ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa Novel

bintavyayi da kallo daga bisani yavgirgiza kai yana fadin

“Yau naga takaina mama ta hadani da wannan yarinya *jangwan*????”

Shigewa yayi motar yadau wayarsa xe kira hydar jin anna buga dayan glass din gefen seat din murmushi yayi yasa hannu ya bude masa yashiga..

“ya harkun gamane?”
“mtsw kyaleta kudi takeso kuma ni bazankashe kudi na a auren da banaso ba”

murmushi hydar yayi tarevda fadin

“Wai kai meyasabaxaka hkra ba kawai ka bata tayi abinda ya kmt”

“toh kai inka matsu ka bata mana zaka wani takurani”

shiru sukayi dikkansu har yakai hydar gida ya saukesa shima ya nufi gida…

Dasalama ya shiga palo ummi da mama ya tarar zaune …

“Inna wuni mama”
“lafiya lau sadeeq harka dawo?”?
“tih masha Allah”

“ya sadeeq sannu da zuwa”

“yauwa ummi ya gidan”

“lafiya lau yaya”
“hk akeso barivna shiga ciki”

“sadeeq kaje kungana da asama’u kuwa”

“eh mama daga can ma nake”

washare baki mama tayi tare da fadin masha Allah kaje babanku na nemanka…

amsawa yayi da toh ya nufi dakinsa aransa yana fadin

“narasa me mana tagani agun husna hm Allah dai ya sa hkn shine mafi alheri”

ansawa yayi da ameen ya cire kayansa..watsa ruwa yaje yayi ya sauya kaya kafin ya nufi dakin baba…

dasallamarsa yashiga baba yaamsa masa..zaune yasamu baba yana jin radio..

“ahh abubakari harka dawo”?
“eh bababandade dashigowa ba”

“toh madallah dama sonake naji inji dai kagama gidan naka ko?”

“eh baba nagama painti ne ya rage shima gobe insha Allah zansa ayi*

“toh maddallah Allah yama albarka”

amsawa yayi da ameen sunsha hira sosai sewajan karfe 8:45pm kafin sadeeq yabar dakin baba ya nufi nasa…

 

???? *Husna*

Can kuwa husna nashiga gida umma dake zaune tana kallo hanan na gefenta… raibace ta samu guri ta zauna

“husna ya akayi ne?”

“umma wai kawai se ace hk xa ayi bikinan ba ko event”

“inji ubanwa?”

“ya sadeeq mana wai baze bani kudi ba”

“be isaba dan ubansa uwar tasa zankira bannidasu”

“wlhi anty husna wannan yaya sadeeq din ya fiye girmankai”
acewar hanan

tsaki husna tayi tare da fadinbanni dashi zan rage masa shi… tana kaiwanan suka jiyo sallamar yaya haneef…

dasallamarsayashigo suka gaishesa ya ansa shima ya gaida umma xama yayi alamun ya gaji…yana fuzar da iska

“husna dan Allah dan dafamin gwaten doya shinake marmarinci”
acewar ya haneef

turo baki husna tayi tana maida hankalinta ga tv

“ke husna bakiji me nace bane”

miqewa tayi tana buga qafa tanufi hanyar daki tana qunwunai…

“gsky ni ban iya girki ba…baga inna me girki can ba kaje tana”

fusace hannef ya miqe ze bita umma ta tsayar dashi tare da fadin

“xonankarka takuramin ‘ya kaje ga inna canakitchen kace tadafa ma”

“haba umma ya zaayi ace yaranan su zauna basu iya komai ba sedai a musu ahaka husnanzatayi aure?

“Inna ruwanka innace bakai zata aura ba?toh wuce kaban wuri yarana yanhutu ne”

afusace haneef ya fice ya bar palon umma tading masif tana fadin
“yarana yanhutu kuma husnar dakake fada dame aikinta zata tafi yauwa”

ahk tayita masifa hartayi shiru dankanta…

 

 

????
[2:17PM, 12/28/2016] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

*03*

 

Zaune mama take wayarta tasoma ruri dasauri ta daga ganin sunan umman husna daya bayyana akan screen din

“Assa**

“Maman ummi kinajina ko?

“Eh innaji amma kya tsaya mugaisa ko?”

“bana buqatar hkn dama inna infada miki ne ki jawa sadeeq kunne yazo ya bama husna kudin dazatayi abubuwan daya kamata ahk za ayi bikin?”

hkr mama tashiga bawa umma kafin tasaukosuka gaisa cike da fara a daga bisani sukai sallama.

Zaune mama take tsakar gida tana jiran fitiwar sadeeq…ummi ce ta fitoh dashirinta na mkrnt

“umma na tafi ”
“toh sekindawo Allah ya miki albarka ”

amsawa tayi da ameen ta fice abinta…ba afi minti biyar ba sadeeq ya fitoh shima cikin shirinsa…

tsugunnawa yayi kusa da mama

“Inna kwana mama”
“daban kwana ba zaka ganni?”
“mama laifin me nayi kuma?”
“me ya hanaka ba husna abinda take buqata kaje ka bata tinkan raina ya baci”

“mama ba kudi a hannu na ne ga aiki gida annayi ga kuma lefen da ake hadawa abubuwan sun minyawa”

nunfashi mama taja tare da fadin
“Sadeequ”

“ya amsa mata da ameen”

“kayi hkr kaji kaje ko nawane ka lallabaka bata kaji?”

gyada kaiyayialamun eh yamiqe yanafadin nizan tafi albarka mama ta samasa kafin ya tafi…

 

????

Misalin karfe 8 sadeeq ya gama shirinsa ze tafi gida ransa bace ya shiga mota beko tsaya ko inna ba se qofar gidansu husna yanaxuwa kuwa yayi sa a hanan ta fitoh ya turata ta kira masa husna ba musu ta koma tanata wani karairaya murmushin takaici yayi yarinya qarama da ita…

ya kusan minti goma tsaye agurin bata fitoh ba ransa dikinda yake battace ne…juyawa yayiya bude marfinmotarsa yajiyo muryarta tana anbatan sunansa…juyawa yayi ya shaqo wuyatan ta ya hada da jikin motarsa

“ke nikika rainawa wayau zaki shanyani a waje?”

daqyar ta somamgn samasama

“toh bakasangidan akwai mutane bane?kasakeni akwai zafi”

“bazan sakeki ba tin ynxu kinakai qarata gun mahaifiyata ko kinaso ki hadani da ita ko?”

“nifa ba***

bata qarasaba yasa dayan hanunsa ya bige bakinta daga bisani yasaketa motarsa yabude ya cito bandir din yandari biyar ya bata karba tayitana murmushi…

wani irin sansane takeji yana shiganta arayuwarta tana mutuwar san sadeeq

kallonsa tayi tana murmush

“kekuma meye hk?”

murmushi ta kumayi
“kawai inna sanka sosai bazan iyajure kamin kishiya ba”

tana kaiwa nan ta shige gida da gudu shiko binta yayida kallon mamaki

“lallai yarinyarnan ta rainani”

dagabisani kumaseya soma dariya shi kadai ahaka yashige motarsa yana driving yana tinazancen husna

 

????????

Abu kamar wasa akwana atashi ba wuya snyi prgms amma ba ko daya wanda sadeeq yaje ranar juma’ah bayan anyi sallar juma’ah aka dauraauren *Abubakar sadeeq* da amaryarsa *Asma’u husna* skan sadakinera dubu dari…masha Allah bikin yayi jama’ah sabd sadeeq ya kasance meson mutane dan hk bikinsa ma sai masha Allah….

Bayan anyi sallahr magrib akazo daukan amarya nasiha aka mata sosai hydar shine kangaba sbd shine abolin ango…

gidan iyayen sadeeq aka fara kaita can suka tarar da sadeeq aka hada hardashi aka musu nasiha sosai amma abun manakitindaaka taho da amarya ba allamun kuka ko hawaye sema in anna hira a mota tayi dariya..

goggi suwaibace ta kasa hkr tasoma fadin

“Wai ita wannan amarya bata kuka ne se dariya”

gabadaya sukasa dariya harda ita husnar kawarta ce hafsa dake gefe tasoma fadin

“goggo karki damuqawar tamu jaruma ce ai”

tabe baki goggotayi ta tsayatana kallon ikon Allah amarya ta yaye gyale anna hira…

kusan rabin hour ya daukesu kafin suka isa gidan…lullube mata fuska sukayi aka fita da ita dik da gidan na cike da mutane hkn be hana husna ganin gidan nata ba gidan yayi kyau sedai masha Allah murmushi kawai husna keyi har aka shiga da ita….

bayan ankaita da mintina aka rako ango fuskarnan tasa babu alamun fara’a atattare da ita…hk yazauna kawayen amarya da abokansa suka gama surutu suka fita bin bayansu yayi dan yimusu rakiya…nanfa suka dinga zaulayarsa har sukasa sa dariya sosai…

husna kuwasuna barin dakin ta niqe dasaurijakar dake gefenta ta dauka ta ciro turaruka da wata night gown ta nufi toilet cikin sauri..

Sauya kayanta tayi kafin ta tafitoh sadeeq ya shigo ganin bata dakin yasa ya juya ze nufi dakinsa domin watsa ruwa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button