ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa Novel

 

Can kuwa husna na zaune tana kallo a laptop kasancewar an dauke wuta sadeeq kuwa danna wayarsa yake anma hankalinsa baya gurin zancen xuci yake tayi

“ynxu kodai na tambayi husna ko ta dawo ne?..ko naje nadubata?amma banso ta rainani dan rabona da ita anjima”

tsaki yayi husna ta juyo ta kallesa

“ya sadeeq me ya faru ne?”

shiru bece mata komai ba ta maimaita har so biyu shiru dan hk ta tabasa a furgice ya juyo

“Aisha”!!!

dasauri tamiqe jinsunan da ya ambata…

“wacece aisha?”

inda inda ya somayi

“su su sunan da dar zamusawa babynmu inkin haihu”

zaro ido tayi tana kallonsa ya hadiye miyau yana gyada kai alamun eh…

“hmm ai nazata sunan watane can wlhi da nikadai nasan me zanmata wuqa zancaka wa yar banza”

Zaro ido yayi a tsorace yana kallonta

“ynxu kina nufin inna kara aure seki kasheta”

“toh kaje ka kara auren mana ka gani…”

tafada tare da daukar laptop dinsa tayi hanyar kofa ya bita da kallo harta murda handle din sekuma ta juyo tana fadin

“kuma zancen wata baby nina fadama banason haihuwa ba ynxu ba”

tana kaiwa nan ta fice daga dakin fuzar da iska yayi tare da jan tsaki….

 

Shatu kuwa batagana girki ba se to 8 fitowa tayi taajiye musu nasu ta dau nata ta shige daki….kasa cin abincin tayi tana tunanin zancen esha…

“gsky dole na bi shawarar esha watoh ni be daukeni a matarsa ba saboda ya rainamin hankalin sena kashe kwanaki bangansa ba…”

hk taira tunani kala-kala daga bisani ta miqe tayi sallahr isha karatu ta tsaya tayi da addu’a se kusan 9 saura kafin ta soma shirin kwanciya..
toilet ta nufa tayi wanka …

*sadeeq*

tsaki sadeeq yayi ya sauko daga kan gadonsa tare da rufe laptop dinsa fitowa yayi daga dakin…

dakin husna ya nufa tana barci ganin hk yasa ya fitoh..har ya kai kofar dakinsa ya tsaya dakin shatu ya kalla ya nufa dakin ahankali ya murda handle din dakin cikin sa’a kofar a bude take…

yaba shiga yaji karar ruwa atoilet alamun tana wanka dan haka ya samu guri ya zauna kan gadonta…kamshin turaren dakinta keta dukan hancinsa….

ita ko shatu tana fitowa daga toilet bata ma lura dashi ba daure taje da towel da kadan ya wuce gwiwarta…
kallonta ya tsaya yi harta karasa gaban dressing mirror cream dinta ta bude ta soma shafawa a hanunta…shiko gogon naka ya sake bakivse kallonta yake aransa yana fadin

“kanar ba shatun dana dauko daga kauye ba”

fuskarta ta soma kallo da madubi aikuwa sukai idohudu da sadeeq..a razane ta juyo ta na qoqarin yin ihu ya miqe da gudu har yana kokarin faduwa ya rufe mata baki tare da riqe gashin kanta…kiciniyar kwace kanta ta somayiya hadeta da bago ransa a bace..

“uban waya baki ikon fita dazu…har kina fita da guntun gyale ..koni baki daukeni a bakin komai bane?

 

 

????????
[2:19PM, 1/11/2017] Baby Afreen: ????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

 

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

 

*14*

Shiru shatu tayi…cixon hanunsa tayi da ya toshe mata baki dasauri ya cire hanunsa riqe matahanu yayi gam

“ka sakeni bakasan akwai zafi ba”

“baki bani amsar maganata ba”

shiru tayi kamar bazatace komai ba seta tuna da zancen esha dan hk ta runtse idonta ta bude tare da fadin

“toh meyasa hkn ze dameka?bayan baka daukeni a matsayin matarka ba…kwananka nawa rabonka da ka ganni?da ka daukoni daga gida hk kace wa babana zaka ajiyeni inma matarka bauta?kuma da ka kawoni me kace min?cewa kayi kayi alkawarin zakamin kome nakeso ko so 1 ka taba zuwa ka tmbyni me nakeso ko akwai abinda nake bukata?”

tana kaiwanan ta fashe da kuka tana fadin

“inkasan bazaka iya adalci a tsakaninmu ba kafadamata ni ma matarka ce ba toh ka sauwaqemin…kuma da kasan bakasona ai da baka yarda ka aureni ba tinda ba wanda yasaka dole…tinda ka kawoni nan gidan ko yan uwanka basu san dani ba balle****!!!!”

Bata karasa zancen ta ba ya daga mata hannu alamunya isa….shiru tayi taba kallonsa…saketa yayi ya fice daga dakin yana fita tayi dariya

“wallahi inkayi wasa agabanta zan tona ma asiri…”

 

_2days later_

Zaune husna take tana chatting taba kallo dan ita aikinta kenan acikin gidan…karar door bell taji ta kwallawa shatu kira akan tazota bude kofar….

Dija ce kawar husna…tana shigowa tabi shatu da harara…shatu ko bata bi ta kanta ba tavwuce kitchen abinta…

dasauri dija ta karasa

“Laaa dija kece ai bansankina tafe ba..shatu kawomata ruwa”

daga can shatu ta amsa da toh

“ke dallah ki tsaya ki saurareni..wacece wannan ”

“ohh shatu yar aikinace ai”

rangwashinta dija tayi akai

“husna bakida hankaline zaki ajiye budurwa irin wanan gidanki waiyar aiki”

dariya husna tayi

“ke karki damu ai inna samusu ido basa haduwa..dan ranar ma data fita tmbyt yayi wai wacece ita”

“wallahi kishiga hankalinki inbakida hankali toh wallahi zasu miki hankali”

“dallah sharesu bakomai”

Dik zanceb da suke akan kunen shatu daje tsaye da jug din ruwa..

“Allah sarki husna dama mijinki be boye miki komai ba”
shine abinda shatu tafada a ranta kafin ta isa palon dauke da jug din ta ajiye agabansu…

 

_Gidan su Esha_

“Hm kalla karki damu da husna ki riqe mijinki kawai kibishi akan yadda yakeson gaba shi zeji jiki inbe fada mataba”

“toh kina fadan hk randa ta ganmu tare fa”?
“Toh inna ruwanki?ai a dadinki ne kema kisamu naki masaukin amatsayin gidanki”

“tohni babbar damuwata shine yan uwansa fa basusan da zamana ba”

“mtsw kefa banzace ..shiyasa nace ki jashi ajikinki ahankali ki lallabashi yakaiki kisansu”

murmushi shatu tayi sukai dariya suka tafe…

 

_Night_

Kwance husna take sadeeq na zaune tabata yayi yaga tariga tayi barci dan hk ya sauko ahankali cikin sanda ya bude dakin ya fita dakin shatu ya nufa…
Ahankali ya kwankwasa… daga can tana kwance tayi tsaki

“ynxu mekuma takeso daddarenan hk?”

miqewa tayi ta bude
kofar dakin sadeeq ta gani a tsaye da sauri ta soma kokarin rufe qofar da sauri ya riqe kofar

“Dan Allah shatu ki tsaya ki saurareni karki min hk mana”

“ai basona kake ba kuma baka damu dani ba dan hk ka tafi kabani wuri”

“dan Allah kiyi hkr mana kar husna ta fitoh ta ganmu hk”

“inna ruwana?ai gwara ta gane gsky dan nagaji da wanan abun”

sake qofar tayi ta juya masa baya ahankali ya shigo dakin tare dasa key a kofar….kusa ya matso ya rungumota jikinsa..

“Shatu kiyi hkr nasan na bata miki amma insha Allah zan gyara”

Shiru tayi bata iya cewa komai ba sbd irin sa qonin da sadeeq ya soma aika mata…kiciniyar kwace kanta tayi amma ta kasa.. nikuwa inna ganin hk na fice daga dakin….

*washe gari*

_11:50am_

Zaune husna take a palo miqewa tayi ta nufi dakin shatu taba fadin

“yau meyasami shatu?bata taba kaiwa hk tana daki ba ko brk yau bata mana ba”

taba shiga dakin ta ga shatu kwance se barci takeyi kokarin tadata ta tasomayi

“ke shatu meyasameki ne?”

“bkm tin jiya daddare jikina ya faramin ciwo shiyasa”

shiru husna tayi daga bisani ta fita segata dauke da cup na ruwa da maganin ciwon jiki ta bama shatu….

shatu wuni tayi aranar kwance a daki itako husna kanar yadda ta saba komai bata kauda ba agidan hk gidan ya wuni da datti sedai ta aika wajan umma aka karbo mata abinci

 

 

????????

????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

.

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

 

*15*

*sadeeq*

shiru sadeeq yake na zuwa gida daidai nan hydar ya shigo fuskarsa dauke da fara’a

“kaga Ango *husna* miji ga *Asma’u* shirin zuwa gida ake hk?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button