HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Wankaken Ganyan Ogun din ta ta dauka ta zuba a cikin miyan tare da rage wutan sosai.

Tuqa tuwon tayi sannan ta Dan yayyafa ruwa saman shi ta sake rage wutan can kasa.

Tarkacen data bata tafara tattarawa tanufi gurin wanke wanke dasu ta wanke su

share kicin din tayi tare da goge duk inda ya baci. Ko ina yadau haske.

Umma data fito wanka take shiryawa Cikin doguwan riganta na atamfa daya samu dakin daya dace dazanan zanin sannan ya kuma amshi fatar jikin ta tare da boye shekarun ta.

Kamshi ne ya cika mata hanci murmushi tayi tare da furta Allah ya miki Albarka Ummu Aimana ya baki miji nagari wanda zai daraja ki ya azurta ki da zuri’a masu Albarka.

Ni dai a hankali na amsa da amin kar tajiyo ni.????????

Karisa shiryawan tayi ta fito ta sameta ta sauke miyan a wuta tana kokarin ajiyewa a gefe.

Kamshin turaren humran umman nata ne yasanar da ita karisowan nata, juyowa tayi tare da kallon ta kana tace

Umma kin fito?

Eh’ Na fito Aiman Sannu da aiki kedai
Lallai yau babanku zai baki tukwici tun kan inyi test na San yayi dadi Dan kamshi ya cika hancina.

Murmushi tayi Cikin jin dadin yabon mahaifiyar nata.,

Toh Umma nagode ta fada.

Yanzu kizo kije ki shirya kafin yaran nan su dawo daga makaranta .

A’a Umma ki bari in karisa kinga na ma tuka tuwon kwashewa ya rage.

Toh sannu ke dai da kokari je ki shirya na kwashe miki.

Ba ta sake jayayya ba ta amsa da toh Umma amma kiyi a hankali Dan kwaliyan ki yayi kyau kar ki bata baba bai gani .

dakuwa ta dungula mata ungo na ki tare da kai mata hanu zata make ta dariya ta sa tare da fita a kicin din Cikin hanzari.

Itama dariyan take yi Dan tasan halin Yar nata da son barkwanci Wanda har Baban ta bata gyale ba.

Zan kama kine ai na zama kakan ki ko Aiman itama dariyan take

Toh Umma daga yabon kwalliyan ki sai nayi laifi

Cikin dariyan itama tace a garin ku haka ake yabo?

Daki ta nufa tana mai furta Allah ya huci zuciyan ummana.

Ba ta jira cewar taba ta shege tana dariya.

Gyada kai tayi tana dariya Aiman kenan inbaki zolaye mutum ba bakya jin dadi kedai Allah dai ya miki Albarka.

Tana shiga dakin ta rage kayan jikin ta, ta fada toilet ruwa ta watsa kana ta dauro alwala ta fito.

zama tayi gaban dressing mirror tana shafa mai, Masallacin dake saman anguwan su ne suka fara kiran sallah,

Agogon dake jikin dakin ta daga kai ta kalla lokaci ba wuya daya saura minti ashirin har tayi a hankali take maganan.

Shiryawa tayi Cikin Riga da wando na Pakistan masu kyan tsari da daukan ido fari da baki sai adon dake gaban rigan da fararen stone.

Bata tsaya yin wani kwaliya ba powder kawai tashafa kana ta gyara giran ta tare da shafa lips stick sai kwalli da ta zizara a idonta.

Shinfida Sallaya tayi tare da daukan hijab ta sa domin ta gabatar da sallar azahar

Sallamar baba da ta jiyo ne ya dakatar da ita tare da nufan tsakar gida da sauri.

Cikin farin Cikin dawowan mahaifin nata ta taryeshi da fara’anta baba sannu da dawowa.

Kallon ta yayi Cikin nuna kulawa da murnan ganin na ta shima ya amsa.

Yauwa Ummu sannu!

Ina wuni baba ta durkusa tana gaishe

Lafiya lau Ummu ya gida

Lafiya lau ta amsa.

Kuna nan lafiya koh.

Lafiya lau Baba.

Toh Masha Allah Umman naku bacci take ne banji motsin ta ba

A’a idon ta biyu ina ga tana sallah ne

OK yayi kyau, Su khalifa ana makaranta kenan.

Eh ta amsa Toh Masha Allah

Mika mata jakan hanunshi yayi ajiye wannan kizo mota ki tayani shigo da wasu kayan.

Hanu biyu tasa ta karba jakan tana mai risinawa, bude dakin shi tayi ta ajiye aciki, kana ta nufi kofar gida domin ta iba kayan.

Ledoji ne manya manya guda uku ta tarar ya fito dasu waje yana rufe Boot din motan.

Nuna mata ledan da hanu yayi dauki wannan Ummu bai da nauyi bude gaban motan akwai wani ledan ki dauka ki shaga dasu zan shigo da sauran.

Toh ‘ ta amsa tare da bude wa ta dauka ta hada da wanda ya nuna mata ta shiga dashi gida Umma ta tarar a tsakar gida ta taryeta tare da karban ledan hanun nata tana mai fadin ina sallah naji Baban ku ya iso.

Eh’ Umma nima nace ina ga sallah ki ke dan banji motsin ki ba.

Karisawa tayi dakin umman kana ta ajiye ledan a Palo ta juyo daki domin ta gabatar da sallar azahar.

Baba ne yakariso tare da sauran ledojin a ‘a hanun sa dakin Umman ya nufa dasu taryan shi tayi da fara’a lale marhabun Abban Aiman barka da hanya.

Ajiye ledojin yayi yana mai kallon ta da jin farin Cikin a zuciyan sa lale dai Umman Aimana da fatan na sameku lafiya.

Alhamdulillah Lafiya lau duk muke.

Dafatan kaima kana lafiya.

Dariya yayi kana yace masha Allah naga alaman hakan duk kuna Cikin annushuwa da kwanciyan hankali koh kewa na bakwa yi.

Ni gani duk na firgice rashin Ku kusa da ni.

Murmushi tayi Oh’ Abban Aimana kenan. Yanzu dai ka zauna kasha ruwa kafin kayi wannan maganan.

Shima dariyan yayi kana ya zauna a kujeran yana mai fadin Bismillah abakin shi.

Murmushi tayi kana ta wuce kitchen tare da dauko mai ruwa mai sanyi tasa a Dan madaidaicin tray kana ta sa cup ta fito ta nufi dakin da sallama.

Wa’alaikis sallam ya amsa tare da dagowa ya sa idon shi a kanta karisawa tayi gaban center table din dakin ta ajiye tray din akai ta dauki cup din ta zuba Tare da karisawa kusa dashi ta zauna tana mika mishi.

kin karba yayi tare da bude bakin shi yana mata alaman ta bashi a baki bata tsaya ja ba ta sa kofin a bakin shi ya bude makogaro ya kwankwanda ma’ishi daga kai yayi yana mai furta

Alhamdulillah.

Nagode hajiya ta tun da na tafi bansha ruwa mai dadin wannan ba.

Murmushi tayi tana mai jin dadin maganan uban yayan nata.

Hanu tasa ta cire hulan dake kansa tana cewa ka dauki rana bazan rage maka wannan kasha iska.

Shima murmushin yayi tare da furta nagode. Allah ya miki Albarka.

Amen ta amsa.

Mikewa tayi tare da kama hanunshi muje ka watsa ruwa ko zaka wartsake nasan ka gaji , tashi yayi ya bita,

dakinshi suka nufa ta hada mishi ruwan wanka kana ta taimaka mai ya rage kayan jikin shi.

Raka shi tayi har Cikin toilet sannan ta jawo mai kofa ta rufe.

Cire mishi
Riga mai guntun hanu da wando na kanana kaya marasa dauyi hade da singlet da boxer tayi ta ajiyasu kan gado tare da feshe su da turare kana ta fita ta koma kitchen ta hado mai abinci.

 

_Love you my fans_❤????????

 

_*Sumiee B.*_
[15/09, 7:04 pm] Sumiee B.: ????

????????

???????? ????

???????? ????????

Typing…..✍????

????‍❤‍???? *AMINTA* ????

_Na_

Sumaiyya Babayo     Abdullahi.
(Sumiee B.)

Follow me on
Wattpad @ Sumiee_b

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

~*We are bearer’s of so golden pen*????~
*~we write assidiously perceive no pain,~*
*~So magical Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????savour our words, for it will cause you no pain.~*

*SADAUKARWA*  _Ga Aishatu Babayo Mrs Abubakar yakubu (Danjuma Master)…_
_Allah yakara dankon kauna da fahimtan juna yabaku zuri’ah masu Albarka! Amen_

******************************

Typing…….????‍????

???? 15/9/2019

Nigeria ????????

????3:38pm

_*Bismillahir Rahmanir_ Rahim………….✍????* _

_Page_ 1⃣1⃣ & 1⃣2⃣

Bayan ta idar da sallah ta dauki papers din da Umma ta bata ta fara marking dinsu.

Muryan Aminiyar na ta jiyo a tsakar gida suna gaisawa da Umma.

Cikin farin Cikin ta duro a gado tare da nufan kofa domin ta taryo ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button