AUREN GADO Page 1 to 10

Binta yayi yana yi mata magana tayi banza tayi dashi. Zaune yake yana dafe kirjin shi, ta shigo “toh kanin uwata Wato da kun hadu saika rika zugo d’an uwan ka yana titsiyeni kamar ubana ko, toh ka fita I dona kuma ka saurare ni, nayiwa Kawata magana Hajiya sa’ade maganar Y’ar ta Salifa idan ka shirya zama da Matar son taka toh ka yarda ka Auri zabin rai na lokacin zanbaka damar da zaka zauna da Matar son taka.
Kallon mahaifiyar tashi yakeyi tareda yin tagumi saida ta ci gaba da fada yace “am sorry momy bazan iya musu dakeba kiyi duk Abinda ya dace insha Allahu zanyi miki biyayya. “What Yaya? Me kake fada? This is too much gaskiya Haba momy p…… “Quit Khaleel Yafada cikin dakamai tsawa, tareda nuna shi da yatsa “not a word again, why are you challenging our mother? Kar in kuma jin kalma daya daga bakin ka. Fita tayi kawai tana amsa wayar fauzy tana dariya “Y’ar Albarka wane irin product kike Amfani dashi na kayan kwalliya?
Wani irin bakin ciki khaleel yaji tareda kallon Ahmed din ya wuce domin shima ya batamai rai. kwanciyar shi yayi kawai yana kallon sama. Dawowa yayi ya tsaya akan shi “Yaya what ever is happening is not right. why zaka zuba ido kana over looking komai, how could you accept the second marriage? Ka manta me kafadamin, kaman ta kafadamin bazaka taba hada Naziya da wata mace ba? She didn’t deserve All this life Yaya, she deserve to be happy. “Hmmm ya kakeso inyi Khaleel? Inyi disobeying mommy oh what? “She is my mother Ina so mu rabu lafiya, and Naziya yes I love her more than my life, yazanyi dole inbi mommy in inaso inga dakyau, ba wata mace da zata samu matsuguni a zuciya ta, ita kadai nakeso ita kadaice zabina, if Auren da mommy zatayi min shine zaisa tabarni da matata in zauna lafiya then be it, am ready to obey what ever she said that’s final. Yafada yana mikewa cikin fushi yayi bathroom.
“She didn’t deserve it. Yafada yana naushin iska, he feels as kamar shi yafi kowa jin ciwon Abinda akeyi mata, ita kanta nuna wa take ba Abinda ke damun ta, tun ranar da tazo gidan nan yaganta tana kuka bai kuma ganin ta cikin bacin rai ba, sai kace bata da zuciya?
Fita yayi fuu dai dai tana shiga kitchen, cikin zafin zuciya ya bi bayan ta, kafin ta ankara jin hucin mutum kawai tayi yana fesa mata numfashi cikin zafi a bayan wuyan ta, kurawa kwantacciyar Sumar dake wurin idon ta yayi, idanun shi sun kada, he don’t really know why zuciyar shi ke tafasa, he is trying to control his Anger da baisan dalilin taba.
“Auzubillahi. Tafada tana ja baya da Sauri domin tsayuwar da yayi a bayan ta ya kaucewa tsarin Addini, kuma shi ba muharramin ta bane, wani irin kallon bakada tarbiya take watsa mai tareda nisan ta kanta daga kusa dashi, he can clearly read her reactions, don haka tuni zuciyar shi ta Kara hawa, “what? Why are you looking at me like that? Yafada yana describing da hannun shi, A haka zaki karasa zaman Rayuwar Auren naki you don’t care about your husband, kawai kiyi bacci ki tashi ki dafa Abinci, shine damuwar ki, you are pretending as if you don’t care about All this wealth, you are such a jocks, kin zauna kin baje ba Abinda ya dameki sai kici kiyi bacci you forget All your responsibilities, look if anything happen to my brother because of you, I won’t forgive you.
Tunda ya fara magana kallon shi takeyi, kuma irin kallon you won’t get away with this, yanayin shiru ta gyara tsayuwar ta tareda daga gira daya, and she look very cute, “oh really? So nice bansan responsibility dina ba? Saboda nayi shiru Ina kallon komai, waya fada maka Ina farin ciki da duk Abinda yake faruwa da zaman Aure na? Nice nakeda complain ba yayan kaba because I know my right, and da kake cewa duk Abinda ya samu yayan ka bazaka yafemin ba, ni kuma in wani Abu ya same ni fa? Kana tunanin iyaye na zasu yafe muku? “And don’t forget he is my husband, kuma munyi Aure saboda Ina son shi ba kiyayya ba, this house Hmm who told you am happy in this house? hakuri nakeyi bisa ga irin tarbiyar da aka dorani akai, iyaye nagari suka daga rayuwata, yawo da shigar da bata dace ba duk iyayen mu sun hane mu, shiga hurumin da bana muba duk iyayen mu sun hane mu, Saboda sudin iyaye ne nagari……… “Nice ba uwar kwarai ba kenan? Mommy tafada cikin tsananin bala’i
Jikin Naziya na rawa tayi Saurin kame bakin ta, tareda dana sanin biyewa zuciyar ta ta tsaya kula khaleel bayan hakan ma bai dace ba, yanzu tun ba aje ko inaba she is regretting……. ????
*Matar Soja*
????????AUREN GADO????????
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun bankina nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, 500 ne kacal nagode,
???? page
1⃣3⃣&1⃣4⃣
………….. “Mommy, magana mukeyi please don’t interfere please. “Karya ne wallahi duk naji Abinda ke faruwa tundaga farko, Wato munafuka sai ki rika nuna halin kirki Wato mugun halin ki na can cikin zuciyar ki ko, “toh kin fada son ranki yanzu ki saurare ni mai miji, yau nawa ga wata? Aure zanyi wa mijin naki rana daya da Khaleel, zan Auro mai Matar kwarai Matar nunawa sa’a ba Y’ar gidan masu kwana kan buzu ba, munafuka kinayi kamar tagari Ashe bakin hali na nan a gefen zani, kin tsaya kina musayar miyau da kanin mijin ki sai kace sa’an ki. Dafe kanshi kawai yayi, you mess up things kawai, Naziya durkushewa tayi for the second time ta saki kuka mai ciwo “kishiya Aure? Bayan ita ko dama ba abata ba ta mori Auren shine ake wani zancen za ayi mata kishiya?.
Tashi tayi da gudu tawuce zuwa daki tabar aikin domin wani irin zafi zuciyar ta keyi mata.
Kukan ta ya taba mishi zuciya fiyeda tunanin mutum wani irin sarawa kanshi keyi kamar zai tsage biyu.
“Kai kuma ka tsaya yarinya karama na zuba maka rashin kunya kana kallon ta, bazaka watsa mata Mari ba, kauce ni in wuce ka batamin rai. Tafada tana fita, sintiri yakeyi a kitchen din yarasa Ina zai sa kanshi, kallon da ta watsa mai ne yafi komai daga mai hankali, she really hate him. Fita yayi da sauri ya Kira maid yace ta karasa aikin girkin yayi dakin shi,
“Ahmed yasamu akan dadduma yana lazimi, yace “Yaya please go to your wife she is crying please. Saurin mikewa yayi me yake faruwa? Wa ya sata kuka? “Is you Yaya kaine sanadi, mommy Tafada mata zakayi Aure please go to her. Yafada zuciyar shi na wani irin rawa, komawa Ahmed yayi gefen gadon ya zauna dabas, “I can’t go khaleel. “Why? Yaya Matar kace, she needs your comfort please. “Mommy tayi min iyaka da ita. “Iyaka? What iyaka? “Yaya hakkin yarinyar nan bazai barka ba karka manta ba mommy ce kawai keda hakki akanka ba, why ka Auro ta idan bazaka iya ba?
Kukan da yaga Ahmed din nayi yasa yayi Saurin zama gefen shi ya rungume shi yana Ajiyar zuciya, “am sorry Yaya please nasan komai, amma kaine kabada kofar komai dake faruwa. Bai iya cewa komai ba sai shesheka yakeyi “am sorry khaleel banda karfin zuciya irin taka am weak.
Saida ya fitar da kwallar tausayin d’an uwan nashi.
Naziya kuwa tana shiga ta kulle kofar ta fada bathroom ta shako kukan ta son ranta, Karar wayar ta tasa ta fita ta dauka ganin number Ahmed dince yasa ta datse kiran kit tareda kiran Aunty Raliya.