HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Runguman juna suka yi cikin doki da murnan ganin junan su.

karasa shiga cikin dakin, suka yi da murmushi dauke a fuskan su.

A bakin gado suka zauna Nana tace kaga teacher wayannan papers din fa da kika baza. Cikin murmushi ta amsa INA rage ma Umma aikin su ne.

Owk yayi kyau.

Kin dauko rana fa tawan bazan kawo miki ruwa, da abinci ni kaina yunwan nake ji amma ke nake jira muci tare na san kina tafe.

Lallai kin kyauta my besty nima shiyasa naki ci nasan zaki jirani, Alkawarine wannan.

Dariya suka sanya sannan ta fita zuwa kitchen, abinci ta hada musu ta sa a tray

Ta je ta a jiye, komawa tayi ta dauko ruwa da zobo a jug hade da cups.

Baby ne ta shigo da gudu ta na fadin Oyoyo baba Oyoyo baba kadan ya rage suyi karo, kallon ta tayi ta na girgiza kai

Hoo my sister sallaman kenan yau kuma. Ina kika baro su Khalifan?

Cikin haki take magana aunty na hango motan baba ne shine na rugo da gudu na barsu a baya.

Dariya tayi toh lallai Yar kanwata. Yanzu kije ki cire uniform kafin Baban yan fito ko good girl.

Toh aunty shigewa daki umman tayi., itama ta shige dakin su….

Taso taso kiga, a hanun nake tafada tana karasa shiga cikin dakin

Cikin murmushi ta taso ta nufi toilet din dakin ta wanke hanun ta tafito, itama shiga tayi ta wanko hanun nata.

Tsakiyan dakin suka baje suka fara kwasan girki. Nana kam sai zuba santi ake kawar nata na mata dariya.

A haka suka karasa cin abinci, shigowan Faty ya sa suka dakata da hiran dasu keyi.

Zo ki kwashe kayan nan Faty ki kai kitchen, toh ta amsa sannan ta karaso ta fara tattara kayan ta nufi waje dasu.

Fira su suke irin na amintatun aminai Cikin nutsuwa da farin ciki…

Wayan ta dauka tana latsawa kar in manta kawata tura min complete Qur’an qira’an Abba Zaria nasan kina dashi.

Allahu Akbar Aiman ta furta lallai kawata an musulunta yau ke ce ki ke Neman qira’a a wayan ki har ma complete Quran naji kike fada.

Kinji ki dai yoo dan na tambaye ki ne kike wannan maganan har da kabbara sai kace wanda nace ki bani Kalmar shahada zan shiga musulunci.

Toh my kawas ai Sanin hali ne a kace yafi Sanin kama, Amma naji dadin jin hakan.

Ni dai bani kiga kafin ki tsaya jawo min aya….

Uhumm gashi ta mika mata, budewa tayi ta fara turawa.

Cigaba da hira sukayi.

Abba ne ya turo kofa ya shigo da sallama a bakin shi.

Wa’alaikum salam.

Suka amsa mai a tare

Ina wuni Aunty Nana ya gaishe ta

Lafiya lau ta’ amsa Abba ya makaranta.

Lafiya lau ya bata amsa

Aunty wai ki zo inji Umma toh ta amsa ina zuwa baba ya fito ne, Eh ya fito

Mikewa tayi tace muje Ku gaisa da baba toh ta amsa tare da mikewa, Amma bani hijab nasa.

Dariya tayi lallai fa wannan Matan wai wannan canje canjen da nake gani a gunki fa. Ni dai ki bani ba nason dogon magana.

Imban sa ba kinfi kowa damuna da ki daina kaza kiyi kaza nayi kuma kinsani gaba da magana….,Allah ya huci zuciyan gimbiya.

Murmushi tayi Yo ai ke din ne wani lokacin. Itama murmushi tayi tare da mika mata hijab ta karba tasa suka fita.

Dakin Umma suka nufa inda baba yake zaune su khalifa suna kewaye da shi.

Da Sallama suka shiga, Nana ne ta durkusa kasa ina wuni baba

Cikin sakin fuska ya amsa mata gaisuwan

Lafiya lau Nana Khadijah ya gurin su Baban naki da mutanen gidan.

Lafiya lau. Baba toh Alhamdulillah. Allah ya muku Albarka.

Amen ta amsa tare da mikewa tana mai jin dadin aduan nashi ta wuce.

Nuna mata ledar dake gefe tayi dauki wannan Aiman kije ki raba a kitchen ki bawa kowa nasa.

Toh ta amsa tare da dauka ta nufi kitchen din dasu bude ledan tayi, kaji ne gasasu a ciki guda biyar kujera ta ja ta dauka tare da fara Rabonsu.

Bangaren nana kuwa da ta Koma dakin ta tarar qira’an ya gama shiga ci gaba tayi da ture turen wasu karatutukan malaman Sunna da suke ciki na audio.

Hotunan ta shiga…Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun ta furta mumunan gamon da tayi Cikin cameran nata.

I can’t belief diz ta furta tare da sake duba hotunan cikin kidima, details din hoton ta duba, just yesterday ta sake fada Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un hawaye ne ya biyo idon ta tare da furta

Why Ummu Why please?

What is wrong with U please?

Har yaushe Salim ya sace zuciyan ki haka da har ya canja ki kika zama irin shi, me kike nema a rayuwan ki haka da har zaki biye masa.

Sambatu ta cigaba dayi ita kadai hawaye na bin kumatun ta.

Ummu da ta gama rabon ta dauko nasu a plate ta nufi dakin tana mai sallama ganin halin da kawar nata take ciki ya sa ta firgici gaban ta ne ya fadi tana karasa shiga Cikin dakin take tambayan ta

Mai yake faruwa ne besty. Mutuwa a kayi ? Karasowa tayi ta ajiye plate din hanun ta tare da kai hanu ta taba ta.

Nana da idon ta yake a runtse sai hawaye ne yake sauka da shashekan kukan da take bata ma San ta shigo ba sai data kai hanu ta taba ta.

Bude idanuwan ta tayi da suka rine suka yi jajawur abinka da farar fata.

Kallon idon ta data yi yakara hadasa ma zuciyan ta bugawa da karfi dan baza ta iya tuna yaushe ta ga hawayen kawar nata ba domin ba Abu karami bane yake sata kuka.

Hanu ta kai zata goge mata hawayen dake kwarara kaman an bude fanfo, kama hanun na ta tayi tare da furta kar ki ta bani.

Cikin mamaki takalle ta! Ci gaba tayi kar ki sake ki ta bani Ummu sakin hanun ta tayi tare da mikewa ta dauki gyalenta da jakan ta.

Shan gaban ta tayi me kike shirin yi ne Nana mai yake damun ki ne menene ki fada min.

Ban Sani ba uwata matsa ki bani hanya in wuce, bazan baki hanya ba ta fada itama idon ta ya ciko da kwalla.

A tahirin kawancen su basu ta ba. Samun matsala har su kai ga samun sa’insa ba.

Amma mai yake faruwa da lokaci daya ta canja mata.

Ratsawa gefen ta tayi ta wuce Cikin hanzari ta ri gata karasawa jikin kofan, key din dake jikin kofan ta murda ta rufe tare da zare key din a hanun ta.

Ki bude min Ummu ki barni inji da abin da ya yake damu na.

Itama hawayen ne ya fara gangara a fuskan ta, haba Nana meye zai dame ki bai dame ni ba ki fada min abin da yake faruwa dan Allah karasa maganan tayi tare da fashewa da kuka.

Dauke idon ta tayi a kanta tare da karasawa Cikin dakin wayan ta dauko tare da cire ta a key ta mika mata tun kan ta karba gaban ta ya fadi shikenan ta gani!

Kasa motsawa tayi daga inda take tsaye, ki karba ta fada. Shiru tayi tare da sakin wani sabon kuka, ganin bata da alaman karban yasa ta karasawa inda take tare da mika mata bata karba ba sai bin screen din wayan da tayi da ido ganin hoton su Na jiya gurin birthday da Salim ya kwato ta bayan ta tare da sakalo qugun ta da hanun sa idon sa a lunshe bakin shi yana sumbatar wuyan ta murmushi ne dauke a fuskan ta.

Har wutan jikin screen din ya dauke bata iya motsi ba.

Ajiye mata wayan tayi jikin dressing mirror sannan tace yanzu zaki iya bude min kofa in tafi.

Durkusawa tayi tare da riko hannayen ta

Dan Allah ki gafarce ni duk duniya idan har ke baki fahimceni ba babu Wanda zai fahimce ni kimin uzuri wallahi…..

Daga mata hanu tayi tare da daka mata tsawa

ENOUGH!!! Ummu

kar ki sake raina min hankali mana Wanda ki kayi ma ya isa haka, me kike dashi daza ki fada min in yarda dake. ni dake mukayi maganan nan waye bai San Salim ba a Cikin garin nan da kewaye, waye bai San halinshi ba, ke da kanki shaidace tun fari haduwan Ku dashi sai da Na nuna miki hakan a she jina kawai kike kina dauka Na Yar iska kin biyemai kuna sheke ayanku,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button