HAUSA NOVEL

AMINTA Complete Hausa Novel

Ina ilimin naki Ummu ?

Ina Sanin ya kamatan ki?

Ina Tunanin ki?

Ina Tarbiyan da aka Baki?

Wallahi kinci Amanan su Umma kin ci amanan *AMINTA* kinci amanar musulunci kuma ki Sani wallahi Allah bazai barki ba, ya kike Tunanin idan su baba suka ga ko jin abin da kike zasuji me kike Tunanin zai biyo baya me yake damun ki ne wai ta karasa maganan ta Na fashewa da kuka itama da tun da ta fara maganan take kuka kaman ranta zai fita.

Dan Allah ki fahimce ni wallahi ni kaina abun nan yana damuna nasani tabbas Na boye miki wannan tarayyan Na mu da Salim , wallahi bansan mai yake da muna naba soyayyar shi yayi galaba akaina tabbas nasan A rayuwa Na ban taba shiga jarrabawa makamanci irin haka ba Amma nayarda da hakan a matsayin kaddarata Na rayuwa.

A fusace ta sake daga mata hanu malama karki ma kaddara sharri dan Allah haka ne kaddara idan har zan amshi uzurin ki Na soyaya toh meye gamin soyaya da ZINA kina Yar musulma. Mai ilimin addini Wanda ake mata kallon Mai hankali da nutsuwa.

A razane ta dago ta kalle ta jin Kalmar zina da ta jefe ta dashi girgiza kai tayi wasu zafafan hawaye suka sake bin kuncin ta.

Haba Nana yanzu abakin ki nakeji wannan kazamamiyan Kalmar kike jefana dashi.

gyada kai tayi sannan ta cigaba da magana ban karyata hoton dakika gani ba amma kisani lalacewa Na bai kai har in aikata zina ba ina kuma Neman tsari da shi.

Kallon ta tayi tana mai share idon ta bude min kofa zan tafi

kiyi hakuri bazan bude miki ba har sai kin saurareni tare da fahimta Na.

Kar ki bata min rai Ummu ki bude min kofa nace sannan kisa aranki daga yau kar ki sake sawa aranki kin Sanni kisani babu ni babu ke ki manta ni acikin rayuwanki.

Nima kuma namiki alkawarin shafe ki Cikin rayuwana, ki koma kirike feedy da feena ku cigaba da jin dadin rayuwanku.

Jin kalaman ta tayi kaman ana sauke mata wani Abu akai. Kwakwaran motsi ta kasa yi…

Isa inda take tayi tare dasa hanu ta fisge key din a hanun ta……

 

_*Sumiee B*_
[16/09, 10:54 pm] Sumiee B.: ????

????????

???????? ????

???????? ????????

Typing…..✍????

????‍❤‍???? *AMINTA* ????

_Na_

Sumaiyya Babayo Abdullahi.
(Sumiee B.)

Follow me on
Wattpad @ Sumiee_b

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*

~*We are bearer’s of so golden pen*????~
*~we write assidiously perceive no pain,~*
*~So magical Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????savour our words, for it will cause you no pain.~*

*SADAUKARWA* _Ga Aishatu Babayo Mrs Abubakar yakubu (Danjuma Master)…_
_Allah yakara dankon kauna da fahimtan juna yabaku zuri’ah masu Albarka! Amen_

*JINGINA* _Ina jin dadin comment din ki Amina Bala Z( Mieynerteey) Allah ya kare uwata ya kuma raya lil bro dina Cikin aminci da rayuwa ingantacciya_ *Amen*

*GAREKI* *AYSHA ABUBAKAR HUSSEIN na group din( jinnul ashique) Takwara na*SUMMY LAWAN* _sharhin ku nasa ni farin ciki kuci gaba da gashi…._????????I love You wujiga wujiga ????????????

_Ina jin dadin aduan ki Ummu Isma’il (Mrs Idris Muhammad Bawa) Uwar gida sarautan Gida ???????? Allah yakara girma._

******************************

_*Bismillahir Rahmanir_ Rahim………….✍????* _

Typing…….????‍????

???? 16/9/2019

Nigeria ????????

????7:33am

_Page_ 1⃣3⃣ & 1⃣4⃣

Key din tasa ta bude kofan Su Faty ta tarar a tsakar gida da alamun suna shirin fita wani gun, kan ta karasa fita Cikin dakin Umma ne ta fito tana jawo kofan daki Juyo wa tayi A’a Nana ba dai tafiya ba zaki yi ba,

Sunkuyar da kai kasa tayi.

Tare da amsawa Eh ba tafiya zanyi ba wai dama zamu leka Gidan Aunty Safiya ne ( kanwar maman ta da suke bayan anguwan su).

OK toh gashi muma zamu shiga Channel 7 mu duba hajiya baba yanzu akayi waya bata ji dadi ba.

Ayya Allah yabata lafiya! Amen ta amsa

Ina Aiman din!

Juyawa tayi Cikin dakin ta hango ta tsaye inda ta barta sannan ta juyo gun Umman ta shiga bayan gida ta bata amsa.

Toh shikenan in ta fito kya fada mata ku jira idan muka dawo sai kuje dan baza mu Dade ba.

Toh Umma kudawo lafiya a gaishe ta.

Amen, zata ji ta fada tare da yin waje dama su duk sun riga da sun fita.

Ta na tsaye har Umma ta fita ta ja kofan gidan ta rufe.

Cire gyalen ta tayi tare da ajiyewa kofan dakin, buta ta dauka ta nufi toilet din tsakar gidan ta kama ruwa ta fito ta daura al’wala.

Shiga dakin tayi domin ta gabatar da sallah la’asar da aka riga aka idar basu samu yi ba dukan su.

Jiyo motsin ta tayi a toilet din dakin alaman ita ma tana al’wala, bata tsaya jiran ta ba ta saka hijab tare da shimfida sallaya ta fara gabatar da sallah.

Itama da ta fito rabawa tayi ta gefen ta ta wuce ta dauki wani sallayan ta shimfida.

Sun kai minti biyar da idar da sallan amma ba Wanda yace ma wani komai, sannan ba Wanda yayi yunkurin tashi da ga kan sallayan.

Kowa da abin da yake Tunanin a zuciyan shi Aiman ne ta kawar da shurun da fadin Nagode kwarai Nana da baki bari Umma ta fahimci abun da yake faruwa ba.

Jingina da jikin gadon tayi tare da runtsa idon ta Zuciyan ta yayi sanyi ba laifi ta samu nutsuwa da tayi sallah.

Tausayin kawar nata taji Na tuno furucin da ta mata dazu cikin bacin rai.

Bude ido tayi ta kalle ta tare da furta kiyi hakuri dazu da Na ki sauraron ki Kin bani mamaki mutuka da abin Dana gani kuma naji bakin ciki ganin hakan.

Amma ina so tsakanin ki da Allah ki fada min abin da yasa har kika biyewa Salim haka. Kuma kiji tsoron Allah kar ki min karya duk da ni zan bada shaida akan ki Na fadan gaskiya amma ganin wannan ya samin wasi wasi a zuciyan Na akan ki Ummu.

Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juyo tana fuskan tan ta tace Na miki Alkawarin fada miki gaskiyan abun da yake furuwa.

Cigaba tayi da magana, Tun farkon haduwan mu dashi a wajen graduation Waliman Peace International Academy da aka gaiyace school din mu Sannan MSSN suka turamu domin mu representing din makarantan mu.

Muna cikin Uniform a lokacin da a ka kira daya daga cikin representative Na makarantan mu dayazo ya gabatar da recitation of the Holly Quran.

Wanda a lokacin ke kika sa ni fita inje inyi duk da bani da niyya naso wani yaje amma kika sa ni fita.

A yanda ya bani labari shikuma ya jema cousin sister dinshi ne domin tana Cikin graduate din.

Fita Na dafara karatu Na yaja hankalin shi kaina Wanda yasa ido a duk motsi na har aka tashi taron, bayan an tashi shine ya biyo mu tare da zuwa ya mana magana a lokacin muna tsaye dasu feedy da suma kawar su ce ta inviting dinsu.

Bamu bashi fuska ba ganin rashin nutsuwa a tattare dashi sannan yanayin suturan jikin shi bana mutunci ba, nan take kuma tabbas a lokacin banji haushi
Yin hakan ba.

Amma wallahi tun daga lokacin Dana fara daga ido na kalleshi naji gaba na ya yanke ya fadi.

Mun dawo Gida, ashe ya bi su feena ya musu magana anan Feedy ta bashi namban wayana na.

Bai kirani nan take ba sai da muka yi tsawon sati biyu acewar sa abin da yasa bai kira ba a washe garin rannan yayi tafiya zuwa Ghana gurin uncle dinshi tsawon sati biyu shiyasa bai kirani ba har sai da ya dawo.

Idan zaki tuna daga San da muka je graduation din nan da kwana biyar na kwanta rashin lafiya Wanda an kasa Sanin mai yake damuna munje asibiti an yi su test ba abin da aka gani, har hajiya baba tace ko nayi gamo ne aka koma na gargajiya Umma kuma ta dage damin adu’a da karatun qurani!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button