ARNE

Farace Sol ,tanada kyw Nagani nafada,..sai dai arziki da rurin mallakar duniya tasa ta zarmewa cikin tsananin son abun duniya
Hajiya mariya bata haihu da wuri a gidan alhaji ba kasancewarsa mai wahalar zama waje daya da kuma Kaddaran Allah…
shekarunsu na hudu da aure ne Allah ya fara bata haihuwa nan aka samo zafar.kafin faryal da ta fito bayan shekara 4 da haihuwar zafar….
Farare ne sol ga bakin gashi yaleyale mai tsayi kwnce akansu sai manya manyar idanunsu,,in kagansu ma zaka dauka yaran larabawa ne…
,taso ta sangarta su da son nuna abun duniya da sakalci irin na yaran manya
amma ena ‘enna salima mahaifiyar alhaji da shi kanshi alhaji sun Sha karfinta wajen tarbiyartar da yaransa
Don’ kuwa ilmin addini ya fara nema musu a gida tun suna kanana sosai ana musu kamr lesson, da malaminsu malam mamman wanda yake zuwa
Wekend tun 10na safe
Faryal duk da ma ita karama CE shekarunta 9 a duniya kawae amma Allah ya azurtata da tausayi da kaifin basira, tanada taurin kai amma zuciyarta Nada saukin tarairaya…
Ga shi Allah ya bata ilimi domin har takara suke da yayan ta wajen daukar karatu…..
Sun girma cike da kauna da tausayin junansu,
nasihohi da wa:azi. Da malam mamman ke yawan musu na mussamman shine yayi tasiri akan Dada gyra tarbiyansu da nagartan su
Domin kuwa Alhji abdullhi ya umurce shi da ya ware lokaci na mussamman na koya musu dabia bisa ka idodin musulunci da basu tarihin akan
halayen manzon Allah SAW.
Komai tare ake musu gurin bacci ne kawae kowa da nashi
dakin.
Surayyahm.s????✍????
: ????????????????????????????????????????
????ARNE????
????????????????????????????????????????
????by????
Surayyahm.s????
*AM££NCI WRIT£R’S ASSOCIATION????✍????*
Page21-22
Waya takeyi ko zama batayi ba
Shafa atu,kedai bari ni wallhy na Shiga uku bakin ciki zai kashe ni a gida na
Meyafaru haka mariya? Kinsan ba abunda a isa ya Sha miki gaba ena duniyan nan kam
Fada min me yafaru
Hmmm shafa_ kinga yadda alhaji ya zuba kudi ma yaron nan Yau a mall kuwa?
Ke kyace shi ya haifesa
Kikace mene?lahhhh ha ila ha illalahu …..
Chab…… mariya a idonki ake wannan jihadin wutan ,lallai kam
ai dama na Fada miki ba kin tsaya Sanya ba ai kwanan nan ma za amance da yaranki a Daura sa akan komai
Kut ,dan Allah dena fadar wannan maganar shafa ..Chab di jam….da kuwa tabbas akuya za taci block
In ban kashe shi ba,shidin wa? arnen banza dan wuta?
tafada tana faman huci
Hmmm toh nidai na Fada miki,ki kara dammara in ba haka ba kuwa zakice na Fada miki
Toh haj shafa ya zanyi yanzu mafita nake so kawae
Kinga yanzu alhaji na annual leave dinsa
Kullum yana gida
Gashi al amarin alhaji ne yanzu sai ahankali shi fa duk lokacin da na kawo maganar yaron nan baya saurara ta
Wai ban isa na taba yaron nan yana nan ba fa
Ke mariya ,ki kwantar da hankalinki cikin satin nan zan zo zamusan abunda zaayi
Yawwa shafa ko naji magana.ki taho ma akwae abubuwan Dana dauko miki kema
Shewa shafa ta buga daga cikin wayrta tace tooooo kawata an gode sosai sai na zo din
Cikin dakin alhaji zaune suke a kan white fairy chairs dake zagaye a wajen an masu kwalliya da jajayen throw pillows
,
Hannu ya miika ya dauko wani carton dauke da kwali madaidata guda biyu
Kowa ya mika masa i yace musu suyi amfani da shi….
Wayace kirar iPhone bakake guda biyu,sannan ya ciro bandir din kudi yan 500 ya basu
Kowa ya ajiye a drawer sa
ware ido waje raphael yayi, da Sauri
Yayi Kasa ya tsunguna ya fara godiya har hawaye sanda yayi
Banace banason kukan nan ba raphael ,
Zafar tashi kuje ku kitmsa gobe fa zai fara binku makaranta..
Da safe karfe 7.30 driver ya ajiye su a new Nigerian international sec schl
,suka nufi kan assmbly sit kowa sai kallon raphael yake musamman ma da yake basu taba ganin zafar da wasu ba kullum su biyu ne da faryal dinsa
Zama kowa yayi akan sit dinsa a assembly hall aka gama musu vayani kamar kullum
Khalid wani dan ajinsu zafar ya taba shi,hey dude wannan bro dinka ne haka?
Hhhhhh khalid me ka gani?
He look like u guys but not exactly yafada yana kashe ma faryal ido
Tsaki taja ta dauke kanta,shegen gulma kawae
Yes he’s my bro ,meet him
Nan Khalid ya mika wa Raphael hannu yana masa wani kallon raini am Khalid garba and u?
Murmushi raphael yayi yace Hey Khalid. , ya juya kansa
Tabe baki Khalid yayai yace wow ,a snub! welcome to d new world….irinku muike so
Nan aka fara Shiga aji kowa ya wuce yaje ajinsu ,raphael na ssic zafar na A
Eta kuma faryarl na jss1A
Surayyahm.s????✍
: ????????????????????????????????????????
????.ARNE????
????????????????????????????????????????
????by????
SurayyaM.S????
*AM££NCI WRIT£R’S ASSOCIATION????✍????*
Page 23-24
Haka rayuwa ta cigaba ma rphael a gidan alhaji abdullhi,idan yana gari saukinsa idan baya nan kuma hatta makarantar Hajiya mariya bata barinshi ya leka
Idan ma yasamu yaje toh itada kanta zata CE zata dauko su,haka zata barsa awajen yanaji yana gani sai dai ya biyo motar haya ya dawo
A makaranta kuwa shakuwar faryal da Raphael ya fi nunawa,saboda ko break ne wajensa take fara zuwa kafin zafar ya fito
Duk da sa idon da sauran yan aji Duke masa,hakan baisa raphael jin wani abi aransa ba duk da ma yasan ba yaron da bayaji da Kansa a makaranta
Musammamn ma khalid da ya sa ma kahon zuka
ga raini da Nuna arziki,sai dan kadan daga cikinsu ne masu nagarta da sanin mutunci mutane
Ranar vocational activities kowa ya Santa kayansa na sports,
Faryal CE a gefe tana kokuwa da gashin kanta da yaki zama cikin p cap dinta
Yaya zafar gyra min mana tafada Lamar zatayi kuka
Ke kincika fitina bakinki kiyi kawaye ba,ai ba Daura miki da zanyi ,ni ba dan aikin ki bane
Turo bako tayi tace ohh haka ne ko? Kaima zaka zo watarana
Nan ta wuce wurin raphael da tun tuni yagama shirinsa kallonsa kawae ta tsaya yi batace komai ba
Faryal ya dai kinda min ido fa?banyi kyw ba ko, murmushi tayi
Daura min kaji? Tafada tana lankwaso muryanta
Toh juya na Daura miki,nan ya kamo suman ta ya daure mata kamar pony tail,(a tattare gashin kamar chuku sai a bar dan kadan ya sauko ta gaba)
Itama tayi kyw sosai,kanta yayi kamar Ariana grande,still batace komai ba ta juya tana kallonsa,
Waro mata idanu yayi yace oh my GOD menene kuma
Kyal kyalewa tayi da dariya tace babu
Zafar ko ko kallon su bayayi hankalinsa yana kan wasannin da ake
Suna cikin tadin shirmensu ne cike da jin dadi da raha,
Yaji an buga masa ball akan hanci…..take jini ya biyo baya
Ya raphael faryal tafada da dan karfi ta mike zata taba shi
Ke,taji an finciko ta,bana hanaki dariya da maza ba,meyasa baki ji,taurin kanki fa yafara isa na faryal
Kut kaidin waye ? Bansanka ba ai,kaga Malm banason rainin wayo tafada tana watsa ma Khalid harara
Raphael baice komai ba illah kokarin goge stain din dake bin hancinsa
Come on sis je ki kira zafar time ya kusa
Zanje na wanke ku sameni a cahn,kama hanya yayi zuwa wash room batare da ya kalli Khalid ba
Itama wucewa tayi tabarsa awajen, a mirror ya hangi Khalid a bayansa ya shi go washroom din shima
Kai dan wahala,me kakeji da shi? Nifa nasan kai ba asalin dan alhaji bane adopted ne
So? Raphael yace
So kadaina kusantar faryal because she is mine,nikadai idan ba haka ba jikin ka zai gaya maka …..