AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

“Shiru yayi kawai yana nazari har suka gama gaishe gaishe suka fita waje domin gaida Malam dake dakin zauren tareda manyan Almajiran shi, a nan khaleel ya Amince yes yayan shi yayi Aure inda ya dace, dattijo na gari mai mutunci, nasihar farko itace “sai kayi hakuri da duk wani shiririta ta mata zakaci ribar zama a duniya ka rike gaskiya kabi maganar mahaifiyar ka kagama lafiya, Allah ya kade fitina ya kuma baku zuri’a tagari. Wani irin girman tsohon khaleel yagani tareda tsantsar mutuncin shi, tabe bakin shi yayi tareda kada kai kawai Wanda shikadai yasan meke zuciyar shi. 

Saida sukabar gidan sukaje harabar katon gidan nasu ya dafashi “Yaya I don’t know much about Al Ada, Amma nagani Ina yaro idan Ana Aure a familyn mu idan ankai Amarya the next day y’an uwan ta nazuwa, why your bride basu zoba kuma sun san zata bukace su? “Hhh Khaleel mutunci kenan da gudun Abin duniya na gidan su Naziya bakaga komai ba ma Indai zuri’ar malam Abubakar ce,  “but Yaya naga younger sister d’in ta ko ita batazo wurin Y’ar uwar taba. “Kasan Abinda momy tayi musu jiya shima zai iya sawa su hana wani zuwa gidan nan. Yafada fuskar shi na canzawa, 

“Is OK muje ciki yau dai zaka tare dakin ka enough of the budan kan. “Hmm Allah yasa. Anyi la’asar koda suka shiga gidan, Wanda tana takaiwa da dawowa daga kitchen zuwa falo domin shirya Abincin Dare, duk Abokan hirar nata suntafi, gashi momy tace tayi tuwo miyar kubewa da kuma farfesun kan rago. 

Tana cikin Adon ta sosai haryanzu tareda baza kamshi kamar Amarya. Har zata fito cikin kitchen din taji muryar su Suna Dariya ta koma, wani irin zafi takeji a kirjin ta she thinks kamar da gangan ma Ahmed ya Aurota ya kawo cikin gidan su domin ta wulakan ta, toh yayi kuskure,  kuma  zata nuna mai Abinda Aka koyar da ita daga gidan su, zai gani tarbiyar Inna bazata taba faduwa kasa banza ba, she cried yerstaday, kuma bazata kuma zubar musu da hawaye ba, aiki kuma Alhamdulillah, bazai gagare taba domin ta horu girki ma zatayi Amfani da nata salon domin gujewa damuwa, da izinin Allah zata basu mamaki. 

Da taimakon mai Aikin take Amfani da kayan wutar, tsab tuwon shinkafa ta dora Wanda tasa mai ruwa wadatacce da zai dahu lugub, sai kan ragon data wanke tas ta zuba a wuta tareda neman kayan kamshi na gargajiya ta daka ta  watsa, tuni kamshi ya cika ko Ina. 

Tayi dai dai kuma hankalin ta kwance tana aikin ta, ya shigo ciki, turus yayi yana kallon ta cikeda mamaki domin dai bai kamata ta shiga kitchen ba, tana Amarya kuma kwana daya a gidan miji a ce tafara aiki bayan ga maids cike da gida,  wucewa yayi wajen firij saida ya bude taji motsi tareda Saurin juyowa tagan shi ya daga gorar ruwa sama yana sha, Saurin juyawa tayi tana cigaba da aikin ta, domin ta lura ya cika girman kai, and she promise zata kiyaye shi tunda baice Mata ba itama bazata taba yimai magana ba. 

Har ya Ajiye gorar ya juya Abun shi yana mamakin halin ta, ko kallo bai ishe taba Wato? Hmmm”. 

Karfe shida ta kammala tuwon tareda miyar kubewa lafiyayya da taji namomi a ciki, maid tace”Aunty Saura Abincin master karami. Kallon ta tayi “da daren ma bayacin Abincin mutane? “Yes saidai Ana dafamai ruwan tea ya hada ko coffee. Shiru tayi kafin tace ta kwaso shrimp   d’in da su crabs, da kanta ta gyara ta wanke tas tasa ta gyara Mata Y’ar citta dasu garlic tace ta daka mata su da Albasa da tarugu saida suka daku ta d’an sa ruwa ta shafe su tsab harda spices, ta saka a oven, ta saka lowest yanda bazai kone ba kafin tayi wanka, maid din ta yanka mai salat ta wanke su tumatur. 

Dakin ta ta koma ta tube tareda shiga wanka, cikin Sauri Sauri, ta dauro Alwala domin ankira magrib, bata tsaya yin dogon Azkar ba ta mike cikin Sauri ta canja zuwa wata doguwar rigar Atamfa mai flay cikin dinkin  da malam ya Mata, tayi kyau sosai, 

ta daura dankwali ta fito. Yanzu duk sunfito Suna falon momy dasu Ahmed harma da Khaleel, yana Rungume da katuwar tab yana dannawa, Suna hira kasa kasa su duka. “Toh hamshakiya abamu Abinci yunwa mukeji. Mommy ta fada. Muryar ta a kwance tace na gama momy zan shirya ne kawai a dining. “Noo ki sa maid ta shinfida mana dadduma anan bazamu hau saman ba,. 

Bakomai yasa tace hakan ba saidan kar su zauna kusa itada Ahmed. Domin sa idawan ta dazu sun tsegunta Mata kamar yana rike Mata hannu ta kasan table, Wanda bazaka taba gane munafukan sungan suba. 

Tunda ta fito Ahmed ya zuba Mata ido wani irin numfashi yakeja a ciki, domin Allah yagani shiba dutse bane, idanun shi ko kyaftawa basayi akan kirjin ta da yake gani, tareda Ayyana irin cika mai Hannun da zasuyi, har wani irin Aunawa yakeyi, he know dai dai Hannun shi ne. Kallo ta yakeyi sosai har mommy ta lura. Tareda Ayyanawa a ranta “Ahmed Indai ni Balkisu ce na haifeka bazaka taba hadamin iri da yar matsiyata ba muje zuwa. 

Tayi k’wafa, Saida ta jera komai tareda turawa khaleel nashi  cimar ta koma gefe ta zauna itama, gaba daya kamshi ya gama cikasu, ita kanta mommy miyon ta ya tsunke,  wani irin murmurshi Ahmed keyi na jin dadi, domin yana ganin yanayin Abincin yasan zaiyi dadi sosai. 

Khaleel ma kallon Abincin shi yakeyi, domin ba ataba hadamai shi da komai ba yana ganin yanda yayi wani irin kyau ga Aroma na tashi.  Momy kallon yanda yake kallon Abincin tayi tace “idan bazaka iyaci ba ayi maka wani? “No is OK, yafada yana daukar fork yafara ci. Wani irin test yaji tareda dadin da baitaba jin yayi ba, domin ta yimai hadin da kowama zai iya ci. Kallon shi Ahmed yayi “yadai brother its good? “Of cos Yaya she is a wonderful cook. Batareda ya kalli side d’in ta ba. 

Shiru kakeji a wurin kowa na zuri, saida taga kowa baiyi complain ba itama ta debi kadan tafaraci, Ahmed sai aika Mata da sakonni yakeyi ta gefen ido, ta dukar da kanta dama suna facing juna itada shi. 

Saida mommy tayi nak tace “next time idan zaki tuka tuwo ki tabbatar yayi sulbi sosai. To kawai tace domin idan dai ba tuwon masara takeso    ya koma ba,  tasan ko hasidin iza hasada yasan tuwon nan ya tuku. Maid din ce ta tayata suka kwashe komai zuwa kitchen, tayi daki domin yin sallah. Suma fita sukayi masallaci. 

Mommy ce zaune a falon tana waya da Zarah “So nakeyi Auren khaleel ayishi cikin Sauri, don haka zanturo miki kudi kifara yomin odar Kaya na gani nafada, domin bikine zamuyi shi na kece raini. 

Shigowa sukayi tayi Saurin Sallama, ta Ajiye wayar, zama sukayi tareda gaidata, tace tom dare yayi ku wuce ku kwanta Allah ya tashemu lafiya. Taci gaba da latsa wayar ta, “mommy in tafi dakina? “Ahmed yafada cikin sanyin murya mai hade da lallashi. “Saurin uban me kakeyi?  Da da bakayi Auren ba uban me ya sameka?  Kaga Ahmed ka fita idona in rufe, saboda aji dadin Asirce ka shiyasa kake kokarin shige Mata, to kabari sai nan da sati daya idan  Agumun da aka kullo Mata ya sirace ehem. Saurin kallon ta khaleel yayi tareda cewa “Haba momy haka ake Aure fisabilillahi? Ai da kin hana kawai yayi Auren wannan irin kwalelen ya isa Haba. “Toh ubana ai kai nasani zaka iya dukana ma, to dak’ar ni kaji, ku tashi ku wuce kubani wuri kafin in canja shawara.  

Khaleel ya fara mikewa fuuu ya wuce saboda takaici, Ahmed ya tsaya tareda zamewa kasa ya dafa kafarta “don Allah momy in laifi nayi miki ki yafemin don Allah, kibarni in sauke hakkin Y’ar mutane ko lekata inyi infito minti biyar ya isa don Allah. Yafada yana zubo da kwalla, tace “minti biyar idan ka wuce hakan zan shigo kuma wallahi bazakaji da kyau ba. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button