciwo Sai Farinciki Ya Lullubeshi Yaga Cewa Lallai Yasami Babbar Damar Dazai Dauki Fansarsa, Kawai Sai Yamanta Da Batun Amanar Dake Tsakanin Iyayensa Da Gidan Sarki, Tunda Dai Sarkin Yajuya Masa Baya Yaqi Yi Masa Alfarma, Nan Take Sarki Yaqi Ramazan Ya Fadada Tunanin Sakan Yadda Haqqansa Zai Cimma Ruwa Domin Yakawar Da Gwamnitin Sarki Lubainu, Bisa Wannan Dalili Ne Yakawo Wannan Gurguwar Shawara Afada Ta Cewar A Aika Da Yan Leqen Asiri Izuwa Ga Iyakokin Qasar Maimakon A Aika Da Dakarun Yaqi, A Zatonsa Sarki Sabon Sarki Zairuf Bashi Da Basirar Gano Illar Yin Hakan, Sbd Hakane Ma Lkcn Dayaji Sarki Zairuf Yakawo Nasa Shawarwarin Masu Matuqar Muhimmanci Da Inganci Sai Zuciyarsa Takadu Matuqa Yakamu Da Tsananin Mamaki Harma Yafara Tunanin Cewa Lallai Wannan Tunani Da Basira Ba Daga Zairuf Bane Shi Kadai, Kodai Sarki Lubainu Ne Yatsara Masa Wannan Dabara Ko Kuma Jaruma Suhailat, Domin Sune Kadai Suke Da Irin Wannan Kwarewa Tayaqi Gami Da Sanin Tuggu Damakircin Samun Nasara, Lkcn Da Sarkin Yaqi Ramazan Yatafi Izuwa Gidansa Bayan An Tashi Daga Fada Sai Yawuce Izuwa Can Wani Gida Nasa Dake Can Bayan Gari Inda Yake Tafiyar Da Harkokinsa Na Sirri, Amma Bai Wuce Kai Tsaye Ba Izuwa Gidan Sai Daya Rinqa Zagaye Yana Yin Kamar Wasu Wuraren Zai Je Yarinqa Bin Hanyoyi Kala Kala Don Kada Ya Kasance Wani Yalabe Yana Biye Dashi Bai Saniba, Duk Sa’adda Sarkin Yaqi Ramazan Yayi Yar Doguwar Tafiya Sai Yai Wuf Yafada Cikin Wata Duhuwar Shida Dokinsa Yabuya Yana Leqen Kan Hanya Kozai Gawani Dan Leqen Asiri Yana Binsa, Hakadai Ya Cigaba Da Tafiya Har Sai Daya Tabbatar Dacewa Babu Mai Binsa Sannan Ya Cigaba Da Tafiyarsa Cikin Kwanciyar Hankali, Har Ya Isa Wannan Gida Nasa Na Sirri Wanda Bashida Maqofci Akusa, Da Isarsa Sai Wadansu Dakaru Guda Hudu Masu Tsaron Gidan Suka Rugo Suka Taryeshi Suna Yimasa Barka Dazuwa Suka Kaamamasa Dokin Yasauqa, Sannan Yashige Cikin Gidan, Shidai Wannan Gida Yaqawatu Ainun Daga Cikinsa Domin Mutum Nashigarsa Zai San Cewa Yashigo Cikin Gidan Mashahurin Attajiri, Masana Damasu Bincike Sun Tabbatar Dacewa Indai Ba Masarautar Birnin Istambul Ba Babu Zuri’ar Wacce Tafisu Sarkin Yaqi Ramazan Qarfin Arziqi Dakudi Acikin Gaba Dayan Birnin Istambul Don Haka Mahaifinsa Sarki Yaqi Ramazan Yamutu Yabar Dukiya Mai Dumbin Yawa Hakama Mahaifiyarsa Sbd Tuntana Matashiya Mahaifinta Daya Kasance Gagarumin Attajiri Yafara Tafiya Da Ita Yawon Fatauci Zuwa Qasashen Duniya Tareda Haja Mai Dumbin Yawa, Inda Itama Idanunta Suka Bude Sosai, Aqarshe Ma Lkcn Daya Mutu Tagaji Dunbin Dukiya Maitarin Yawa, Yawan Da Ita Kanta Batasan Adadintaba, Kuma Ta Cigaba Da Gudanar Da Harkokinta Na Fatauci Ta Tara Yara Da Mayaqa A Sassa Sassa Daban Daban Na Duniya, Takai Cewa Tadaina Gudanar Da Fataucinta Da Mutane Gama Gari Saidai Manyan Sarakuna Da Manyan Attajiran Dasuka Shahara Aduniya Wajen Dukiya Da Dunbin Kadarori Haka Itama Mahaifiyar Sarkin Yaqi Ta Cigaba Da Tara Dumbin Dukiya Hartayi Aure Ta Haifi Sarkin Yaqi Ramazan Wanda Ya Kasance Shine Danta Itama Guda Daya Tal! Saidai Wani Abin Mamaki Kwata Kwata Mahaifiyarsa Ta Hanashi Yakoyi Harkar Kasuwanci, Maimakon Hakan Sai Ta Bayar Dashi Gawani Tsohon Sarki Yaqin Abinin Don Ya Horar Dashi Yaqi, Arana Ta Farko Da Ramazan Ya Halarci Horon Yaqin, Yayi Matuqar Shan Wahala Yadawo Gida Yana Kuka, Yana Shiga Turakar Mahaifiyarsa Yasameta Tana Zaune Tanacin Inibi Ga Bayi Nan Suna Tayi Mata H [1/23, 00:54] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part E Lokacin da sarki Lubainu Yadauki Tambulan Na Ruwa Inibi Yazuba Acikin Kofin Zinaren Yakama Sha, Itakuwa Jaruma Suhailat Sai Tajuya Tatafi Masauqinta Zuciyarta Cike Da Saqe Saqe Gamida Wasi Wasi, Tana Mai Tambayar Kanta Acikin Zuciyarta, Shin Wani Irin Matakin Tsaro Kuma Sarki Lubainu Zai Dauka Akaina Da Jama’ata Alhalin Zamu Iya Baiwa Kanmu Kariya Daga Kowanne Irin Hari Daza’a Kawo Mana? Kuma Ai Babu ‘yan Fashi Ko ‘yan Harin Sumame Acikin Dajin Dake Kewayen Birninsa Ko Cikin Birnin Bare Yaji Tsoro Ko Za’a Kawo Mana Harin MAMAYAR BAZATO! Hakadai Jaruma Suhailat Taci Gabaga Da Wannan Tunani Har Ta Isa Dakinta Ta Kwanta Akan Gado, Kwanciyarta Kedawuya Sai Barci Ya Saceta Sbd Har A Sannan Maganin Barci Da Likita Ya Shayar Da Ita Bai Gama Sakintaba, Kashe Garikuwa Da Farkon Yammaci Jaruma Suhailat Tayi Shirin Fita Farauta Daji, Amma Sataqi Sanarda Mahaifinta Sadauki Zahar, Shikansa Sarki Lubainu Din Bata Sake Sanar Dashiba, Kawai Saita Debi Zakwaquran Dakaru Guda Huhu Kacal Daga Cikin Jama’arta Suka Ficn Daga Cikin Birnin Istambul Dayake Jaruma Suhailat Tasan Cewa Idan Ja Baiyana Kanta Fili Mutane Ne Zasuta Binta Suna Kallonta Sbd Kyawunta Saitayi Bad Dakama Tayi Shigar Maza Aka Nada Mata Rawani Aka Kumayi Ma Gemu Da Gashin Baki, Maimakon Suyi Shigar Mafarauta Sai Sukayi Shigar Fatake, Tundaga Nesa Dakarun Sumame Da Sarki Bauzur Ya Baiwa Kwangilar Sato Jaruma Suhailat Suka Hango Matane Biyar Sun Fito Daga Cikin Birnin Istambul Acikin Shigar Fatake Sai Suka Fito Daga Inda Suke Boye Suka Musu Qawanya, Sudai Wadannan Dakarun Sumame A Cikin Shigar Baqaqen Kaya Suke Kuma Sun Rufe Fuskokinsu Da Baqin Rawani Idanunsu Kadai Akegani Kuma Suna Dauke Da Takubba, Wuqaqe Da Kwari Da Bakag Kuma Adadinsu Yafi Dubu, Kawai Sai Shugaban Dakarun Sumamen Wani Garjejen Qato Mai Qirar Sadauki Tamkar Zanashi Akayi, Ya Dubi Su Jaruma Suhailat Yadaka Musu Tsawa Yace Kukuma Suwaye, Daga In Zuwa Ina? Kodajin Wannan Tambaya Sairan Jaruma Suhailat Yabaci Taga Cewa Ai Wannan Tambaya Ce Ma Tarainin Wayo! Har Tabudi Baki Zata Bashi Amsa, Amma Saita Tuna Cewa Tanayin Magana Zata Tonawa Kanta Asiri Aji Muryarta Agane Cewa Ita Macece, Don Haka Sai Tayi Shiru, Take Daya Daga Cikin Dakarun Nata Yadubi Shugabau Dakarun Sumamen Yace, Mu Fatakene Daga Birnin Hasur, Kuma Mungama Cin Kasuwane Acikin Birnin Istambul, Yanzu Muna Kan Hanyarmu Ta Komawa Birninmu, Kodajin Wannan Batu Sai Shugaban Dakarun Sumamen Yabushe Da Dariya Lkc Guda Kuma Ya Turbune Fuskarsa Yasake Daka Musu Tsawa A Karo Na Biyu Yace, Yaku Wadannan Qananan Kwari Kadaku Maishemu Sakarkaru Ku Raina Mana Hankali, A Inakuka Taba Ganin Fatake Babu Hajah Kuma Babu Kudin Dasuka Samo Na Ciniki, Kun Cika Fuskokinku Da Tarin Gemun Banza Kamar Wadansu Bokaye, To Kusani Cema Muba Barayi Bane, Domin Munsani Cewa Ba Ayin Sata Anan Birnin Istambul, Muna Neman Wata Mace Ne Guda Daya Wai Ita Jaruma Suhailat! Ta Tunda Yanzu Daga Cikin Birnin Kuke Kokuma Yanzu Nan Takobina Tasha Jinanku, Kodajin Wannan Batu Sai Dakarun Jaruma Suhailat Suka Dubi Junansu Suk Dariya Sbd Sun R Kwatsam! Sai Jaruma Suhailat Taga An Harbo Wadansu Qananan Allurori Sun Tsire Dakarun Nata Shida Acikin Wuyansu Sun Zube Qasa Matattu, Cikin Tsananin Fishi Da Mugun Baqin Zafin Nama Jaruma Suhailat Tadaka Tsalle Sama Daga Kan Dokinta Tana Mai Zare Takobinta Tayi Shawagi Akan Dakarun Sumamen, Kafin Taduro Qasa Tasare Kawunan Mutum Arba’in Sai Ga Jini Na Tsiri Ta Cikin Dungulmin Wuyansu, Koda Ganin Haka Sai Dakarun Sumamen Suka Taso Mata Gaba Dayansu Suka Afka Mata Da Yaqi, Nanfa Jaruma Suhailat Tarinqa Ragargazar Dakarun Sumamen Tamkar Tana Sassabe A Gona Duk Inda Tasa Gabanta Sai Dai Kaga Maza Na Zubewa Qasa Rututu, Koda Shugaban Dakarun Yaqura Jaruma Suhailat Idanu Yalura Da Yanayin Yaqinta Saiya Dakawa Yaran Sa Tsawa Suka Jada Baya Suka Bar Jaruma Suhailat A Tsakiyarsu Tana Fuskantar Shugaban Nasu, Shugaban Yanuna Jaruma Suhailat Da Dan Yatsansa Na Hagu Yace, Na Rantse Da Gemun Ubana Wannan Jaruma Suhailat Ce Tayi Shigar Maza! Idan Kin Isi Ki Baiyana Kanki Nagani!! Kina Zaton Ni Wawane Harda Bazan Iya Shaida Yanayin Yaqinkiba Alhali Naga Duk Irin Gumurzun Dakikayi Da Sarki Lubainu? Koda Shugaban Dakarun Sumame Yazo Nan A Jawabinsa Sai Jaruma Suhailat Tasa Hannunta Tacire Rawanin Dake Kanta Gamida Gemun Data Saka A Fuskarta Tayi Wurgi Dasu Kyakkyawar Fuskarta Ta Bayyaxa Qarara Afili, Koda Ganinta Sai Shugaban Dakarun Ya Bushe Da Mahaukaciyar Dariya Mugunta Yadubi Jaruma Suhailat Yace, Yake Sarauniyar Matan Duniya Kiyi Sani Cewa Ba A Turomu Domin Mukashekiba Komu Lalata Wannan Kyakkyawan Jiki Naki Ba Wanda Gaba Dayan Dinaren Duniya Bazai Iya Siyansa Ba, Ina Mai Shawartarki Daki Miqa Wuya Agaremu Mukamaki Salin Alin Mukaiki Ga Shugabanmu Don Cika Aikinmu Idan Kuma Kinqi Tozamu Yi Amfani Da Hanyar Dazata Fisshemu, Kafin Shugaban Dakarun Yagama Rufe Bakinsa Tuni Jaruma Suhailat Ta Tari Numfashinsa Tanamai Dakamasa Tsawa Tace, Yakai Wannan Qaton Banza, Karen Farautar Azzalumai, Maza Kasanar Dani Wanda Ya Aikoku Ku Kamani Ku Kaini Gareshi Ko Yanzunnan Kuzama Abincin Ungulaye!! Kodajin Haka Sai Shugaban DakarunYa Tuntsire Da Mahaukaciyar Dariza Sannan Yadubi Sauran Yaran Nasa Yayi Musu Wata Inkiya, Take Suduka Suka Dauko Wani Siririn Dututu Mai Kamada Qaho Suka Hurashi Sai Ga Wadansu Irin Allurai Sunfito Daga Cikin Bututun Sunyi Kan Jaruma Suhailat Zasu Tsittsireta, Cikin Baqin Zafin Nama Nagaban Kwatance Jaruma Suhaila Ta Daka Tsalle Sama Tayi Amfani Da Takobinta Da Garkuwarta Ta Karkade Alluran Wadanda Adadinsu Yakai Dubu Biyu, Aikuwa Sai Kaiqayi Yakoma Kan Masheqiya, Ma’ana Su Alluran Suka Koma Kan Wadanda Suka Hurosu Suka Sossokesu Suka Zube Qasa Suka Kama Barcin Dole, Kafin Jaruma Suhailat Tadora Qasa Ta Dirqa Bayan Shugaban Dakarun Ta Dora Kaifin Takobinta Akan Wuyansa, Nanfa Jikin Shugaban Dakarun Yakama Qyarma Sbd Yaga Mutuwa Muraran! Jaruma Suhailt Tadubi Shugaban Dakarun Tace, Maza Ka Sanar Dani Ubangidanka Wanda Yaturoka Ka Kamani Inba Hakaba Kuwa Yanzu Nan Zan Sharbe Maqogwaronka Da Wannan Takobi Nawa, Kafin Badakaren Yabude Baki Yayi Magana Tuni An Gabzawa Jaruma Suhailat Wawan Naushi Aqeyarta Ta Bayan [8/13, 12:15] khamis idris muhammad: Ta Kawai Sai Ta Sulale Qasa Sumammiya, Bawani Bane Ya Baiyana Awajen Ba Tsulum Yasumar Da Jaruma Suhailat Face Sarki Bauzur, Koda Sarki Bauzur Yaga Yasami Wannan Nasara Sai Ya Bushe Da Dariyar Farin Ciki, Sannan Yadubi Shugaban Dakarun Yadaka Masa Tsawa Yace, Sakaran Banza Tunda Kakasa Idi Aikinka Baka Da Sauran Cikon Kudi Awajena, Kayata Kanka Kona Qasasa Aikin Da Jaruma Suhailat Tabari Yanzunnan, Dajin Ha Badakaren Yajuwa Da Baya Yaruga Izuwa Cikni Daji Batare Da Ya Yarda Yayi Ko Waiwayeba, Cikin Matuqar Farin Ciki Sarki Bauzur Yasunkuya Ya Ciccibi Jaruma Suhailat Da Hannayensa Biyu Sannan Yabace Bat! Daga Wajen Tamkar Bai Taba Baiyana Awajenba, Sarki Bauzur Baisake Bayya Ako Inaba Sai A Wannan Gida Daya Kama Haya Wanda Ke Can Bayan Garin Birnin Istambul, Kaitsaye Ya Shige Da Jaruma Suhailat Izuwa Cikin Turakar Barci Yaturo Qofar Turakar Ya Kulleta Sannan Yaje Ya Shimfideta Jaruma Suhailat Akan Wani Gado Na Alfarma Jikinsa Na Karkarwa Kuma Cikin Zaquwa Da Doki, Yai Sauri Yatuje Rawanin Kansa Kuma Yacire Alkyabbarsa, Yanashirin Afkwa Jaruma Suhailat Kenan Kawai Saiyaji Katangar Dakin Taruguje, Tsakiyarta Yafaso Saiga Sarki Lubainu Yaratso Ta Ciki Tamkar Bayyanar Walqiya Daga Sama, Kafin Sarki Bauzur Yayi Wani Yunquri Tuni Sarki Lubainu Ya Gabza Masa Wani Wawan Naushi Aqirji, Sbd Qarfin Naushin Sai Da Sarki Bauzur Yafado Qasa Acikin Tsananin Galabaita Yakasa Miqewa Tsaye, A Lkcn Ne Sarki Lubainu Yadubi Sarki Bauzur Cikin Tsananin Fishi Yadaka Masa Tsawa Yace, Kai Tsohon Annamimi Kuma Maci Amana, Kayi Sani Cewa Taguwar Manya tafiqarfin Wuyan Yara! Wane Kaika Ce Zakayi Taraiya Da Masoyiyata? Tokasani Cewa Wannan Babban Laifi Daka Aikata Sai Hukunci Ya Shafi Gaba Dayan Jama’arka, Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Bauzur Ya Yunqura Dakyar Yamiqe Tsaye Sannan Yazare Wadansu Gajerun Adduna Guda Biyu Daga Kuibin Cinyoyinsa Ya Kwarara Uban Ihu Sannan Yadubi Sarki Lubainu Cikin Tsananin Fishi Da Qiyayya Yace, Yakai Tsohon Abokin Gaba, Kayi Sani Cewa Nadade Ina Tanadin Wannan Rana Wacce Zamuyi GABA DA GABA Dagani Saikai! Kaine Kadai Sarkin Da Yatsone Mini Ido Akaf Wannan Nahiya Gaba Daya! Kaine Kadai Wanda Nadade Ina Shakka, Amma Yanzu Danaga Wannan Kyakkyawar Budurwa Kuma Naga Kana Neman Mallaketa Saina Kawarda Haqurin Da Nadade Inayi Tsawon Shekaru, Bazai Taba Yiwuwa Kafimu Mulki, Kudi Da Daukaka Ba Sannan Kuma Ace Ka Auri Macen Da Babu Kamarta Akyau Aduk Duniya! Naso Nacika Burina Na Sanin Wannan Kyakkyar Budurwa Kafin Kai Domin Ina Nasami Hakan Nagama Dakai Koda Kuwa Ka Kasheni Ka Malleketa Amma Tunda Ka Katsemin Burina Tofa Yanzu Sai Abinda Hali Yayi! GANI GAKA, Kuma DAGANI SAIKAI, Gakuma Tauraruwar Matan Duniya Jaruma Suhailat Akwance A Gabanmu Cikin Halin Suma, Idan Kasami Nasarar Kasheni Shikenan Saika Dauki Abarka Kutafi, Idan Kuma Nine Nasamu Nasara Kasheka, Zanje Nakame Birninka Nahau KARAGAR MULKINKA Kuma Na Aure Jaruma Suhailat Nabarwa Duniya Tarihin Da Har Abada Baza A Taba Mancewa Daniba, Koda Sarki Bauzur Yazonan A Zancensa Sairan Sarki Lubainu Yabaci Zuciyarsa Takama Tafarfasa Kamar Zata Qone, Nantake Shima Yazare Takobinsa Kuma Yacire Garkuwarsa Ajikin Cinyarsa Yariqe Ya Fuskanci Sarki Bauzur Suka Kama Hararar Juna, Daga Can Kuma Sai Duk Subiyun Suka Dako Tsalle Sama Sukahadu Acikin Iska Suka Ruguntsume Da AZABBBEN YAQI, Yazamana Cewa Suna Kaiwa Junansu Sara Dasuka Cikin Tsananin Zafin Nama, JURIYA DA BAJINTA, Faruwar Hakan Keda Wuya Sai Jaruma Suhailat Ta Farfado Daga Dogon Sumanda Tayig Koda Tabude Idannunta Tadubi Dakin Datake Ciki Kuma Taga Sarki Lubainu Da Sarki Bauzur Suna Fafata Qazamin Yaqi Saita Cika Da Tsananin Mamaki, Kawai Saita Miqe Zaune Ta Zubawa Su Sarki Lubainu Idanu Tana Mamaki, Ba Komaine Yabata Mamaki Ba Face Ganin Cewa Ashe Akwai Gwarzon Jarumin Da Zai Iyada Sarki Lubainu Bata Saniba, Saida Su Sarki Lubainu Suka Rugurguje Gaba Dayan Katangun Wannan Dakin Dasuke Gumurzu Aciki Sbd Masifaffen Yaqin Dasuke Fafatawa, Ita Kanta Jaruma Suhailat Inda Badon Tana Tsale Tsale Da Kauce Kauce Ba Datuni Sun Cutar Da Ita, Hakadai Suka Cigaba Dakaiwa Junansu SARA DA SUKA Cikin Mugun Nufi Har Izuwa Tsawon Sa’a Guda Batare Da D ayansu Yasami Nasarar Koda Lakutar Jikin Dayaba, Bisa Dole Sukaja Dabaya Taku Shida Sukayi Cirko Cirko Suna Haki Da Kallon Juna Tamkar Zakaru, Kawai Sai Sarki Bauzur Yawatsowa Sarki Lubainu Kibiyoyin Tsafi Sama Da Guda Dubu Suka Taho Dagudu Cikin Iska Zasu Tsireshi, Amma Suka Kamada Wuta Suka Qone Qurumus Suka Zama Toka Tunma Kafin Su Iso Jikin Sarki Lubainu Nanfa Suka Cigabada Dakaiwa Junansu Miyagun Hare Hare Daqarfin Sihiri Amma Duk Abanza, Domin Sihirin Tsafin Yaqi Yayi Tasiri Akan Kowannensu, Koda Ganinhaka Sai Sarki Lubainu Ya Bushe Da Dariya Sannan Dubi Sarki Bauzur Yace, Tabbasa Na Yarda Kadade Kana Shiri Da Tanadi Akan Wannan Rana Dazamu Hadu, To Amma Kasani Cewa Ba’asan Maci Tuwoba Sai Miya Taqare! Kuma Masu Salon Magana Sunyi Gsky Dasuke Cewa Kyan Fada Akwana Anayi! Domin A Sannanne Ake Sanin Waye Jurarre Kuma Waye Gwani Mai Nasara? Yanzune Zamuyi Yaqi Da Dukkan Tsagwron Qarfin Damtsenmu Dakuma Kwarewarmu A Yaqi. Idan Na Kasheka Tabbas Qasarka Da Jama’arka Sun Zama Nawa, Idan Kuma Kaine Ka Kasheni Nayarda Kasata Jama’ata Dakuma Masoyiyata Jaruma Suhailat Sun Zama Naka, Sarki Lubainu Yajuya Ya Kalli Jaruma Suhailat Yace, Yake Masoyiyata Ina Mai Roqonki Da Koda Kinga Sarki Bauzur Zai Sami Nasara Akaina Kada Ki Taimaka Mini, Idan Harya Kasheni Kema Saiki Kwaci Kanki A Hannunsa Don Nasan Zaki Iya Samun Sa’ar Hakan, Koda Gama Fadin Hakan Sai Sarki Lubainu Yaruga Izuwa Kan Sarki Bauzur Suka Runguntsume Da Sabon AZABABBEN YAQI Akaro Nabiyu Amma Wannan Karon Sai Sukb Sauya Salon Fada Suka Hada Dakaiwa Junansu Naushi Da Bugu Da Hannu Daqafa Gamida Kai SARA DA SUKA! Wohoho!! Idan Qarfi Ya Hadu Daqarfi, Kuma Gwani Yayi Karo Da Gwani Sai Gumurzu Yazamo Abin Al’ajabi, Kuma Abin Tsoro Mai Dadin Kallo, Shikansa Sarki Lubainu Yayi Matuqar Mamaki Yadda Akayi Sarki Bauzur Yakeda Wannan Gagagarumin Qarfi Da Jarumtaka, Haka Kuma Yaboye Kansa Tuntuni Baiyi FITO NA FITO Dashiba, Ya Tsaya Yana Shakkarsa Alhalin Yanada Wannan Babban Shiri [8/13, 12:16] khamisidrismuhammad: Haka, Saida Suka Shafe Sa’a Guda Suna Wannan BAKIN ARTABU, Kwatsam! Sai Sarki Bauzur Ya Shammaci Sarki Lubainu Yadebo Ruburbushin Qasar Gini Yawatsa Masa A Ido, Kafin Sarki Lubainu Ya Mutsttsike Idanunsa Tuni Sarki Bauzur Ya Danqara Masa Sara Aqirji, Take Wajen Yadare Jini Yai Tsartuwa, Amma Sbd Tsananin Juriya Da Jarumtaka Ko Ihu Sarki Lubainu Baiyiba, Kuma Duk Da Haka Idanunsa Arufe Suke Sai Yayi Amfani Da Kunnensa Yagano Inda Sarki Bauzur Ke Tsaye Don Haka Sai Yadaka Tsalle Sama Ya Shallake Sarki Bauzar, Ta Baya Ya Danqarawa Sarki Bauzur Martanin Sara A Gadon Bayansa, [8/13, 12:16] khamis idris muhammad: Take Shima Bauzur Bayansa Ya Dare Jini Yai Tsartuwa Da Feshi, Bai San Sa’adda Yakurma Uban Ihu Ba Sakamakon Tsananin Zafi Da Zogin Dayaji, Duk Subiyun Sai Suka Kife Qasa A Lkcn Dajini Kezuba Ajikinsu, Cikin Firgici Jaruma Suhailat Ta Yunqura Zata Ruga Izuwa Kan Sarki Lubainu, Amma Sai Yadaga Mata Hannu Yana Mai Yimata Nunida Tadakata, Nan Take Sarki Lubainu Da Sarki Bauzur Suka Yunqura Cikin Matuqar Qarfin Hali Da Juriya Suka Miqe Tsaye Duk Da Cewa Jiri Na Dibarsu Sakamakon Jininda Suke Zubarwa Ajikin Nasu, Nan Fa Suka Tsaya Suna Kallon Juna Cikin Harara Da Tsananin Qiyayya, Daga Can Sai Suka Sake Rugowa Da Gudu Izuwa Kanjuna Cikin Mugun Nufi, Kai Dagani Kasan Cewa A Wannan MUGUWAR HADUWA Daza A Yi Dole Ne Cikin Biyu Ayi Guda, Kodai Suyi RAGAS Wato Sukashe Junansu, Kokuma Dayansu Yasami Nasarar Kashe Daya, Aikuwa Suna Haduwa Sai Kowannensu Ya Kaiwa Dan Uwansa Muguwar Suka A Ciki Amma Sai Suka Kare Sukar Da Takubbansu, Tartsatsin Wuta Yatashi Akan Takubban, Kawai Sai Sarki Bauzur Yasake Kawowa Sarki Lubainu Suka A Maqoshi, Cikin Baqin Zafin Nama Sarki Lubainu Ya Sunkuya Tsinin Takobin Ya Soki Iska, Kafin Sarki Bauzur Yaqara Kawo Masa Wani Harin Tuni Sarki Lubainu Yayi Wata Irin Katantanwa Aqasa Kuma Yatale Qafafunsa A Qasan Ya Sokawa Sarki Bauzur Takobin A Ciki, Take Takobin Ta Lume Tafaso Gadon Bayan Sarki Bauzur Jini Yafara Feshi, Kawai Sai Jaruma Suhailat Taga Sarki Bauzur Yaqame Atsaye Kuma Takobinsa Ta Subuce Daga Hannunsa Tafadi Qasa, Sai Ga Jini Nazuba Ta Bakinsa, A Sannan Ne Sarki Lubainu Ya Yunqura Domin Yamiqe Tsaye Amma Sai Yafadi Qasa Sakamakon Jirinda Yakwashe Shi, Koda Ganin Haka Sai Jaruma Suhailat Tarugo Da Gudu Ta Sunkuci Sarki Lubainu Cikin Dimauta Ta Azashi A Kafadarta Danufin Ta Ruga Waje Dagudu, Har Izuwa Wannan Lkc Sarki Bauzur Natsaye Yazama Gawa Amma Bai Fadi Qasaba, Kawai Sai Jaruma Suhailat Taji Sarki Lubainu Yace, Ciromin Takobina Daga Jikin Wannan Babban Maqiyi Nawa, Cikin Sauri Ta Waiga Takama Qotar Takobin Ta Zarota Daga Cikin Sarki Bauzu Tana Zarewa Ne Gawar Sarki Bauzur Takifeqasa Jaruma Suhailat Taruga Waje Da Gudu Dauke Da Sarki Lubainu A Kafadarta Ta Duro Tsakiyar Gidan, Koda Dakarun Sarki Bauzur Suka Hango Gawar Sarkinsu Kwance A Cikin Dakin Sai Dukkaninsu Suka Yarda Makamansu Suka Arce, A Guje Jaruma Suhailat Suka Isa Wajen Wani Doki Ta Dora Sarki Lubainu Akai Sannan Itama Tahau Ta Zabureshi Da Gudu Tanufi Cikin Gari, Jaruma Suhailat Tana Cikin Gudu Akan Dokin Ne Saita Lura Cewa Sarki Lubainu Fa Yasuma, Donko Motsi Bayayi, Kuma Har A Sannan Jini Na Cigaba Dazuba Ajikinsa, Nanfa Ta Dimauce Ta Kurma Uban Ihu Kuma Tafashe Dakuka Tana Mai Qarawa Dokinta Qaimin Gudu Sbd Gani Take Kamar Kafin Ta Isa Gidan Sarautar Sarki Lubainu Ya Mutu, Tundaga Nesa Damasu Gadin Qofar Gidan Sarautar Suka Hango Jaruma Suhailat Dauke Da Sarki Lubainu Bisa Doki Cikin Jini Saisuka Dimauce Suka Bude Qofar Dasauri Kuma Suka Busa Qaho Alamar Cewa Ba Lfy, Aikuwa Sai Dakarun Gidan Sarautar Suka Kama Guje Guje Da Shirye Shirye Ana Debo Makaman Yaqi Don Anzata Yaqine Ya Barke, Jaruma Suhailat Na Isowa Harabar Turakar Sarki Sai Hadimai Suka Rugo Suka Karbi Sarki Aka Shigar Dashi Cikin Turakar Kuma Aka Ruga Aka Kirawo Likitansa, Har Likitan Yagama Dinke Raunin Dake Kan Qirjin Sarki Lubainu Aka Sa Masa Magani Bai Farfado Ba Kuma Ba Cikakken Numfashi A Qirjin Nasa, Inbanda Ma Likitan Ya Tabbatar Dacewa Sarki Lubainu Bai Mutuba Da Kowa Yazata Ya Mutu Din, A Wannan Lkc Turakar Sarki Lubainu Tacika Da Dukkan Fadawansa Da Hadimansa Anyi Jugum Jugum, Wasuma Sun Dan Fara Koke Koke Masu Taurin Zuciyane Ke Zubarda Hawaye Kawai, Ita Kuwa Jaruma Suhailat Kuka Take Tayi Sosai Tana Zubarda Hawaye Mai Yawa, Al’amarin Dayasa Kowa Awajen Yagane Cewa Lallai Tana Son Sarki Lubainu, Bayan Likita Yadubi Gaba Dayan Hadiman Sarki Da Fadawan Yace, Akwai Buqaqatar Kowa Yafita Yabar Sarki Dagashi Sai Masu Yimasa Hidima Da Jaruma Suhailat Domin Sukadai Yake Buqata Ayanzu, Kada Kowa Yaqara Shigowa Wajensa Hasai Bayan Yadawo Cikin Hayya Cinsa, Kodajin Haka Sai Kowa Yafice Akabar Jaruma Suhailat Ita Kadai Zaune A Gefen Gadon Da Sarki Lubainu Ke Kwance Taqurawa Fuskarsa Idanu Tana Zubarda Hawaye, Sukansu Hadiman Sarki Fita Sukayi Suka Tsaya Abakin Qofar Dakin Suna Jiransuji An Kirasu Domin Aiwatarda Wani Umurni, Sai Da Darn Yaraba, A Lkc Da Jaruma Suhailat Tafara Gyan Gyadi Sbd Dadewar Datayi Azaune Gamida Gajiya Sannan Sarki Lubainu Ya Farfado Daga Dogon Sumanda Yayi, Kodaya Bude Idanunsa A Hankali Yaga Suhailat Zaune A Gabansa Gyangyadi Sai Farin Ciki Ya Lullubeshi Bisa Ganin Cewa Lallai Jaruma Suhailat Tadamu Da Rayuwarsa Tunda Gashima Takasa Tafiya Tabarshi, Kamar A Mafarki Jaruma Suhailat Taji Ankirawo Runanta Suhailau!! Jaruma Suhailat Tafarka Firgigit! Tadubi Inda Sarki Lubainuke Kwance Aikuwa Saita Kamuda Tsananin Mamaki Domin Ganinsa Tayi Azaune Yaqura Mata Idanu Yana Murmushi, Cikin Tsananin Farin Ciki Jaruma Suhailat Ta Yunqura Zata Rungumeshi Sai Sukaji An Kwankwasa Qofar Turakar Wani Hadimi Yace, Ya Shugabana Ga Mahaifin Jaruma Suhailat Yazo Dubaka, Yafi Sa’a Hudu Tsaye Aqofar Dakin Nan Yana Jiran Ka Tashi Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Lubainu Yace Abudemasa Yashigo, Take Hadimin Yabude Qofar Sai Ga Sadauki Zahar Ya Shigo Fuskarsa Cike Da Annuri, Jaruma Suhailat Tamiqe Tsaye Taruga Gareshi Suka Rungume Juna Cikin Murna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata Yamatso Gaban Sarki Lubainu Ya Risina Yakwashi Gaisuwa Yace, Barkanka Da Shallake Harin Mutuwa Yakai Wannan Sarki, Tabbas Kayi Babbar Sa’a Daya Kasance Saranda Sarki Bauzur Yayi Maka Aqirji Bai Taba Qasusuwanka Qirjinka Ba, Tsokar Nama Kawai Yadara, Amma Ka Zubar Da Jini Mai Tsananin Yawa Wanda Shiyasa Ka Kusa Rasa Rayuwarka Gaba Daya, Koda Gama Fadin Hakan Sai Sadauki Zahar Yajuyo Yadubi Jaruma Suhailat Fuskarsa A Murtuke Yace, Amma Ai Duk Laifinkine Yake ‘yata Sbd Me Zakifita Farauta Daji Batare Dakinje Mini Sallama Ba? Shin Kin Manta Ne Cewa Duk Sa’adda Zamu Fita Farauta Daji Saina Shafa Kanki? To Kisani Cewa Wannan Shafar Kai Danake Yiwa Dukkan Jama’armu Tsarine Nake Baku Daga Dukan Tsautsayi, Yanzu Ashi Kinjanyo Munyi Asarar Mutane Shida, Kinsa Matayensu Sun Zama Gwaraye ‘ya’yansu Sun Zama Marayu, Yanzu Haka Suna Can Gaban Kabarurrukansu Sunata Faman Kuka, Kekanki In Ba Don Sarki Lubainu Yanemi Yarasa Ba Kuma Yatafi Nemanki Datuni Sarki Bauzur Yagama Lalata Rayuwarki, Waqilama Ya Kasheki Bayan Yagama Buqatarsa Dake, Kisani Cewa Sau Tari Qarfin Mutum Da Iya Yaqinsa Bashike Bashi Nasara Ba Akwai Sa’a Sannan Neman Shawara Gamai Aiwatar Dawani Lamari Yanada Matuqar Amfani Da Fa’ida, Shiyasa Ma Akace Aikin Mai Shawara Baya Bace Saidai Kawai Ba Sirri Aciki, Ina Mai Horonki Kadaki Sake Aikata Irin Wannan Babban Kuskurn Dakika Aikata, Lkcn Da Sadauki Zahar Yazo Nan Azancensa Sai Hawaye Ya Zubowa Jaruma Suhailat Ta Durqusa Bisa Gwiwoyinta Agaban Sadauki Zahar Tace, Ka Gafarceni Yakai Abbana, Tabbas Nayi Nadama Bisa Wannan Kuskure Dana Aikata! Ya Abbana Kana Ganin Yanzu Dame Yakamata Nabiya Diyyar Mutanenmu Shida Dasuja Mutu?” Mu Hadu A Littafi Nagaba wato na TAKWAS 8 Kuma na karshe Donjin Cigaban Wannan Qayataccen Qasaitacce Labari, Dag Mai Dece Muku Kewa A Kullum Da Koyaushe. KHAMIS IDRIS MUHAMMAD Shugaban Marubuta Littafin Yaqi. ABDUL’AZIZ SANI M/GINI. Post navigation [ad_2]