ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa Novel

“sunanki aisha ko?”

“eh amma anna cemin shatu” nabasa ansa kanta na qasa….

“Ok shatu dan Allah innaso kimin wata alfarma ne”

“tame fa?”

“yauwa…kinga ni innada mata sunanta husna”

dasauro shatu ta dago takallesa cike da mamaki daga bisani ta sauke kanta qasa

“Kiyi hkr nasan bazakiji dadin abinda zan fada ba… matata bata da hkr balle intaji ance naqara aure bazaman lfy….dan Allah so nake kizauna a matsayin me aiki agidanan kafin daga baya sena sama miki gidanki”

Dasauri ta dago tana kallonsa dai dainan sukaji qarar door bell..

 

 

????
[10:48AM, 1/7/2017] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

 

_In dedication to_
swt????
*????Abba gana????*

fatyafreen.blogspot.com
*or*

http://fatyafreen.blogspot.com/2017/01/ashe-kishiyatace.html

 

*09*

Atsorace sadeeq ya miqe da sauri ya nufi bakin qofar

“Waye ne?”

“nine oga”!!

jinmuryar megadi yasa yasauke ajiyar zuciya shatu dake tsaye a lkcin ta riga tagama fahimtarsa…

“meya faru?”
“oga daman innaso nadanje masiyo abu na dawo ne karka jini shiru”

“toh bkm seka dawo”

yana gama fadan hk ya juya yana kallon shatu wacce take zaune tayi saurin sa kanta a qasa tana wasa da yatsunta…

“kinyi shuru bakice komai ba…kiyarda danj wlhi zan baki dik wani abunda mata ke buqata agun mijinta zan miki komai da komai..amma dan Allah kiyi hkr ki rufamin asiri kinji?”

gyada kai tayi alamun eh tare da fadin bakomai.. murmushi yayi tare da fadin bari naje na samo miki abinda zakici daganan zan daukota daga gida…

Gyada kai tayi ya miqe yana share zufar fuskarsa ita ko binsa da kallo tayi har ya fice daga dakin..

Yana fita ya shige motarsa haryakai bakin gate ya tina da me gadin bayanan…tsaki yayi ya fita ya bude gate din ya fitar da motar kafin ya rufe gate din ya koma cikin motarsa….

*Husna*

“kunga ni zan tafi saboda yaudinan sadeeq ze dawo”

“toh aikuwa ykmt kotashi kitafi tin dazu kinzauna anan”

“ynxu xantafi mama toh aban abinci na kai masa”

“jeki dau foodflask kibawa inna ta zuba abincin”

tafiya tasomayi zuwa kitchen din dake palon tadaki foodflask din kafin ta fitoh ta kaiwa inna…shinkaface da wake da miya taji kifi da nama ga kuma kayan lambu anyanka a sama…tana karba ko godiya bayi ba ta soma fadin

“dija xo muje ko se anjima zaki tafi gida?”

“a’a ynxu xan tafi nima…

sallama sukawa umma suka fice abinsu…dija ce ta riga sauka kafin aka qarasa da husna har qofar gida….

 

*sadeeq*

sadeeq kuwa tinda ya fita ya nufi restaurant ya musu takeaway na abinci harda na husna …. gidan mama ya fara zuwa

“ahh sadeequ yaushe agari”

mama ta fada fuskarta dauke da murmushi…ummi ceta fitoh tana masa sannu da zuwa…

“inna wuni mama”

“lafiya lau sadeeq yaushe ka iso ne?
” wallahi banwani jima ba”

“Allah sarki sannu sannu…ko zakaci abinci ne?”

“yaya inna tsarabar qauyen ?”

“kaik kekam da surutu kike jeki sanyo mishi tuwo yaci kafin ya tafi.”..

murmushi yayi yama umma godiya…

miqewa ummi tayi ta nufi kitchen ta fitoh dauke da plate.

“tuwon shinkafane biyan gyada…kaci muje kaban tsarabata”

“ai bazan baki ynxu ba sekinzo har gida”

“lallaikam baxani gidanka ba inje ah-**”

kafin ta qarasa maganarta mama ta bige mata baki da gudu ta miqe ta nufi daki tare da qarasa xancenta

“inje amin rashin mutunci nida gidan yayana”

murmushi sadeeq yayi mama kuwa ta fara fada daqyar sadeeq ya rarrasheta …ya rasa meyasa mama takeson husna hk…

Yana gama ci ya miqe ya na gwada numbern husna amma a kulle…

miqewa yayi yama mama sallama ya nufi gidansu husna…

da sallamarsa ya shiga ya gaida umma cike da fara’a ta ansa…

“yaushe ka dawone?”

“umma ynxu ndw dama nazo daukan husna ne”

“kash aikuwa kunyi sabani tafi qilama ynxu ta isa…”

dasauri ya miqe tsaye dik yabi ya rude

“umma bari na tafi se anjima”

amsawa kawai tayi ta bisa da kallo aranta tana fadin “toh meya sameshi?”

tabe baki umma tayi shikuwa ficewa yayi cikin sauri ya nufi motarsa yasoma driving in high speed

“kardai husna ta isa gida” “toh ynxu kar shatu tayi subutan baki tinda basanin husna tayi ba…kuma kar husna tayi wani abun na rashin hankali”

shafa gemunsa yayi tare da fuzarda isakan bakinsa cike da tashin hankali…

 

*husna*

kwankwasa gate tayi cikin sa’a me gadin ya dawo ya bude mata qofar…

“sannu da zuwa hajiya…ai kuwa oga ya fita”

“laaa ya dawo ne?”

“eh! ok nagode”

ciki ta shiga ta murda handle din tajiabude ..shiga tayi tare da cire gyalenta qoqarin jefar da gyalen take akan kujera sukai ido hudu da shatu…

sun jima suna kallon junansu ..cike da tashin hankali bama kamar husna tacika tayi famm… ahankali ta ajiye gyalen hankali da kular dake hanunta…

“meya kawo ki nan?”

husna ta fada fuskar bako alamar murmushi…kame kame shatu ta farayi

“ni ni ni matar matar!!!!

Dasauri husna ta finciko shatu…tare da zaro ido

“ke matar wa?

 

 

????
[7:11PM, 1/8/2017] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

 

_In dedication to_
*????Abba gana????*

fatyafreen.blogspot.com

 

*10*

“ke matar wa?”

“ni matar matar da aka kawo me aiki

wani irin ajiyar zuciya husna tayi tare da fadawa kan kujera ta zauna…

daga bisani ta miqe tare da fadin
“waye ya kawoki?”

cikin sanyin jiki shatu ta soma magana
“me megidan ne ya kawoni yaje ya**

kan ta karasa maganarta sukaji an banko qofa dasauri suka kalle kofar a tare

sadeeq ne ya shigo kamar wanda aka koro sa yana zare ido…

“ya sadeeq meya faru a cewar husna tare da qarasowa ta riqesa”

sauke numfashinsa yayi tariqe suka zauna shatu dai ta bisu da ido ne kawai…

kallonta ta husna tayi daga bisani ta daka mata tsawa tare da fadin

“dallah jeki dauka min ruwa na basa kin wani tsiremu da ido”

magana husna tayi tana nuna kitchen …sumi2 shatu ta nufi hanyar kitchen sadeeq ya bita da kallo ganin hk yasa ta juyovda fuskar sadeeq zuwa kallonta…

“ya sadeeq wacece wannan?”

“ba ba ke kika ce kina son me aiki ba…shine na na kawota ”

“ok daga inna kake ne hk?”

daidai nan shatu tashigo dauke da cup ta karba tare da bama sadeeq ruwan…ganin shatu a tsaye yasa husna ta daka mata tsawa

“kiwuce kije kiyi wanke wanken mana koni xan miki?”

Dasauri sadeeq ya dago suka hada ido da shatu dasauri ya saukar da kansa kasa tsabar kunya…

Dasauri shatu ta nufi kitchen tana sharar haway e
“Ita da gidan mijinta ta koma yar aiki”

Sadeeq kuwa kallon husna yayi ya riqo fuskarta

“Husna meyasa zakina mata ihu xakisa taji tsoranki ”

Turo baki husna tayi tana fadin
“to kawai se ta tsaya tana kallonka?”

dariya yayi yaja karamin bakinta ..dik abinda suke shatu na bakin qofa tana kallonsu.share guntun hawayen dake isonta tayi ta shige kitchen din….

Kallon kitchen din tayi ko inna akwai datti nanfa ta goge ta soma wanke kwanu kan ta da gama ta gyara ko inna tsaf …

Tana fitowa husna kadai ta iske palon

“Harkin gana ne?”

“eh nagama”

“tohshiga dakina gashi can ki gyara minshi”

cikin sanyin jiki ta shiga dakin ta soma gyara…

Husna kuma miqewa tayi ta nufi dakin sadeeq jin yana wanka yasa yasa ta fitoh ..ba awani jima ba shatu ta fitoh…

“shiga dakin mijina ki gyaramin kuma kiyi sauri ki gama kafin ya fitoh daga wanka…”

toh kawai shatu tace ta nufi dakin sadeeq ahankali ta tura qofar dakin tashiga da sallamarta..

ganin ba kowa yasa ta soma kauda kayan dake kan gadon wasu ajiyewa kawai take inda taga yaa mata dan batasan mazauninsu ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button