AUREN GADO Page 1 to 10

Saurin wucewa dakin yayi yana karewa gadon nashi kallo yaga yanda zanin ya zame gaba daya, saboda zaman da sukayi a gefen shi, kuma bakaramin jujjuyawa Ahmed yarikayi ba saboda mugun feelings din da yakeji, shigowa yayi yace “Sorry Bari in gyara mana gadon, shiru yayi har yagama ya wuce bathroom, yana kallon yayan nashi bai ce tak ba, ganin yayo wanka yafito yaganshi a tsayen yace “yadai ko wankan kaima zakayi? “No ba munyi wanka ba kaima naga weather din is OK why you bath again? “Hhhh oh come on brother ko bakaga ma tata ta shigo ba kaima kasan dole inyi wanka ai. “in ten minutes? Ya fada batareda ya san maganar ta fito ba, “of cos is enough for me. Ya bashi Amsa tareda hayewa gadon ya kwanta cikeda farin ciki, kafin ya tuno da tea ya diro ya tsiyaya ya farasha yana lumshe idanun shi.
Komawa yayi kan kujera ya zauna yana danna waya har Ahmed yagama ya haye gadon yana cewa “ga coffee idan zakasha narage maka. “Uhm. Kawai ya Amsa, ganin Sam bazai iya bacci ba ya mike ya shiga bathroom wanka yayi tareda Alwala yadawo dakin yatada sallah.
Gefen Naziya kuwa, tayi bacci cikin kwanciyar hankali tareda farin ciki, tasan Allah yabata miji mai halin kwarai kuma da yardar Allah zata tayashi yiwa mahaifiyar shi biyayya.
Sabo da tashi da wuri Karfe hudu ta tashi, saida ta yi sallar nafila kafin biyar tayi farillah, ta zauna Azkar zuwa Karfe shida ta fito cikin karamin hijabi zuwa kitchen, ta shirya musu breakfast mai lafiya. Kafin bakwai da rabi ta kammala ta gyara ko Ina takoma tayi wanka, shiryawa tayi cikin Riga da zani, tafito tsab, tana kamshi.
Kiran mommy yasa ta fito da gudu tana amsawa ta ganta hakimce, dukawa tayi ta gaida ita, “ke bakisan kiyi pleasing uwar miji ba ta hanyar shiga dakina ki gyaramin da kuma dakin khaleel, toh daga yau gyaran dakunan mu na Hannun ki idan kin tashi. “Toh mommy. “Oya a shirya mana breakfast anan yau ma.
Fitowa Ahmed yayi idanun shi kur akanta yana aika Mata da sako tareda murmurshi mai cikeda sirrika. Itama tayimai tareda dukar da kanta tafara aikin ta,
“Ina Ibrahim din? Bacci yakeyi jiya baiyi bacci da wuri ba yace sai ya tashi. “Aa nifa banason wasa da ciki, ke Naziya yi Sauri ki kaiwa dana Abinci a daki karya kwanta da yunwa. “Mommy da kin Bari ya tashi. “Wuce maza ki kaimai. tafada, tana cewa “jeki zanyi serving din mu maza ki tabbatar yaci kafin ya kwanta. Jim tayi kamar bazataje ba tace “me kike jira? Cikin tsawa, da Sauri ta dakko tray ta shirya mai komai nashi ta wuce jiki a sanyaye “Allah yagani itadai jinin ta bai hadu dana gayen nan ba, baiyi mata ba Sam, da Sallama ta shiga dakin, yana kwance a tree seater a kudun dune, fuskar shi ce kawai a bude. Idanun shi biyu yana kallon sama, Sallamar ta yasa ya d’an juyo cikeda yanga, ta tsaya daga nesa muryar ta na rawa ga shi inji Mommy, ta dora akan karamin table zata juya, “Serve me. Yafada cikin isa, tayi Saurin juyowa “wannan mugun d’an rainin wayau ne, batason musu don haka cikin Sauri ta juyo batareda ta kalle shiba ta hada mai komai tafita cikin Sauri.
“Hmmm kawai yace yafara cin Abincin shi. Yana lumshe idanun shi.
Komawa tayi falon tace tabashi. Kafin ta zauna tafara nata Karin.
Toh haka dai kwanaki keta tafiya yau Naziya ta kai wata daya cur Agidan komai na gidan tundaga gyaran dakunan su zuwa kitchen ya koma Hannun ta, complain din momy ya riga ya shiga jikinta, Ahmed kuwa yanzu ganin shima gagarar ta yakeyi domin dokar mommy tayi nisa yanzu, tun yana rokonta harya hakura ya zura ido, sai rama yakeyi a tsaye saboda damuwa baya ko son haduwa da Naziya saidai suyi chart da wayar da ya siya mata katuwa wadda ta boyeta a dakin ta bata Bari mommy tagani ba, by now ta fuskanci muguwar kiyayyar da mommy ke mata. Idan ya fita aiki kuwa yana kiranta kullum bata hakuri yakeyi,. Tana kwantar mai da hankali domin ta saki jiki dashi sosai, yanzu har marmarin ganin shi takeyi akusa da ita she is missing his touch, rabon da ya rungume ta tun a dakin Khaleel, kullum Aunty Raliya shawarwari take bata wainda Sam basuda Amfani a wurin ta tunda an hanata sakewa da mijin ta. Iyakar ta dashi sai ban hakuri tareda Sanya mata Albarka a kullum “Naziya ke Y’ar Aljannah ce, watara na zakiyi farin ciki, ki Kara hakuri komai mai wucewa ne.
Bikin khaleel Ansa rana wata daya mommy sai shiri akeyi An shirya event Kala Kala, khaleel ko a jikin shi domin Amaryar ma ko wayar ta baya dauka, Wanda ta watsa shi a kwandon shara tunda dai uwar miji na sonta ai zata wataya kuma dole ya sota.
Zaune suke a office din yayan nashi ya kalle shi “brother sai ramewa kakeyi are you Alright? “Am not khaleel, yama zan zama cikin kwanciyar hankali bayan kana ganin me yake faruwa? “Am sorry Yaya bansan yanda zantaimake kaba. “Is OK yanzu kaga maganar shigo da kaya zai zo dai dai da lokacin Auran ka naso kaje da kanka, ko zaka Bari kaje honey moon gaba daya? Yafada yana d’an murmurshin karfin hali. “Noo wane irin honey moon? Zantafi kawai idan nadawo ai ba guduwa zatayi ba. OK kafadawa mommy ba ruwana.
Karfe biyu suka shigo gidan, an baje akwatunan sunkai saiti bakwai an narka dukiya kamar za asiyo mutum, suna shigowa tace “Yauwa khaleel zoku gani komai yaji? Tafada cikeda farin ciki, ya zauna yana kallon kayan tareda mamaki ” mommy kayan Waye duka? “Ga rainin wayau, na Matar ka ne mana. “Duka? Yes gaskiya aa a raba biyu abawa Naziya rabi. “Why zan bata rabi? Saboda am sure ba ayi mata irin haka ba. Yafada cikin zafin rai, “bazan bayar ba domin batasan darajar suba, fitar kunya nakeson inyi dasu gidan minister guda dole akai Abinda baza a raina muba, Kuma ka nemo motar da za a hada mai tsada ta mata. Ahmed ne ya katse maganar “Zamuyi placing oder momy na kayan mu sai kasa a turo motar da kakeso kafin katafi.
Saurin kallon shi tayi tareda cewa “Ina zaije? “China zai shigo mana da wasu kaya. “Yaushe? Nan da sati uku. “Saboda mugunta? yaro zaiyi Aure ya Amarce shine zaka turashi wajen kwaso kaya? “Mommy, ni nace zanje ba Yaya ya sani ba, I want to go. “You are not going don haka ya shirya shi yaje, tunda nashi Auren baida Amfani, idan kanaso kaji dadi Ahmed sai ka Auro zabin zuciya ta Amma Indai Inada rai bazan hada iri da yar masu zama akan buzuba a mallake min da’.
Kallon momyn yakeyi wani iri, sometimes sai yaji kamar ba ita ta haifeshi ba, domin duk uwa tana son farin cikin d’an ta. Tashi yayi kawai yayi dakin shi dai dai tana fitowa ya ganta Amma saboda ciwon da kirjin shi ke mai yakasa ko tsayawa yayi mata magana. Kallon shi tayi sosai, taga ramar shi a yau tareda yanda yayi sanyi sosai, duk da ba mai hayaniya bane,
Jikin ta yayi sanyi, Allah yagani yanzu ba Abinda takeso irin su zauna suyi hira ido da ido ita dashi domin kullum soyayyar shi karuwa takeyi a zuciyar ta.
Kallon momyn khaleel yayi “mommy me kike nufi da d’an uwana? “Kamar ya? “Momy ki barshi ya samu natsuwa mommy don’t you see how sad he is? Bakya ganin yanda yake ramewa? Mommy Yayana na cikin damuwa sosai, I beg of you kibarshi ya huta haka. Wani irin kallon zanci ubanka tayi mai kafin ta mike cikin fada tayi dakin Khaleel din, “zanje inji dalilin da zai rika hadani da kai kana titsiyeni kamar ubana.