YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

……’kwa’kwaluwarta ce ta tsaya ta daina processing na wani lokaci kafin daga baya ta cigaba da bugawa, ji take mgnrsa ba iya cikin kunnuwanta kad’ai suka tsaya ba har cikin zuciyarta take jin komai ,ta sake matsowa sosai kusa da mahaifinta wasu zafafan hawaye suka shiga gangarowa akan kuncinta.   Tafukan hannuwanta ta d’aura a saman kafafuwansa dady Cikin mataanancin kuka, gabadayan idanunta dake zubar da ruwan hawaye ta tsurawa mahaifinta tana kallonsa tana son ya karyata mata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa, yace “mata wasa yake mata ba gaske bane ,saboda d’acin kalmar tafi kowace kalma muni da zafi me ta’bo zuciya da wuyar mantawa , Amman sake maimaita kalmar da dady yayi ya tabbatar mata da iyakacin gaskiyarsa yake nufin raba aurenta da fu’ad a.

 take ta dinga furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “shikenan ta faru dani takare ta fad’i hk acikin ranta cikin matsanancin tashin hankali” yaushe ne zan sake samu ‘yancin da rayuwa mai dadi kmr rayuwarta ta baya ?

,tun kafin jamar gurin suyi yunkurin mgn tashiga fad’i” shikenan shikenan !!! dady naji na amince na yarda da wannan sharad’in naka matukar zaka ya femin , domin ni yanzu nafi son farin cikinka a kan farin cikin kowa, duk abinda kake so shi zanyi ,bani da za’bin daya wuce naka ..

Tana mgn tana kuka zuciyarta na rawa da gargadinta a kan abinda take shirin aikatawa rayuwata ..

  “tana son fu’ad tamkar ranta, kuma bata jin cewa xata iya ci-gaba da rayuwa ba tare dashi ba,Amman a halin yanzu ta za’bi farincikin mahaifinta akan ta cigaba da zama dashi ,zata cigaba rayuwarta babu shi acikin duniyarta , ta gwamaci ta yiwa mahaifinta biyayya a karo na farko ko rayuwarta zata daidaita ,koda kuwa rabuwa da fu’ad din zai zama silar barinta duniya…..

a yanzu ta yarda ta fad’a kowane irin yanayi ne matuƙar dai mahaifinta zai yi farin ciki ya amshita amatsayin diyarsa sa’banin shekarun baya ,da ya fita lamarinta ……

 “xata yi k’ok’arin k’arasa fitar da ragowar soyayyar fu’ad daga cikin xuciyar tayi rayuwarta da iyayenta da tilon diyarta.

Kanta a sunkuye ta cigaba maimata mgn “Daddy na yarda ..,dady na amince duk Abinda kake so a halin yanzu zan yi, ba ni da wani buri a rayuwata sama da na faranta maka, sama da na kyautata maka nayi maka biyayya a kan duk abinda kake bukata daga gare ni, duk abinda kake so xan yi maka shi Daddy….

Takarasa mgnr tana wani irin kuka me ta’ba zuciya kuka take sosai tmkr ranta zai fita gabadaya duniya ta cukud’e mata waje daya bata ta’ba hk tashin hankali irin wannan da take ciki yake da muni da ciwo ba ,ta d’auka rashin son da dady yakewa fu’ad zai tsaya a iya hk ne ,ta d’auka rad’ad’in tuni ta tsaya a wancan lokacin ,ta d’auka ko darajar samun nasreen atsananinsu zai sauk’ak’awa zuciyarsa kiyayyar fu’ad …..

Amman da kalamansa na yanzu ta fahimci komai ya sauya agareta ,ta gane ita din ba kowa bace, tasoma fahimtar talaka marashi da galihu ya fita kwanciyar hankali sau dubu.

 yanzu wakilla najma datake kallo mafi kaskancin gani akanta tafita kwanciyar hankali da walwala .

“yau din tazo mata da tashin hankali da rud’anin rayuwa maramisaltu “ya zatayi da kaddarar data gifta mata da rayuwarta gabadaya? Parlour’n ya d’auki shiru ,gabadaya jama’ar dake zaune acikinsa sun rafka uban tagumi, ban da sautin kukan me’ad bakajin sautin komai acikin parlour’n …..

Yayinda Mahaifinta yaji dadin jin kalaman daya fito daga bakin ‘yar tasa, a nan take ya fahimci me’ad dinsa ta sauya ,ta samu natsuwa, ta k’ara hankali fiyye da lokutan baya, sannan da gaske take nufin nadamar abinda tayi masa a baya ,sannan a halin yanzu yasan ko zuwa gaba yace mata “ga abinda yake son tayi masa tayi batare da sa’bawa umarninsa ba.

 cike da matsanancin farinciki da jin dadi yace “me’ad na yafe miki duniya da lahira Allah kuma yayi miki albarka, Sannan amatsayina, na mahaifi gareki ina umartarki daki baro hotel din da kika kama ki dawo gidan ubanki da zama .

Alhaji gali yayi saurin sauke hannunsa dayayi tagumi dashi tare da numfasawa yace ” yanzu alhj ediris wannan d’ayen hukuncin daka yanke kana ganin abune me bulewa, raba ma’aurata da rana tsaka alhalin suna son junansu..? “Ni aganina hkn bai kamata ba ,idan shi yaron laifi yayi maka kamatayi a nemeshi ya baka hakuri ba rabashi da matarsa ba alhalin tana son shi …

Da sauri me’ad ta d’ago idanunta da har wannan lokacin basu daina tsiyayar ruwan hawaye ba tace “No…..dady kubar hukuncin da mahaifina ya yanke akaina kawai kada ku tursashi ,ni koda ina son fu’ad zan iya rabuwa dashi, ballanatana ahalin yanzu babu d’igonsa sonsa ko daya araina ni dai ku taya sake bawa mahaifina hakuri, nagode nagode da kulawarku gareni ,yadda kuka tsaya kuka gyara tsakanina da mahaifina, ina muku adduar allah ya biya muku bukatunku na alkairi, nagode nagode har bansan irin godiyar da zan muku ba ..

jikinsu yayi mugun mugun sanyi babu wanda ya sake yunkurin cewa komai bisa lafazin bakin me’ad ,hk kowanensu ya tashi jiki a sanyaye suka soma mikawa juna hannu suna sallama da juna tare da k’ok’arin barin parlour’n,a tare suka fita har me’ad kowane yashiga motarsa itama tashiga nata motarta da niyyar d’auko nasreen daga school sannan .

kasa tukin tayi ta gangarawa gefen titi tayi parking tare da d’aura kanta saman sitiyari ta fashe da wani irin gigitaccen kuka, gbdy tasoma datasanin barin gidan mijinta datayi 

…kuka take sosai yayinda zuciyarta ke sake bud’ewa a wajajen ,da duk ciwoka suka samu muhalli, jikinta yayi mata sanyi,zuciyarta ta dinga tsinkewa har take jin tmkr batayiwa kanta adalcin rabuwa dashi ba,”ina Zata sake samun madadinsa? 

“Ina Zata samu jarumi jajjirtaccen miji irinsa ?

bata San lokacin data d’auka tsaye agurin ba zuciyarta ke mata zafi had’e da tsinkewa ahankali take sake jin ciwon abinda fu’ad din yayi mata , sai da taci kukanta ta koshi sannan ta tada motar tabar gurin .

a kan hanyarta ta dawo gida bayan ta d’auko nasreen, yarinyar take tambayarta abinda ke damunta “momy me ke damunki da alamun kina cikin damuwa koma nace kmr kinyi kuka ko..? 

“Bby banyi kuka ba idona ke min ciwo ,hk gefen kaina kmr zai fita kimin addua kinji bby …. ta k’arasa mgnr tana meida hawayen da yayi k’ok’arin zubowa .

nasreen ta d’aura hannunta akan na momy’nta dake Kan giyar mota sannan muryarta a raunane tace ” momy allah ya baki lfy ,but ki daina damuwa,Dan Nasan damuwa ne akan auren dady ko?

” but momy ina tabbatar miki dady ba zai auri daya daga cikinsu ba ,saboda dady najin mgnta ba zai yi abinda banaso ba ,nagaya masa banason yayi miki kishiya da aunty sajida da najma. ..

girgiza kanta kawai me’ad tayi “yaro duk inda yake yaro ne … hanyar da nasreen taga me’ad ta d’auka ne sa’banin masaukinsu yasa ta sake fuskantarta sosai “momy ina kuma zaki kaimu ba hotel zamu ba ,? Tayi uwar tmby jikinta na rawa rawa “Dan Allah karki kaimu gidan grandpa yacika fad’a dayawa sannan kuma bayason dady’na nima….”short up there my friend I don’t want here any from you just keep your mouth short …tacigaba da tukinta batare da ta sake kallon inda take ba .

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button