HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Ahankali ta furta *SO* baka min adalci ba wallahi.

Turan kofan gidan tayi tashiga tare da sallama abakinta.

Shiru taji tsakar gidan ba kowa dakin Umma tanufa tare da saka kai ciki tana mai sallama.

Baby ne ta taso da gudu tana mai mata oyoyo. Daga ta sama tayi tana mai murmushin gareta. Dafadin.

Oyoyo my sister.

Aunty mun dawo makaranta bakya nan wai kinje walima shine Baki jirani muntafi ba.

Dariya tayi tana sauke ta a hanunta tare da zama kan kujera tajawota jikinta.

A’a my sister idan Na jira sai kundawo a islamiyya ai bazamu samu zuwa ba dare zaiyi kan muje antashi.

Yanzu ma kinga nayi dare inata sauri

Aunty ba baba da umma sunce bakyau kaiwa magrib a anguwa ba amma ke kinkai yau.

Toh aini ba anguwa naje ba my sister gurin walima ne kuma karatu ake agurin.

Toh AUNTY kinkawo min abin waliman?

Zuciyan tane yabuga domin Sam ta manta da Yar kanwan nata bata riko mata komai ba.

Koh Dan takare kanta yakamata tashigo dawani Abu tunda tayi karya da walimah.

Dakewa tayi kaman da gaske ta qaqaro murmushi tare da furta nakawomiki my sister.

Tashi tayi ajikin ta Na tsale tana fadin baza’abama su yaya khalifa da Abba ba koh.

Naki ne ke kadai babyna.

Rugawa tayi aguje tanufi dakin yayun nata tana fadin Aunty takawomin abun dadi bazan bakuba.

Khalifa sarkin zuciya ne yatareta toh ina ruwanmu inkika ci kifimu girma.

Allah yarinyan nan kina wasa dani ko. Buya tayi bayan yaya Abba tasan halin yaya khalifa yanzu zai maketa.

Abba ko dariya yaketa kyalkyalawa tun shigowan nata.
Cikin zolaya shima yace ni zaki sammin koh kanwata.

A can kuwa da tun shigan ta Ta hango Umma Na sallah acikin bedroom dake labulen dakin a dage yake.

Dan haka ta zauna tana jiran idarwan nata. Ta dauki mintuna biyar da zama nata.

Umma ta idar tare da mikewa tana kiciniyar cire hijabi jikin ta batare da ta kalli inda take ba.

Gabantane yasake fadiwa, dakewa tayi tare da furta sannu da gida Umma !

“Yauwa” ta amsa

Sake dakewa tayi Umma kiyi hakuri nakai da……

Ya isa tafada tana mai daga mata hanu

Daga ina kike…..???

Cikinta ne yaba da sautin qululululu..

A zuciyanta tana tunanin koh wani yaganta ne!

Sanin mahaifiyan nata dasaurin gano mutum idan tayi karya yasa ta kokarin dakewa da boye firgicin data ke ciki.

Umma kiyi hakuri Nima ba’ason raina nakai haka ba awaje, matsala akasamu aka canja venue din waliman aka mayar dashi can wajen police staff college dake express, samun abun hawa agurin yana da wahala gaske kin sani Umma bare yamma yayi shine muka jira aka mayar da amarya aka dawo aka dauke mu…

Tana maganan ne cikin nitsuwa da kwantar da murya karkare maganan tayi da Ki gafarceni Umma Nima duk hankalina yatashi nadamu wallahi indawo gida.

Kada kai tayi tare da gamsuwa da bayanin data mata.

Ina kika jefa wayanki nakira babanku ma yakira Baki daga ba.

Tunda muka Shiga nasa wayan a silent damuka fito Na manta bancire ba.

Sake gyada kai tayi.
kiringa lura dai Aiman ki kiyaye duk abin da zai zubar miki da kimarki Amatsayinki Na mace mai daraja kiyi kokari zama mutum nagari domin YAN uwanki suyi koyi dake zanyi alfahari dahakan.

Gyada kai tayi tana mai tsarguwan kodai Umma tasan abinda takeyine???

Insha Allah Umma zan kiyaye

Allah yamuku Albarka ta fada,

Amen ta amsa.

Baba bai dawo bane?

Eh baisamu karisowa ba sha’anin karfe sai Gobe insha Allah Zai Dawo

Allah yakaimu yakuma dawo dashi lafiya, Amen umman ta ‘amsa

Tashi tayi tanufi kofa fita kicibis sukayi da baby data kwaso a guje sauri tayi ta tare ta kan ta kai kasa.

Ummana ne tafara magana Baby wai banhana ki guje gujen nan bane idan dare yayine wai.

Umma wallahi YAYA khalifa ne yabiyo ni zai dakeni.

Ehen kin tsokaneshi badole ya dakeki ba.

Dariya tayi tana mai fadin Umma kinsan fa khalifa da zuciya kaman kuturu mai zata mai Na duka da darenan.

Aunty ina abin dadin dakika kawomin gabanta ne yafadi naga takaina ni Aiman nasha gurin Umma yarinyan nan tanaso ta kureni cikin zuciyanta take fada azahiri kuwa dakewa tayi tare da furta gashinan my sister tana maganan tana bude jaka kaman gaske..

Ha’ah kar dai Na manta my baby ina saurin in dawo tana maganan tanasake duduba cikin jakanta.

Dagowa tayi muje daki imbaki pop corn Na manta dashi amma zanyi waya Gobe akawomin.

Shigewa tayi tafara gaba har takai kofa zata fita Umma ne takirawo ta idan kingama abinda zakiyi kizo kikarbi pepers dinnan ki ajiye gurinki kifara ragemin marking dinsu ko zuwa da safe.
ne.

Da toh ta amsa tafita baby nagaba bude kofan dakin nasu tayi tashiga Faty ne kwance akan gado tayi daidai tana sharan bacci harda munshari.

Kallon ta tayi tana mai furta kaga Kasan Umma har ankai China abacci.

Pop corn ta daukawa baby tabata tare da rakata tabude mata kofa ta fita.

Alhamdulillah tafada Allah ka yafeni tana mai daga hanunta sama.

 

 

 

 

 

 

 

 

Sumiee B.
[13/09, 12:52 pm] Sumiee B.: ????

????????

???????? ????

???????? ????????

Typing…..✍????

????‍❤‍???? *AMINTA* ????

_Na_

Sumaiyya Babayo  Abdullahi.
(Sumiee B.)

Follow me on
Wattpad @ Sumiee_b

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~❄We beare’s of soon golden, We write aassiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍????~*

*SADAUKARWA*  _Ga Aishatu Babayo Mrs Abubakar yakubu (Danjuma Master)…_
_Allah yakara dankon kauna da fahimtan juna yabaku zuri’ah masu Albarka_! _Amen_

*FATAN ALKHAIRI__* _Gareki  Mrs. fureratu usman mainasara (Furetu)  tabbas soyaya gamon jinine, hadin Allah kuma. haduwata dake Alkhairi ne kuma inajin hakan ajikina kaman yanda zuciyoyinmu sukayi saurin AMINTA.  Wannan yakara tabbatar min dahakan. Kisani har abada bazan manta dake ba. Tare da halacinki gareni. Zanyi kewarki mutuka! Ina miki fatan Alkhairi a arayuwanki tare da fatan nasara cikin karatunki._

“””””””””””””””””””””””””””””’

_Bismillahir Rahmanir Rahim…………_✍????

Typing…….????‍????

???? 12/9/2019

Nigeria ????????

????7:30am

_Page_ 7⃣ & 8⃣

Rage kayan jikinta tayi tare da fadawa toilet din dake manne jikin dakin ta watsa ruwa sannan ta daura al’wala ta fito a gurguje.

Jallabiyan ta dauko ta saka tare da hijabi tafara gabatar da sallar magrib kana ta daura da isha.

Bata tashi ba sai da ta daura da shafa’i da wuturi

tana idarwa tamika hanunta jikin bed side ta dauko Alqurani tare da budewa tafara rairo karatu qurani cikin sasanyan muryanta mai tartare da nutsuwa.

Wayanta ne yake Neman dauki, bata kula ba tacigaba da karatunta saida takarata shafi uku cikin suratoul maryam ta dakata.

Daga hannuwanta tayi tare da kwararo adua. Shafawa tayi tamike tare da ninke sallayan.

Agurguje tashafa mai tare da shiryawa cikin kayan baci , Riga da wando marasa nauyi.

Hijabi tadaura akai tare da nufan dakin mahaifiyan nata cikin sallama tashiga.

Ta same umman nata a kishingide tana nazarin wani littafi, daga kai tayi tana sauke littafin hanunta tare da dubanta tana mai amsa sallaman

kingama take tambayanta

Eh nagama umma!

Kinci abinci kuwa dan banji motsinki a kitchen ba.

A’a banci ba umma dare yayi tea kawai zansha

Toh Yar ka’ida wani yasaki kaiwa Daren, kidai ringa kiyayewa da cikin ki fa kinsan matsalanki Na ulcer idan yatashi miki baya miki da wasa amma bakya kiyayewa. Abinci akodayaushe aringa masa cin ganin dama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button