HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Cikin dariya tace toh zan kiyaye umma amma fa ni yunwan ne banaji shiyasa.

Toh aishikenan! Umma ta furta

Mika mata papers din tayi tare da mata bayaninsu

Gyada kai tayi tana mai fahimtan abin datake nufi, tare da karban papers din.

Sallama tamata da mukwana lafiya

Allah yasa ta amsa karkimanta kirufe kofan gida kiduba su khalifa.

Toh ta amsa!

Kitchen tanufa tahada tea taje ta ajiye adaki hade da papers din kana tadawo taduba su khalifa suna bacci jawomusu kofa tayi tare da rufe duk wani kofan daya kamata.

Daki takoma ta zauna gefen gado tana mai jawo stool tare da daura kofin tea din akai.

Tana juyawa ahankali da hanunta wayanta ta jawo ta duba 8 missed call tagani

Agogo tafara dubawa karfe goma da minti shabiyar.

Duba Masu missed call din tayi taga Aminiyarta takira sau biyu feena da feedy sai mai gayya X-Boy Wanda yakira har so hudu.

Aminiyar nata tafara kira
sai dai harya katse bata daga ba sake kira tayi akaro Na biyu harya kusa katsewa aka daga.

Assalamu Alaikum.

Ta furta daga dayan bangaren aka amsa

Wa’alaikis salam

Kardai Na tasheki kinfara bacci cewar Aiman.

Wallahi bacci yayi gaba dani.

Ayya sorry my dear, yakike kwana biyu haduwa yayi wuya.

Kedai bari jiya naso shigowa inganki amma wani uzurin yahana ni amma Insha Allah gobe zanshigo.

OK Allah yakaimu saina ganki.

Aff” sorry ban reply miki msg dinki ba naga birthday wishes thankyou so much.

Allah yabar kauna da zumunci.

Amen ta furta sai nashigo katse wayan tayi tana mai laluban namban Feedy bangajiya tamata tare da godiya kana takira Feena itama

Yaza’ayine da gift din nan ne cewar Feena. Karkidamu ki ajiye agurin ki kafin in bukata OK bye suka yi sallama.

Tana katse wayan Kiranshi na shigowa Tea dinta daya rage kadan tadauka ta karisa kan ta daga har yakusa yankewa.

Haka suka lalace agurin da hira tare da fadama juna kalaman soyaya, sundauki tsawon minti ashirin kafin sukayi sallama cikin bege da annushuwa.

Toilet ta shiga tayi brush kana ta daura Al’wala tafito tayi aduan kwanciya ta kwanta.

Kiran sallar Fari da asuba a kunenta Wanda ta ginu akan tashi da zaran ankira Assalatu. Juyi tayi hade da miqa tana mai furta.

_*Alhamdulillahil lazi ahyana ba’ada ma amatana wa’ilaihil nushur.*_

Adua’an tashi daga bacci. kafanta ta sauke kasa tana mai furta *Bismillah*

Toilet tanufa tana mai karanto

_*Allahumma inni a’uzubika minal qubusuwal qaba’is.*_

Kafan hagu tafara sawa tare da bismillah abakinta.

Bangaren mahaifiyan nata itama ta tashi tare da daura Al’wala tazauna bisa sallaya tana muraji’an karatun qurani.

Bangaren Aiman ma hakan yakasance tana fitowa tashifida sallaya tare da daukan qurani tafara muraji’ah.

Sun kasance ahaka har fitowan alfijir aka kira sallah kafinnan suka dakata.

Tashin Faty tayi daga bacci tayi sallah, itakuma ta tashi ta fara gabatar da raka’atul fijir.

Umma ce ta tashi su khalifa da Abba sukayi Al’wala suka gabatar da raka’atul fijir kafin suka nufi masallaci.

Bayan duk sun gabatar da sallar asuba tare da yin aduoinsu da azkhar duk suka hallaci dakin mahaifiyan nasu domin daukan karatun qurani da sauran littatafan Addini. Wanda Al’adan gidan kenan.

Banda Aiman ciki domin tunda tayi sauka tayi hadda aka sallameta saidai tayi mura ji’anta.

Wani lokacin kuma ita take Jan ragamar karatun idan mahaifiyar tasu bata samu dama ba.

Wayanta ne yayi kara tajawo tare da dagawa takara akunne.

Assalamu Alaikum my Prince

Tafurta ta dayan bangaren X-Boy ne ya amsa da “Hello my princess ” .

Dafatan kintashi lafiya my Angel

lafiya lau ta amsa

Ya gajiyanki najiya

Alhamdulillah.

Yanaka gajiyan?

Gajiya babu ko kiris sahibata tunda naji muryanki naji Na wartsake, sai kewanki danake ciki tsamo tsamo.

Uhummm nima haka nake cikin kewan tsamo tsamo..

Dariya yayi Wanda tajiyo sautinshi yasata murmusawa

how can you prove this my princess
After All dayanzu zance zanzo inganki zaki fara kawo excuse.

Murmushi mai sauti tayi kana tace so kake ka kureni dasafen nan marairace murya tayi  cikin shagwaba. Ba damuwa nagane ka…

Dariya duka suka sanya, Yanzu mai kakeyi ta tambaya.

Dafatan dai baka makara sallar asuba ba.

Na’am my malama ban makara ba yabata amsa

Kinsan idan Abu yashiga ranka tare da kudira niyya akai yana da mutukar wahala ka manta.

My princess shigowanki rayuwata babban nasarace agareni kin haskamin rayuwata daga duhu zuwa haske kin maidani mutum mai nagarta kin tunatar dani ni kaina Wanda Na manta da hakan. Sannan uwa Uba kin So ni tare da nuna min kauna. Wallahi ko haka Allah yadauki rayuwata inaga nagama dace gidan duniya akan rayuwan danayi abaya. Bani da abin dazan biyaki wallahi saboda wannan hallacin inaga kudi bai isa yasiya ba. Saidai inmiki aduan kasancewa cikin farinciki gidan duniya dana lahira.

Ajiyan zuciya ta sauke maganganunshi sun ratsa ta Wanda tabbas tasan gaskiya yake fada.

Ahankali ta furta Amen my Prince tare da kai. amen shima ya amsa.

Yanzu zan dan kwanta ne princess kafin lokacin office yayi.

Yakamata kam kahuta. Nima kwanciyan zanyi.

“Well” ya furta muhadu a mafarki

Dariya tayi OK mu hadu a can din

OK I love you

I love you too.

Ta furta tare da katse wayan.

Ajiye wayan tayi gefen gadon tare da jawo bargo ta kwanta, hotunan shine suke tamata gizo tare da jin zazafan kaunarshi nasake shiganta.

Bangaranshi ma hakan ne yakasance yakwata hotonta tane yake tamasa gizo wayan shi yadauka tare da shiga gallery yana kallon hotunan su Na jiya da videos din daya dauka yana mai murmushi tare da shiga begenta yana mai rayawa inama yaganta gefenshi yanzu.

Moment din jiya da ita yaketa tunawa yana murmushi ahaka har bacci yadaukeshi.

Tara saura Faty ne ta tasheta

Aunty! Aunty! Aunty!

Tana mai bubuga bayanta.

Mika tayi hade da dafe kanta daya Sara mata.

Oh’ Faty so nawa zance miki idan ina bacci karki tasheni ne.

Baya taja dan kartaji bugu Umma ne fa tace inzo intasheki muzamu tafi makaranta.

Amsawa tayi da Toh ina zuwa saikun dawo.

Komawa tayi ta kwanta tacigaba da baccinta.

Goma saura a firgice ta farka tare da durowa agado tana mai tuna sakon kiran umma da aka mata kaman amafarki taji shi dan bacci Na idon ta.

Saukowa tayi agadon tanufi toilet tare da watsa ruwa hade da dauro Al’wala

fitowa tayi tashirya cikin Riga da skirt Na atamfa kana tashinfida sallaya ta gabatar da salatul duha (sallan wal’ha).

Tana idarwa ta nufi toilet ta wanke kana tafito ta gyara dakin tare da kunna mai turaren wuta ta ja kofa tarufe

Fitowa tayi ta iske umma a kitchen tana wanke kayan miya.

Risinawa tayi tare da fadin ina kwana umma. Cikin sakin fuska ta amsa lafiya kalau Aiman kintashi

Eh natashi su baby sun wuce makaranta naji gidan shiru

Eh” sun wuce Fatima bata tasheki bane, Ta tasheni bacci ne bai sakeni ba Umma

murmushi tayi Amma kin iya sawata agaba da tsokanan baccinta yayi yawa, ai duk basu kaiki bacci ba

dariya tayi tana fadin kai umma wani bacci nake dayawa daza ahada da yarannan karma Faty taji labari.

Dariya tayi Toh ga chips can a kula ki iba kiyi breakfast, kisamu kizo ki kama aikin nan babanku yana hanya.

Toh Allah yakawoshi lafiya ta furta tana mai shiga cikin kitchen din plate tadauka ta iba tare da daukan cup ta hada tea

fitowa tayi ta zauna kan dakalin dake gefen kitchen din tana ci suna Dan taba hira jifa jifa umma kuma Na aikace aikacen ta a kitchen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button