HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

A zahirin gaskiya tun da muka dawo idan har zan zauna ba abin Dana ke gani a idona sai hoton shi da dare bana iya bacci tunanin shi ya kan hanani ta buka komai tun ban dauki hakan wani Abu ba ina waskewa har na yarda na amince da tabbas na kamu da son wannan mutumin nayi kuka nayi adua tare da Neman mafita gurin Allah, Amma wallahi kaman Ana kara rura min wutan sonshi ne.

Yawan Tunanin Dana ke yi da rashin samun barci yasa na kwanta rashin lafiya.

Wanda ke shaida ce akan hakan yanayin Dana shiga.

Umma ta cigaba da min adua ba laifi ina samun sauki a jikina amma tabbas bacci sai dai ya kwasheni bana iyayi, A lokacin har ke kinsha tambayana ina ne yake miki ciwo ince kirjina.

Wanda su Umma ma amsan Dana ke basu kenan, sanina daku kayi da chronic Ulcer yasa kuke gamsuwa da hakan, sai dai yanayin ciwon nawa baiyi kaman da ulcer ba.

Washe garin ran da Salim ya dawo daga Ghana ya kira wayana, Wanda shima tun da ya tafi a takure yake Tunanin ya hanashi sakat.

Randa ya kirani ina kwance a daki ina aikin Tunanin nashi kiran waya ya shigo waya na ganin bakon namba yasa ban daga ba har ya tsinke aka sake kira a karo na biyu dauka nayi tare da karawa a kunne batare da na yi magana ba.

Shima shirun yayi sai ajiyar zuciyan danaji an sauke banyi magana ba danaga shirun yayi yawa na kashe wayan ban kai ga ajiyewa ba kira ya sake shigowa kin dauka nayi har ta katse a ka sake kira jefa wayan nayi a silent ma gaba daya.

Message ya turo min kaman haka

Ummu Aimana ki Sani kaunar ki tariga da ta gama illa ga duk wani jijiyoyin jikina tun daga rannan Dana fara sauraron muryanki cikin qiran alqurani.
Duk da a lokacin banga fuskan ki ba saboda niqabin da ke fuskan ki amma zuciyana ta kasa hakuri dake.
Ban taba fargaban tsayawa gaban mace in mata magana ba sai a kanki, ban taba kasa yi wa wata mace maganan duk Dana ke so ba sai gunki Ummu ki na min kwargiji.
tabbas kece Matan data dace ta zama uwar yayan Salim.

Saka wayana da nayi a silent yasa ban ji shigowan sakon ba har sai Dana dauki wayan domin kiran ki.

Ganin sako ya sani budewa tare da fara karantawa. Bazan kwantan ta miki farin ciki Dana shiga ba a lokacin saboda ko ba komai na fahimci mai wannan sakon.

Duk halin da nake ciki duk sanadin shi ne Allah ya dawo min dashi lokacin Dana ke cikin bukatan hakan duk da ina da daman dazan iya Neman shi a lakocin amma nasa a raina koh zan mutu da kaunar shi bazan kai kaina inda yake ba mutukar bai sake waiwayana ba.

Wallahi tun da naga sakon nan na nemi kaso 75% na cikin abin da nake ji na rasa, murmushi na da fara’ana yadawo kaman bani ba hatta Umma tayi mamakin hakan mutuka amma sai dai tabar wa Allah komai tare da hamdala na lallai Allah ya amsa aduan ta, kema idan bani manta ba Dana kira ki a wayan kinyi mamakin jin muryana cikin walwala da farin ciki kuma bakiyi shiru ba har sai da kika tambaye ni ma.

Bayan sallar isha’i wayanshi ya sake shigowa banyi kasa a gwiwa ba na dauka tare da yin sallama.

Amsawa yayi sannan ya gabatar da kanshi Tare da tambayana kin tuna ni?

Amsawa nayi da Eh’ nagane ka

Good da fatan kinga sako na, ina kuma fatan zaki amince ki karbi soyayana.

Duk da nasan tsarin rayuwa na danaki ba iri daya bane kaman Yadda kawarki ta fada amma ita soyaya bata duba wannan, bata duba matsayin mutum ko al’adanshi dabi’anshi, ko akasin haka.

Dafatan kin fahimci ni.

Na’am na fahimce ka amma ka bani lokaci zan yi Tunanin akan hakan.

Shikenan nagode da lokacin da kika bani.

Sallama mukayi na katse wayan.

Haka muka cigaba da yin waya jifa jifa har ya kai ga na amsa mai tare da amince mai da tayin soyayan shi, min cigaba da soyyaya cikin sirri muna liqe da waya a kodayaushe

A lokacin anyi hutun makaranta mai dogon zango Wanda idan muka koma zamu shiga ajin karshe a makarantan secondary,

karbo min form din Bliss Computer institute da ke sparkling junction da baba yayi ya bani daman haduwa dashi a koda yaushe zai zo mu hadu idan na tashi kafin in wuce Gida.

Min cigaba da haka kafin aka koma makaranta a haka na koma zuwa da yamma.

Gaiyata na yayi wani party daya shirya domin nishadi anan nafara fahimtan wasu halaiyan sa da bansani ba.

kaman yanda kika Sanni ma’abociyan son sa doguwan riga Abaya hakan ne ya kasance na sa na na fita a Gida da niyan zuwa computer school na tafi party. a karon farko dana fara ma iyayena karya.

yazo ya dauke ni, muna fara tafiya ya Ciro kaya daya siya min musamman domin partyn., a Leda ya mika min, bayanda baiyi dani ba da kafin mu karasa zai tsaya in canja naki yarda a karon farko damu ka samu jayayya dashi… Wanda har yayi fushi ya ja yayi parking tare da cigaba da lallaba ni insa Na ki a karshe dai dole ya hakura muka tafi a haka, duk da a lokacin banga aibun kwaliyana ba Abayana Na sa ba ki mai adon ja sannan Na rolling jar gyale akaina takhalmi da jaka duk ja.

Sanda muka karaso hotel din tun daga nan nakasa yarda da gaske ni din ce kuwa yau wai nabiyo wani sarauyi party a hotel, a haka muka karasa shiga yayi parking muka fito ganin wasu YAN mata nayi sun nufo mu suna zuwa da murnan su suke furta X-Boy atare suna daga hanunsu alaman jinjina, murmushi ne shimfide a fuskan shi tare da Kiran sunayen su Rabina, Juliet har kun iso kenan! Ban karaya ba sai gani danayi sun rungume juna a gabana tare da kissing juna daya bayan daya sannan ya jiyo yana mai musu nuni dani da hanu tare da fadin this is my wife to be. Wow suka furta a tare she is beautiful. Suna mai min kallon up & down.

Nima kallon su nake cikin shigansu da duk Rabin jikin su a waje yake.

Kama hanuna yayi a karon farko wanda kidiman Dana ke ciki yasa nakasa hanashi kama hanun nawa.

Cikin reception din hotel din muka karasa nidai binshi kawai na keyi yanda naga suna welcoming din shi yasa Na fahimci lallai ba bako bane a gurin.

Kutsawa mukayi ciki ina biye dashi kaman jela, dakin Dana ga an rubuta Room B/24 ya tsaya tare da kutsawa ya shiga ciki parlo ne madaidaici mai Kyan tsari, zama yayi kan kujera tare da fadin baby ki zauna mu dan huta kafin time yayi…, maganan da take Neman gagara Na da kyar Na iya fisgowa, please me nake shirin ganine haka am I dreaming or it happen in reality.

Dariya yayi tare da matsowa kusa dani ya sa hanun shi saman kafada Na you are not dreaming my princess do you want me to prove you…., ban kai ga ba shi amsa ba naji bakin shi Cikin nawa ya fara kissing dina…. Nayi kokarin in kwace kai Na amma Na kasa fara romancing dina yayi ta ko ina har sai da nayi laushi, fara kokarin raba ni da kayan jikina yayi wanda har yayi nasaran cire min abayan jikina kuka Na keyi sosai ina rokon shi daya yi hakuri ya rufamin asiri kar ya cutar dani, amma bai saurara min ba muna cikin wannan yanayin aka turo kofan dakin aka shigo, dagowo yayi a fusace. ko a jikin ta duk da a yanayin data same mu a ciki bai hanata fara’a da karisowa inda muke ba cikin takunnta da duk jikin ta yana kadawa… Nida tun shigowanta nasamu Na dauki a bayata Na zura kama hanun shi tayi tare da fadin Baby why are you disturbing your self a irin wayannan Villagers din ta fada tana mai nuna ni da hanu…..Shi da ya birkice ya rasa control dinshi idon shi ya kada yayi jajur tabbas duk abin da yake yi bai taba jin feelings irin wanda yaji ba yau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button