ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa Novel

tafara yaye zanin gadon kenan sadeeq ya fitoh daure da towel tana dagowa suka hada ido…

sosa kai tasomayi tare da juya bayanta tana fadin

“Dama tace ne na gyara ma dakin”

tana fadan hk tasoma tafiya zuwa qofa da sauri ya damqo hanunta

“ki tsaya kiji”

“a a gsky kabari karta sa**”

bata karasa zancenta ba sukaji anturo qofar dakin

 

 

????????
[10:22AM, 1/10/2017] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

*11*

Jin anturo qofa yasa yayi saurin saketa itama tana kokarin kwace hanunta saketan dayayi yasa ta fadi akasa gaban husna…

“wayyoh sannu garin ya hk”
acewar husna

dasauri shatu ta miqe sadeeq kuwa juyawa yayi ya waske kamar be ga abinda ya faru ba…cikin sauri shatu ta bar dakin..

Gurinsa husna ta nufa tare da karban towel din tana goge masa jikinsa…

“Nayi kewarka sosai kwana biyu”

“bayan baki damu dani ba tinda na tafi ba ki kira ba”

turo bakovtayi saboda batada na cewa dan hk ta soma kokarin juyawa da sauri sadeeq ya jawota ya rungumeta jikinsa yana shaqar kamshin turarenta …in low voice ya soma fadin

“Nima nayi kewarki sosai”

Murmushi sukawa junansu ya sunku ceta zuwa kan gado….saqoni ya fara aika mata dasu kan kace me itama tafara maida martani…

Sundauki lokuta ahaka ganin yana qoqarin wuce gona da iri yasa husna ta soma kokarin kuka tana turesa

“meya faru husna?”

“Nafadama banaso????..banaso ko”

“haba husna bakisan kina cutar dani ba kuma zaki hadu da fushin ubangiji kika cigaba da hk”

“nidai nace banaso”

tafada tare da juya masa baya …murmushi yayi tare da fadin

“toh fadamin meyasa bakyaso?ba kyaso mu haifi yaranmu ne?”

a harzuqe ta soma magana

“Cabdijan banaso”

Zaro ido yayi cike da mamaki yana kallonta…

“bakyaso fa kikace?”

gyada masa kai tayi alamun eh…

“toh fadamin meyasa”

“saboda bazan iya wahala da yara ba..kuma ni bazan bata lokacina akansu ba…banason kukansu..kaiii ni banshirya haihuwan ba”

sadeeq da tunda ta fara magana ya sake baki yana kallonta cike da mamaki….

ita kuwa tana kaiwanan ta zari rigarta a bakin qofa ta tsaya tasa kafin fice shiko binta kawai yake da ido…..

 

*washe gari*

Tinda sassage shatu ta tashi ta gyara palo tayi moping din ko inna har kitchen ta share tsakar gidan…

ko inna yayi tsaf turaren wuta da husna ta nuna mata sawa tasa ko inna ya dau kamshi….

kitchen ta shiga dan taga me ta iya dafawa…indomie ta hango murmushi tayi ta dauko ta soma dafawa ta dafa kwai hk taje ta jera musu a palo ta koma daki tayi kwanciyarta…

Sadeeq na fitowa ya ga ko inna tsaf se kamshine yake tashi murmushi yayi yasan aikin shatu ne…amma a cewarsa ba abinda ze yi da yar kauye karma ta raina sa…hanyar dakin husna ya nufa ganin tana barci yasa ya juyo abinsa….

Foodflask na abinci ya gani yana zuwa yaga indomie ce murmushi yayi zauna rabon dayashi abinci agida da safe tin lkcin da ake aiko musu da brk…

yaci indomie din sosai kafin ya tashi har yayi hanyar dakin shatu se ya juya ya fice abinsa…

Akwana a tashi ba wuya yau watan shatu daya acikin gidan amma haduwarta da sadeeq befi a qirga ba dan ya fita daga harkarta …gashi suna zaman lafiya da husna basa wani fada ta koyamata abubuwa irinsu kwalliya dan ita husna ta lura da sadeeq bawani damuwa yayi da shatu ba shiyasa harta samu karfin gwiwar koya mata kwalliya…

 

_Tuesday_

“shatu! shatu!!”

“na am anty gani”

“Zokije kiyi cefane yanma na qarayi”

amsawa tayi da toh husna tabata kudi taje ta siyo abubuwan da za ayi abinci dashi…

daukar hijab dinta tayi ta fice…tafe take taji horn din mota abayanta tsayawa tayi dan ganin waye wannan….

 

 

????????

????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

 

*12*

Tana juyawa taga wata budurwa ta fitoh daga motar fuskarta dauke da murmushi

“sannu baiwar Allah..sunana Aisha anma zakiyi iya cemin *esha* gidanmu ne wancan me blue gate din…

murmushi shatu tayi

“Laaa ai sunan mu daya… sunana Aisha nima anma anna cemin *shatu* kuma gidanmu ne agaban kusa da gidanku”

“laaa kinga sunanmu daya ga kuma gidanmu a kusa…”

murmushi dikkabsu sukayi esha ta qara da

“inna zakije ne hay mota muje na kaiki”

Nn ta fadawa esha inda zataje suka hau mota suna hira abinsu…

*Washe gari*

“Anty nagama aikina dan Allah innaso inje gidansu kawata indawo”

murmushi husna tayi

“ohhh su shatu yaushe aka fara kawaye bansani ba? hm ban hanaki fita ba adawo lfy amma karki dade sbd abincin dare”

. Amsawa tayi da toh tashiga daki tasa wasu english wears dinta da husna ta siyamata riga da skrt ta yafa gylenta ta fitoh

“Anty na tafi”
“toh adawo lfy”

Fita shatu tayi.n tana fita daidai nan sadeeq ya danno kan motar sa hango wata yayi ta fitoh daga gidan kwata kwata hankalinsa be kai masa cewar shatu bace saboda irin shigar da tayi baya tinanin shatu zatayi hkn

Itako shatu bamatasan yana zuwa ba shigewarta tayi gidansu esha…shikuma horn yayi me gadi ya bude masa….

Da sallamarsa ya shiga fuskarsa dauke da fara’a …amsawa husna tayi ta taho ta tarbesa….

zama yayi ta kawo masa ruwa tare da dauko kulolin abincin tadire masa….

“yauwa kamar kinsan yinwa nakeji..”

murmushi tayi ta soma zuba masa abincin

“husna wacece wanan ta fita a gidanan ynxu?”

dariya husna tafaryi tana fadin

“lallai yaya sadeeq…shatu ce fa me aikin da ka”**

bata karasa xancenta ba ya katseta da fadin

“shatu ce ta koma hk?”

gyada kai tayi tana fadin

“aikuwa ai ynxu ta zama yanmata”

shiru yayi ya luluqa duniyar tunani ita ko kallonta tacigabadayi

_”yanxu shatu ce ta koma haka? ya za ayi ta fita bata fadamin ba?kuma jibi irin shigar da ta fita dashi…lallai yau zanyi maganin yarinyarnan”_

Shatu kuwa tana shiga gidan palo ta nufa mumy ta ga zaune da kanwar esha da sukecewa princess(fatymah)….

da sallama ta shiga suka ansa mata cikev da fara’a tsugunawa tayi tana fadin

“Inna wuni mumy”

“lafiya lau shatu ya antyn taki?”

“lfy lau take…”

rufe bakinta keda wuya esha ta fitoh daga kitchen dauke da kwano ….

“laaaa shatu ashe dai zakizo nazata wasa kike ai”

murmushi kawai shatu tayi tana…princess ce ta soma fadin

“Anty kawarki na da kyau..”

dariya sukayi dikkansu esha taja shatu suka nufi dakinta….

Suna shiga kan gado suka hayesuka fara hira

“yauwa shatu ranar namiki tmby baki bani ansa ba”

“wace tambaya fa?”
“matar gidan yayarkice ko me?”

shiru shatu tayi

“ke abar maganar nan dan Allah”

“Dan Allah ki fadamin ko baki yarda dani bane?”

“A’a kawata ba hk bane”

“toh fadamin meye ?”

shiru shatu tayi daga bisani shatu ta kwashe komai ta fada mata…

wani irin dundu esha ta kaima shatu…ihu shatu tayi tana fadin

“ke da zafi fa”

“mtsw!! ke ynxu banda hauka ki zauna kinawa kishiyarki bauta…ita bata komai seke?”

“toh yakikeso nayi?tinda bayasona”

“dallah can ai dole ya soki ..kuma ke baki biyo ta hanyar da ze soki bane”

“kamanya?”

“kamasa xakiyi a tafin hanunki …tinda kin fita iya komai …ki kama mijinki se yadda kikayi dashi”

“Allah kawata?”

“kwarai kuwa tsaya kallon ruwa kwado ya miki ido”

dariya suka kwashe dashi harda tafawa…esha ta je gurin kunen shatu ta soma mata magana da banji me suke fada ba….

 

 

????????

[12:06PM, 1/11/2017] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

*13*

Misalin karfe 5pm shatu ta bar gidansu esha tana shiga taga motar sadeeq tasan yana nan…tabe baki tayi ta shige ciki abinta ganin ba kowa a palo yasa ta shige kitchen tasoma dora abincin dare….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button