HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

_Page_ 1⃣ & 2⃣

Cikin nutsuwa take tsara kwalliya Wanda ta dauki tsawon minti talatin tanayi.

fuskarta tadau shaki tare da fittar da annuri Duk da Kwalliyar ba mai nauyi bane,
amma ya yadace da fuskar ta tare dafito mata da kyawunta Na ainihi.

Vibration din wayan tane yasa ta dakatawa da abin da takeyi tare da kai hanu tadaga. tana mai karawa akune

_Assalamu alaikum._

tafurta cikin sasanyan muryanta mai tattare da nutsuwa ga duk mai sauraro.

_Wa’alaikis salam._

My malama aka amsa ta dayan bangaren.

ke kadai ake jira dafatan kingama duk wani shiri…

farin ciki ne ya ziyarci zuciyanta jin abin daya furta.

Gyada kai tayi kaman yana ganinta.

kana ta amsa ina nan tafe “my prince”

Insha Allah in the next 30minute I will be with You.

OK “my princess” ya amsa

Su feedy da Feena sun iso?

“Eh sun iso ke kawai muke jira.

OK. Saina kariso. bata jira cewar sa ba ta katse wayan.

Cikin hanzarin ta tashi tare da bude akwatin kayanta.

fitowa tayi da Riga da wando Wanda jarumin nata ya tanada mata su musamman Dan wannan ranan.

Rigar yakasance pink mai dauke da rubutun princess agaban rigar da kalar fari mai sheki da daukan ido wandon daya kasance pencil fari ne qal Wanda jikinshi crazy ne ta ko ina.

Cire tawul din dake jikin tayi tare dafara sa kayan cikin hanzari.

wandon tafara sawa Wandon, tsayinshi dakadan yawuce gwiwanta, kana tazira rigan Wanda yazauna das ajikin ta.

Tare da fito da dukwani shape Na jikinta.

Dan kunne ta sa tare da sarka dasuka kasance farare masu sheki da daukan ido Wanda sarkan yana dauke da harafin *A* ajikinshi Agogo da awarwaro duk fararene masu sheki Wanda suka dace da kwalliyanta.

Gashin kanta daya sha gyara yaketa sheki ta kara gyarawa tare da feshe oil shen.

Takalmi da jaka sun kasance farare inda takalmin yakasance mai mai rufafen sama da tsini.

Turare tadauka tare da feshe jikin ta dashi. kallon kanta tayi a mirror tana murmushi tare da daukan wayanta tana cire selfie.????

basaina fada muku kyan datayi ba. amma Ku kiyasta da kanku.

bakin Abaya mai Dan kauri tadauko ta dora akai tare da farin hijab data sa. jaka ta dauka tare da zuba yan tarkacen ta aciki.

fitowa tayi tare da nufan dakin mahaifiyar ta cikin tafiyanta mai nutsuwa tayi sallama tare dashiga dakin.

mahaifiyar nata dake zaune tana nazarin wasu takaddu tadago da murmushi a fuskanta tana mai amsa mata sallaman.

sunkuyar da kai kasa tayi tana murmushi…

Umma! nashirya zan wuce.

Toh Aiman! adawo lafiya.

Amma kinso ki makara ince waliman karfe hudu kikace.

Daga kanta tayi tana mai kallon agogo dake manne jikin bagon dakin take maganan yanzu karfe hudu da rabi ake nema.

Eh ta amsa
naso makara Umma shiyasa nake sauri.

toh kidai hanzarta, kedince komai cikin sanyi zanga ranan dazakiyi Abu cikin lokaci batare da ya kure miki ba.

Dariya tayi dajin maganan umman nata. azuciyar ta kuma tana mai takaicin karyan datayi.

mika mata Dari Biyar tayi

Ungo wannan ki hau abin hawa. Adawo lafiya
karba tayi cikin sanyi jiki tare da jin tausayin mahaifiyar nata.

Nagode Umma saina dawo.

Yauwa adawo lafiya.

Allah yasa umman ta amsa tare da mai da kai kan abin datakeyi.

Ficewa tayi cikin hanzari dake gidan abakin hanya ne bata sha wahalan samun abin hawa ba.

tayi sa’an samun adaidaita sahu.

hanu tasa mai cikin hanzari bai karisa tsayawa ba taleka tare da fadin Ray field.!!!

bata jira amsan shi ba tashiga shima ja yayi Dan ya fahimci passenger nashi tana sauri.

tambayan ta yayi

daidai ina a rayfield hajiya?

Queen’s Palace Hotel. tabashi amsa atakaice.

hanunta ta daga tare da duba agogon dake daure a hanunta.

biyar saura, tafurta Ahankali lokaci yatafi.

wayanta ta ciro a jaka tare da danna kiran feedy bugu biyu ta daga.

“Hello! Ina kike ne kinshanyamu fa.

ganinan tafe nakusa karisowa.

In less than ten minutes zan iya shigowa kufito mu hadu a bakin gate.

OK sai kin kariso.
Katse wayan tayi tana mai rutse idon ta iskan dake kadawa yana shiganta.

Tana mai jin soyayan shi yana ratsa illahirin jikin ta.

dake basu da nisa dagurin kuma hanyance mai kyau yasa suka iso cikin mintinan dabasu Gaza goma ba.

tsayiwar adaidaita sahun yayi daidai da fitowan su feena daga gate din.

Fitowa tayi tana mai tambayanshi nawa ne kudinka.

Dari uku ya amsa.
mika mishi Dari biyar tayi yabata canjin Dari biyu.

Cikin murmushi su feedy suka tare ta suna mai tsokanan ta kaga Matan Liman ina daki da wannan shigan?

cikin Dariya take fadin bana son iskanci wani tambayane wannan mukarisa please!

zuciyana duk yazaku yaga farin cikinta.

nabarshi yanata jira.

Dariya suka sanya duka feena tana mai furta lallai fa farin ciki manya.

Gate din suka nufa tare da kutsawa ciki can gefe feedy ta nuna.

mutsaya daga can kicire wannan damuwan.

Dariya suka kara sanyawa suna mai nufan inda tanuna musu.

Suna tsayawa tacire hijabin tare da wurgawa feedy ninke min karyayi squeeze kana tacire abayan tana mai wurga ma feena ga naki kema.

“Wow”!!!
Suka furta atare

baby U r looking takeaway ???????? cewar feedy…

Feena kuwa kasa furta komai tayi sai Dariya datake gaskiya kin cinye kowa agurin nan.

Yau nasan X-Boy sai yarasa inda zai saka ranshi ganin sahiban ahaka.

Dake yau yafara gani na ahakan koh!! ta amsa mata!!!

Dariya suka sake kwashewa dashi.

bude jakanta tayi tafito da powder tasake daidaita fuskan ta tare da sake fesa turare.

gashin kanta daya sha gyara yasauka har gadon bayanta ta sake gyarawa.

kutsawa sukayi ciki hall din.

tana mai dannan kiran gwanin nata awaya.

daga wa yayi.
“Hello”baby kin iso?
Na iso baby…!!!
“Am sorry I keep you waiting…”
“but gamunan muna karisowa hall din”
“karki damu my princess”.

Farin ciki ne ya ziyarci zuciyanshi tare da dokin yin tozali da abar kaunar tashi.

Cikin hanzari ya sanarwa Mc karisowan nata.

fita cikin hall din yayi domin ya taryo ta.

Yana fitowa ya hangonta tsakiyan su feena da feedy sun nufo hall din.

cikin tafiyanshi Na matashi mai tashe da jini ajiki yanufosu yana mai murmushi ga sahiban tasa.

Shiga yayi cikin fararen kaya. Wando da ya kasance fari pencil mai crazy Riga,agogo,Takalmi, duk farare makeken glass din dake idonshi ya kasance baki sai chain din dake wuyanshi Fari.

itama cikin takunna mai kaman hawainiya take karisowa tare da mayar mai da martanin murmushi.

Mantawa suka yi dasu feedy da Feena suna karisowa ya bude hanunwansa yana mai alaman rungumanta.

batayi kasa a gwiwa ba tashige tare da rungumanshi shima.

Wani irin shock su duka saukaji kokarin sakeshi tayi tare da ja da baya daga runguman daya mata takasa.

Kara matse ta yayi yana mai jin tsikar jikin shi natashi cikin karfin hali yake rada mata akunne

“Omoh! “baby you are looking more than beautiful ”
“Happy birthday” Once more my princess…..

Feena Ne tayi karfin hali tare da gyaran murya.

Dago wa yayi yadora idonshi akansu Wanda shi sam bai lura dasu ba tun fitowanshi.

sakin ta yayi tare da dafa kafadun ta da hanunshi.

am sorry friends ban lura dazuwanku ba.

baza kalura ba inji Feena ta amsa a katsale.

ita Wanda muka taho tare ma ta manta damu bare kai.

Hada hanuwanshi yayi yana mai alamar roko Dariya su duka sukayi Dan X-Boy akwai son barkwanci.

karisawa sukayi cikin hall din inda hanunshi Na sakale a qugunta su feedy suka Mara musu baya.

dauriya kawai take tana tafiya domin duk yagama saukar mata da kasala.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button