HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Inda take fada mata Nana tana gaisheta tana ma zuwa anjima

amsawa tayi da INA amsawa Allah yakawota lafiya.

Dan Allah kiyi da jikinki Aiman karki tsaya sanyin nan naki kaman baki da lakka har babanku yadawo bamu gama abinci ba.

Gashinan narage aiyukan Tuwon shinkafa da miyan Ogun za ‘ayi sai zobo Toh nariga Dana gama zobon gashinan nasa a frige.

Da Toh ta’amsa tana mai tashi ta’ajiye plate da cup din datagama breakfast

Dakin mahaifiyan nata tashiga ta kintsa mata tare da sharewa

kunna turaren wuta tayi ta jawo kofan dakin ta rufe ta nufi dakin su khalifa ta duba tare da gyara musu dan abin daba’arasa ba Duk da sunyi iya yinsu saboda ankoyar dasu hakan kafin sutafi makaranta zasu gyara gado Sannan suyi shara.

Bata nufi dakin Baban nasu ba Dan tasan umma ne keyi ko yana nan ko bayanan tana tashi zata share ta kunna mai turare taja tarufe.

Tsinstiya tadauka ta share tsakan gidan tare da Jan ruwa a rigiya ta wanke tsakar gidan Fess.

Wanke hanuwanta tayi tare da nufan Kitchen din Wanda tasamu umma har ta blanding kayan miyan a blander tana kan zuba maggi a tafashen naman data Dora.

Umma kije ki kintsa bazan karisa

Toh Aiman Allah ya yimiki Albarka

Amen ta amsa tana mai jin dadin aduan mahaifiyan nata.

 

 

 

 

 

 

_*Sumiee B*._
[14/09, 9:07 pm] Sumiee B.: ????

????????

???????? ????

???????? ????????

Typing…..✍????

????‍❤‍???? *AMINTA* ????

_Na_

Sumaiyya Babayo Abdullahi
(Sumiee B.)

Follow me on
Wattpad @ Sumiee_b

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

~*We are bearer’s of so golden pen*????~
*~we write assidiously perceive no pain,~*
*~So magical Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????savour our words, for it will cause you no pain.~*

*SADAUKARWA* _Ga Aishatu Babayo Mrs Abubakar yakubu (Danjuma Master)…_
_Allah yakara dankon kauna da fahimtan juna yabaku zuri’ah masu Albarka! Amen_

*_Fatan Alkhairi ga shugaba, sarkin golden pen writers association Umar Dalha Allah ubangiji ya kareka tare da biyan ka da mafificin Alkhairi. Kokarin da kake akan mu bamu’isa mu biyaka ba sai dai muma fatan samun nasara cikin dukkanin al’amurorin ka na gidan duniya da lahira._*

******************************
*YAN UWA RABIN JIKI*

????

*Mrs. Aishatu Babayo*
*Mrs. Jamila Babayo*
*Mrs. Zainab Babayo*
*Mrs. Yahanasu Babayo*
*Mrs. Hafsat Babayo*
*Miss. Fauziya Babayo*
*Maryam Babayo* *Khadijah Babayo*
___________________________
*Abdullahi Babayo*
*Kabiru Babayo*
*Jibrin Babayo*
*Shu’aibu Babayo*
*Ibrahim Babayo*
*Aminu Babayo*
*Yusuf Babayo*
*Abubakar Babayo*

_*Allah yakara hade kawunan mu ya kuma sa Albarka a cikin rayuwan mu.*_

_Toh fa fans kar ace nayi son kai ban anbanci wata ba Dan tace lallai tanason shiga cikin familyn *Babayo*???????? kuzama Judges idan sunan ya rhymes. toh????‍♀????

Habeeba Babayo!!!!! ???????????? ya kuka ji….❓yaba da ma’ana kuwa ????????

********************************

_*Bismillahir Rahmanir_ Rahim………….✍????* _

Typing…….????‍????

???? 14/9/2019

Nigeria ????????

????12:21pm

_Page_ 9⃣ & ????

Murmushi dauke a fuskan ta tace bazan karisa yanka miki ganyen.

Da toh ta amsa tana mai duba tafashen naman da yake wuta.

Karisa yanka ganyen tayi kana ta wanke tare da tsane shi a kwando ta wanke hanun ta tafice a kicin din.

Jikin tane ya bata masoyin nata Na kiran ta a waya share wa tayi tare da basar wa ta cigaba da aiki amma zuciyan ta ya kasa amincewa da hakan.

Wanda dole ta dakata da abin da takeyi ta nufi daki, tana bude kofan dakin ta tarar wayan ta Na Neman agaji cikin hanzari ta karisa tare dakai hanu zata daga kan ta daga wayan ya tsinke.

Kan takai ga duba mai kiran wani kiran ya sake shigowa, Wanda sunan da ta saving namban masoyin nata ne ya baiyana kan screen din wayan.

Tun kan ta dauka ta shiga shauki da farin ciki.

Dauka tayi tare da zamewa jikin gado ta kishingide.

Ta bangaran shi kuwa ajiyar zuciya yayi tare da Furta

Baby baki tashi bane?

Murmushi mai sauti tayi Wanda sai da ya ratsa illahirin jikin shi. Kana ta amsa da

Na tashi my Prince!

Good” ya furta yana mai jingina da kujera.

How was your dream?

I know bani kadai na yi mafarki ba baby kema kinyi!

Fada min yaya mafarkin ki?

Murmushi tasake yi sannan tace its was exactly as yours.

“Wow” are you sure my dear?

Yes Darling!

“Well ”

Yanzu yaza ayi ina son ganin ki my princess

Can we meet today please? Ya marairace murya

Kwantar da kanta tayi tare da sake rage muryan ta kaman mai rada kana tace

kasan baba yayi tafiya baisamu dawowa jiya ba amma yau yana hanya ya kusa karisowa.

Idan yayi tafiya ya dawo ba ya fita ko ina sai dai masallaci.

Kaga bazai yiwu infita ba Dan yau bansan karyan dazan yi ba.

Sannan bestyna ta kiran zata zo min wuni kaga ba chance din fita.

Kada kai yayi yana mai jin dadin sauraron muryan nata, kaman kar ta tsaya da maganan.

Shirun dataji ne yasa ta furta Hello”, Hello kana jina?

Ina jinki my princess cigaba da magana.

Ba kaji mai nace bane.

Na ji my princess muryan na kine a koda yaushe kaman ana kara masa Zuma baby, ya shagalar dani na fada wata duniyan.

Murmushi mai sauti tayi Wanda yake baiyana jin dadin furucin nasa har cikin ranta. Kana tace

My Prince kaima haka naka muryan yake ai ko ma ince yafi hakan.

Hmm kidai fadi gaskiya. Yanzu ni dai kimin alfarma idan zaki raka Nana ki sanar dani sai in zo in ganki ko minti biyu ne.

Ajiyan zuciya ta sauke da har saida ya jiyo sautin.

Kana tace shikenan my Prince zanyi kokarin hakan.

Karka kirani daga yanzu saina kiraka.

OK Ranki shi Dade dariya suka sanya duka.

Yanzu kinga zan iya katabus a office tun dazu tunanin ki ya hanani aikata komai.

Dariya tayi kana tace shikenan sai kajini I love you my Prince!

I love you too my princess.

Karan saukan kiss ne ya daki kunen ta cikin sauri ta cire wayan a kunne tare da katsewa gaba daya tana mai murmushi.

Da hanzari ta dira a gadon tuno tafashen nama da yake wuta.

Cikin sauri ta nufi kicin inda ta tarar har ruwan ya fara komawa jikin shi.

Cikin hanzari ta kashe wutan tare da saukewa.

Tukunya ta dauka ta sake dauraye Cikin shi da ruwa duk da a wanke yake, kunna wuta tayi ta Dora tukunyan akai tare da zuba manjanta a Cikin, yanka Albasa tayi tasa ta soya man kana ta zuba tafashashen naman tare da soya shi sama sama ta kwashe.

Markadaden kayan miyan ta, ta dauka ta zuba Cikin mai din Kana ta rufe tukunyan.

Tukunyan daza tayi tuwo ta dauka ta daureyi Cikin kana ta dauki ruwan zafi dake Cikin electric kettle ta tsaida ruwan tuwon dashi, kunna wuta tayi ta daura akai.

Daukan jikakiyar shinkafan tayi tare da daurayewa ta zub da ruwan sai da ta wanke shi sosai ta tsiyaye ruwan ta’ajiyeshi a gefe. bude miyan ta da yake ta tafasa tayi tare da juyawa sannan ta zuba nikakiyan agusin ta a ciki rufewa ta sake yi sannan ta dauki shinkafan ta data wanke tafara zubawa a ruwan data sa da yake shirin tafasa, gama zuba shinkafan tayi da hanzari ta koma kan miyan, ludayi tasa ta juyashi sosai kana ta dauki Dandano, Curry, tyme, garlic powder da gishiri yan daidai ta zuba sake juyashi tayi sannan ta rufe tukunyan.

daukan gandan ta data yanka shi kanana tayi ta sake wankewa tare da bude miyan ta zuba aciki, Cat fish din ta ta dauka Wanda ta wanke shi da ruwan Dumi da gishiri ta zuba aciki hade da naman juyawa tayi sosai ta sa murfin tukunyan ta rufe sannan ta duba tuwonta da yake ta tafasa tare da bude murfin tukunyan kadan sannan ta rage wutan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button