HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Da daskararriyan muryanshi ya amsa Don’t mentioned that again blessing please walk out i have not invite you for now, allow me pls. Sanin halin nashi yasa batayi kasa a gwiwa ba ta fita tare da jawo musu kofa…..kuka Na sake ba kakautawa…jingina a kujera yayi ya rutsa idonshi tare da dafa kanshi.

Sakowa yayi tare da durkuso da gwiwoyinsa kasa, Dan Allah kiyi hakuri ki gafarce ni Na tuba wallahi ba niyya Na ba kenan akanki sharrin shaidan ne.

Wallahi ina sonki bazan taba cutar dake ba kiyi hakuri da abin danayi Na roke ki.

Cikin kuka na furta Allah ya Isa tsakani Na dakai Wallahi Allah sai ya sakamin Ashe dama yaudara ta kayi kana da burin da kake so ka cima a kaina shiyasa ka yaudareni da kalaman ka.

Toh Allah ya fika kuma tabbas nana ta yi gaskiya kai ba abokin tafiya Na bane.

Kuma daga yau ba ni ba kai kasa wannan aranka.

Karasa maganan nayi da sabuwan kukan daya sake kufce min…

Tabbas ya shiga kidima tsugono yayi a kasa yana min magiya har da kuka shabe shabe yana roko na inyafemai yayi kuskure, tare da roko Na in fada mai duk abin da nake so wallahi zai min idan har zai sa in canja furuci na Na, ganin lokaci Na qurewa kuma yanda yake zubar da hawaye sai tunani ya fado min ga duk fahimtan rayuwan shi danayi tabbas har dadiro ya ajiye a hotel dinnan toh mai zai hana inyi kokari inga Na sa shi ya daina wannan munanan dabi’un nashi ko dan darajan soyayyan da nake mishi kuma sannan Zan samu lada gurin Allah muddin nazama sillar shiryuwan shi, ance so hana ganin laifi tabbas hakane domin duk abin nan daya faru wallahi banji tsanan shi ba sai ma soyayyarshi da ta sake ruruwa cikin zuciyana.

Amsa mishi nayi tare da kafa mishi sharadin zai Daina Neman mata zuwa party, da sigari da yake sha duk zai daina.

Nan take yamin alqawari da Yadaina kada kai nayi tare da mikewa muka fito tare. Gurin partyn yasha kayatarwa jama’a sun cika mata da maza ana ta rawa shiga yayi ni kuma najirashi a waje ina kallon duk abin da ake ta jikin window Yana shiga ya bada umarnin a tsayar da kidan tare da kar ban mic ya fara bayanin an tashi a wannan partyn kowa ya kama gabansa sannan yayi kira ga abokanayen nashi da kar wani ya sake inviting dinshi wani party ko wani iri ne.

Cecekuce ne ya karade cikin hall din bai jira wata wata ba ya mika musu mic din tare da ficewa cikin gurin binshi tayi suka nufi hanyan Gida can baya da gidan mu ya tsaya duk da a lokacin an fara kiraye kirayen sallar magrib, sauke ni yayi tare da cigaba da jaddada min da yardan Allah yabar duk wayannan dabi’un.

In takaice miki labarin dai a haka wallahi sai da ya dena zuwa duk wani party idan har bana birthday bane ko Na biki ya bar neme nemen mata da yake, sigari ce dai har yau bai barta ba, su feena kuma da feedy da kika gansun gun birthday nan, tun lokacin birthday shi kafin nawa danaje muka sake kullawa dasu inda ya tilas ta min saka kayan daya siyo domin nasa wanda nayi hakan sai wannan najiya shima, maganan taba ni da romancing dina kuma da yake wlhy Na kasa hanashi Sam sai dai innaga zai wuce gona da iri nakan nuna a’a amma wallahi Nana ban taba aikata zina ba ki fahimce ni. Karasa maganan tayi tana mai fashewa da kuka.

Ajiyan zuciya ta sauke shikenan! Na fahimce ki amma kinyi wauta Ummu kina ganin shaidan yadaina shiga tsakanin Ku kenan muddin zaku kebe Ku biyu, me yasa zaki zabi sabawa Allah akan faranta ran wanda Allah ne ya halice shi dake dashi din duka kuma bai haliceku dan komai ba sai don Ku bauta mai.

Kisani kina da sauran lokaci da za ki gyara kuskuren ki har yanzu, kiyi amfani da karatun ki ummu, kar ki bari tarbiyan dasu Umma suka shekara goma sha takwas suna baki ya tashi a banza.

wallahi Allah bazai barki ba idan har kikayi hakan.

Tabbas *AMINTA* na dake ban taba tunanin zaki boye min wani Abu makamancin wannan ba, amma na miki uzuri tunda ba abun alkhairi bane shi yasa kika boye min, sai dai ki Sani kaman yanda kika kafa ma X-Boy sharadi ya amince kema zan kafa miki nawa sharadin yanzu.

Dagowa tayi tana kallon ta dauke kai tayi tare da cigaba da magana na Baki zabi cikin biyu dole a yi daya Ummu

na daya zaki zaba ko Ni ko X-Boy!!!

ban damu ki zabeni ba dan nasan soyayyan da ki ke mai ba karami bane tunda har zaki iya munafurtan Mafi kusanci da soyuwan mutanan dasu ke tare dake .

amma sai dai ki Sani muddin kika zabi cigaba da tarayya da X-Boy Ummu toh wallahi kinji na rantse miki ba abin da zai hana ban fadawa baba da Umma abin da kika fada min yanzu ba kuma wallahi bazan rufe su da komai ba.

domin idan nayi hakan har suka gane dakansu tabbas zasu ce na munafurce su kuma ni zasu fara zargi domin duk duniya basu San ki da wata kawa ba sama dani kaman yanda nima haka aka sanki a gidanmu.

Dan haka dabara tarage game shiga rijiya. Na barki lafiya tashi tayi tare da daukan jakan ta da gyale.

Kallon ta tayi Ki Sani na baki kwana uku abin da kika yanke ki kirani ki fada min kar ki manta na tura hotunan nan duka a wayana kin ga ina da hujjan dazan ji dadin fada musu.

Gaba tayi tana mai fadin na barki lafiya……. Har ta fita bata iya motsawa daga inda take ba kan ta ya dau caji.

Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun ta shiga ambatowa.

Harsu Umma suka dawo tana zaune inda ta barta, Sannu da zuwa ta musu tare da tambayan jikin hajiya baba.

_*Toh fa ya zata kasance shin Ummu zata zabi X-Boy ne tabar AMINIYAR nata ta’kuma amince da iyayenta su San abin da take boye musu koh qaqa.*_

_Kucigaba da bin alqalamin sumiee domin ganin yanda zata kaya._

Gaskiya har Dana gobe irin wannan typing haka mai yawa.????????

 

 

_Love you my fans!_????

_*Sumiee B*_
[19/09, 9:50 pm] Sumiee B.: ????

????????

???????? ????

???????? ????????

Typing…..✍????

????‍❤‍???? *AMINTA* ????

_Na_

Sumaiyya Babayo Abdullahi.
(Sumiee B.)

Follow me on
Wattpad @ Sumiee_b

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

~*We are bearer’s of so golden pen*????~
*~we write assidiously perceive no pain,~*
*~So magical Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????savour our words, for it will cause you no pain.~*

*SADAUKARWA*  _*Ga Aishatu Babayo Mrs Abubakar yakubu (Danjuma Master)…_
_Allah yakara dankon kauna da fahimtan juna yabaku zuri’ah masu Albarka! Amen_

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button