ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

ASHE KISHIYA TA CE Complete Hausa Novel

“hmm gida zanje wlhi nagaji”

“ok nikuwa damau akwai abinda nakeso na tmbyk”

“kabari se gobe ynxu sauri nake”
“plx tambaya kawai zanmaka”
“ok inna jinka”

murmushi hydar yayi yana fadin

“gani nayi ka canja kwana biyu,inna tinanin akwai abinda kake boyemin”

dagowa yayi ya kallesa aransa yana fadin
“kodai na fadamasa ne?kaiii karna fada masa yasa dole se anfadawa su mama”

sunansa da hydar ya kira ne ya dawo dashi daga tinanin dayakeyi…
girgizakai ya shigayi

“bkm abokina baabinda nake boyema”
“shknan sadeeq intayi wari zamuji dan daga reaction dinkav ynxu ma mutun ze gane”

shiru sadeeq yayi daga bisani hydar ya fice daga office din..ajiyar zuciya sadeeq yayi ya tattara takardunsa guri daya ya fice….

Yana isa gida ya tararda husna tana kallo…

dasalamarsa ya shiga ta tarbesa cile da fara’a daga bisani ya zauna ta kawo masa abincin da aka kawomata…..

Yajima azaune bega shatu ba yanata leqe husna kam hankalinta nakan tv

“husna wai inna mutuniyar taki ne?”

dasauri husna ta gyara zamanta tana fadin
“yauwa ya sadeeq ka shiga ka dubata kozaka bata wasu magungunan batajin dadi dik yau baymta fitoh ba….”

shirucyayi na yan mintina ya miqe ya nufi dakin itako ta gyara kwanciyarta tacigaba da chatting
….

Yana shiga yasawa kofar dakin key…ita ko shatu a zatonta husna ce… kamar daga samata taji mutun kusa da ita ya rungumota….da sauri ta tashi ganin sadeeq yasa ta bata rai….

“Meya kawoka nan?”
“kiyi hkr nazo dubaki ne..ya jikin”

“kaini lafiyata lau fa ka kyaleni”

“toh husna tace baki fita ba wai baki da lfy…kuma baki gyara ko inna ba ka palo dik kaca kaca.”

Murmushin takaici shatu tayi
“toh na gaji ne….ni ba yar aikin ku bace…gwarama ka kyaleni se nayi niya zan gyara”

Sake baki yayi yana kallonta aransa yana fadin

“lallai shatu ta goge…yaushe ta iya magana hk”

gyara kwanciyarta tayi shiko ya kwanta gefenta yana shafa mata…kan kace me barci yayi awun gaba da su….

Cikin barci yaji anna motsi kusa dashi…ahankali ya soma bude idonsa shatu ya gani kusa dashi da sauri ya miqe kamarwani mahaukaci…yana fita palo ya ga husna kwance itama se sharbar barcinta takeyi…

ajiyarzuciya y sauke kafin ya wuce dakinsa..

*washe gari*
_saturday_

Cikin shirinta na fita husna ta fitoh daga dakinta…shatu na gyaran palo ta wuceta ta shige dalin sadeeq

“ya sadeeq na shirya zan tafi”

“toh karfe nawa zaki dawo senaxo na daukeki”

“bayan anyi sallar magrib”

murmushi yayiya bata kudi ta fice abinta tana zuwa palo ta iske shatu

“shatu xanje anguwa seda magrib zandawo ki tmby mijinakome yakeso seki dafa masa”

“toh” kawaishatu tace ta cigaba da aikinta husna kuwa ta fice…

Shatu shiga kitchen tayi ta somawanke wanke tin najiya da batayi ba takeyi tanayi tana tsaki….kanar daga sama taji mutun ya rungumota ta baya ihu tasa sbd ta tsorata…

“ke nine fa”

ganinshine yasa ta kaimasa duka

“kaji yadda katsora tani kuwa?”

dariya yayi sukaita hira harta gama wankewanken yana mata dauraya….

Atakaice dai zancemuku aranar sadeeq da shatu sunsha syyy kamar dama masoyan ne ko nace kamar dama sun saba…

har bayan isha sadeeq be dauko husna ba…ita ko can husna dataji shiru ta soma kiran sadeeq yana ganin kiranta ya tina da zeje ya daukota nan ya shiga bata hkr akan baya gida ne but ze biyo ya dauketa.

Haka rayuwa ta cigaban musu yau watan shatu 2 da zuwa gidan ..tin daga lkcin dik bayan kwana biyu a dakin shatu yake kwana seda asbah inya fita massalaci inya dawo seya wuce dakinsa…

*Wata ranar juma’ah*

 

 

????????

????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

 

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

 

*16*

*wata ranar juma’ah*

Husna ce ta fitoh daga daki da ear-pis akunenta tana jin krtu…

Zama tayi tasa wani indian film *Twist of faith* tacire ear-pies din tare dasa wayarta a caji..zama tayi tasoma kallo…

Karar door bell sukaji nan danan ta miqe taje tabude kofa dija ce ihu tayi cike da murna ta rungume dija…zama sukayi sukafara hirar yaushe gamo…

karar door bell suka kumaji..dija ce ta miqe taje ta bude…ummi ce gaishe da dija tayi ta anasa ciki ciki…hk ma husna…

guri ta samu ta zauna su husna kuwa hira suke tayi abinsu…

ummi kuwa tsaki tayi aranta tana fadin

“mtsw wlhi badan mama ba banga me ze kawoni gidanan ba”

tana kaiwa nana sukaji anfitoh daga kitchen da gudu dikka suka maida hankali agurin….shatu ce ta fitoh tana qaqarin amai dakinta tayi da gudu suka bita da kallo….
husna kuwa ko ajikinta sema tabe baki datayi ta juya gun dija….

“yauwa kawata kina bani labari”
“dallah dakata…innace wanan yarinyarce kikacemin sadeeq ya kawota a matsayin yar aiki?”

“eh itace me ya faru?”
“baki gani ba? cikine da ita fa?”

miqewa ummi tayi ta nufi dakin shatu dija ta rakata da harara

“hhhh lallai dija toh in ciki ne ma da ita daga can kauyen nasu ta kwasoshi innaga…kinga mubar maganarnan”

hknan dija ta hkr da zancen badan taso ba…

*shatu*

 

Shatu taba shiga daki amai ta dinga kwarawa kamar zata amayar da komai na cikinta….

Ummi na shiga ta tai maka ta batavruwavta kuskura bakinta ta dauraye gurin…zama sukayi saman gadon ummi na mata sannu…sanda taga tadavsamu sauki kafin ummi ta soma fadin

“sunana ummi kuma ni kanwar me gidan ce..ya akai bansanki ba?”

dasauri shatu ta dago ta kalleta
“ni me aiki ce”

“ok watanki nawa agidanan?”

“zankai wata biyu”

“Allah sarki…dama kin taba aurene yar uwa?”
“a’ah”
shatu ta fada atakaice

murmushi ummi tayi tare da fadin

“oh!!! toh wannan cikin nawaye shi kuma?”

atsorace shatu ta kalli ummi tare da rufe mata baki…

“kinga zo mu fita anan”

miqewa sukayi cikin sa’a da suka fitoh ba kowa a palon..kamar muna fukai sukaita sanda har suka fice….gidan su esha suka shige mumy ta sanar dasu cewar esha na daki…

“ahhh shatu sanunku da zuwa …baquwa kikayi ne?

“eh kanwar sadeeq ce”

“ohhh bari na kawo miki abunsha”

miqewa tayi tafita se gata dauke da juice ahanunta…

nanfa ta zauna …ummi ce ta fara fadin

“kin kawoni nan baki bani ansata ba”

shiru shatu tayi batace komai ba …esha ce ta soma fadin

“meke faruwane tsakaninku?”

“kinga alamun ciki na gani a jikinta shinefa nake tmbyrt nawaye taqi fada”
acewar ummi

dasauri esha ta kalli shatu…

“CIKI!!! shatu ciki ne dake?”

dariya esha ta farayi ..kutashi muje asibiti…
miqewa tayi ta zari gyalenta suka fuce…
ummi kuwa asibitinsu sadeeq ta musu kwatance suje batare data fadamusu ba…

suna zuwa aka gwadata daga qarshe dai result ya nuna shatu na dauke da ciki…

kuka shatu ta faryi akan se an zubar da cikin

“Wayyoh esha ku ceceni ku xubar da wannan cikin”

tana kaiwanan jiriya dibeta ta zube aqasa…da gusu ummita juya ta nufo office din sadeeq ko sallama babu ta banka qofar..ganinta yasa yamiqe

“ummi meya faru meya kawoki nan?”

“yaya kazo me me aikin gidanka ce ta suma tana da wai se an xubar”

cikintashin hankali yasoma fadin

“tana inna”
.”tana waje”

cikin sauri suka fita suna zuwa suka iske esha tana kuka rungumecda shatu…

yana zuwa gun yafara zagin nurses din daje wucewa ba shiri suka dauketa aka bata daki…
y

 

 

????????

????????????????????????
~*Ashe kishiyatace*~

_Na_

*Faty Afreen*

 

_In dedication to_
*????Abba gana????*

 

*17*

Ba shiri suka dauketa aka bata daki..iya gigicewa sadeeq ya gamayi abokinsa hydar da ummi sake baki sukayi suna kallonsa abun mamaki yadda ya gigice akan shatu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button